Sashe 32
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taj bai ji ta amsa ba har ya isa zauren ya tsaya. Ya sa rai za ta jima sai gashi bai fi minti biyu ba ta fito. Bakin nan a gaba.
"Kya hua Hamdiyya?" Ya zolaye ta.
Shi yake yaren ita take jin kunya.
"Ba na jin indiyanci."
"Na ga mata suna son movies É—insu. A nan ku ke tsintar kalmomi. Sisters É—ina dai na san haka su ke."
"To banda ni. Ba na kalla. Kuma namiji mai gani ma ba kula shi nake ba."
"Allah Ya so ni kenan." Taj ya ce yana neman haÉ—a ido da ita amma ta ki yarda.
Mamaki ya bata don bata yarda da furucinsa ba ta ce "Ba ka gani?"
"Ko Salman Khan É—in da ki ka kirani rannan ban sani ba."
"Allah ban yarda ba" ta ce kai tsaye.
Taj ya yi dariyar da amonta ya zauna daram a zuciyarta. Bata sani ba ko ana kiran maza cute. Ita dai da yana dariyar nema ya yi ya sauke mata bangon da take ginawa a tsakaninsu. Shammatarta da ya yi da tambayar da fito daga bakinsa ce ta yanke mata shagalar da ta so yi.
"Laifin me nayi miki ne da ya zamana tsakaninmu babu kallon kirki sai harara? Ko don ban faÉ—a miki na san ki ba a Abuja?"
Shiru tayi. Ya sake maimaita tambayar amma sai ta kawar da kanta. Bai yi fushi ba ya ajiye girma da matsayinsa ya faÉ—a mata abubuwan da su ka wakana tun lokacin da Firdaus ta faÉ—a masa sunanta da biyota gida da ya yi.
"Dalilinki na zo gidan nan amma yanzu ba don ke kaÉ—ai na nemi kusanci da Abba ba. Ina ji a jikina zamu amfani juna in sha Allah."
Kasa magana tayi. Sai tunani da yawa da take fama dasu. Da yaga tayi shiru ne ya nemi jin ta bakinta. Sai ta faɗi abin da bai taɓa tsammani ba.
"Da Abbanmu ya rasa wajen sana'arsa nayi murna ni dai. Na so ace wata sana'ar ya samu ba komawa girki ba."
Taj yaji tamkar ta watsa masa ruwan zafi.
"Kema ba kya son namiji mai girki ne? Ko kuwa wanda ya taɓa rayuwa irin ta Abba?"
"Mene ne maraba? Duk namijin dake girki ba ɗan daudu sunansa ba? Har yanzu ba sunan da ake kiran Abbanmu kenan ba saboda yaƙi yin wani aikin sai na mata."
"Daina magana irin haka Hamdi" Taj ya kwaɓeta "yanzu har za ki iya aibata sana'ar da mahaifinki yake yi miki komai cikinta kuma wadda Allah bai haramta ba?"
Kuka ta saka masa "Baka ji muryarsa ba? Idan yana tafiya meye marabarsa da ma..."
"Ya isa..." ya kaɗa kai yana mamakinta ƙwarai da gaske "indai za ki iya waɗannan maganganu akansa to waye a waje ba zai yi ba? I thought idan kowa ya ƙyamaci mahaifin mutum shi yana son abinsa."
"Nima ina son sa. Amma wallahi bana son sana'arsa." Ta kalle shi ido cikin ido "kuma bana son duk wanda zai taimaka masa akan cigaba da sana'ar girki."
Tunowa da Alhaji ya dinga yi da kalamanta masu ɗaci. Cikin ɓacin rai ya ce "nima ban ce ina son ki ba. So kada ki yarda ki min rashin kunya akan sana'ata. I am a Chef and I love what I do."
Bata san ta É—aga murya ba ta ce "to wa ya hanaka dama? Meye na sanya Abbana a ciki?"
A ganinsa bata ma cancanci ya faɗa mata kuɗurinsa na taimakawa Abba ya rage ko bai daina duka abubuwan mata ba. So yake ya nuna masa zai iya sana'arsa cikin nutsuwa ba tare da ya yi koyi da mace ba. Shi yasa ya ɗauki riƙaƙƙun maza waɗanda ko magana su ka yi sai an san namiji ne na gaske aiki. Girki daban, daudu daban. Wannan abin yake so hausawa masu fahimta irin ta Alhaji da wannan mara kunyar yarinyar da yake jin soyayyarta har yanzu su gane.
"Saboda na isa." Ya faÉ—i don taji haushi.
"Me kake nufi? Abbana yaronka ne?"
"Uba na É—auke shi mai sawa ya hana. Wanda kuma da ni ya haifa ba zan guje shi ba."
"Na ce maka ina son Abbana. Girkin ne bana so."
Ya zata yi ya fahimceta? Indai Abba bai daina sana'arsa ba, gani take ba zai taɓa rabuwa da ɗabi'un da ya koyi girki cikinsu ba na daudanci. Idan mutum yana abu maras kyau a ganinta nesanta dashi, shi ne yafi alkhairi.
Shi kuma Taj so yake ta gane cewa sana'ar ba ita ce ta mayar dashi haka ba. Haɗa biyun da mutane su ke yi, shi ne musabbabin da yasa mazan dake son girki da dama a ƙasar hausa su ke karkacewa su yi koyi da jinsin mata. A ganinsu kamar girki ba zai cika ba sai da waɗannan ɗabi'un.
Ran kowa a ɓace su ka rabu. Don ko amsa bai iya sake bata ba ya fice abinsa. Ita kuwa tana shiga gida taji saukar lafiyayyen mari daga wajen Yaya.
Huci take rai a ɓace "ki ka ce ba ki son duk mai taimakon mahaifinki akan sana'arsa Hamdi? Saboda kin tashi duk runtsi duk wuya bai taɓa ƙin kawo abin da za a ci a yi sutura ba? Ashe baki dawo daga rakiyar zuciya ta ƙyamar babanki ba?"
Hannunta akan kumatu tana jin zafi har ranta ta ce "Yaya ku daina yi min irin fahimtar nan. Ina son Abba mana. Girkin ne kawai...Yaya har yanzu muryar mata gare shi fa"
Sai kuka mai cin rai. Yaya ma kukan take yi. Duk cikin ƴaƴanta dama kafiya da sanya abu a rai babu wanda ya kai Hamdi. Kowa na zaton rigimarsu da Ummi ta kashe mata waccan ƙiyayya. Ashe har yanzu bata son sana'ar. To amma wacce take so ya yi? Bayan mutane suna da wuyar uzuri da ƙarɓar kuskure. A yanayi da ɗabi'unsa, duk inda ya sanya ƙafa neman taimako ko son fara sana'a sai ace ɗan daudu ne. Girkin ne kaɗai idan ya yi sai an bishi an saya. Da shi kaɗai yake tsaye a ƙafafunsa. Banda wauta da ƙuruciya me zai sa ta ƴarsa ta zauna ta faɗawa wanda ya killace mata uba daga gaban murhun da kowa yake ganinsa a da. Yanzu sai ya gama ya dawo iyakarsa kitchen. Ba a ganshi ba balle ma a aibata shi. Kuma saboda duka kitchen ɗin maza ne har ya fara ƙoƙarin gyara tafiyarsa.
"Kin bani kunya wallahi."
"Yaya..."
"Tashi ki bani wuri."
Ɗakinsu ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita. Soyayyar da take yiwa Taj ta ɗauki sabon salo. Haushinsa kawai take ji. Ba ma ta son shi. Kuma ba za ta taɓa son nashi ba.
"Aikin banza. Meye abin burgewa a namiji mai girki? To da me matarsa ma za ta burge shi?" Ta ayyana a ranta duk cikin kukan.
Shi a ranar kasa gane kansa aka yi a Happy Taj. Da yaga komai ƙanƙantar abu sai ya yi faɗa sai ya koma office ɗinsa kawai ya rufe ƙofa. Kan 3 seater yaje zai kwanta ya tuna Hamdi ta taɓa kwanciya a kai sai ya tashi yana tsaki.
"Ashe yarinyar nan bata da kunya? Na iya haƙura ma da Alhaji ya koreni balle wata ƙaramar yarinya?"
Daga inda suke kowannensu ya dage yana sauke fushinsa ta hanyar ƙara faɗawa zuciyarsa girman laifin ɗayan. Shi dai Taj baya son wadda ta kasa ganin ƙoƙarin mahaifinta a matsayin da Allah Ya ajiye shi. Ita kuma Hamdi gani take tsabar mugunta ce ma za ta sa ya cigaba da ingiza mata uba akan hanyar da babansa ya kore shi a kanta.
***
An yi Kamun Sajida ranar laraba cikin farinciki da taron dangi. Hamdi tuni ta ajiye wani Taj ana ta sha'ani. Wannan karon ko ciwon kai bata ce tana yi ba saboda tsananin farinciki. Sajida ta sami wanda take so kuma yake sonta ba tare da ya taɓa goranta mata ba. Damuwar su Yaya da tsoron ƴan matansu ba za su auro ba ta kau. Komai nasu na rufin asiri sun yi domin fitar da juna kai kunya.
Alhamis aka yi sisters' a wani event centre. Ranar dai har rawa Hamdi tayi tunda taron mata ne. Sai da Anti Labiba ma ta janyeta saboda ko gajiya bata yi. Ana canja kiÉ—a take komawa.
"Wannan ko ke ce amaryar sai haka."
Wata Æ´ar uwarsu ta kare mata "barta tayi. Ranar nata auren ai ba yi za ta yi."
*
Ana can ana shagalin biki wasu motoci biyu masu kyau su ka yi parking a ƙofar gidan Abba. A tsaye yake da Kamal da Taj. Kamal ne ya zo bashi tashi gudunmawar wadda ta kasance ta kayan abinci. Saɓanin ta Taj da ya bashi kuɗi. Yana ta cewa sun yi yawa da almajirai na kaiwa cikin gidan waɗannan motoci su ka tsaya.
Ƴar Ficika ne ya fara fitowa daga motar gaban yana murnar ganin Abba a ƙofar gida.
"WaÉ—annan mutanen ne su ka zo nemanka nace musu ai ka tashi daga wurin. To sai..." ya juya ya nuna wani Alhaji da ya nufosu yana takawa kamar baya so "wannan Alhajin ya nemi in kawo shi wurinka. Har za mu je restoran É—in sai na tuna É—azu ka ce min kana gida."
Abba ya yi murmushi "ai da ka sa wani ya rako shi ma."
"Yaran nawa duk basu san nan É—in ba."
Abba ya miƙawa mutumin hannu domin su gaisa sai ya ƙi ɗaga nasa. Kallon wulaƙanci kawai yake yiwa Abban. Shi da ragowar mazan da su ka firfito daga motocin har su biyar.
"Kai ne Habibu Simagade?"
Abba ya ɗan murmusa "a da kenan." Ya kuma miƙa hannun mutumin bai karɓa ba dai.
"Ni ne uban Safwan mahaifi."
Mamaki ya bayyana a fuskar Abba. Tabbas ga kama nan. To amma ba wani abu bane tunda da ana neman aure kawunnansa ne su ka zo.
"Allah Sarki. Bari nasa ayi shimfiÉ—a a ciki."
"Barshi. Zuwa nayi na faÉ—a maka cewa idan ka kuskura aka É—aura aurensa da Æ´arka gobe sai na É—aure duka mutanen gidan nan."
"Alhaji me ya faru?" Abba ya ce da fargaba. Taj da Kamal ma hankalinsu tashi ya yi.