Sashe 75
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me kuma nayi?" Hamdi tayi tambayar cikin faÉ—uwar gaba don ta fara tsorata. So take ta ganta a cikin gida kawai.
"Baki yi komai ba sai taɓa zuciyar Tajuddin."
Wayancewa tayi saboda take takensa da take gani ta ce "Wai ka san ma'anar sunanka kuwa?"
Shi ma da gatse ya bata amsa "Ta yaya zan sani baki faÉ—a min ba?"
"Taj yana nufin crown, kaga Tajuddin yana nufin..." ta fara cewa ya katseta.
"Ina son ki Hamdiyya Habib Umar"
Sannan ya turo kanta ta hanyar turo kanta gaba da hannunsa da ya sanya a bayan kan. Sauran maganganun da su ke bakunansu basu sami damar shiga kunne ba saboda sabon al'amarin da Taj ya kawo musu. Tun hankalin Hamdi na kan ƙofar gidansu har ta manta a ina take. Sunan Taj ne kaɗai yake tafiya tare da bugun zuciyarta.
Kamar ba za su rabu ba. Taj ne ya yi ta maza ya É—aga kai yana kallonta da murmushi.
"It seems like zama dani ya fara shafarki fa yarinyar nan. Haka ake so. Wani abin ma sai gobe ko?"
"Kai da ka ce bacci za ka yi kafin mu ci kaz..." kasa ƙarasawa tayi ta kama laɓɓanta ta ɓame da ta ankara da katoɓarar da take shirin yi. Ba za ta so ya fassarata da rashin kunya ba. Ta sunkuyar da kai tana faman matsa hannuwa kamar mai tausar gajiya. Sai dai ta makaro!
Haɓarta Taj ya ɗago a hankali ta kawar da kai gefe ido a rufe. Yana murmushi ya ce,
"Kalle ni nan." Ya É—age gira
"Ni fa ba haka nake nufi ba." Hamdi ta ce kamar tayi kuka don wani kallon kya yi kya gama Taj yake yi mata.
"Me ki ka ji na ce?"
Cikin shagwaɓa Hamdi ta ce "to ka daina yi min irin wannan kallon."
Amsar da ya tanada don ya cigaba da tsokanarta ya fasa faÉ—i da yaji kamar an kwaÉ—a masa guduma a ka. Haka kawai lokaci É—aya abin ya ta'azzara.
Numfashi ya ja da ƙarfi sannan ya ce "Kira min Abba don Allah."
"Ƙara ta za ka kai?"
Jikinsa nauyi ya yiwa ƙafafunsa sai gashi ya yo kanta gabaɗaya. Da fari ta zaci wasa ne sai da taji ya sakar mata nauyi yana jan hailala a hankali. Ruɗewa ajin ƙarshe Hamdi tayi. Ta tattaɓa shi tana kiransa bata ji ya amsa ba. Kansa ta ɗago ta sanya hannunta ɗaya ta dafa kumatunsa.
"Don Girman Allah ka tashi. Wannan ba wasa bane wallahi."
Nan ma shiru sai numfashinsa da yake fita da sauri sauri. Da ƙyar ta yunƙura ta ɗauko jakarta ta zaro waya. Abba ta kira ya fito da gaggawa da yaji yanayin muryarta.
Da farko da ya hango ƙafafun Taj ta ƙofar gaba inda take zaune har zai koma. Kunya ta kama shi sai yaji Hamdi na kiransa da ƙarfi.
"Abba zo ka gani."
Ko da ya ƙarasa bai san lokacin da ya kai hannu ya ɗago Taj ɗin daga jikinta ba. Yadda duka gaɓɓanta su ke karkarwa haka nasa su ka fara. Da rawar baki Hamdi ta iya faɗa masa iya abin da ta san ya faru.
Ido Taj É—in ya buÉ—e a hankali da yaji an É—aga shi. Hamdi ta buÉ—e bayan motar Abba ya taimaka masa ya shiga.
"Bari na duba waye yake gida tsakanin yaran Mal. Baƙo da Halliru sai mu kai shi asibiti."
Da sauri ya yi gaba zuwa gidan maƙotansa da su ka iya tuƙin mota. Tafiyarsa ke da wuya kiran Alhaji ya shigo wayar Taj. Da kansa ya zaro ta daga aljihu ya miƙawa Hamdi. Cike da dauriya da cije baki ya ce mata idan Kamal ne kada ta sanar dashi don baya son tayar masa da hankali. In sun je asibiti sai a faɗa masa.
Screen É—in ta kalla lokacin kiran farko ya katse ta É—aga kai domin faÉ—a masa sunan da ta gani sai kawai ya kwantar da nasa kan a cinyarta ya rufe idon.
"Ɗauki ko ki kashe. Ƙarar tana damuna."
RuÉ—anin ciwon nasa da wata fargaba da ta shigeta saboda tsoron mai kiran ne su ka sa ta kiransa da sunan da taga Taj ya yi saving numbar.
"Alhajina ina wuni?"
Alhaji ya cire wayar daga kunnensa ya duba sunan don ya fara kokonton wa ya kira.
"Alhajinki kuma?"
"Au...lahhh...Alhajinsa nake nufi" Hamdi ta sake gigicewa da ƙarfin amon muryarsa.
"Shi wa?" Ya tambayeta yana yafito Inna da hannu. Wayarta ya karɓa zai kira Taj ɗin. A zatonsa ko ya daina amfani da wannan layin da ya sani.
Aunawa tayi taga idan ta ce masa Taj kai tsaye zai ce bata da kunya. Kuma ita ma dai nauyin sunan take ji.
"Shi ɗin dai" ta ce da ƙaramar murya. Ta ƙara da ɗan bayani a fakaice "uhmm...Hamdiyya ce"
Kai tsaye kuwa ya ganeta ya ce "Hamdiyya ina Taj? Bashi wayar."
Ɗan taɓa shi tayi ta ce masa Alhaji ne sai ya nuna mata kansa. Rabonsa da ganin sunan mahaifinsa a allon wayarsa ace ya kira shi ba zai iya tunawa ba. Sai dai kuma yau ya kira a yanayin da ba zai iya magana ba.
"Ba ya iya magana saboda ciwon kai."
Katse ta ya yi kafin ta ƙarasa "bashi da lafiya ko? Me ku ke yi baku kai shi asibiti ba? Ba shi wayar na ce!"
Muryarsa da take tattare da tashin hankali ta fito mata da sauti na umarni kuma cikin faɗa. Sai ta share ta sanar dashi cewa ba zai iya tuƙi ba. Amma Abbanta ya tafi neman wanda zai ja motar a maƙota.
"Shi me yake yi da ba zai tuƙa motar ba? In bashi da ita ya ja ta Taj ɗin mana."
Da ƙaramar murya ta amsa masa "bai iya tuƙi ba."
Fargabar ɓata lokaci da halin da Taj zai iya shiga ne su ka saka shi juyawa ga Inna ya yi magana wadda ta shiga raɗau kunnuwan Hamdi "kinga illar daudanci ko? A shekarun Habibu ace bai iya tuƙi ba kamar ba namiji ba."
Wannan magana ta sanya Hamdi jin nauyi da wani irin zafi a zuciyarta. Idanunta kuwa su ka soma zafi tunda dama kukan a kusa yake a dalilin ciwon Taj. Da hawayen ya zubo sai idon yayi kamar an baɗa barkono saboda tsananin ƙuncin da take ji. Abban nata yake faɗawa waɗannan maganganun? Ta tuna dama ya so a kashe auren. Babu mamaki sai da ya faɗa masa abin da yafi wannan ciwo a gaban idonsa. Kasa daurewa tayi tana ganin kamar in tayi shiru ta yarda mahaifinta bashi da daraja. Sai da ta kalli fuskar Taj taji kunya, amma duk da haka bata ji a ranta za ta fasa faɗa masar abin da yazo bakinta ba.
Numfashinta har canjawa yayi saboda ɓacin rai. Ta buɗe baki za ta yi magana Taj ya tashi zaune ya karɓe wayar. Jiran abin da zai ce tayi sai taga ya miƙawa Abba da ya dawo yana tsaye a baƙin ƙofa wayar.
"Alhaji ne" kawai ya ce ya damƙa masa wayar.
Magana su ka yi akan asibitin da za su haÉ—u su jira isowar Alhajin.
Ita dai Hamdi ta bi Taj da kallon da har zuciyarsa bai yi masa daɗi ba har Halliru ya tada motar su ka hau titi. Duka wayar yana iya jiyo abin da Alhajin yake faɗi. A daidai lokacin da take shirin bada amsa ya daure ya karɓi wayar saboda a ganinsa idan ta yiwa Alhaji rashin kunyar da ya tabbatar tana gab da yi, to babu makawa gazawar Abba zai cigaba da gani. Har ma ya ce ya kasa yiwa ƴaƴansa tarbiyya.
Hannunta ya riƙe ya ɗan matse ta zare abinta ko kallonsa bata yi. Ya dinga ƙoƙarin su haɗa ido nan ma ta fuske. Ba don an fara tafiya ba kuma ga dare da tabbas sauka za ta yi. Fahimta ɗaya ta yiwa abin da ya yi. Ya shigarwa mahaifinsa kamar kowanne ɗan halak, amma ita ya hanata tsayawa nata uban. Wata zuciyar ma tayi mata nuni da cewa ƙarshenta shi ma bai ɗauke shi cikakken namiji ba. Abin da take ji na baƙinciki yaƙi sauka. Har su ka isa banda sharar ƙwalla babu abin da take yi.
*
Da Bishir yana parking Alhaji bai yi mamakin ganin motar Kamal a wajen ba. Shi kaÉ—ai ma ya lura sai bai faÉ—awa Æ´aÆ´an nasa ba saboda a tunaninsa dama dole Kamal ya sami labarin halin da É—an uwansa yake ciki.
Suna fitowa daga mota su Hamdi su ka iso. Bishir da Abba su ka ƙarasa bakin motar su ka taimakawa Taj ya fito.
"Ya kuke kama ni ne kamar wani gurgu. I can walk on my own" ya zame hannayensu daga kafaÉ—unsa.
Hannun wanda bai taɓa zato bane ya maye gurbin nasu. Inda Alhaji ya janyo shi jikinsa ya kuma tallafe shi ta hanyar riƙe kafadar damansa da hannunsa na hagu. Sai ya zamana Taj na manne da jikin mahaifinsa. Bishir da Abba kallon juna su ka yi cikin mamaki da jindaɗi. Shi kuwa Taj neman ciwon kan ya yi ya rasa. Komai ya tattara ya koma zuciyarsa. Inda ta cika fam da wani irin farinciki mara misaltuwa.
"Mu je ciki a duba ka." Alhaji ya faÉ—a yana mai soma takawa a hankali don kada ya wahalar dashi.
Taj ya juya ya haÉ—a ido da Hamdi zai ce ta taho su shiga sai kawai yaga ta É—auke kai. Abba da Halliru ta fuskanta.
"Abba ku taho mu tafi kada mu rasa abin hawa."
"Ki bari mu ji abin da yake damunsa mana."
Fuskarta a cunkushe ta É—aga kai daga kallon wayarta ta kuma cewa "Shabiyu ta kusa fa kuma ba abin hawa garemu ba."
"Hamdi ki kwantar da hankalinki na kira Bawalle (mai adaidaita sahu maƙocinsu) zai zo ya ɗaukemu."
Abba Habibu ya faɗi yana duban Alhaji da yanayi na ban haƙuri game da kalaman ƴarsa. Kada ace bata damu da mijinta ba.
"Ba sai ka kira kowa ba. Zan kai ku da kaina ma" Cewar Bishir.
"Ka bar shi mun gode. Adaidaitan ma ya ishemu." Ita ce amsar da Hamdi ta bashi kai tsaye.