Sashe 44
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata jira jin me za su ce ba ta fita. Anti ma fita tayi da niyyar yiwa Daddy magana. Bata maraba da tumbling É—in Æ´arta da Hajja take yi. Ita ma Anisa bayansu ta bi. Sai dai kafin ta fita ta tsaya tayi masa magana.
"Allah Ya sanya alkhairi Ya Taj."
"Nagode Anisa. Kuma don Allah kada ya zama reason na lalacewar zumuncinmu."
"Tun farko dama kayi min bayani. Babu wani abu. Sai mun zo ganin amarya."
Da ya rage su biyu a falon Taj ya kalli Amma "that went well right?"
"I think so." Ta bashi amsa da fatan hakan ne.
Breakfast ta kawo musu. Bayan sun gama ya faÉ—a mata komai ds komai da ya danganci Abba da aurensa.
"Yaron nan da a É—an daba ka tashi sai an wahala da kai. Banda rigima ka rasa Æ´ar wanda za ka auro sai Simagade? Kai yanzu ka yarda Yaya Hayatu ba zai kawo matsala a gaba ba?"
"Da Allah na dogara Amma. Bana son yin wannan tunanin saboda ban hango abin da zai rabani da Hamdi ba."
"Sunanta ya min daÉ—i fa. Hamdiyya. ÆŠazu da ka faÉ—a har zan magana na kama bakina kafin Hajja ta zageni."
Cikin farincikin shiryawa da Amma ya bar gidan da yamma. Ta so ya kwana amma ya dage gara yaje hotel. Zaman nasa a ganinsa tamkar rashin kunya ne. Zai kyautu ya bawa mutanen gidan damar sake karɓarsa idan ciwon abin da su ke tunanin laifi ne ya ragu.
***
A yau sha'anin biki ya ƙare. Kakan Safwan ya wakilta masu ɗauko amarya Sajida zuwa gidansa. Dama Umman Safwan ɗin bata da damuwa ko kaɗan. Babansa ne baya so. Bayan koke koken amarya da ƴan uwanta da kuma Yaya, gidan kakannin Safwan aka wuce da ita.
Tsohon nan ya yi musu nasiha sosai da jan kunne.
"Sai kun ji kon ƙi ji. Ku gani kuma ku ƙi gani sannan auren zai yi ƙarko. Musamman gareki jikata" Sajida ta kalle shi da jan ido "duk wanda ya sami dama a dangin nan zai faɗa miki magana son rai akan asalinki. Wannan ko ka hana wani sai ya yi. Saboda haka ki koyi kawar da kai. Inda ba za ki iya ba kuma ki kare martabar mahaifinki. Ina mai tabbatar miki da an kwana biyu zai bi jiki. Kowa zai haƙura matuƙar kun zauna lafiya. Kun bawa maraɗa kunya."
Safwan ne kaÉ—ai ya iya yi masa godiya. Sajida kuwa in banda sharar hawaye babu abin da take yi.
*
Ana can ana ƙarasa guntattakin gyara a gidan amarya Zee ta fice daga ɗakin da Hamdi take yiwa turaren wuta ta koma wajen gate ta kira Taj. Yamma ce liƙis. Tana ta addu'ar samunsa a wayar. Tayi sa'a kuwa bugun farko ya ɗauka. Sai kuma ya kashe ya kirata.
"Zee amarya."
Sake tsokanarta ya yi "to uwargida. Tun yanzu har an fara kishi kenan."
"Don Allah ka bari"
Yanayin muryarta ba yadda ya saba ji bane. Shi yasa bai ja wasan ba ya nemi ta sanar dashi dalilin kiran. Muryarta rawa ta fara, sai kuma ta kama kuka. A haka ta faÉ—a masa maganganun da taji Abba yana faÉ—awa Hamdi jiya ba tare da sun san ta biyo su ba.
Ashe tun shigowar Hamdi cikin gidan ta taso za ta tsokaneta akan me taje yi a waje sai taga Abba ya ja ta zuwa soro. Fuskarsa da ta gani da damuwa ita tayi sanadin binsu da tayi. Tana gama jin abin da ya ce tayi saurin komawa ciki.
Jijiyar kansa tashi tayi sosai. Æacin rai ya rufar masa. Ya rasa dalilin da yasa Alhaji yake yi masa haka.
"Ya Taj don Allah ka saketa ba sai tayi maka abin da zai ɓatawa Abbs suna ba."
"Yi shiru Zee. Maganar nan da wa kika yi bayan ni?"
"Babu kowa." Ta ja hanci.
"To don Allah ki yi min alƙawarin riƙeta a ranki kin ji."
"Sakin fa?"
"Hamdi ta zo kenan. Idan ku ka yi wasa ma duk sai ta riga ku haihuwa."
Wayar ta cire daga kunnenta saboda kunyar kalamansa. Kamar ya sani ya ce
"Oh sorry, ƙanwa ce fa ke."
"Idan tayi maka laifin da zai sa ka saketa fa?"
"Kada ki damu. Just focus on yourself. Ki gama karatunki ki kuma riƙe mutumcin aurenki. Ni da Hamdi in sha Allah anyi auren kenan."
"Tsoro nake ji kada babanka ya yiwa Abba wani abu."
"In sha Allah babu abin da zai faru. Ina son sister É—inki. Zan kuma tsare mutumcinta da na duka family É—inku."
Ya ɗauki lokaci sosai wajen kwantar mata da hankali. Sannan ya yi mata godiya da ta tunkare shi da zancen. Wayar Kamal ya nema da su ka gama don ya faɗa masa yaji a kashe. Ya yi ɗan tsaki. Tun asuba fa Kamal ba yadda ya saba yake ba. Komai daina yi masa daɗi yake saboda yana jin tamkar wani ɓangare na jikinsa baya tare dashi.
Jirgin tara na safe ya yi booking ta waya kafin ya kwanta.
***
Hannuwa da ƙafafunsa ya kalla hankalinsa ya sake tashi. A kumbure suke. Fuskarsa kuwa kamar an hura balloon. Magungunan jiya ya ɗauko yayi ta dubawa ko akwai wanda ya sha ba daidai ba amma babu. Gabansa ya dinga faɗuwa da tunanin me zai faru idan yanayinsa ya cigaba a haka. Babbar matsalarsa ma ita ce yadda zai samu ya bar gidan ba tare da kowa ya gan shi ba. Daga daren jiya zuwa yanzu ya fita hayyacinsa baki ɗaya. Wayarsa ya nema ya kunna domin magana da likitarsa sai yaji ana taɓa ƙofar ɗakinsa.
Hankalinsa ya sake tashi da ya kalli kansa a madubi.
"Waye?" Ya furta da ɗan ƙarfi.
Shiru yaji babu amsa. Sai zura muƙullai da ake tayi a ƙofar. A gwaji na biyar aka buɗe ƙofar ɗakin wanda bai taɓa zaton akwai spare key ba. Idanunsa da ƙyar su ke buɗuwa saboda hasken fitilun waje da su ka shigo.
"Abba? Bishir?"
Fitilar ɗakinsa aka kunna gami da rufe ƙofar ɗakin nasa.
"Kamal? Shaye shaye kake yi?"
A gigice ya ɗago idanunsa da suke buɗewa da ƙyar saboda kumburi ya kalli wadda ke tsaye a kansa.
"Umma?"=
RAYUWA DA GIÆI 20
Batul Mamman💖
_Gaisuwa ta musamman ga baiwar Allah da ta tura saƙo OpenDiaries. Ina fata kin sami sauƙi. Allah Ya inganta Ya raba lafiya. Abba Habibu Simagade yace a baki haƙuri ba niyyarsa kenan ba. Shafin yau naki ne._
Ina ƙara tunatar da masu karatu posts weekdays ne kawai don Allah. Nagode sosai. SonSo
***
Na ɗan taƙin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta so ƙullewa har ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa'a sai ya tuno abin da ya tanadi faɗawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya ɗaga hannuwa da ƙafafunsa yadda za ta gansu sosai.
"Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?" Ta ƙarasa inda yake tana tattaɓa shi.
"Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka sosai."
"Subhanallahi" ta matsa hannunsa na dama "akwai zafi?"
Kai ya girgiza mata. Ya zauna ya shirga mata bayanin ƙanzon kurege wai allergy gare shi kuma har yanzu likitan bai gano mene ne jikin nasa baya so ba.
"Anya ya san aikinsa kuwa? Me yasa baka je wurin yayarka ba?"
Gaban Kamal ya faɗi da tsoron kada Umma ta matsa masa akan zuwa wajen Yaya Kubra. Ita ce babba wajen Mama kuma sananniyar likitar ɓangaren lalurorin mata. Yana zuwa wajenta asirinsa zai tono.
"Ita da take gynae? Wannan ba ɓangarenta bane."
"Amma ai ba za ta kasa sanin likitan da ya dace da kai ba a asibitin Malam (AKTHA) ko? Ni dai bari nayi mata waya. Wannan kumburin ya bani tsoro. Har wani baƙi naga kayi."
"Kai Umma, idonki ne." Ya wayance.
Da ƙyar ya hanata kiran yayar tasu. Ya tabbatar mata likitan da yake gani ma ƙwararre ne. Harkar allergy wani zubin sai an wahala kafin a gano mene ne jiki baya so har yake reacting irin haka. Baiwar Allah sai ta yarda da zancen nasa. Ta kira masa Abba ta ce ya zo ya kai shi asibiti.
"Amma me ya sa ka ɓoye mana? Jiya ina kallonka kafin ku fita wajen sirikin Taj da Innarku ka shige kitchen ka watsa magani. Kuma yau kowa ya ce bai sanyaka a ido ba. Shi ne tsoro ya kamani. Ko ƙwaya ka fara sha."
Halin ciwon da yake ciki bai hana shi dariya ba.
"Abin da ban yi da ƙuruciya ba Umma?"
"Yo Allah na tuba shaye shaye lokaci gare shi? Kai dai kawai Allah Ya kare ku da sauran zuri'ar musulmi. Zamanin ya zo da hanyoyin ɓata tatbiyar tsofaffi balle kuma matasa masu jini a jika."
Tunaninsa na yadda zai je wajen likitarsa cikin sauƙi ya sami solution. Umma ta sa Abba ya kai shi asibitin. A hanya kafin ya ƙarasa ya tura mata saƙo ta bashi amsa. Roƙonta ya yi da sirranta lalurarsa a gaban Abba.
Da taimakon Abba ya iya shiga asibitin. Dauriya da ƙarfinsa sun soma ƙarewa. Wata Nos tana ganinsu ta hanzarta kiran likitar wadda dalilinsa ma ta fito don yau ranar hutunta ce.
Wata kyakkyawar matashiya ce ta fito sanye da baƙar abaya da ƙaramin hijab. A fuskarta gilashi ne mai ɗan kauri dake taimakawa ganinta. Madaidaicin tsayi gareta amma kuma she is a bit chubby. Sai dai ƙibar ba mai yawa bace. Ɗakin taimakon gaggawa tasa aka shigar mata da Kamal aka kwantar akan gado.
Abba ya gama tsorata da yanayinsa. Yana ganin ta farke sirinji cikin sauri ya ce "Doctor kinga jikin nasa duk ya rikice kafin mu ƙaraso. Don Allah ki gane mene ne ba ya so sai mu kiyaye."
"ÆŠan bamu wuri" ta ce idanunta akan Kamal. Patient É—inta mai É—an banzan taurin kai.
Hankali a tashe Abba ya fita. Ya shiga fareti a wajen yana addu'ar a shawo kan matsalar da wuri.
Yana fita Mubina ta rufe ƙofar emergency ɗin ta shiga bawa Kamal taimakon da ya kamata. Kimanin minti talatin kafin jikin nasa ya fara daidaita. Ya buɗe ido a hankali ya sauka cikin nata.
Ranta a ɓace yake sosai. Kallon da tayi masa ya sanya shi murmushi. Ya đaga hannunsa guda ba wanda take yi masa ƙarin ruwa ba ya kama kunnensa.
"Sorry."