← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 96

Sashe 42

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah Ya tsare hanya" ta furta kamar an matse bakin.

"Baki roƙa min samun nasarar abin da zai kai ni ba."

"Me zai kai ka?"

"Maganar aurena da wata ƙanwata. Tunda ke ba sona kike ba gara na kawo wadda za ta so ni, nima na so ta."

Yana kallon yadda fuskarta ta haɗe kamar hadari. Ya gimtse harda yi mata sai da safe ya wuce. A mota ta sami damar yin murmushi mai haɗe da dariya. Ya gama ganota. Tana so tana kaiwa kasuwa. Birkita mata lissafi kawai zai yi ta haƙura don kanta ta karɓi zuciyar da ya jima da miƙa mata.

A nata ɓangaren tana shiga gida ta sauke ajiyar zuciya. Wato da ya miƙo takardar da take barazanar nema anya za ta iya karɓa kuwa? Ita kaɗai ta dinga saƙe saƙe. Sai kuma ta kama murmushi da ta tuna maganganunsu. Ko ba a faɗa ba ta san tsokana ce da shi. A ƙarshe dai ta gaji da kokawa da zuciyarta ta amince za ta bashi dama. She will give this pure feeling she has for him a chance.

Ƙofar ɗakinsu ta kama za ta buɗe taji kira daga Abba. Soro ya ja hannunta su ka koma don a nan ne kawai ya san babu kunnen da zai ji su. Ya gama ninke Yaya ya nuna mata babu matsala don ta kwantar da hankalinta. Tsoron da yaji yanzu shi ne na ganin dawowar Hamdi daga wajen Taj. Idan ya bari alaƙarsu tayi nisa ƴarsa zai bari da jidali. Ya rasa abin yi sama da faɗa mata halin da ake ciki. Cikin hikima ya bata labarin Taj tun daga farko har zuwa aurensu. Taji wani irin tausayinsa da kwaɗayin ya daidaita da babansa. Hankalinta bai ƙarasa tashi ba sai da Abba ya faɗa mata tsakaninsa da Alh. Hayatu da yadda aka yi aurensu. Da kuma sharaɗin da ya gindaya masa.

"Ko mahaifiyarku ban sanarwa gaskiya ba. Shi kuma Taj nayi imanin ba zai taɓa sakinki ba idan yaji daga ina umarnin ya fito. Zaɓi ɗaya ya rage min..."

Kuka take a lokacin ta ce "mene ne Abba? Me za mu yi?"

"Ki nuna masa na kya sonsa. Na tabbatar idan yayi tunanin da gaske kike zai sauwaƙe miki. Ni kuma zan baki goyon baya. In ta kama sai ya fita daga rayuwarmu bakiɗaya ya sami salama."

"Abba kada ka saka kanka a ciki. Yanzu banda Æ´an uwansa kana cikin waÉ—anda yake yiwa kallon uba. Ya ma faÉ—a min. Idan ka juya masa baya it will break his heart."

"Ki yafe min Hamdiyya. Koma mene ne ni na cuceku. Rayuwa tana gaba amma kullum ana yanke muku hukunci da abin da na shuka a baya."

Zuciyarta rauni tayi mara misaltuwa. Bayan shuɗewar lokaci tana gudun mahaifinta yau da kanta ta rungume shi tana kuka. Shi kaɗai yake ta haɗiyar abubuwa domin farincikinsu amma kullum ƙorafi take yi.

"Abba ka yafe min nima. Ba zan ƙara faɗin aibun sana'arka ba. Kuma in sha Allahu babu mai jin zancen nan. Zan yi ƙoƙari in ga ya haƙura da auren da kansa."

"Allah Ya yi miki albarka. Allah Ya bamu ikon sakawa Taj da abin da yafi buƙata a rayuwarsa wato albarkar duka iyayensa."

Amin ɗin a zuci ta iya faɗinta. Ta shige ɗaki ta kwanta tana zubar da hawayen damuwar da tafi ƙarfin shekarunta
RAYUWA DA GIƁI 19

Batul Mamman💖

***

Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haɗuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal ɗin bai ɗauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ƙalau ba. Abba ƙaninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba.

"Happiness ya fito sallar asuba kuwa?"

Abba ya ɗan wartsake idanu "ya fito amma yau ya riga kowa baro masallacin. Saƙo ne?"

"Ɗan leƙa min shi please."

Abba baya son fita don bacci ne sosai a idonsa ya ce "Ya Taj ya dai kamata ku rage wayar asubar nan. Kai kayi aure, idan shi ma ya yi wallahi za ku dinga samun matsala da matanku."

"Za ka tashi ko kuwa?" Taj ya ɗan ɗaga murya da ƙoƙarinsa na ɓoye yadda ya damu.

Yana jin ƙunƙunin Abba har ya isa ƙofar ɗakin Kamal. Sallama ya haɗa da ƙwanƙwasawa.

Da ƙyar Kamal ya iya buɗe jajayen idanunsa da su ka kumbura kamar wanda ya kwana yana kuka. Jikinsa gabaɗaya ciwo yake yi. Kansa kamar ana sara guduma saboda azabar ciwo.

"Waye?" Muryarsa ta fito a dusashe.

"Ya Taj ke nemanka." Abba ya faɗa yana saita bakinsa da ƙofar yadda za a ji da kyau "na sanar dashi. Can I go back to bed now?"

"Thanks" Taj ya ce da kulawa.

Wayar Kamal ya sake nema. Yadda yaji muryarsa ya tayar masa da hankali. Amma Kamal ɗin ya tabbatar masa da mura ce ta kama shi da zazzaɓi.

"Allah Ya ƙara sauƙi. Ko na bar tafiyar yau muje asibiti?" Hamdi ce ta faɗo masa ya yi murmushi.

"Ka tafi kafin Amma ta sauka a garin nan duk mu shiga tara."

"Don Allah ka je asibiti dai. Bana so ana raina mura da zazzaɓi. Ciwukan gaske ne."

"To doctor." Kamal ya zolaye shi.

Suna gama wayar ya ɗauki ƴar jakarsa ta goyo (backpack) wadda ya sanya duka abubuwan buƙatarsa a ciki. Ƙananan kaya ya saka ya koma matashi sosai. Haramar tafiya ya yi sai ya tuna yadda Kamal ya damu kada Ahmad yaji babu daɗi akan halin da Salwa ke ciki. Lokaci ya duba akwai đan saura. Ya fito falo ya kira wayar Ahmad ɗin.

"Yaya na shirya zan tafi."

Ahmad ya miƙe da sauri. Dama bai koma bacci ba tun sallar asuba.

"Bari na zo na kai ka airport."

"Ka barshi. Zan sami adaidaita sahu."

Fitowa Ahmad ɗin ya yi. Su ka gaisa sannan ya miƙa masa key ɗin motar Kamal.

"Incase ban sami dawowa akan lokaci ba, ina sa rai jibi motata za ta iso. In bawa mutumin numbarka sai ya kawota nan ya ajiye?"

"Da ina zai kai?" Cewar Ahmad yana zura muƙullin a aljihun wando.

Zama Taj ya yi ya buƙaci yin magana da shi na mintuna kaɗan.

"Yaya akan Salwa ne."

Ahmad ya ɗan ɓata rai "ka cire lamarin yarinyar nan daga gabanka ka fuskanci matsalolinka."

"A'a Yaya. Idan da kara nima ƙanwata ce. Ba kuma zan so ta shiga irin wannan yanayin akan wani ba."

"Shin ka taɓa yi mata magana ko nuna mata alamun soyayya ne?"

Ya kaÉ—a kai da sauri "a'a."

"To ka gani. Rigima ce kawai irin ta ta. Tun abin nata bai yi nisa ba na bata shawara taƙi ji. Ya take so ayi mata? Ana forcing soyayya ne?"

Taj dai duk nauyin yayan nasa yake ji. Sai yanzu ya gane manufar Kamal.

"Duk da haka ni dai ka rarrasheta. Allah Ya bata wanda ya fini. Mafi alkhairi."

"Kada ka damu. Dama a gidansu babanta ya yi mata miji. Amma kaga don fitina taƙi komawa gida. Wai tana jiran service kuma."

Dariya su ka yi su biyun. Ahmad ya kwantar masa da hankali. Da ace soyayya su ke yi yanzu ya gujeta shi ne zai zama rashin kyautawa. Amma tunda hakan bata taɓa faruwa ba babu mai ɗora masa laifi. Ahmad ya sako jallabiya ya kai shi airport tunda jirgin sassafe zai bi.

*

Yadda Amma taga rana jiya haka taga dare. Wajajen ƙarfe biyar ta sami labarin auren Taj daga wajen matar ɗaya daga cikin ƴan uwanta. Ba don shekaru ba da tabbas ƙaryata ta za ta yi. Ta dai daure su ka gama wayar. Yaya Babba ta fara kira ya ce mata haka ne. Ji tayi tamkar an kwaɗa mata guduma. Taj ya yi aure bata sani ba. Kuma har dare bai kira ba. Haka ta ƙarasa wunin ranar cike da fargabar kada mutan gidan su ji.

Da taga Allah Ya taimaketa har bayan Isha babu wanda ya ce komai shi ne Daddy na gama cin abinci ta ce masa tana son zuwa Kano gobe.

Kamar Anti jira take ta shigo falon a lokacin "Hummm, Maman Ihsan kenan. Kin gaji da ɓoye ɓoyen?"

Gabanta faÉ—uwa ya yi amma ta dake.
"Ɓoyo kuma? Wani abin ne ya faru?"

"Kada ki raina min hankali mana. Za ki ce ba da saninki Taj ya yi aure bane? Ko kin zata bamu sani ba?"

Anti ta faɗi da matuƙar ɓacin rai. Taci burin suruka da shi saboda ya haɗa dukkan abin so. Kyau, kuɗi, suna da kuma kyawawan ɗabi'u. Idan Anisa ta sami miji irinsa ta wuce raini a wurin kowa. A dangi ma sai an dinga bata girma na musamman.

"Yadda ki ka ji maganar nan nima haka na ji ta. Kuma dalilinta nake son zuwa Kanon ma kenan. Babu wanda ya neme ni. Sai aure kawai naji."

"Ai in duk jikina kunne ne ni ba zan yarda ba. Yaudara ce dai an yiwa Æ´ata."

Ran Amma ya soma ɓaci ta ce "Ita Anisan ce ta ce ya yaudare ta?"

Hankali kwance Daddy ya gama cin abincinsa sannan ya tsawatar musu.

"Idan kuma ban isa daku ba sai ku fita ku ƙarasa."

Amma kwantar da murya tayi ta bashi haƙuri sannan tayi masa bayanin rashin sanin auren.

"Idan haka ne kuwa kema bai mutuntaki ba. Kuma ya nuna bai san alkhairi ba."

Wani irin kallo Amma ta yiwa Anti. Bata son cigaba da rigima a daren nan amma take taken Antin so ta a cigaba da maganar har Hajja ta ji.

Daddy sallamarsu ya yi akan su bar zancen zuwa washegari. Anti na fita ta koma ɗakinta inda ta sami Anisa a zaune da waya a hannu. Zuciya ta raya mata Taj take kira ƙila yaƙi ɗauka. Ai kuwa ta tashi ta nufi ɗakin Hajja tana kuka ta karanta mata ƙarya da gaskiya. Wani abin idan ta faɗa sai Anisa ta riƙe baki don mamakin yadda uwa take yanko ƙarya bisa son zuciya.

"Damuwata yanzu yadda ta saka shi a ranta."

"Anti don Allah ki daina kuka. Ni wallahi na haƙura."
Chapter 42 · 0% Book details