← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 96

Sashe 10

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kansa sake ƙullewa ya yi amma babu halin tambaya. Sai ma ƙarin bayani da Alhajin ya yi masa cewa ya bari jibi zai kai shi da kansa don ya sami damar hađa kayansa.

"Ba na kuma son jin zancen nan a bakin kowa har matan gidan don na san za su so hanaka tafiya."

"To Alhaji" ya amsa a ladabce.

Kamal kaÉ—ai ya sanarwa abin da yake faruwa. Da taimakonsa ma ya gama haÉ—a kaya. Ranar da za su tafi Alhaji ya faÉ—a masa zai dawo daga kasuwa da azahar sai ya kai shi.

"Happy" Kamal ya kira Taj suna zaune a É—aki "ba ka mamakin chanjin ra'ayinsa?"

"Ni fargaba ce ma tafi damuna. Naga ko kaÉ—an bai nuna fushi ba duk da Allah Ya sani ba da wannan manufar na kai wa Baba Yaya takardun ba."

"In sha Allahu ma babu komai. Dama tsoron da naji da ka ce wai ya ce kada a faÉ—awa kowa."

Bugun ƙofa gami da sallamar Bishir ce ta hana Taj sake yin magana. Saƙon Alhaji ne yana jiransa a mota.

A take yaji gabansa ya yanke ya faÉ—i. Ya tashi jiki a mace sai Kamal da Bishir É—in ne su ka É—auko masa kayansa. Kowa yaga ana loda kaya a booth É—in Alhaji sai ya yi mamaki amma an rasa mai tambaya don babu fuska.

"Ka shiga ka yiwa uwayenka sallama." Alhaji ya umarce shi da ya fito.

Inna bata gida. Sai su Hajiya. Su ka biyo shi waje kuwa su na tambayar Alhaji me ya faru Taj zai koma gidan Yaya Babba. Cewa ya yi su koma. Idan ya dawo zai yi musu bayani.

A mota haka su ka tafi ko numfashi mai sauti Taj baya iya ja. Kamar tare su ke don ana buÉ—e musu gate su ka ga Yaya Babba yana fitowa daga mota. Dawowarsa kenan daga office. Yayi mamakin ganin Alhaji kaÉ—ai ko direba babu da Taj. Sai dai wannan ba komai bane a yayin da yaga ya buÉ—e booth Taj na sauke kaya.

"Hayatu me yake faruwa ne?" Ya matso kusa dasu don jiran su gama su shigo ciki ma ba zai iya ba.

Alhaji ya dubi ɗan uwansa yana mai baƙincikin yadda yayi masa katsalandan a cikin harkar gidansa. Shi kuwa Taj yana jin haka wani irin tsoro ya kama shi. Kenan Baba Yaya ba shi ya nemi ya dawo gidansa kamar yadda Alhaji ya faɗa masa ba.

"Ga Taj nan. Suna na ne kawai addini bai halatta min cire masa ba amma daga yau na bar maka shi."

Yaya Babba ya girgiza da furucinsa matuƙa. Fuskar ƙanin nasa a haɗe take kamar baƙin hadari.

"Me ya yi zafi? Don na ce zan mayar dashi makarantar da yake so?"

"Ai ban hanaka ba tunda ka isa. Shi ma da na isa dashi ina mai umartarsa kada ya dawo min gida."

"Hayatu bana son rashin hankali." Yaya Babba ya fara faÉ—a.

"Ai kuwa bai kamata ka kira biyayyata gareka da rashin hankali ba." Ya cigaba da magana kai tsaye babu tauna lafuzza don yau dole ya amayar da ɓacin ransa "saboda gudun shiga haƙƙi ban taɓa yiwa kowa iko da ɗansa ba. Amma sau biyu Yaya kana bawa yaron nan abin da nake son hanawa. Hakan ba komai zai janyo min ba illa baƙin jini daga gare shi. Koda yayi min biyayya zata zama bisa tursasawa ba don son rai ba. Maganin kar ayi, kar a soma. Tunda ka nuna masa za ka iya bashi abin da na hana sai ka riƙe shi na bar maka."

"Ni kake faÉ—awa magana Hayatu? Ashe zumuncinmu bai kai nayi umarni ko hani ga tsatsonka ba tare da ka É—aga kai ba?" Yaya Babba ya faÉ—i yana mai jin ciwon maganganun da kunnuwansa ke ji.

Musayar yawun da suke ba ƙaramin tadawa Taj hankali tayi ba. Ya durƙusa a ƙasa yana kuka yake roƙonsu da su yi haƙuri.

"Wallahi ba zan sake tada zancen nan ba har abada. Ku yafe min don Allah."

"Baka isa ba! Karatu ko ba kyauta aka baka ba sai kayi shi. Tunda ka iya raina ƙoƙarina akanka ka haɗani da ɗan uwana dole ka cika burinka."

Taj na kuka ya riƙe ƙafar mahaifinsa yana roƙon yafiyarsa. Yaya Babba ma idanunsa sun kaɗa sun yi ja. A haka ya ja girmansa don gudun rigima ya bashi haƙuri.

"Kayi haƙuri. Ban yi zurfin tunani ba, da ban shiga huruminka ba. Don Allah ka ɗauki ɗanka ku tafi."

"Na gama magana. Wallahi daga yau Taj ya bar gidana..."

"Kada ka rantse." Ya yi nufin dakatar dashi sai dai ya makara.

Suna ji suna gani Alhaji ya juya ya shige motarsa yayi gaba. Taj ya bi motar a rikice kafin ya sami wuri kusa da akwatinsa ya zauna cikin wani irin yanayi na rashin kuzari. Zuciyarsa wani irin ƙunci kawai ke yawo a cikinta. Bai san lokacin da aka kwashe kayansa ba. Sai hannuwa da yaji na ɗan uwansa, ƙaramin ɗan Yaya Babba wanda ya kasance sakonsa ya tayar dashi. Da ƙyar ya yarda ya shiga gidan. Mummy tana kuka tana bashi baki tare da alƙawarin gobe Yaya Babba zai mayar da shi.

***

A wannan rana ko gyangyaɗi Taj bai samu ba. Kuma haka ta kasance a ɓangaren Baba Yaya da Alhaji da Inna. Don bayan ta dawo gida da ya sanar dasu hukuncin da ya ɗauka har suma tayi. Gidan ya rikice da koke koke. Iyalin Alh. Hayatu su ka taru su ka juya masa baya daga matansa har ƴaƴansu. Hakan kuwa bai yi masa komai ba face ƙara tsanar turbar da Taj yake son bi. Da kuma abin da Yaya Babba yayi masa.

Washegari duka Æ´aÆ´an Marigayi Alh. Sule su ka taru a gidansu dake Soron É—inki inda mata guda É—aya da ta rage musu a matsayin uwa take. Ita ce mata ta uku cikin matansa. Zama irin na da yasa ita da Æ´aÆ´an sauran abokan zamanta su ka cigaba da zumunci tamkar lokacin da mahaifinsu yake da rai.

Ita Yaya Babba ya kaiwa ƙarar Alhaji tun a jiya. Tasa aka kira mata kowa dake kusa. Amma ma dake nesa dama ta iso kwana huɗu da su ka wuce hutun shekara. Tana Abuja da niyar tahowa bayan sati guda. Amma kiran Gwaggo yasa ta biyo jirgin ƙarfe tara na safe.

Bayan an zazzauna Yaya Babba ya mayar da iya abin da ya faru ta ɓangarensa. Tun daga wayar da Mama ta yiwa Mummy da suna India har zuwa yadda ta kasance jiya. Aka tambayi Alhaji sai kaɗa baki ya yi ya ce bashi da abin sake tofawa.

"Yanzu Hayatu har kayi girman da za ka nuna mana iko akan ƴaƴanka?" Yayarsa mace mai bin Yaya Babba wadda daga ita sai shi tayi maganar da ƙwalla a idonta "na zata za ka yi farinciki da zumuncin da muke dashi wanda mu ka ɗora ƴaƴanmu da jikoki. Kai ba abin alfaharinka bane ace ɗanka yaje neman sauƙi a wajen ɗan uwanka? Shi kuma bai bashi kunya ba ya share masa hawaye."

Ransa sosuwa ya yi da har suke ganin laifinsa.
"A cikinku akwai wanda zai bar ɗansa namiji ya ɓata lokaci a jami'a yana koyon girki da yadda ake sarrafa kayan abinci?"

"Me zai hana tunda ba haramun bane" wani ƙaninsa ya amsa kai tsaye. Wasu duk su ka amsa da za su iya.

"Wallahi ƙarya kuke yi. Ni ban taɓa ganin namiji a arewa mai sana'ar abinci ba wanda baya abin mata."

"Saboda al'adar bahaushe ta mayar dashi aikin mata kaɗai ba. Amma a kudu da sauran ƙasashen duniya maza nawa ne su ka yi fice da girki kuma in ba faɗa su ka yi ba sai ka rantse ma ƴan dambe ne."

"Ni yanzu me kuke so daga gareni?"

Gwaggo ta dube shi. Haƙiƙa akwai ciwo wurin iyaye idan ƴaƴansu su ka ƙi bin umarninsu. Gashi mutum mai aƙida wanda baya son ko yaya aga gazawar nasa. Kuma dole yanzu yaga kamar an haɗe masa kai. Don ko ita idan zata yi rantsuwa ta san babu kaffara da matuƙar wahala in ka cire Yaya Babba da Amma a sami mai barin ɗansa namiji ya yi wannan karatun.

"Hayatu kaje gidan Jafaru ka É—auko É—anka maganar nan ta mutu daga yau."

"Ai nayi rantsuwa Gwaggo. Akan Taj wallahi ba zan yi kaffara ba."

Cikin fushi Yaya Babba yace "Nima kuma wallahi ba zan zama silar raba É—a da iyayensa ba. Idan rashin albarka ya bishi a dalilinka duniya ni za ta zaga."

Gwaggo dai gajiya tayi da basu baki ta kama hawaye tana cewa don babansu baya duniya shi yasa su ke yi mata haka.

Amma da bata ce uffan ba tun farkon zamansu ce ta katse musayar yawun da suke.

"Gwaggo ki zama shaida. A gaban kowa duk sun yi rantsuwa ba za su zauna da Taj ba. To ni ina so kuma dashi zan koma. Zan taƙaita hutuna mu baku wuri ku sha iska."

Kallonta kowa ya kama yi kafin kuma mazan su nuna a gidansu zai zauna.

"Jamila zai bi domin babu amfanin ya zauna a nan kowa yana yi masa kallon wanda uba ya kora." Gwaggo ta kashe maganar.

"Gwaggo ina so ki min shaidar ƙarshe. Yadda kowa baya son a shiga abin da ya shafe shi da đansa to nima kada wanda ya shigar min gonata. Zan yiwa Taj abin da zan yiwa ɗan cikina tsakani da Allah."

Kafin kowa ya sake magana ta tashi ta fice daga gidan gabaÉ—aya.
Chapter 10 · 0% Book details