← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 96

Sashe 64

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hamdi ta kalli ɗakinsu da babu kowa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ce sannan tayi magana.

"A da ba."

"Yanzu fa?"

"Nima ban sani ba. Salawaitu yake so. Ni kuma sai in yi ta son shi? Haka ake yi?"

Murmushi ya yi. Ya sami amsarsa koda ba kai tsaye bane.
"A'a gaskiya. Abin da nake so dake dai don Allah ki bar abubuwan nan tsakaninmu. In ki ka bari wani yaji har aka raba auren ina mai tabbatar miki Salawaitun zai aura."

Wawan duka Taj ya kai masa a baya. Baya ƙaunar zancen Salwa tuntuni balle yanzu da yake cikin damuwa shi da amaryarsa.

Ajiyar zuciya tayi "Ba zan faÉ—a ba"

A ransa yake auno yadda zai tsokanesu duk su biyun idan komai ya daidaita. Yana gama wayar ya koma kan Taj.

"Happy ina ganin wannan maganar fa ba tamu bace mu biyu."

"Me kake nufi? In faÉ—awa wani? In aka ce na sake ta fa?" Ya soma magana cikin tashin hankali.

Nutsuwa Kamal ya yi wanda yasa Taj ya gyara zama.
"Me ka ke tunani?"

"Ka faÉ—awa Inna."

"Inna kuma? Me za tayi?"

"Duk matsalar duniya Happy uwa ce ƙarshenta. Ko bata magance ba in sha Allahu za ta faɗa maka yadda za ka yi. Sannan ga addu'arta da bata da shamaki. Abin naku kamar asiri."

Kallonsa Taj ya yi "kai duka matsalolinka kake faÉ—awa Hajiya?"

"Wanda ya dace lallai ta sani ba."

Kallon tuhuma Taj ya yi masa
"Me yasa ka ɓoye mata ciwonka bayan ka san idan tayi addu'a za ta karɓu?"

Gaban Kamal faɗuwa yayi. Cikin sarƙewar harshe ya ce "ai...dama. hhhh. Saboda gudun tashin hankalinsu ne."

"I see" kawai Taj ya ce.

Kamal duk ya ruɗe "Kayi haƙuri don Allah. Ban ɓoye da wata manufa ba."

A nutse Taj ya karance shi. Inda ya dosa daban da inda yake tunanin Kamal ya dosa. Kenan akwai abin da Happiness yake ɓoyewa wanda bai sani ba? Shi ne mai dogon bakin faɗa masa komai wato.

"Akwai abin da ka ke ɓoye mana ne banda allergy da asirinka ya tonu?"

Wani gwauron numfashi da Kamal yaja sai da Taj yaji hantar cikinsa ta kaÉ—a. Babu shakka akwai sirrin da bai sani ba. Zai kuma sani ne don Kamal bai isa ya ninke shi baibai ba tunda ya gano da matsala.

"Shi ne. Allergy É—in ne. A China ma ya tashi. Ba ka ga har wani duhu nayi ba?"

"Na gani. Yanzu nake shirin cewa ko man bleaching ɗin naka ne ya ƙare a can?"

Kamal ya taso ya yi kansa. Su ka gama zolayar juna sannan Taj ya koma cikin Happy Taj.

***
Shiru shiru Salwa tana jiran wayar Taj amma ko flashing babu. Hankalinta ya soma tashi. Kwanakin da aka É—iba domin aurensu sun kusa. Ta kira Mami tana ta kuka. Mamin ta ce mata ta taho gida.

"Idan na ƙara nesa dashi ai babu lallai ya tuna dani ma."

"Ki taho nace miki. Zan sake shiri."

Ta samu Salwan ta amince za ta dawo. Sai dai bata san ta ina za ta fara ba. Alh. Mukhtar ya sake kiran Alhaji akan maganar ranar da za su je wajen kawunsa amma ƙememe yaƙi ɗauka. Baya son yi masa ƙarya sannan kuma baya son faɗa masa gaskiya. Idan ya faɗi gaskiyar girmansa da kullum yake tattali ne zai zube. Daga baya ne ya tausaya masa da yawan wayar ya ɗauka ya ce ya ƙara wata guda. Saboda wasu uzurirrika da su ka taso masa. Alh. Mukhtar dai tunda ya sami amsar bawa Mami hankalinsa ya kwanta.

"Nufinsa sai waccan yarinyar ta tare sannan zai auri Salwa?"

"Ina laifi?"

"Ai kuwa akwai shi tunda nima ban zauna da kishiya ba. Ƴata ma daga ita sai miji."

***

Girki ya faɗo kan Inna ranar Juma'a. Da ta haɗa abincin Alhaji Bishir na shigowa ta ce ya kai masa. Kuma bata leƙa ɓangaren ba kamar yadda su ka saba. Mai girki za ta je ta zuba masa abinci su yi hira. Idan ya gama ta aikawa sauran matan cewa ya dawo. Duk za su zo a ɗan taɓa hira sannan su tashi.

Abinci ya yi kusan awa guda Alhaji yana kallonsa. Ga yunwa ga gajiya amma yaƙi zubawa. So yake yaga iya gudun ruwan Zainabu Abu. To dai tun bayan masallaci har la'asar bata shigo ba. Da ya dawo daga masallaci cikin gidan ya shiga ya wuce ɗakinta. Jallabiya ce a jikinsa yana danna counter mai fasalin carbi ta sama.
Babu kowa a falo. Ya shige uwar ɗakin. Yana sanya ƙafa ita kuma tana ɗora waya a kunne. Don ya san da wa take magana ta kira Taj da sabon suna.

"Angon Hamdi"

A tunanin Alhaji ko da gangan ta ɗauki wayar. Hannu yasa ya karɓe. Ganin sunan Taj da gaske sai ya miƙa mata. Ita kuwa ta saka speaker yadda ta saba idan ita kaɗai ce a ɗakin saboda wayarsu bata ƙarewa da wuri.

"Inna kina ji na kuwa?"

"Me ka ce?"

Bai san yadda za ta ɗauki maganar ba amma dole ya đauki shawarar Kamal yau. Faɗan da su ka yi da Hamdi a motarsa Allah ne kawai ya bashi ikon mallakar kansa ya buɗe mata ƙofa ya ce ta fita. Daga zuwa kai mata kati cibi ya zama ƙari. Saboda yau ta iya bakinta bata ce komai ba shi ne ya ce ba a yi mata tarbiyar godiya ba. Ai kamar jira take. Tunda ta buɗe baki ta fara surfa rashin kunya sai da yaji inama bai je gidan ba.

Gyaran murya ya yi "na ce ko za a fasa bikin?"

Alhaji da ya kama hanyar fita sai gashi ya dawo. Inna tayi sauri za ta mayar da wayar iya kunnenta ya harɗe fuska. Taɓe baki tayi a ranta ta ce ana so ana kaiwa kasuwa. Dama taji yadda ya rikice da yaji bashi da lafiya.

"Kai da ka san baka son biki ne yasa ka bari mu ka zazzage asusunmu? Haƙuri za ka yi kawai."

"Uhmmm, Inna ba bikin ba. Auren nake nufi."

Bata san lokacin da ta gyara zama ba.
"Ka fara shaye shaye ne? Auren? Saki fa kenan."

Baya son yawan tada maganar don ransa ƙara ɓaci yake. Amma dolensa ya faɗa mata gaskiya.

"Matsaloli muke ta samu. Kullum sai mun yi faÉ—a."

"Wannan shaiÉ—an ne kawai. Ku dage da addu'a." Ta ce, hankalinta ya soma kwanciya.

"Inna har marinta nayi."

Shiru ya yi yana jiran yaji me za ta ce. Ta kalli Alhaji shi ma ya kalleta.

"Taj ka sameni a gidan Yaya Malam (yayanta na biyu.)"

Ta miƙe ta dubi Alhaji da ya yi tsaye kamar an dasa shi.

"Ka yi min izinin fita?"

"Jeki."

Hijabi kawai ta ɗauka ta fita ta shiga ɗakunan su Hajiya ta ce musu ga inda za ta je. Duk su ka bata saƙon gaisuwa ga iyalin gidan. Direba ta kira su ka tafi. Aka bar Alhaji da tunani. Yadda hankalinsa ya tashi sai da yaji kamar ya ce Taj din yazo gida. Abin da mamaki ace wai shi ne da marin mace. Wace irin tarbiyya Habibu ya yiwa ƴaƴansa?

*

Ƙasa da awa guda uwa da ɗa su ka keɓe a falon maigidan. Taj ya zayyane mata abubuwan da su ka faru. Bata ko tambaye shi me ya kai shi tafiya da Hamdi wurin sana'arsa ba.

"Idan na fahimta da kyau tun daga zuwan Salwa ku ka fara faÉ—an?"

"Haka ne. Na so yi mata bayanin babu komai a tsakaninmu amma ta rufe ido tana gaya min maganganu."

Inna tayi salati sannan ta ce "ya maganar azkar? Kana yi?"

Kai ya sunkuyar "ina yi."

"Ni da kai ne Taj. Ka faÉ—a min gaskiya."

"Allah ina ƙoƙartawa Inna." Ya kuma faɗa don ta yarda da shi.

Aikin gama ya riga ya gama. Ko yana yi dama ba zai hana ƙaddara da ikon Allah faruwa ba. Sai dai ya sauƙaƙa.
GargaÉ—insa tayi akan kada ya yarda su sake haÉ—uwa. Wayar ma ko ita ta kira kada ya É—auka. Sannan mafi mahimmanci ya tabbatar kalmar saki bata shiga tsakaninsu ba.

"Ka tashi ka tafi. Za ka ji ni in sha Allah idan mun gama magana da Yaya Malam. In ma sihiri ne to in sha Allah zai koma ya ci mai shi. Addu'a, sadaka, qiyamul laili da hanyoyin neman kusanci da Allah nake so ka runguma kaji ko?"

Ya gyaÉ—a mata kai kamar yaro.
"Ki yi haƙuri na tayar miki da hankali. Alhaji ya kamata na nema..."

Wani irin tausayinsa ne ya kama ta. Ta dafa kansa tayi masa addu'o'in neman tsari wanda Ayatul Kursiyyu ke kan gaba. Sai da ya tafi ta fashe da kuka. Duk ya wani rame. Kana ganinsa ka san hankalinsa ne ba a kwance ba. A gidan ta zauna har yayan nata ya dawo ta faÉ—a masa. Ya kwantar mata da hankali.

"Kada ki ƙulla sharri akan wanda ki ke zargi. Shi zargi dama bashi da kyau a addini. Zan kira shi ya zo gobe in sha Allah."

"Yaya har zasu yi lafiya kafin bikin?" Ta tambaye shi da damuwa.

"Ke ta biki ma kike wato?"

"A'a, tsorona kada ta tare yadda yake cewa yana jin kamar yayi ta dukanta yaje ya lahanta Æ´ar mutane."

Kwantar mata da hankali ya yi.
"Allah zamu roƙa ba mutum ba. Shi kuma ba ayi maSa gaggawa. Tunda ya ce idan mun roƙa zai bamu to ki saka ranki a inuwa. Ko daga ina matsalar take bata wuce Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi ba."

Da ƙwarin gwiwarta ta fita daga gidan. A ranar yadda ta hana idonta bacci haka ta tada Taj. Shi kuma ya sami kansa da turawa Hamdi saƙo.

(Idan Allah Yasa kin gani kafin safiya ki tashi ki yi sallah da addu'a. Idan akwai alkhairi cikin aurenmu Allah Ya warware mana matsala.)

Sai uku da rabi ta gani da ta tashi fitsari. Ta ɗauro alwala ta zauna tana ta kuka. Zee na jinta amma ta ƙyale. Yaya ce ta bata aikin sanya mata ido saboda kwanakin nan kowa ya san ta canja.

A ɓangaren Alh. Hayatu kuwa, yana ganin shigowar Inna ya kira Yaya Malam.

"Ka biyo sahun É—anka ne?" Malam ya faÉ—i kai tsaye domin duka gidansu dai haushinsa su ke ji.
Chapter 64 · 0% Book details