Sashe 91
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kana ji na Ahmad? Albarkacin ka zan sassauta mata. Amma lallai ka ja mata kunne. Idan ma hauka ne to tayi a wani wajen."
Bai ji daÉ—i ba amma kuma bai ji haushin yayar tasa ba saboda ya san gaskiya ce take faÉ—a. Kuma Salwa ce ta jawo wa kanta
"Ƙalau take wallahi. Tsabar son zuciya ne da rashin tawakkali. Idan tana da zuciya ko aurenta ya ce zai yi ai ta ce bata so a yanzu. Saka ni a speaker"
Yaya Hajiyayye ta saka. Ahmad ya kalli inda Kamal yake kwance ya ƙara jin nauyi a zuciyarsa. Ga damuwar gaske amma haka kawai Salwa tana tayar masa da hankali.
"Idan kin fita ki koma asibiti ko ki wuce gidan ubanki kin ji ko. Na gaji. Ba ni na haife ki ba saboda haka ba za ki saka min hawan jini ba. Duk abin da ki ka zaɓarwa kan ki daga yau ya rage naki. Kada ki yarda ki koma gidana."
Bai jira jin ta bakin kowa ba ya katse call ɗin. Salwa ta bi su da kallo ɗaiɗai. Ta muzanta ajin ƙarshe. Haka ta miƙe ta yi ƙwafa da ƙarfi ta fita.
"Ƴar banzar yarinya. A dalilin ki yau har rungume rungumen ango da amarya sai da na gani." Yaya Hajiyayye ta cigaba da mita.
Taj ya kama dariya. Hamdi kuwa hanyar ɗaki ta nufa, Firdaus na yi mata dariya. A lokaci guda falon ya mamaye da ƙaurin girkin da ya rasa kulawar waɗanda su ka ɗora shi. Su huɗun dake falo a tare su ka yi hanyar kitchen ɗin.
***
Tsinuwa da zagi da mummunar addu'a babu irin wanda Salwa bata yiwa Ummi ba da ta fito. Ta tari adaidaita sahu amma ta rasa ina za ta ce ya kaita. Sai da ya yi shirin tafiya tayi saurin faɗin sunan unguwar da za ta. Suna tafe a hanya tayi mamaki ƙwarai da ta gane gidan. Sau ɗaya ta taɓa biyo Ummi a baya bayan sun tashi daga wata haɗuwa da su ka yi kafin bikin su Hamdi.
Zuciya tana ta ingiza ta. Baƙinciki da ɓacin ran da take ciki ya yi yawa. Da ta ƙwanƙwasa ƙofa Siyama ce ta buɗe.
"Ummi nake nema."
"Wa zan ce mata?" Siyama ta tambaya a tsorace. Fuskar Salwa abin tsoro. Kana ganinta ka san ba da alkhairi ta zo ba.
Daga tambayar Salwa ta gane Ummi tana ciki. Bata ɓata lokaci ba ta hankaɗe Siyama gefe ta faɗa cikin gidan tana ƙwala kira.
"Ummi. Ummi. Ummi..."
A firgice Ummi ta fito daga É—akin Iyaa inda aka saka ta gyaran wardrobe. Gabanta ya faÉ—i da ta tabbatar Salwa ce ba muryar ke mata gizo ba.
"Me ya kawo ki gidan mu? Wa ma ya nuna miki?" Ummi ta ja hannunta su ka koma ƙofar gida.
Iyaa da Baba Maje fitowa su ka yi daga É—akinsa da Baballe inda su ke tattaunawa akan ginin gidansa inda Zee za ta tare. Wajen su ka je amma Ummi da Salwa basu ankare da su ba.
Salwa ta cakumi wuyan Ummi "Ni za ki ha'inta? Turaren da ku ka bani dama ba wanda zai sa Ya Taj ya saki wannan Æ´ar É—an daudun bane ya aure ni?"
Tsohuwar bully an saba dambe. Ummi mantawa tayi da inda take ta doke hannun Salwa ita ma ta riƙe mata wuyan riga.
"Banza a banza...duk soyayyar da za a siya da asiri wallahi na raina ta. Turare kuma ba na kashe aure bane."
Don baƙin ciki Salwa harda kuka ta ce "Na mene ne? Me ku ka sa nayi?"
"Ummi..."
Iyaa ta fara kiranta horrified da jin abin da su ke cewa. Sai dai da wuri Baba Maje ya yi mata nuni da tayi shiru. Abin kunya har mutane sun fara taruwa.
"Ki jira ki gani amma tabbas soyayyarsa ba ta ciki."
"Wani aikin ku ka saka ni?"
"Alh. Usaini dai ya saka ki. Ni mene ne nawa a ciki?"
Cikin karaji Salwa ta ce "Waye Alh. Usaini? Me nayi Ummi? Turaren mene ne?"
"Turaren kassara sana'ar mijin Hamdi." Ta amsa mata da yanayin tsokana.
Ai tana rufe baki Salwa ta daddage ta kai mata wawura. Kan kace meye wannan dambe ya kacame a tsakaninsu. Duka harda yaga riguna a gaban mutane. Iyaa hawaye kawai take zubarwa. Baba Maje kuwa cikin gida ya koma yana mai jin kunyar abin da ƴarsa tayi na zubar musu da mutumci. Baballe duk zafinsa akan Ummi shi ma komawa yayi yana mai jan hannun Siyama. Ƴan unguwa su ka yi ƙoƙarin rabasu abu yaci tura. Wani kawai sai ya kira ƴan sanda. Daga cikin gidan su ka ji jiniyar motar. Baba Maje ya ce kada wanda ya fita.
Aka tattara su sai Police station. Nambar Baba Maje Ummi ta bayar. Da aka kira shi akan case ɗin ya ce zai zo. Suna gama magana ya kashe wayarsa gabaɗaya. Ya kuma ce da su iyalinsa kada wanda ya amsa kiran baƙuwar namba. Ummi ta zauna ta koyi hankali.
Salwa ta fi Ummi tsurewa. Kwana a nan abu ne da ba za ta iya ba. Gashi ita ɗin mai laifi ce. Ta kasa bada numbar Zahra saboda gudun tashin hankalin da za su yi da Ahmad. Garin Kano cike yake da dangin Mami, yau ga ranarsu amma babu wanda za ta iya kira kai tsaye saboda ba ayi mu'amalar arziƙi ba. Ƙarshe nambar babanta ta bayar. Aka kira shi sau biyar baya kusa bai ɗauka ba.
"Tunda baku da kowa mu bamu rasa masaukin baƙi. A wuce dasu su shiga su huta." Cewar DPO ya na barin inda su ke.
Hankali a tashe Salwa ta ce "Don Allah ka sa a sake kiran Babana. Ni wallahi ba zan iya kwana a nan ba."
Ummi kuwa ko gezau. Bata shaida ta shiga one chance ba sai da aka haɗa su cell ɗaya da wasu yan daban mata. Ashe damben su da Salwa wasa ne. Irin dukan da aka yi musu a cell đin ya ƙazanta. Babu wadda jikinta bai amsa ba. Kafin wani lokaci kowacce fa kama kukan gaske.
***
Saboda yawan kiran waya sai da kunnen Ahmad ya yi zafi. Duk wasu ƴan uwa Mami na kusa da na nesa ya dinga kira yana neman taimakonsu akan kula da itaa asibiti. Duk wanda ya kira suna yabon yadda ya kiyaye zumunci amma kowa da irin labarin cin kashin da Mami tayi masa a baya. Bottom line dai babu mai zuwa. Ya shiga damuwa sosai. Kamar ya faɗawa Alhaji sai dai yana tsoron me zai faru. Daɗin daɗawa ga Kamal a kwance sai na'u'rori. Kansa ya ƙulle.
Lokaci guda wata shawara ta zo masa. Ya kira likitan Mami ya ce a bashi Nos guda da za ta zauna da Mami tsahon sati É—aya kafin ya dawo. Zai biya ko nawa ne. Aka tsadance ya tura kuÉ—in a take su kuma su ka tura wadda za ta iya É—akin. Sai lokacin ya sami nutsuwa ya kira Baban Salwa ya tambayi ko ta koma.
"Bata dawo ba amma zan kira ta. Ina so ka zare hannunka a kanta. Zan yi maganin abin da kaina."
***
Kwanaki huɗu bayan nan Taj ya shirya zai koma Happy Taj. Hamdi ta dasa masa rigima kala kala. Rarrashi iri daban daban yayi mata. Ƙarshe ba shi ya fita ba sai ƙarfe goma da minti kusan arba'in. Ya fara kaita gida saboda suna sa ran tafiyar Yaya ta samu nan da kwana biyar. Yana zuwa yaran kitchen ɗinsa su ka ce yau gwaji za su yi masa su tabbatar aure bai mantar dashi girki ba.
"Kada daÉ—in abincin amarya yasa ka manta naka."
Kowa yayi dariya kuwa. Shi kuma ya Æ™arÉ“i ragamar dafa chicken kabsa. A lokacin ne kuma aikin su Alh. Usaini ya yi tasirin gaske. Ya haÉ—a spices É—insa tunda abin da zai dafa dama spices ne sinadarin sa. Komai ya ajiye a gefe yayi marinating kazar. Bai á¸anÉ—ana ba tunda hannu ya gama sabawa. Cikin Æ™warewarsa ya gama haÄ‘a komai saura jiran dahuwar abinci. Yana duba list É—in abubuwan da aka Æ™aro da baya nan yaga wasu cikin ma'aikatansa sun shigo kitchen É—in a guje.
"Sir baka ji ƙauri ba?" Wani ya tambaye shi da ya ce me ya faru.
Ya juya ya buá¸e tukunyar. Ƙauri ya sake cika kitchen É—in. Kowa na tari banda shi. Shinkfar tayi É“aki ta Æ™one babu abin mora a ciki. Abin ya É—aure masa kai. Ya faki idonsu ya da dangwali gishiri ya lasa. Ko É—igo bai ji É—anÉ—anon sa ba. Ya sake É—ora wata shinkafar ita kuma da ya gama aka yi serving ga masu saye babu wanda yaci rabi. Haka aka dinga dawo da plates É—in cike da abinci. Bakinsa still babu taste. Yasa yaran kitchen É—in É—anÉ—awa. Kowa ya kai baki sai ya gumtse abinsa ya dangana bakin shara ya tofar. Akwai wanda ya soma amai a gabansa ma.
"Me kuke ji?" Yayi tambayar calmly.
"Gishiri da garlic sun yi yawa sosai. Yawan daido duk dauriya mutum ba zai iya rufe ya ci ba."
Hankalinsa sayiwani irin tashi yayi. Bai yiwa kowa sallama ba ya fita. Yana zuwa gida ya buÉ—e fridge ya É—auki mixed fruit juice É—in da ya haÉ—a da hannunsa jiya. Nan ma shiru baki da hanci bai ji komai ba.
***
Abba Habibu da iyalinsa suna tattaunawa game da waÉ—anda Yaya za ta bi saboda ta sami muharrami.
"Abba dama dai ka jira ka samu wasu kuÉ—in kun tafi tare." Cewar Zee
"Yanzu Allah Ya kirata. Ku dai ku yi mata addu'a. Banda abin ku mijin Labiba ai ya zama É—an gida. Yan uwan nasa da zai yi tafiyar dasu jiya har kirana su ka yi mu ka gaisa."
"To kun gani ko..." Abba ya ce da murna.
Suna wannan hirar Halifa ya buÉ—e passport É—in Yaya yana gani.
"Laah Yaya wane irin blood group ne wannan O minus?"
Hamdi ta karɓe ta kalla " ya kamata in ɗan yi studying bambancin blood group ɗinnan. Nima anyi min test ɗinsa amma ban duba ba da shi da geno type."
"Da aka yi min sai da mutumin ya ce min wai jinina na musamman ne don yana wahala."