← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 96

Sashe 63

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anti Zinatu ta nuna musu hakan ba zai yiwu ba
"Wannan gaskiya ne. To amma Hajiya kun san shiri irin namu yana buƙatar lokaci. Ina laifin wata guda ko biyu? Mai ƴaƴa mata baya rasa ɗan tanadinsa. To amma ba zai isa ace mun rufeta mun kai ɗakin miji ba gaskiya."

Jin haka Amma ta ce mata "Hajiya Zinatu mu ba baƙin juna bane. Wuri guda muka tashi. Babu zancen ɓoye ɓoye. Na tabbata kun san akan girki Yaya Hayatu ya kori ɗansa daga gida. Haka nan ba za mu manta yadda ya juyawa kyakkyawar zumuntarsa da Yaya Habibu baya akan ƙaddarar da ta same shi ba."

"Haka ne."

"Babu wanda ya taɓa kawowa zai amince da auren nan amma gashi anyi. Mu duka nan muna tsoron kada jinkiri yasa ya ɓullo da wani abin. Tunda ko me Taj ya yi baya burge shi. Don Allah ku barmu mu bawa duk maraɗa da mahassada kunya."

Ita dai Yaya jikinta ya soma sanyi. Anya ba wani abin su ka ji ba wanda yasa su ke so a gaggauta bikin nan? Kada fa azo a mayar mata da ƴa ƙaramar bazawara idan Alhaji ya canja ra'ayi.

Bata yi nauyin baki ba kuwa ta faÉ—a musu.
"Ni dai idan kun san da matsala don Allah ku faÉ—a mana sai a yiwa tufkar hanci tun wuri."

"Ko ɗaya. In sha Allahu alkhairi zamu ƙulla. Mu dai fatanmu ku bamu haɗin kai. Zancen shiri kuma wallahi Innar Taj da ƴan uwanta sun ce ko tsinke kada ku damu da saye. Komai na biki su za su yi." Cewar Umma don ta kwantar musu da hankali.

"Ayi haka?"

Amma ta ce "An ma yi. Ba don abubuwan da su ka gabata ba ina da yaƙinin da Yaya Hayatu ne zai aurar da ƴaƴan gidan nan. Haka nan Allah Ya haɗa jininsu wanda a yanzu idan ina kallon Taj da Kamal su suke tuna min. Bambancin shekaru bai hana su ƙulla kyakkyawar mu'amala ba."

Yaya da Anti Zinatu sun yi ta ja amma babu yadda su ka iya da waɗannan gogaggun matan. Ƙarshe Yaya ta ce bari ta sansanar da Abba. Ɗaki ta koma ta kira shi a waya. Ya tuna yadda su ka yi da Taj yace ta amince. Zai san yadda ya yi tunda anyi aure Hamdi ba ikonsu bace. Idan su ka cigaba da ja'inja ba zai amfanesu ba. Yau ko ƙofa Taj ya ƙwanƙwasa yace a bashi matarsa basu da hurumin hanawa a shari'a. Balle kuma bidi'o'in biki da ko babu su aure ya ɗauro.

Sun nuna jindaÉ—insu da amsar da ta kawo. Cikin farinciki Mama ta zayyane musu yadda su ka yi nasu tsarin bikin. Idan akwai abin da su Yaya su ke so sai su faÉ—a. Alhamis mai kamawa za ayi kamu. Ranar Juma'a kuma dinner. Asabar ana la'asar za su zo su É—auki amarya. A kaita gidan Alh. Hayatu. Daga nan Taj zai É—auketa (wannan shirin Amma ne. Tayi rantsuwar Taj ba zai fara rayuwar aure ba sai ya taka gidan mahaifinsa. Kuma da izinin uban.)

Iyaa ta ce hakan ya yi musu. Ranar asabar za su yi yininsu a gida. Kuma tana roƙon a barsu su ɗauki nauyin abinsu. Dariya ta bawa su Hajiya. Kowa ya yi na'am da yadda zaman ya kasance. Aka rabu cikin mutumci. Bayan an cika musu ciki da daddaɗan abinci.

***

"Ba za ka ci ba?"

Hamdi ta tambayi Taj bayan ya ajiye mata wani faffaɗan plate mai kyau da haɗaɗɗiyar shinkafar da sabo yasa bai jima ba ya gama dafawa. Asalinta girkin mutanen Afghanistan ne amma ya ta sami karɓuwa a wasu sassa na ƙasashen Asia. Afghani Pulao dafaffiyar shinkafar basmati ce wadda cikin kayan ƙamshin dafata harda sinadarin cumin da cardamom. Sai kuma naman ƙaramar dabba wanda ake marinating ɗinsa da kayan ƙamshi kafin a dafa shi ya yi laushi luguf. Ita kuma shinkafar ana haɗata da caras da aka yayyanka sirara kuma ƙanana. A haɗa shi da raisin (bushasshen inibi) wanda ake soyawa sama sama da sugar sannan a haɗa da nuts.

Kansa da ya soma juyawa tun baysn ya sake arba da ita yake matsawa da hannu É—aya.

"Ki ci kawai. Bana jin yunwa."

Ba shiri ta ture plate É—in.

"Meye haka?" Ya ɓata rai. Zuciyar tana kuma ciwo shi.

Ita ma baki ba linzami yau ta turo shi "na san me ka zuba tunda na shiga tsakaninka da Salawaitu."

Dariyar dole ta sa Taj "Salwa ce ta koma Salawaitu?"

"Gaskiya dai na faɗa. Gashi nan ranka ya ɓaci don na canja mata suna."

"Ke za ki ji daɗi a ɓata naki?" Ya tambaya yana ƙarewa yadda take murguɗe murguɗen baki kallo.

"Mutum ya daɗe bai ɓata ba. Kuma na faɗa ɗin. Salawaitu, Salwanatu, Sal..."

Hannunsa da yake jin kamar ƙwaƙwalwar kansa gareshi, yana marmarin sake dukanta ya damƙe a da ɗan uwansa ta baya. Dukanta yake so ya ƙara yi. Rashin kunyarta da a mizanin masu tunani ma wani ko kallonta ba zai yi ba idan tana yi shi ne yake jin kamar ya kama ta da duka.

"Ki ci abincin nan kafin na dawo."

Ya kama ƙofa zai fita yana ji tayi siririn tsaki. Innalillahi...har tafin ƙafarsa yake jin ɓacin rai. Garam haka ya buga ƙofa ya sake rufeta a ciki.

Ta zauna tana ta faman girgiza ƙafa. Bata so ya fita ba tare da rigimar ta girmi haka ba. Ya saketa kawai ta huta. Ta kalli abincin ta janyo plate ɗin a fusace.

"Idan ban ci ba ma waccan Salonin zai bawa." Ta faÉ—awa kanta domin ta sami nutsuwar ci.

*

Mota Taj ya koma. Idanunsa jawur kawai don yaƙi biyewa zuciyarsa. Shi ya tabbatar da zai taɓa lafiyarta tabbas zai ji dama a ransa. Kamal ya kira ta whtsapp.

Bawan Allah sauƙi ya samu tunda aka fara sabon treatment. Kusan babu sauran kumburi. Sai duhu da yayi wanda a da ya ɗara Taj haske. Fari ne sosai kamar duka ƴaƴan Hajiya.

"Happiness"

Ya kira shi da wata irin murya mai rauni. Abin da yake faruwa tsakaninsa da Hamdi a ƙasa da awa biyu is not normal. Ta yaya zai dinga jin son dukanta kamar ba matar aurensa ba? Yarinyar da ɗazun nan yake jin zai iya keta bille ya aikata kowacce irin rashin kunya yau ɗinnan akanta.

Da tsokana ya ce "Happy nawa na gargajiya. Ka kai Mrs Happy gidan Sajidan ko kuwa naka gidan?"

Taj ya É—an yi murmushi "I'm in trouble Happiness. Yaushe za ka dawo?"

Salati Kamal ya yi kafin ya hau shi da faɗa "wane irin rashin haƙuri ne da kai ne Happy? Kwana nawa ya rage ta tare? Yanzu tana ina? Allah Yasa ba hotel ka kai musu ƴa ba."

"Ba shi bane. Kai ma ka san É—azu wasa nake maka..wata matsalar ce daban."

Hankalin Kamal kwanciya ya yi. Da safe da su ka yi waya ne Taj yace masa zai je kai Hamdi gidan Sajida. Amma fa har gidan da za su zauna sai sun je. Kamal ya dinga yi masa magiyar kada ya kunyata su amma ya dage sai sun je saboda kawai jindaÉ—in tsokanar É—an uwan nasa.

"Ina jin ka to. Me ya faru? Ba dai sakin ta kayi ba?"

Kamar zai yi kuka ya ce "Marinta nayi Kamal. I slapped Hamdi har hannuna ya fito a kumatunta."

Tashi tsaye Kamal ya yi. Ya koma ya zauna sannan ya kuma tashi.

"Mari? Hamdin? Me tayi?"

Yadda ta kasance daga shigowar Salwa har fitarta Taj ya faÉ—a masa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."

"Sai rashin kunya take min. Ni kuma ina jin kamar na shaƙeta na huta."

"Daina faÉ—a Happy. In sha Allah zan yi booking next flight na taho."

"Ana haka dama? Kana son mutum kuma kaji kana son inflicting pain a jikinsa? Happiness indai haka ake aure wallahi kada kayi. It hurts...so much."

"Kuka kake yi? Happy?" Shiru bai amsa ba "Tajuddin?"

Katse wayar Taj yayi. Ya shafa idonsa yaji shi a jiƙe.

"What is wrong with me?"

ÆŠazu ma sun kallon juna da Hamdi ya yi hawayen nan. Shi yasa ya juya mata baya kafin ta gani.

Bai yarda ya sake komawa saman ba sai da su ka yi jam'in la'asar yaga fitar Abba. Ya koma ya sameta tayi sallah ita ma. Kanta a ƙasa tana ta avoiding kallonsa. Hakan ya fiye masa komai.

"Zo mu tafi."

Kamar jira take ta miƙe. Ta hanyar da su ka zo su ka koma.

Salwa baƙin naci sai da taga fitar motarsa sannan ta tashi ta tafi gida. Yau yadda zuciyarta take wasai har girkin dare ta yiwa Gwaggonta.

***

Abu ya ƙara taɓarɓarewa tsakanin Hamdi da Taj amma babu wanda ya sani. Yanzu ko a waya su ke magana sai anyi faɗa. A kwana na uku wanda ranar ne Kamal ya dawo ya sanya Taj a gaba ya kira Hamdi. Irin faɗan da suke yi ya tayar masa da hankali sosai.

"Ni wannan abu ya ishe ni. Kaje ka auri Salwa. Ka cinyeta. Ka haÉ—iyeta ma duka. Amma don Allah ka rabu dani. Bana sonka. Bana son auren."

Guntun tsaki ya yi "matsalata dake bakinki baya shiru. Just keep quite for once. Maybe zamu iya komawa daidai idan kina kama bakinki."

"Anƙi ɗin."

"Kin san zan iya zuwa har gidan in hukunta ki ko?" Ya gargaÉ—eta. Kafin ya kira kuma kamar ana azalzalar zuciyarsa. Kewarta kawai ke damunsa.

"Kuma aka ce maka iyayena za su zuba ido kayi yadda kake so?" Tana wani irin cije baki ta ce " Bar ganin Abbana yana yi maka aiki. Wallahi kana kuma taɓani idan na sanar dashi zai rama min."

"Me ya kawo zancen iyaye kuma?"

"Naga Æ´aÆ´an masu kuÉ—i sun raina iyayen irinmu ne."

"Allah ki kiyayeni."

Ya soma magana Kamal ya karɓe wayar. Sallama ya yi wadda Hamdi tana ji nutsuwarta ta dawo harda gaishe shi.

"Me yake faruwa Hamdiyya?"

Kuka ta saka masa. Duk tambayar duniya ta kasa bashi amsa sai "shi ne" kawai da take ta faɗi. Da ƙyar ya rarrasheta sannan ya yi mata tambaya.

"Kina son sa?"

"Shi ma ba sona yake ba." Ta amsa da kuka.

Kamal ya kwantar da murya "wa yake ta tashi? Ƙanwata nake tambaya. Kina son Taj?"
Chapter 63 · 0% Book details