Sashe 19
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taj ta sosa ƙeya "tuba nake Hajjo tawa ni kaɗai."
Ƴar tsohuwar ta yatsina fuska "bana son daɗin baki. Ai da uwarka Jamila ce a gidan nan ba za ka saka aiki a gaba ka kasa zuwa ba."
Anisa babbar Æ´ar Anti ta nuna rashin jindaÉ—in wannan furuci "abin kuma harda zagi Hajjo?"
"Fita ko ban guri ai ba kiranki nayi ba."
"Ya Taj na biyo."
Hajjo ta haÉ—e fuska tana neman abin duka "Duk gidan nan babu wanda ya isa ya yi min iko da É—aki saboda haka get out."
Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa "yeeyyyy, Hajjo ta tuno zama cikin turawa."
"Zan zagi babanki wallahi. Zo ki fice."
Kafaɗa Anisa ta noƙe ai kuwa Hajjo ta bita da daƙuwa hannu bibbiyu.
"Na iyayenki su uku."
Alamun rashin jindaÉ—i Anisa ta nuna wanda Taj ya lura. Da ka ya yi mata ishara ta fita daga É—akin.
"Hajjo sai ki yi ta zagar mana iyaye saboda Allah? Kinga bata jidaÉ—i ba daga É—an yin wasa da kakarta."
Lura tayi shima kamar bai jidaɗin ba sai kuma ta saki fuska. Ita a dole Taj ne kaɗai jikanta namiji na wajen babban ɗanta. Tunda ya koma hannun Amma bata taɓa canja masa ba. Saboda tun asali dama kakarsa wadda ta haifi Alhaji da ita ƙawaye ne da su ka yi ƴan matanci tare.
Ita ta fara zayyano masa ƙorafinta akan zaman Amma ita kaɗai a gida ga mijinta a wata uwa duniyar.
"Saura bai fi sati uku ba na koma in sha Allahu. Kuma zan zauna har tayi ritayar. Ai na san zamana ne sharaÉ—in da yasa ki ka yarda ta cigaba da aikin."
Hajjo ta ƙara sakin fuskarta saboda Taj akwai iya tsara zance.
"Ka san ita mace bata tsufa da buƙatar kulawa. Yau ko ƙwan fitila ne ya mutu wata idan babu namiji a gidan sai dai ta zauna a duhu."
Haƙuri ya sake bata da yaga ya samo kanta kuma ya yi mata bayanin gininsa da ya yi nisa.
"Shi uban taurin kan har yanzu baku daidaita bane?"
Dariya Taj ya yi. Kamar ba ita ta nuna ta daina ƴan mintuna ƙadan baya ba.
"An dawo kansa kuma?"
Ko a jikinta ta ce "Ai Hayatun ne akwai wuyar sha'ani sai ka rantse ni na haife shi. Don ita babar tasu haka take ba cas ba as."
"Ahhhh. Ni fa Hajjo zan tashi wallahi. Harda kakata kuma."
Yadda ya ɓata fuska sai da tayi dariya. Daga nan aka kashe maganar dawowar Amma. Sai kuma ta sako zancen da yake cin ranta. Dama can ba dawowar Amman bace a gabanta. Tafi kowa sanin halinta tunda a gabansu ta tashi. Ita ce ma ta haɗa auren nata da ɗanta. Da gangan ta tayar mata da hankali yanzu kawai don Taj ɗin yazo. Don tayi imanin indai yaji ba zai ƙasa a gwiwa ba zai zo neman sulhu.
"Tajo."
Babu yadda ya iya. Dole yake amsa sunan nan da baya son a faÉ—i indai daga bakinta ne.
"Nace wai me zai hana ka nemi ƙanwarka Anisa ku daidaita? Karatunta sai gudu yake har an shiga aji huɗu a jami'ar nan."
Gabansa yaji ya faɗi. Duk kirkin Hajjo kowa ya san rigimammiya ce ta buga misali. Yanzun nan sai ta yiwa mutum dabaibayin da zai sarƙe wuyansa bai sani ba.
Ƙofa ya kalla tana gama maganar "Hajjo daina faɗa kada ta zata gaske ne ta soma jin haushina don na tabbatar ba za ta rasa masoyi ba."
Shan kunu tayi harda yi masa daƙuwa.
"Ƙaniyarka Tajo."
Ya sunkuyar da kai yana sauraron sababinta.
"Da akwai wanin ai ka san ni ba mai yiwa jikoki shisshigi bace. Sannan na tabbata da daga cikin Jamila ta fito ba ma za ka ce komai ba."
Hankalinsa tashi ya yi ya miƙe tsaye yana ɗan tausar kafaɗarta.
"Allah Ya huci zuciyarki. Ba haka nake nufi ba."
"Za ka yi mata maganar ko na kirata yanzu?"
Gani ya yi za ta rushe masa ginin da bai fara saka tubali ba akan yarinyar nan Hamdiyya. Shi yasa da saurinsa ya ce ta bari shi zai yi.
"Alƙawari fa za ka yi min."
"In sha Allahu zan yi mata magana."
Tana jin haka ta washe baki hankali kwance. A ranar da washegari da zai taho bata sake tada wata rigimar ba. Daddy kawai ta kira ta ce masa tayi mai wuyar. Ya fara shiri don ba za ta zuba ido ya bar ƴan mata a gabansa babu aure ba. Da yaji waye zaɓin da ta yiwa Anisa sai taga ya fita farinciki. Kuma da murnarsa ya kira Amma ya faɗa mata. Sai ta nuna masa ta fishi jindaɗi domin ita ba butulu bace. Duk wata gudunmawa da ta dace financially da morally ya bata wajen kulawa da cikar burin Taj.
***
Rayuwa ta fara tsanani ga iyalin Abba. Da yake mutum ne mai sakarwa iyali aji daɗi da abin da Allah Ya hore masa, yanzu da ajiyar ta soma ƙasa sai suke ƙuntata. Yawancin samunsa in ka cire buƙatun gida to anyi amfani dasu wajen tarin kayan ɗaki da yake yiwa ƴan matansa. Komai na mutum uku yake saya. Yaya bata san yiwa ƴaƴa komai ba ta wannan fannin don bata sana'ar komai. Tun da ƙuruciya babu irin nacin da bata yi ba amma sam yaƙi yarda tayi saboda a cewarsa ta gama aikinta da ta aure shi. Nan kuwa yana tausayin lafiyarta ne. A ganinsa rashin imani ne zai sa ya sanya rai da ta dinga neman kuɗi a yanayin da take ciki. Gashi dama bai tsira daga dariya da surutun mutane ba. Idan ya bari tana shiga jama'a da sunan sana'a babu mamaki a karyar mata zuciya da zancen lalurarta. Shi yasa ya yiwa tufkar hanci da wurwuri.
Sauƙinsu ɗaya yanzu a gidan shi ne kitson da Sajida take yi. Hamdi kuma satinta biyu da dawowa gida Anti Labiban Abuja da ta zo Kano ta roƙi alfarmar tafiya da ita idan za ta koma. Kowa ya san miskilancin Hamdi idan ta so. Suna ta zaton za ta ƙi. Sai gashi da kanta ta amince za ta bita. Weekend na zagayowa kuwa su ka tafi.
*
Abin haushi da takaici da Taj ya tambayi Firdaus game da yarinyar da ta kasance overall a makarantarsu wai bata san komai a kanta ba.
"Ba ƙawarki bace?"
"Hamdiyya ai bata da ƙawa ko ɗaya. Sai da case ɗin babanta ya tashi ne ma ta ɗan sake da mutane."
Interest ya nuna na son jin me ya faru da baban nata. Firdaus kuwa ta zage ta kora masa jawabi tiryan tiryan. Har hukuncin da makaranta ta ɗauka akan ƙawayen Ummi tunda ita an cireta.
Tana gama jawabin ta tashi tayi gaba abinta. Ta bar shi da shiga ruÉ—ani da mamaki. Ba kuma komai bane ya sanya haka illa tuna sunan mahaifin Hamdi da kuma sana'arsa da Firdaus ta faÉ—a.
Tunani barkatai ya shiga yi game da yadda aka haihu a ragaya. Indai shi ne Habibun da Alhaji yake ƙyamar ya yi koyi da halayyarsa to yaya aka yi ya yi aure? Me ya faru da rayuwarsa? Kuma wace irin rayuwa yake yi yanzu?
Tabbas zai so sani. Shi Tajuddin zai so ƙwarai ya shiga cikin rayuwarsa ba don ƴarsa kaɗai da ta tarwatsa masa zuciya ba. Wasu burika ne suka mamaye zuciyarsa wanda zai so ya cimma in har shi ne wanda Alhaji ya sani ɗin.
Kwana biyar kacal su ka ɗauka shi da Kamal wurin neman Habibu Simagade na Soron ɗinki. Sai gashi an kai su har ƙofar gidansa. Mutumin da ya rako su magidanci ne amma har su ka isa hirarsa akansa bata wuce alkhairinsa da kyakkyawar tarbiyar ahalinsa ba.
"Ai wato banda ance kowa da ƙaddararsa da in kaga wani aka ce maka zai sami sauyin rayuwa sai ka ƙaryata."
"Me yasa ka ce haka?" Kamal da Taj bai ɓoyewa komai ba illa son Hamdi ya tambayi mutumin.
Shi kuwa ya daina tafiya tare da binsu da kallon rashin yarda. Sannan ya nuna Taj.
"Ka ce min kai sana'ar girki kake yi. ÆŠan uwanka kuma kasuwanci."
"Haka ne."
Da faÉ—a-faÉ—a ya cigaba da magana "zamanin yanzu ai babu yarda a tsakanin mutane. Da naji aikin naka na zata taimakon Habibu ka zo yi. Shi yasa ma zan kai ku gidan."
Taj ya yi murmushi "sana'ar girki yake kenan?"
"Watannin baya ba. Kafin ƴan hassada su sako shi a gaba su ka ƙwace wurin da yake haya. Banda haka ko garau garau Habibu ya dafa maka wallahi sai ka ji bambanci."
Duk surutun mutumin nan bai ƙara yarda ya đara daga inda yake tsaye ba yana jiran su faɗa masa gaskiya ko su waye su sai ga Abba ya fito. Daga yanayin tafiyarsa da kamanni da ya gani da Hamdi Taj ya gane shi. Kafin ya iso wurin da su ke ya tsaya ya fi sau huɗu yana gaisawa da mutane. Wannan abu ya sake burge Taj sosai har bai san lokacin da haƙoransa su ka bayyana da farincikin da ya shiga ba.
RAYUWA DA GIÆI 11
Batul Mamman💖
Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani.
"Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya."
"Dakata Mal. Habibu. WaÉ—annan fa kai su ke nema."
Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taɓa haɗuwa dasu ba.
"To Allah dai Yasa lafiya" ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba.
Kamal ne ya amsa masa "lafiya ƙalau." Sannan ya gabatar da kansa da Taj.
Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama.
"Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta É—aukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce."