← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 96

Sashe 29

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Halin da ta shiga yana ci wa Abba da Yaya tuwo a ƙwarya. Gani su ke kamar sanadiyarsu rayuwar ƴar aminansu ta gurɓace. Yayinda su Baba Maje kuma su ke ganin dubunta ce ta cika. Halayen da take ɓoyewa su ka bayyana. Ba don abin da ta yiwa Hamdi ba da haka za ta yi ta ha'intarsu ƙila har gidan miji tana rayuwa biyu ba a sani ba.

Ummi ta sake É—aura É—ammarar watsa rayuwar Hamdi a duk lokacin da nata auren ya tashi. Kuma tsakin da tayi ba komai ya janyo ba sai takaicin lokacin ramuwarta da bai yi ba.

***

Kimanin sati uku kafin bikin Sajida aka gama komai da ya dace a HAPPY TAJ. An kashe kuɗi domin ƙawata wajen yadda zai janyo mutane. Taj da Abba da kansu su ka dinga yiwa mutane gwaji idan sun zo neman aiki. Banda yaran Abba, sai da su ka ƙara mutane masu ayyuka daban daban a kitchen ɗinsu. Girki, wanke wanke, serving abinci, waiters, cashiers da masu yin fruit juice, mocktails da icecream. Gabaɗaya kitchen ɗin maza ne. Sannan ya nemi inda za su dinga sayen kayan abinci. Komai ya tafi cikin tsari. Ƙannensa Bishir da Abba su ya damƙawa ragamar tabbatar da kayan buƙatar kitchen ba za su yanke ba. Sun daidaita da masu kayan masarufi na kasuwa akan wannan. Spices kuma na recipe ɗinsh za su dinga haɗawa saboda haka raw ɗin kawai su ka nemi mai kawowa. Dankali da kayan miya kuma fresh masu kyau da tsafta daga wajen ƙawar wata sister ɗinsu Rumanatu mazauniyar Jos (08065530483) za su dinga saya. Ya zamana dai babu inda su ka bari haka nan.

Masu naman tsire ko gashi su ma interview da gwaji aka yi musu. Iyawa kaɗai bata da garanti sai an duba tsaftar mutum da ingancin kayansa. Haka kuma aka yi a ɓangaren kayan fulawa. Saboda kawai Taj yana son ɗaukar Hamdi sai ya ce bakery ɗinsu mata za a saka.

Application babu kama hannun yaro. Da ƙyar su ka zaɓa don babu laifi a Kano akwai masu sarrafa fulawa daban daban da kayansu suke da inganci. Wata ƙanwarsa da ta dinga zuzuta masa ƙawarta Zahra wadda aka fi sani da Donutfairy (08065156303), dole yace a nemota. Ya ɗanɗana doughnut, banana bread da youghurt ɗinta. A take ya nemi signing contract da ita tunda matar aure ce. Aka ƙayyade adadin abin da za ta dinga kawowa kullum da farashinta.

Ɓangaren Kamal ma boutique ya tashi sai wanda ya gani. Garden da wurin wasan yara duka an gama zuba ma'aikata. Ranar Juma'a aka yi sauka domin kore kowanne shaiɗanci da neman albarka daga Allah. Sai kuma aka sanya sati mai zuwa a matsayin ranar buɗe restaurant ɗin. Anyi ta sanya talla ta gidajen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta. Akwai discount ga mutanen da za su zo a wannan rana. Ga kyaututtuka na yara domin za su yi gasa da wasanni.

Garin Kano ya É—auka. Ko ina ka zaga ana jiran ranar buÉ—e Happy Taj.

*

Gidan Alh. Hayatu ya hargitse da shiryawa wannan rana. In ka duna status da stories ɗin ƴaƴa da jikokin gidan ds su ka tasa, gabaɗayansu abin da su ke ɗorawa kenan. Sai kuma hoton Taj sanye da wasu fararen kaya na girki ya riƙe irin kaskon nan na zamani mai ɗan zurfi da dogon mariƙi a hannu ɗaya, sai kuma cokalin juyawa a ɗaya hannun. Harɗe hannuwansa ya yi dasu irin yanayin tsayuwar Black Panther idan sun yi alamar Wakanda Forever. Yayi matuƙar kyau da kwarjini a hoton. Ƙaryar mutum ya gan shi ya danganta shi da mace. Murmushin fuskarsa yafi komai tafiya da hankalin mai kallo.

Yadda ake ta shiri da farinciki a gidan Alh. Hayatu, haka ma su Sajida su ke ta murnar wannan ɗaguwar daraja da mahaifinsu zai samu idan ya fara aiki a Happy Taj. Har anko Abba ya yiwa ƴaƴansa. Yaya kuwa nata kayan sun fi nasu tsada ma. Kowa ya yi murna banda Hajiya Hamdi. Gani take ba a rabu da Bukar bane an haifi Habu. Abbanta zai baro local ƴan daudu su Ƴar Ficika, ya koma hannun international ɗan daudu wai shi Taj. Ita dai da tana da iko da ta hana shi wallahi. Har mamakin yadda kowa na gidan yake ƙaunar Taj ɗinnan take yi.

***

Komai nisan dare gari zai waye. Bayan shafe shekara guda da Æ´an watanni, gobe ne ranar da za a buÉ—e Happy Taj.

Tunda aka saka rana Hajiya, Mama, Umma da Inna duk kawaicinta su ke roƙon Alhaji da ya yi musu izinin zuwa. Amsar da ya basu ita ce ba zai hana kowa fita ba amma idan sun tafi kada su dawo. Mama da Inna har kuka su ka yi. Ya ce ai bai hana su ba. Kowacce tana da damar zuwa amma tabbas bai yarda su dawo gidansa. Hajiya ta kai ƙararsa wajen Yaya Babba sai dai dattijon ya ce ba zai ƙara yiwa rayuwar ƙanin nass katsalandan ba. Har yau yana ganin laifinsa ne korar Taj da Alhaji ya yi.

Suna ji suna gani Æ´an uwansu da na mijinsu da Æ´aÆ´ansu duk zasu amma ya yi musu shamaki. Walwala da farinciki sai su ka yiwa gidan kaÉ—an.

Taj bai fasa sanar da Alhaji duk abubuwansa ba kamar yadda Amma ta koya masa. Saboda haka duk wani abu da ya danganci restaurant ɗinnan tamkar dashi ake yi. Har hotuna da bidiyo yake tura masa. Bidiyon ƙarshe da aka yi kamar film na minti ɗaya da rabi shi yafi komai ƙayatarwa. An bi ko ina a wurin daga gate har ƙurya. Ga ma'aikata da shi kan shi CEO Taj cikin farinciki suna ta aiki a wajen. Ya kwanta tun wajen tara na dare sai ya kasa bacci. Kewar ɗan nasa tayi masa wani irin kamu. Ya yi kusan awa biyu yana juyi a kwance ƙarshe ya tashi ya ɗauki muƙulli ya fice.

Kowa ya yi mamakin fitarsa a wannan lokacin. Kamal zai bi shi Hajiya ta hana.

"Wallahi kewar Taj yake. Ku rabu dashi. Bashi da aiki sai kallon waya. Rannan da kunnena naji muryar Taj a wannan bidiyon da yara ke yawan kunnawa. Tunda girman kai ya hana shi dawo dashi gida sai ya yi ta wahala shi É—aya."

"Hajiyarmu yau da kanki?" Abba ya faÉ—i da mamaki. Don ita bata da zafi kamar sauran matan.

"Fita idona ni."

Ta koma É—akinta ta kwanta. Sauran matan ma duk su ka watse. Inna ce da ta shiga É—aki ta dinga addu'ar Allah Ya daidaita lamura tsakanin uba da É—an.

To dai Alhaji bai zame ko ina ba sai Happy Taj. Shi da ya jima bai yi tuƙi ba ko a jikinsa yau. Ga dare amma haka ya fito ya tsaya a bakin gate ɗin. Ya kalli ginin da wani irin pride yana jinjina kai. Tabbas yana cikin farinciki. Taj bai lalace yadda ya zata ba. Kuma a yau ya ɗauki sama da mutum ashirin aiki da kuɗin halalinsa.

"Allah Ya yi maka albarka" ya furta a zuciyarsa.

Ya kai hannu ya dafa gate É—in. Jiniya har ta fara wiii, wiii sau biyu sai É—if ta É—auke. Alh. Hayatu ya sake dafa gate É—in a karo na biyu yaji shiru. Addu'a sosai ya karanta ya tofa a jiki sannan ya koma mota ya tafi.

Taj dake ciki yana ƙarasa wasu cike ciken takardu ya share ƙwalla bayan tafiyar Alhajin. A gaban kwamfuta yake aikin inda take nuna masa ko ina da taimakon cctv. Yana ganin zuwan Alhajin ya ajiye aikin gabansa. Zuciyarsa ta shiga wani irin bugu mai tsanani. Ya tashi zai fita sai kuma ya fasa. Yana gudun kada zuwan nasa ya janyo wata matsalar tsakaninsu. Shi ya kashe jiniyar alarm ɗin tsaro da Alhaji ya taɓa gate ɗin. Yana ganin ya tafi ya fito ya ɗora hannunsa a inda ƙiyasinsa ya nuna mas Alhajin ya saka nashi ya sumbata. Wannan abu ya sanya shi farkawa da wani irin farinciki, jindaɗi da annashuwa washegari.

*

Amma da iyalin gidanta harda Hajjo a Kano su ka kwana. Da misalin ƙarfe biyu da za a buɗe gate ɗin ita da Anti da ƴaƴansu suna sahun gaba. Iman ɗinta dake Lagos ma ta zo da ƴaƴanta. Ga Anisa da Anti takanas tasa aka kira mai kwalliya ta gyare mata fuska. Ita kanta wani irin nishaɗi take ji a zuciyarta. Idan Allah Ya bata Taj, sai tafi kowa murna.

Ya Ahmad ma da iyalinsa suna kan layi. Anti Zahra da su Hayat an sha ado kamar za su biki. Salwa kuwa musamman Mami ta aiko mata da sababbin kaya daga Bauchi. Light make up tayi amma ba yadda za ayi ta wuce lafiyayyen namiji ya kasa yi mata kallo na biyu.

A cikin wani adaidaita sahu dake fake a wurin kuwa Hamdi ce take cika tana batsewa. Sajida da su Zee sun fito suna tsaye a bakin gate. Yaya kuwa duk yadda Abba ya kaɗa ya raya taƙi zuwa. Wai abin yara ne. Sai dai shi da ya santa yafi kowa fahimta. Har kullum bata fiye son su fita lokaci guda ba. A ganinta suna zubar da darajar ƴaƴansu ne. Uba ga yadda yake, ita kuma tun ƙuruciya har da girmanta ba a rasa yaran dake kwaikwayon tafiyarta. Sai ta zaɓi ɓoye kanta a gida don kawai ta tsira da mutumcinta.

Yau Abba har fushi ya yi amma taƙi. Wurin sana'arsa da take sa ran samun ɗaga darajarsa bai dace da ita ba. Yaran nasu basu san wainar da ake toyawa ba. Da Hamdi ba za ta taɓa yarda ta fito ba. Su duka suna ƙaunar Yaya kuma basa jin kunyarta.

"Ya Hamdi ki fito mana" Halifa ya dawo ya kuma kiranta don shi baya fushi. Su Zee ne su ka gaji da jiran ta sauko su ka yi tafiyarsu.

Da ƙyar ya samu ta fito. Haka kawai da su ka isa gate ɗin ta fara jin yanayinta ya sauya. Ita da bata son zuwa sai farinciki ya ziyarceta har tayi murmushi bayan ta saka ƙafarta a ciki. Tunda ababen hawa basu shiga saboda cikowa, a hagunta Salwa ce take shigowa, a damanta kuma ba tare da ta kula ba Anisa ce da su ka taɓa haɗuwa a Abuja watannin baya.

"Assalam alaikum wa rahmatullah"
Chapter 29 · 0% Book details