← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 96

Sashe 5

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Za a iya cewa Taj da Kamal wasu manyan jigo ne na farincikin gidan Alhaji. Indai suna gida to in sha Allahu dariya da nishaɗi baya yankewa. Zolaya da wasa duk halinsu ne. Har suna su ka sanyawa juna. Kamal ya kira Taj Happy, shi kuma Taj ya kira shi Happiness. Irin faɗan nan na sakonni da wuya kaga sun yi. Sannan daga yayyensu har ƙanne ba za ka ji wanda ya kai ƙararsu akan sun masa ba daidai ba. Duk kuwa da kasancewar Taj mai tsokana lamba ɗaya. To amma yana da tsoron yin laifin da za a hukunta shi. Shi kuwa Kamal dama green snake ne. Sai ya yi abu ya koma gefe kamar ba shi ba.

Tun tasowarsu akwai wata irin shaƙuwa ta musamman tsakanin Alhaji da Taj. Shi dai da zarar mahaifinsu ya dawo to ya gama wasu wasanni. Yana daga cikin lokutan da akan gansu wuri daban daban shi da Kamal. A gefensa yake zama yana yi masa tambayoyi musamman akan kasuwanci. Nan da nan ya zama sunansa abokan harkokin Alhajin su ka fi sani. Kowa ya buɗe baki sai ya ce Taj. Har dai aka fara hannunka mai sanda a gidan ana cewa da alama shi zai gaji Alhajin. Yawan maganar yasa Inna ta fara jin abin yana damunta. Bata son rigima ta ɓullo daga ɓangarenta. Shi yasa wata rana su na zaune su biyu da Alhajin ta tayar masa da zancen.

"To ke banda abin ki mene ne a ciki? Duk uba ai yana son magaji a fannin da ya yi zarra musamman idan halattacce ne."

Wasa taga ya mayar da zancen ta girgiza kai.

"Kaga yana da yayye. Idan ana cewa magajinka wani zai yi zaton irin abin nan ne na son ture wasu don wata manufa."

Kallonta ya yi yaga sosai ta shiga damuwa.

"Ku mata sai a barku. Tunaninku kullum babu nisa. Musulunci dai ya riga ya gama mana komai. Yau ko dama na kwanta yadda shari'a ta tsara haka za a raba abin da na bari a bawa Æ´aÆ´ana. Babu wani fifiko."

"Na sani"

"Amma duk da haka kina damuwa saboda kada a ce Hayatu ya fifita ɗanki akan na sauran. Ƙila ma kina ƙarawa da cewa za a zargi ko don mahaifiyarki ƙanwar mahaifina ce."

"A'a wallahi" ta ce da sauri.

Ya sake yin murmushi sannan ya ɗan tuna mata baya. A gidansu cikin maza su goma sha uku shi kaɗai ne ɗan kasuwa kamar baban su. Sauran duk aikin gwamnati su ke yi. Shi kuwa ya ajiye kwalin tun daga degree na farko ya rungumi sana'ar gidan ba tare da an tauye ƴan uwansa da komai ba. Duk abin da ya tara yanzu arziƙinsa ne na guminsa. Ya ma zamana duka ƴan uwan nasa duk wanda ɗansa namiji ya gama sakandire sai ya tura masa shi kasuwa na shekara ɗaya. A haka yanzu akwai mutum bakwai cikin ƴaƴansu da su ke jikinsa.

"Zan yi maganin damuwar nan anjima idan an zo cin abincin dare."

Bai manta ba kuwa. Dama al'adar gidan idan ba baƙi gare shi ba duka tare ake cin abinci a babban falo. Ƴan shekaru kusa da juna ake haɗawa a kwano guda. Matansa ma yawanci tare su ke ci. Ana gamawa yaran za su nufe shi da buƙatunsu. Ko fensir ne ya karye sun fi gane su sanar dashi. Yana daga zaune zai sa a bashi reza don yafi gane mata ya fiƙe. Wasu ya koya musu homework. Masu buƙatar kuɗi ko wani abu makamancin haka duk a wannan zaman ake yi. Ana gamawa zai ja su sallar Isha sannan ya tashi. Su kuma daga nan za su ɓalle da hira. Ƙananun da duk mai ra'ayi su tarkata su koma wurin Hajiya indai ba girkinta bane domin jin daɗaɗan tatsuniyoyi.

"Mal. Bishir wai me ka ke son zama ne idan ka girma?"

Bishir ya É—ago kai daga rubutun da yake yi na homework ya kalli baban nasu.

"Shoe shiner."

Falon gabaÉ—aya aka bushe da dariya harda Alhajin. Shekarar Bishir bakwai a lokacin.

Kuka ya soma yi yana cewa "Alhaji kaga suna yi min dariya ko?"

"Rabu dasu. Tambayar ma ta saraya a kanka sai ka ƙara girma. Duk wanda ya sake dariya kuma bana bashi da takalmin sallah. Dama kai zan bawa ka raba."

Da haka ya kawo ƙarshen kukan nasa. Ya mayar da tambayar ka ga Abba.

"Babana fa?"

Murmushi ya yi "Alhaji ni police zan zama."

"Ni dai bana son khaki Abba. Don Allah ka zaɓi aikin da ba zai dinga hana ni bacci mai daɗi ba" cewar Mama.

Alh. Hayatu ya ce a ƙyale yara a bisu da addu'a.

"Taj kuma fa?"

Abin nema ya samu. Kowa ya zuba masa ido ana jiran a ji ya ce kasuwanci irin na baban nasa sai ya basu mugun mamaki.

"Chef! Mai girki." Ya ce hankali kwance yana murmushi.

Da yake yafi kusa da Umma a inda yake zaune bata san ma lokacin da ta buge bakinsa ba saboda wani hargitsatsen kallo da Alhaji ya watsa masa.

"Bar dukansa Jamila. Barshi ya maimaita."

Ko ɗar bai ji ba ya sake faɗin abin da ya ce da ƙwarin gwiwa.

"Chef. Mai dafa abinci a restau..."

"TAJUDDIN!!!"

Tsawar ta gigita kowa. Ƴar autarsu ma kuka ta saka harda zubar da abincin da aka ajiye a gabanta tana ci da kanta.

"Ku tashi ku bani wuri." Ya faÉ—a a fusace.

Da yake a lokacin sun kai shekara sha huɗu shi da Kamal duk da hankalinsu. Shi yasa Taj ya gane abin da ya faɗa bai sami karɓuwa ba. Bin sahun ƴan uwansa ya yi ya tashi.

"Ina za ka? Zama zaka yi ka faÉ—a min me ya burge ka da daudanci har kake tunanin kawo min wannan shaiÉ—ancin cikin gida."

A tsorace ya zauna yana kallo kowa ya tashi har iyayensu mata. Alhaji ya ɗan sausauta murya don ji yake kamar ya fara duka akan ɗan da yake matuƙar danne soyayyarsa. Ya tambaye shi ko ya taɓa yin girki a rayuwarsa.

"Abincin da aka gama ci yanzu ma ni nayi miya. Wallahi Alhaji na iya girki sosai. Indai babu islamiyya ni nake na dare."

Sai da ya cije leɓe don wani irin sarawa kansa ya yi sannan ya ce "kirawo min uwayenka ka ce su same ni a ɗaki."

***

A ɗakin Hajiya su ka tare su huɗu ashe suna ta caccakar Mama. Musamman Umma wadda ta jima da hango ɓacin rana a dalilin wannan abu.

"Na sha faɗa miki ki hana yaron nan shiga kitchen ki ka ƙi. Tun ana ɓare maggi har ta kai yana ɗora sanwar gidan nan."

Mama da karayar murya ta ce "saboda Allah yanzu a ce mutum yana da yaro amma ba zai koya masa ayyukan cikin gida ba? Girki ai ba lallai sai mace ba. Kuma ra'ayinsa ne tunda duk yadda su ke da Kamal shi ko magin baya ɓarewa."

Hajiya ta ce "Amma tun farko kin san Alhaji yaƙi jinin ganin mazan gidan nan da tsintsiya ma balle girki. Yana gani yake cewa a daina saka su kada su zama ƴan daudu. Ko kin manta tashin hankalin da aka taɓa yi akan gugar kuɓewa?"

Wata rana ne kusan shekara uku da su ka wuce mai aikinsu ta fita bata dawo da wuri ba. Girkin Hajiya ne ita ma sun fita dubiya dukkansu. Suna dawowa taga ba'ayi tuwon dare ba. Shi ne ta rabawa Ahmad, Kamal da Taj gugar kuɓewa ita kuma da taimakon yan matan gidan ta ɗora tuwo. Alhaji da ya shigo yaga suna aikin nan a falo ya dinga faɗa ba ji ba gani. Sai da ya yi sati baya cin abincin gidan yana kuma gargadi da tuna musu aikin namiji da mace a gida ba ɗaya bane.

Mama ta É—an kalli Inna da tayi shiru kawai tana kallonsu.
"Ki ce wani abu mana. Ko kema laifina kike gani?"

"Laifi kamar yaya? Neman mafita kawai zamu yi kafin ya tasa mu a gaba don na san..."

Laluben É—akin da Taj ya É—aga da sallama ya katse mata magana.

"Alhaji yana kiranku a samansa."

Hajiya kiransa tayi ganin jikinsa duk ya yi sanyi.

"Girki ko a gidanka kana da damar yi Taj amma kada ka sake cewa za ka zama mai abinci ko daɗin ji babu. Duk wani namiji mai sana'ar abinci ɗan daudu ne. Su kuwa Allah baya son su tunda sun zaɓi jinsi kishiyar wanda ya basu."

Kai ya gyaÉ—a kawai ya fice. Sanin cewa zai haÉ—u da Ahmad da Kamal kuma lallai ba za su goyi bayansa ba sai ya gudu É—akin Inna. Wuri ya samu ya kwanta ya rufe idanunsa yana tunani.

Kasuwanci da yake nacin koyo a wurin Alhaji ba don komai bane sai don yana da muradin buÉ—e gidan abincin da yake son ya yi suna. A rayuwarsa babu inda yake shiga yaji kamar an sabunta masa duniya kamar kitchen. Kuma a iya saninsa maza da yawa su na girki. Suna da shekara goma Alhaji ke kai yara Umra. Idan mutum ya yi shabiyar a kai shi Hajji. A Saudiyya in ka cire Takaru babu inda ya ga mata suna sayar da wani abu na ci. Maza ke girkawa su sayar. Maza musulmai magidanta waÉ—anda basu da wata siffa da duk hangen mutum zai danganta su da mata. Idan sana'ar haramtacciya ce ga namiji da waÉ—annan basu kai labari ba. Shi kam yana son girki kuma in Allah Ya so ita ce sana'ar da zai yi.

A ɗakin Alhaji kuwa faɗansa har falon ƙasa. Don ma ƴaƴan kowa ya shige ɗaki. Manyan sun haɗe kawunansu da ƙananan a ɗakunan iyayensu a ƙasa.

Ya fusata sosai don ko da su ka shiga É—akin maganinsa na hawan jini yake sha.

"Ni za ku ha'inta? Girkin nan ba yau ya fara ba tunda ya ce shi ya yi miyar dare. Ace ko sau ɗaya idanuna basu taɓa gani ba. Abin da mamaki."

Mama ce ta fara bada haƙuri "na bari ne kawai saboda ganin yawanci gidajen da su ke da yara maza duk ana koya musu girki. Hakan bai sa sun yi koyi da ɗabi'un mata ba."
Chapter 5 · 0% Book details