← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 96

Sashe 45

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya kake so nayi da kai? Ni a rayuwata babu abin da na tsana kamar ɓoye ɓoye."

Ya ɗage gira ɗaya "a taƙaice dai kin tsaneni."

Shan kunu tayi "ban ce ba."

"Don Allah ki yi haƙuri." Ya tashi zaune "Zan iya tafiya?"

"Jikin naka..."

Sallama aka yi, kafin ta amsa Alhaji ya turo ƙofar ta buɗe gabaɗaya su ka shigo tare da Abba. Kai idan kaga fuskar shi sai ya baka tsoro. Hannuwan babbar rigarsa sun sauko amma yau ya manta da wani matsayi. Ɗansa kawai yake son gani.

"Me ya same ka?" Ya kalli Dr. Mubina "Doctor me ya same shi?"

Kamal bai bari tayi magana ba don ya kula ganin Alhaji ya kiÉ—ima ta.

"Allergy ne Alhaji."

"Kai ne likitan?" Ya sake dubanta idanunsa na daÉ—a firgita ta "ina jin ki."

"Allergy ne kamar yadda ya ce."

"To an gano mene ne jikin nasa baya so domin a kiyaye?"

"A'a, muna dai kan..."

Kafaɗarsa Alhaji ya riƙe "Kai tashi. Visar ina da ina gareka yanzu da ba su ƙare ba?"

Mubina taga yadda bakinsa ya kasa tattaro amsa saboda sanin kafiyar Alhajin.

"Don Allah ka ɗan ƙara mana lokaci Alhaji. Lifestyle changes muke ta gwadawa. In sha Allah a hankali zamu gane trigger ɗin."

"A hankali fa ki ka ce doctor. Jira zan yi har sai wani mummunan abu ya same shi?"

"Kayi haƙuri. Rashin bamu dama yana daga cikin abubuwan da ke sa a dinga ganin kamar bamu san aikinmu ba."

Yadda ta tare shi kai tsaye ta bashi wannan amsa sai ya sanya shi murmushi. Yana son mutane masu confidence.

"Ya sunanki ne?"

"Mubina...Mubina Sa'id Kibiya."

Fuskar Alhaji washewa tayi. Shi ne harda dariya irin tasu ta manya.

"Ikon Allah. Ke ƴar wajen Marigayi Dr. Sa'id ce?" Ta gyaɗa kai a hankali "kai masha Allah. Ƙasar nan ba ƙaramin rashi tayi ba. Arewa tayi rashin jajirtaccen likita. Allah Ya masa rahama."

Idanun Mubina da ƴar ƙwalla ta ce "amin."

Sakin jiki Alhaji ya yi su ka gama magana ya ce ya bata damar yiwa Kamal dukkan abin da ya dace domin samun sauƙinsa. Ya ƙara da cewa baya so ta sallame shi a yau. A kumbure gaɓoɓinsa su ke duk da a haka Abba ya ce wai ya saɓe. Fita su ka yi da Abban zai raka shi. Kamal kuma Mubina ta ce lallai ya koma ya kwanta.

"Ai dole na. Idan na koma gida yau ba za mu ƙare da daɗi ba."

"Gaskiya yana son ka." Ta faÉ—i tana murmushin yadda uban ya nuna kulawarsa akansa.

"Ai baki ga komai ba. Sai Æ´arsa na labour room ake gane waye Alhaji. Wallahi in dai ba baya gari ba da shi ake zaman asibiti daga lokacin da yaji an tafi haihuwar har a fito da baby."

"Kun ji daɗi. Shi ne kake ɓoye masa halin da kake ciki?"

"Duk tsaurinsa yana da mugun rauni akan Æ´aÆ´a. Sanin matsalata alhalin babu abin da zai iya yi min damunsa kawai zai yi."

Haƙura Mubina tayi. Ta kula da indai izinin Kamal take jira babu wani cigaba da za a samu wajen binciken sama masa waraka. Zaɓi guda ya rage mata. Za kuma tayi amfani dashi in sha Allahu.

Bata tashi ƙara sanin wane irin gida ya fito ba sai da taga matan gidansu da ƴan uwansa suna ta tururuwar shigowa. Ɗakin ba ma zai ɗauki rabinsu ba domin kuwa harda jikoki. Wannan yasa ta tunani akan hanyarta ta gida. Yanzu a ce duk yawan nan nasu babu wanda jininsa da na Kamal ya zo daidai?

***

Taj bai tashi sanin a asibiti Kamal ya kwana ba sai da safe. Da fari ya yi niyyar komawa gidan Amma domin su gaisa da Daddy. Sai ga wayar Naja tana sanar dashi labarin da ta samu daga gida. Ya duba wayarsa babu wanda ya kira shi. Jinjina kai ya yi ya ɗauki jakarsa ya fita. Allah Ya taimake shi bai haɗu da ɓacin rana ba. Jirgin ya tashi akan lokaci. Kai tsaye asibitin ya wuce daga airport. Ya samu ana ta rikici a bakin ƙofa tsakanin wata nos da ƴan uwansu mata. Ta tare ƙofar ta hana mutum biyar shiga. Na ciki su bakwai su ma tayi tayi sun ƙi fitowa. Ana ƙorafin sun yi yawa a ɗakin, su kuma sun ce babu wanda ya isa yasa su fita daga wajen ɗan uwansu.

"Ga wani ma nan ya shigo. Shi daga wani garin ma yake." Autar gidan ta faÉ—i a tsiwace.

"To ko ma dai waye zuwa za ku yi ku fita. Idan ba haka ba zan sanar da na gaba dani. Doka ce ba a son a wuce mutum uku a ɗakin mara lafiya." Nos ɗin ta ce da takaicin waɗannan mutane. Bakiɗayansu kamar masu kan dutse. An rasa mai lallaɓata ta haƙura ko kuma yasa baki su fita.

Wata ma cewa tayi "ku sallame shi mana. Muma yayarmu likita ce. Allah na tuba don dai ƙarin ruwa da allura wanne ne ba za ta iya ba?"

Ran Nos ɗinnan ya ɓaci matuƙa. Idan an zo ita za a yiwa faɗan barinsu a ɗakin. Da taga Taj ne ma ta ɗan saki rai. Ta san dai duk yadda za ayi namiji daban yake da mata.

"Kai ma É—an gidansu ne?"

Caraf wata mai tsohon ciki ta ce "Baki ga kama da mara lafiyan ba?"

"Don Allah ka faɗa musu su ragu. A bakin aikina nake. In kowa bai min magana ba wallahi likitarsa sai tayi. Ta ce baya buƙatar hayaniya."

"Ya Taj barni da ita. So take ta nuna mana ta fi mu son É—an uwanmu. Ba fa surutu zamu yi ba."

Kamal ba jin an ambaci Taj ya yi hamdala. Shi ma sun ƙi sauraronsa. Kansa har ya fara ciwo. A tunaninsu allergy ɗin ne shi yasa su ka dage. Basu san halin da yake ciki magana ma dauriya kawai yake yi ba.

"Happy. Don Allah kasa su bi dokar asibitin. Ni kaina doctor É—in ba za ta barni ba idan ta gansu."

Nos dai tana jin sunan da aka kira Taj daga waje da wanda mara lafiyan nan ya kira shi, bata san lokacin da ta ce "Happy Taj? Kai ne mai HappyTaj don Allah?"

Ƴan bani na iyan gidan Alh. Hayatu ne su ka amsa mata. Harda mai cewa da ta ɗauka su ɗin local mutane ne take son wulaƙanta su.

"A bakin aikina nake." Ta nanata musu.

Da laluma da rarrashi Taj ya samu su ka bi tsarin asibitin. Da mutum bibbiyu aka dinga shiga ana fita. Nos ɗin tayi masa godiya bayan kowa ya tafi ta barshi ya shiga shi kaɗai. Abin mamaki yana zama ya kira sunan Kamal sai yaji shiru. Ɗaga kansa ke da wuya yaga ashe bacci ne ya ɗauke shi. Saurin bacci ba ɗabi'ar Kamal bace. Kuma bai fi minti biyar da raka ƴan uwansa waje ba don ya tabbatar sun tafi. Ya yi tsammanin zai dawo su yi hira ma tunda yaga kamar jikin da sauƙi. Hankalinsa sai bai kwanta ba. Anya allergy ne kawai? To ko kuma allurar bacci aka yi masa? Shi kaɗai ya dinga saƙe saƙe a ransa har Mubina ta shigo.

Haɗuwar farko ta jinjinawa soyayyar dake tsakanin ƴan uwan biyu. Lokacin Kamal ya tashi har Taj ya bashi labarin yadda su ka yi a Abuja. Ya ɗora da mitar me yasa ya zama na ƙarshen sanin bashi da lafiya. Cacar bakinsu su ka yi aka daidaita. Sai ga Kamal kamar ba shi ba. Jikinsa ma yayi ƙwari sannan kumburin duk ya sauka.

"Zan sallameka amma akwai magunguna da zan sabunta maka. Don Allah kada kayi wasa dasu."

Tashi Taj ya yi ya ce "Idan akwai a pharmacy É—inku ki bani na siyo kafin mu tafi."

"A'a ka barshi kawai" in ji Kamal

"Ba duka za a samu ba." Ita kuma ta ce da sauri.

Murmushi Taj ya yi, amma a zuciyarsa yaji rashin yarda dasu. Zargin nasa bai sami É—orewa ba da yaga da gaske Mubina wata kulawa ta musamman take bawa Kamal. DaÉ—i ya kama shi. Wannan karon da alama za a dace, Kamal zai daina gudun matan da yaga yana yi.

"Bari na baku wuri ku ƙarasa maganan. Na san ba komai na patient ya kamata wasu su ji ba."

"Har akwai abin da ya shafeni wanda bai kamata kaji ba?" Kamal ya faÉ—i yana É—auke kai daga hararar da Mubina take masa.

"In ta faÉ—a ka sanar dani. Bari na duba ko Bishir ya zo."

Ficewa ya yi ya barsu. Mubina ta sami sakewar ƙara sanar dashi dokokin da ya kamata ya kiyaye.

"Me yasa ya fita?"

"Ya zata akwai wani abu tsakaninmu. Bai san ni yanzu soyayya ko sadakarta aka bani zan mayarwa mai ita ba."

Murmushin zuci kawai Mubina tayi. In zai ɓoyewa kowa ita ba zai yaudareta ba. Tana da saurin karantar mutane. Tun farkon zuwan Kamal asibitin ta fahimci ya kamu da sonta. Sai dai bayan ya gama faɗa mata alamomin ciwonsa da aka yi gwaji ta sanar dashi lalurar shikenan komai nasa ya sauya. Soyayyar da take gani ƙuruƙuru ta koma yaƙin neman lafiya. Da ya gane da wuya lafiyar ta samu sai ya zama mai mugun sadaukarwa ga duk wanda yake mu'amala dasu. Musamman wannan ɗan uwan nasa Taj. A halin da ake ciki za ta cigaba da adana soyayyarta ta mayar da hankali wurin ganin ya sami lafiya. Bata son ta bari komai ya shiga tsakanin aikinta a kan samun sauƙinsa.

***
Chapter 45 · 0% Book details