← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 96

Sashe 25

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi kuwa."

"Ka daina damuwa. Ba a yiwa namiji auren dole fa" Kamal É—in ya yi murmushi.

"Happiness bana son takura ne. Sannan bana son ungratefulness. Ƙinta tamkar ban godewa kyautatawarsu bane."

"Don ka taimaki mutum kuma bai kamata ka ɗora masa nauyin da zai takura shi ba. Ni shawarata kawai tunda Hajjon ta ɗan fahimta ka cigaba da jan ƙafa. Kuna fara magana a fito mata as unromantic as possible. Kada ka sanya mata false hope. In anyi sa'a ta gudu da kanta."

Sai a lokacin Taj yaji sanyi a ransa. Ya miƙawa Kamal hannu.

"Happiness nawa ni kaÉ—ai. Yadda ka ce hakan za ayi. Thanks bro"

***

Hamdi bata taɓa shiga motar haya a Abuja ba ita kaɗai. Ko yawon da su ka dinga fita da Anti Labiba farkon zuwanta, yawanci mijin Antin ke kai su. Ko kuma Anti Labiban ta kira bold ko uber. Hankalinta kwance yake tunda akwai idon garin. Yau da take ita kaɗai ne dai duniyar tayi mata zafi.

Na farko dai direban motar a ƙoyasinta zai yi biyunta. Ga jiki da bai ɓuya ba. Sannan babu tantama ba bahaushe bane. Inda zasu je kuma bata sani ba. Anti Labiba dai ta ce mata zasu bi ta titin hanyar Central Mosque ɗin da su ka taɓa zuwa. To gashi an fi minti shabiyar a titi amma babu masallaci babu alamunsa. Banda hawa da sauka akan wasu gadoji da ko wuƙa aka ɗora mata ba za ta gane ko ɗaya ba, babu abin da yake yi. Ga gudu da ta lura yana yi kamar walƙiya.

Hanjin cikinta su ka sami wuri su ka cure wuri guda. Zuciyarta tana harbawa kamar za ta fito waje. Sai kuma bisa rashin sa'a aka kira shi da wata wayar ba wadda take gabansa tana nuna hanya ba. Ya sanya earpiece a kunne É—aya yana magana da yaren da bata ji. 'Passenger' da kuma 'get ready, I will be there soon' kaÉ—ai ta iya tantancewa.

Habawa, duk wani labari da ta taɓa ji game da satar mutane sai da ya dawo mata. Jikinta ya dinga rawa. A hankali ta kama shessheƙar kuka don bata so yaji. Ta fiddo wayar da Anti Labiba ta bata da za ta taho ta tura mata message.

(Anti zai sayar dani a hanya ban san inda muke ba amma titin yayi kama da bayan gari)

Ta rubuta a jere ko waƙafi babu tsakanin rubutun. Gashi tana zama a motar ya danna lock ta gaba. Gilasai duk an ɗagesu an sakar mata AC.

Anti Labiba na kashingiɗe a falo message ɗin ya shigo. Ta tashi zaune a gigice. Ta dinga kiran Hamdi wayar taƙi shiga. Cikin matsanancin tsoro ta kira nambar Anisa da su ka yi magana ɗazu.

*

Abinci ta shiryo a tray ta fito dashi wayar ta shigo. Bata É—auka ba sai da ta ajiye tray É—in a gabansu Taj. Ta É—auki wayar daga kan tray É—in.

"Dama yanzu nake shirin nemanki. Naga bata iso ba har yanzu."

Anti Labiba ta É—ora hannu a ka "bata zo ba? Sun kusa minti arba'in da biyar da barin gida fa."

Anisa da bata da saurin fushi tayi musu uzuri da cewa "maybe hold up ne. Kin san yamma tayi. An fara dawowa daga office."

"Uhmm uhmm dai. Bari na turo miki message É—in da tayi min yanzu. Zan nemi maigidan na sanar dashi."

Zama Anisa tayi don ta gama kawo komai falon. Ta sha kwalliya sosai tayi kyau. Ta buÉ—e abincin tana tambayar Taj me za ta zuba masa wayar Anti Labiba ta sake shigowa. Tambayarta tayi taga text É—in ta ce yanzu za ta duba. Ai tana karantawa ta kama salati.

"Me ya faru?" Taj ya zare wayar a hannunta don jikinta rawa yake yi.

"Anti! Anti!!" Shi ne sunan da take kira hankali a tashe.

Antin ta fito da mayafi a hannu don kiran ya tsorata ta. Taj da Kamal su ma duka babu mai nutsuwa.

"Wai yarinyar da na bawa aikin snacks ce ta taho tun É—azu amma kinga bata ido ba."

Anti ta ja tsaki "haba Anisa. Shi ne ki ke min wannan kiran mai firgitarwa?"

Wayarta ta soma lalube Taj ya miƙa mata bayan ya gama karantawa. Ta damƙawa Antin. Itama tana karantawa su ka kira Anti Labiba. Kuka ma take a lokacin.

"Wayarta ko ta shiga bata É—auka. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

"Ki ce ta turo numbar mutumin tunda dole akwai numbarsa akan app É—in da zai yi magana da passenger."

Da gaggawa Anisa ta faɗi saƙon. Anti Labiba ta tura musu.

***

Direba na tafiya ya fara jin sautin kuka na tashi kaɗan kaɗan. Gabansa ya yanke ya faɗi da ya ɗan leƙa ta madubi ya tabbata yarinyar da ya ɗauko ce take yi.

Dama ana cewa fa wasu fasinjojin ba da alkhairi suke zuwa ba. Wasu ma sharri su ke ƙullawa mutane. Kaddai irinsu ya ɗauko yau?

"Madam, what is wrong?" Ya kwantar da murya ya tambayeta.

Ita kuma jin ya kirata sai kawai ta fashe da kuka sosai.
"Please take me home."

"We are almost at your destination. Did something happen?"

Hamdi ta kalli titin. Babu sawun mutane sosai. Ita da zai sayar ko ya cirewa sassan jiki zai yiwa daÉ—in baki?

"Zan sauka...drop me here."

Direba ya kalli wajen sai yaji fargaba ta dirar masa. Bisa shawarar map ɗin bolt da yake bi an nuna akwai hazard akan hanyar da tafi saurin kai mutum inda zai je. Hazard ɗin kuwa yana iya zama hatsari, lalacewar mota ko goslow ɗin da ya hargitsa titi. Sai map ɗin ta zaɓar masa wata hanyar daban. Shi kuma baya son bi saboda nisanta sosai. Kuskurensa shi ne da ya ɗauke hanya bai yi mata bayani ba. Kukan da take a firgice ne ya tuna masa da hakan. Ya soma bata haƙuri da rarrashi. Amma fir Hamdi taƙi yin shiru. Ita dole ya sauketa. Shi kuma yana tsoron buɗe motar bai san me zai faru ba. Mutane ma yanzu basu fiye bincike ba. Wanda yafi rauni yana faɗin abu sai kawai a hau a zauna.

Suna haka Anisa ta kira shi. Tambayarsa tayi game da fasinjar da ya É—auko. Cike da farinciki kuwa ya faÉ—a mata abin da yake faruwa.

"Let me talk to her."

Ai ko wayar ƙin yarda tayi ta karɓa. Karshe sai speaker ya saka yadda za ta ji.

"Ki kwantar da hankalinki. Ya ce hanya ce bata da kyau shi yasa ya canja wata. Amma yanzu zai kawoki."

"Ni dai ki zo ki karɓi kayanki don Allah. Daga nan in ya kuma tada mota Allah ihu zan masa. Tun ɗazu fa muke yawo..." ta fashe da wani kukan.

Anisa ta rasa irin bayanin da za ta yi mata. Sai kawai ta bawa Taj wayar.

"Naji kamar yarinya ce, please ka É—an kwantar mata da hankali Yaya."

A tsiwace Hamdi ta ce "ni ba yarinya bace. Na yafe kuÉ—in. Ku zo ku É—auka ko na bar masa a mota."

Ita a wautarta in ta nuna bata tsoro ƙila a haƙura da cutar da ita.

Yadda take magana sai ya bawa Taj dariya. Kai kana ji za ka san a mugun tsorace take. Wayar ya kara a kunnensa.

"Big girl."

Anisa da Kamal harma da Anti su ka yi dariya. Da ta amsa abinta.

"Na'am."

"Ni yayan Anisa ne. Yanzu zan sa direban ya turo min location É—in ku. Sai na zo na kai ki gida. Haka ya yi?"

"Eh, amma don Allah minti nawa? Kaga fitsari ya matseni."

ÆŠaga kai ya yi sai yaga duk sun yi alamun tausayawa gareta.

"Zan yi sauri in sha Allah."

Cikin mintuna kaɗan kuwa direban ya tura masa da location ta whatsapp ɗin Anisa. Su ka shiga motar Kamal su uku. Kamal ɗin ke tuƙawa. Anisa tana baya. Lokaci zuwa lokaci kuma Hamdi sai tayi flashing da wayar direban. Ta ma manta ko bashi bata yi ba. Sai ya rabu da ita tunda ta daina kukan.

"Kun kusa?"

"Saura kaÉ—an."

Anisa ta kira Anti Labiba ta ce mata za su kawo Hamdi gida.

"Don Allah ku yi haƙuri. Baƙuwa ce a garin."

"Ban ji haushi ba. Ni tsorona ma firgitar da tayi kada ya zauna mata a rai." Cewar Anisa.

Wasa wasa sun yi minti shabiyar kafin su isa. Unguwannin ne da tazara a tsakaninsu.

Motar na doso su Hamdi ta kama handle za ta buɗe. Shi ma direban duk ya ƙagu. Yana ganin sun yi parking a bayansu ya cire lock. Babu takalmi haka ta jeho ƙafafunta waje ta fito. Mayafin da ta yafa akan riga da siket ɗin jikinta ya rufe rabin fuskata. Wayar Anti Labiban ma bata ɗauka ba ta fito da sauri.

Mayafin da ta gyara ne ya bayyana fuskarta sosai. Taj yana fitowa su ka haɗa ido. Zuciyarsa sai da tayi wani irin abu saboda ganin abin da bai taɓa zato ba.

"Hamdi?" Ya furta a can ƙasan maƙoshi shiyasa babu wanda yaji.

Ita kuwa bata ma gane me ta kalla ba. Burinta dai ya cika ta fita daga motar mutumin. Kamal ya ƙarasa wurin direban ya bashi haƙuri tare da cewa ƙanwarsu ce. Shi ma ya bada haƙurin rashin yi mata bayani wanda ya janyo wannan ruɗanin.

"Ga kayanta" ya ce da yaga suna shirin tafiya.

Kwalaye ne madaidaita guda biyu. ÆŠaya doughnut. ÆŠayan kuma meatpie da samosa. Sai kuma ledar youghurt wanda Hauwa ce da kanta tayi.

Anisa ce ta kula Hamdi bata da takalmi da ta zauna a baya. Za ta fita ta É—auko mata sai Taj ya ce ta zauna. Shi ya É—auko harda wayar yana ta mamakin wannan coincidence. Ashe tana Abuja. Shi yasa baya ganinta a gidansu. Murmushi kawai ya dinga yi har su ka soma tafiya. Hanyar gidan da ba ganewa za ta yi ba shi ma Anti Labiba ce ta turo kwatance. Anisa ta ce ta gane. Idan sun isa unguwar za ta kira sai ta kwatanta gidan.

"Shhh" Hamdi ta fara yi da baki saboda fitsarin da ya gama matsarta. Tun a na farko Taj ya ji. Hankalinsa gabaÉ—aya yana bayan motar.

"Step on it Kamal (ƙara sauri)" ya ce a hankali don kada taji kunya.

Kamar a kunnen Anisa ya faÉ—a sai cewa tayi "eh kuwa. A matse take sosai" tana kallonta.
Chapter 25 · 0% Book details