← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 96

Sashe 65

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murje ido ya yi tunda in ba a nan ba babu wanda zai tambaya kuma
"A gabana ta fara wayar shi yasa. Da gaske ya mari matarsa?"

"Ƙwarai kuwa."

"Kaga abin da nake faÉ—a ai. Namiji mai irin sana'arsa fa ji yake kamar shi ma mace ne. Shi yasa yake daidaita tunaninsa da nata. Cikakken namiji ba zai fara kai hannu daga aure ko wata ba ayi ba."

Yaya Malam dai dariya kawai ya yi. Ya shaida duk wata rigima da yake yi bata yi tasirin hana shi son É—ansa ba. Abin da yaji ya faÉ—a masa. Ya yi godiya su ka yi sallama.

Washegari ya san da zancen kai lefe da maza za su yi. An kira shi ya gani bayan an kammala komai. Harda akwatuna huÉ—un da Amma ta taho dasu waÉ—anda kayan ciki su ka amsa sunan kayan Æ´ar gata. Tunda ba dashi za a yi ba babu wanda ya sa masa ido da ya yi sammakon fita. Ko matansa bai faÉ—a musu inda za shi ba. Ya dai yi musu sallama ya fice. Yana zama a mota ya ce da direbansa Bauchi za su je.

"Bauchi Alhaji?"

"Ba ka san hanya bane?"

Da sauri ya hau bada haƙuri "na sani. Allah Ya kai mu lafiya."

"Amin"

Zuciyarsa a baka take da ɓacin rai. Bai runtsa ba jiya tunda ya yi waya da Yaya Malam. Arziƙin rabon Ahmad dake tsakaninsa da Mami yasa ba zai haɗata da hukuma ba. Amma tabbas sai tayi nadamar kai ɗansa gaban ƴan iskan bokayenta. Bai san bata da masaniyar abin da Salwa tayi ba.

***

Tun dare Ƴar Ficika da yaransa su ke aikin kayan kwalamar da za a tarbi masu kawo lefe dasu. Shi ya ce da Abba lallai ko ruwa kada ya siya. Za su kawo komai.

"Abin zai yi yawa. Don Allah kada ka wahalar da kan ka. Kada ka manta girma fa ya cimmana."

Yar Ficika ya karya kai yana riƙe da ƙasan jallabiyarsa.

"Haba Simagade, ina aikin yake a nan? Ai idan daɗin miya bai karya ludayi ba, wahala ba za ta karya guga ba. Ka ganni nan..." ya bubbuga ƙafa a ƙasa "digirgir nake a tsaye. Abin da zan yi in daɗaɗa maka ba zai taɓa zame min wahala ba."

Abba ya yi masa godiya. Ƴar Ficika ya koma cikin kitchen ɗinsu inda ake ta yanka naman kaza. Guda cikin yaran ya samu yana gyara wutar gashi.

"Tasalluwa me za ayi da wannan uban garwashi?"

"Ba gasa naman za ayi ba?"

Duka Ƴar Ficika ya kai masa a ƙeya "sai shegen rawar kai yawa akwalan keke. Abin da ya kamata ba shi kake yi ba. A zafin nan za a gasa nama tun yanzu a ajiye? Ba sai ya buga ba?"

Tasalluwa ya ɓata rai "daga abin arziƙi?"

"Idan aka basu naman yana hamami ai raini za ka jawowa É—iyar tamu. Ko baka san É—an Alh. Hayatu Maitakalmi take aure ba?"

Tasalluwa ya tafa hannuwa "eyyee, ashe abin babba ne, wai an kashe kwarkwata da taɓarya. Aikin na bajinta zamu yi."

Wani dake kusa yana jin hirar tasu ya ce "ai ke dai Allah Ya kawo kuÉ—i talauci yaji kunya. Nan da lokacin da za ta haihu kaji hamsin za mu babbake ba ashirin ba."

"Ahayyeeee"

Su ka dinga tafawa ana tsara irin girkin da za ayi idan Hamdi ta haihu. A cewarsu aikin yau ba ayi yadda ya kamata ba saboda tsadar rayuwar da ake fama. A haka kuma ba ƙaramin ƙaƙari Ƴar Ficika ya yi ba. Kaji ashirin za su yiwa gashin tukuba, meatpie, donut da cake duka guda ɗari ɗari yaran da su ka ƙware a nan fannin su ke yi. Sai abincin gargajiya. Tuwon shinkafa da miyar gyaɗa da kabewa wadda taji naman rago da alayyahu, waina, funkaso da alkubus kuma da farfesun kai da ƙafar rago. Sai lemon ginger da zoɓo da su ka ƙware wajen yi ana zubawa a sababbin robobi masu tambarin sunan gidan abincin nasu. Shi dai ya haƙura ya san ya makara, da wuya ya haifa. To amma fa wanda Simagade ya haifo musu sai inda ƙarfi ya ƙare.
RAYUWA DA GIƁI 26

Batul Mamman💖

***

Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya ɗauki Hamdi kafin ƴan kawo lefe su iso take yi. Zee da ƙanwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ƴan rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane taƙamaimai me yake damunsa. Halin da take ciki kenan yanzu. Tana son Taj, sannan kuma tana gudun kasancewa inuwa guda da shi.

A daren jiya ne da tana addu'a ta fara mamakin wannan sabon al'amari da ya tunkaro su. Alaƙarta da Taj ba irin wadda ake shan wahalar farata bace. Lokaci guda su ka yi clicking kamar hagu da daman mayen ƙarfe. Irin wannan rashin sakewar kafin a saba duk basu fuskanta ba. Lokaci guda su ka karbi juna a sabon matsayin da Allah Ya ajiyesu.

"HAMDIYYA!"

Firgigit ta dawo hayyacinta da jin kiran Yaya da ƙarfi.

"Tunanin me kike yi haka?"

"Babu komai" ta miƙe tsaye tana neman mayafinta.

"Me ki ke nema?" Yaya ta tambayeta.

"Mayafina."

"Wanda ki ka yafa kuma fa"

Kallon jikinta tayi ta ce "au..."

"Zauna Hamdi. Magana za mu yi."

Bata kawo komai ba tunda a tunaninta ta ɓoye yanayinta sosai ta zauna. Yaya ta tsareta da tambayar me yake damunta kwana biyu. Ta fara rantse rantse Yaya ta ce bata san zance ba.

"Idan ba wata uwar gareki a waje wadda ta dace da sanin damuwarki ba ina son sanin me ya sanyaki kwana kina sallah da kuka."

Gaban Hamdi faÉ—uwa ya yi. Ba za ta iya faÉ—awa kowa Taj ya mareta ba. Haka kawai take ganin kamar za su yi rabuwa ta har abada idan aka sani.

"Yaya babu komai."

"Kina ganin saboda lalurata da yanayin Abbanku bamu isa mu share miki hawaye idan kina da damuwa ba ko?"

Ɓacin ran uwa abin gudu. Nan da nan hankalinta ya tashi ta soma bata haƙuri.
"Ki daina faÉ—in haka. Wa nake da shi bayan ku?"

Da wata irin murya mai ban tausayi Yaya ta ce "Ba yau ki ka fara ba. Tun ƙuruciyarki na san kin tashi da ganin kamar bamu cika iyaye ba."

Kuka sosai Hamdi tayi. Wannan banzan tunanin tun yaushe ta ajiye shi. Ummi ta ankarar da ita girman mahaifinta a lokacin da take ganiyar gudun a alaƙantasu. Yaya ce dama tun farko bata taɓa rainawa ba. Tana son abarta a yadda take. Wannan furucin da tayi ne dai ya sake karyar mata da zuciya tayi ta kuka tana bata haƙuri.

Bayan wani ɗan lokaci da Yayan ta ce ta haƙura shi ne ta faɗa mata rabin gaskiyar zancen. Akwai mai son Taj, ta dawo da wayar da su ka taɓa yi ta ce ai matar har kiranta tayi ta tsorata ta.

"Wai idan na yarda na tare sai ta illata rayuwata."

Dariya taga Yaya tayi kafin kuma ta ce,

"Shi ne kike kuka? Kodayake Allah ki ke gayawa. Ya isar miki akan komai. Duk da haka cewa Yayi ka tashi In taimakeka. Kada ki yarda wata mace ta zama silar hawayenki a gidan miji."

"Ko da yafi sonta?" Hamdi ta tambayeta tana kuka.

Da yake Yaya bata saba ganin ƴar tata ta nuna rauni irin haka ba sai take ganin son da take yiwa Taj ne kawai bata son abin da zai shiga tsakaninsu. Kalaman da za su kwantar mata da hankali ta zaɓo. A cikin ranta kuma tana ƙudurta yi mata addu'a da sauran ƴan uwanta akan kada Allah Ya haɗa mazajensu da matan banza.

"Yafi son nata ya aureki? Ko kin manta ba tayinki aka yi masa ba?"

"Haka ne."

"Ki cigaba da addu'a sannan ki dage ki ƙwaci kanki a gidan aure. Mu bamu san boka da malami ba. Kuma bamu san makirci da sharri ba. Indai kin tsaya a tarbiyar musulunci ta zaman aure da kuma riƙo da dabarun zaman duniya za ki ga baki da yawan damuwa."

Kai tsaye ta ce "Yaya kin koya mana dabarun zaman duniyar ne?"

Yaya tayi dariya "Hamdi kenan. Da gaske ki ke son kare martabar aurenki. Hakan ya yi kyau. Lusarar mace bata taba burge miji dama." Ta gyara zama "su dabarun zaman duniya yau ce take koya maka. Sai kuma amfani da dama idan ta zo da kuma zurfafa tunani da hangen nesa. Sauri ko gaggawa a komai ɓata lamura suke. Saboda haka don wata ta kira ki tana surutu kada ki yarda ya zama dalilin da za ki ce kin gama aure ko kin bar mata miji. Ki ƙoƙarta. Sai idan kin yi naki kin ga mijin ƙwallon mangwaro ne sannan za ki jefar dashi ki huta."

Ji tayi kamar an sauke mata dutse daga zuciyarta. Ta faɗa jikin Yaya tana dariya mai haɗe da jin kunya. Yaya ta rungume abarta tana shi mata albarka. Da Zee ta leƙo domin ta faɗa musu zuwan direban da zai ka su tayi mamakin yadda ta gansu.

"Wallahi nima sai anyi dani."

Ta daka tsalle dama idan shirmenta ya motsa sai addu'a, ta faɗa kansu. Sai washhh ɗin Yaya kawai kake ji tana cewa su tashi za su ɓalla ƙashin da bashi da ƙwari.

***

Cikin ginin wani kamfanin robobi wanda a halin yanzu shi ne dukiyar taƙamar Alh. Mukhtar da iyalinsa direban Alhaji ya shiga. Akwai mota a gabansu ta wasu manyan ƴan kasuwa guda biyu wanda su ma direba ne ya kawo su. Su ne su ka yi musu jagora har wurin.

Da su ka firfito da girmamawa su ka zo wajen motar Alh. Hayatu su ka sske tarbarsa tunda dama a hanya su ka haÉ—u da farko.

"Alhaji ni fa ka sanya ni a duhu da ka ce mu faÉ—awa Alh. Mukhtar lallai ya tafi kamfani yau duk da asabar ce kana son ganinsa. Allah Yasa lafiya dai." Cewar guda daga cikinsu.

Fuskar Alh. Hayatu babu fara'a ko É—igo ya ce masa "lafiyar kenan. Yana da kyau mutum ya dinga zaga dukiyarsa ne saboda halin rayuwa."
Chapter 65 · 0% Book details