Sashe 78
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren Alhaji kuma Kamal, Bishir da Abba da ya dawo daga baya duk ɗaki guda su ka kwana da Taj. Alhaji yana jiyo hayaniyar murnarsu kamar ba dare ba. Sai ya tuna ƙuruciyarsu da kuma samartakarsu da ya katse na tsayin shekaru. Rashin jindaɗin abin da yayi gami da tunanin wane ciwo ke damun Kamal sai su ka hana shi baccin kirki.
Wuraren huɗu da rabi yaji alamun an buɗe ƙofar ɓangaren nasa. Dama baccin babu nauyi. Da sauri ya leƙa domin ya gani ko jikin Taj ne ya tashi. Fitowarsa tayi daidai da fitar Kamal. Nan jikinsa ya sake mutuwa. Ya koma bakin gado ya zauna. Baccin da bai koma ba kenan sai kawai ya ta da nafila. Yana ji aka soma kiraye kirayen assalatu. A zuciyarsa ya ƙudurta sauka ya tashi su Taj nan da minti talatin sai su yi alwala su tafi masallaci.
Ko minti goma ba ayi ba yaji ana buɗe gate a hankali. Ya sake tashi ya leƙa sai ya hango motar Kamal ce ta fita. Bai yi wata wata ba ya sauka ƙasa da muƙullin wata sabuwar motarsa. Da kansa ya ja hankalinsa a matuƙar tashe. Rabonsa da tuƙi ya ma manta. Cikin sa'a da yabi hanyar asibitin sai ya hangi motar Kamal tunda titi fayau yake dai motoci jifa jifa.
Haka ya bishi har asibitin ba tare da ya sani ba. Yana parking bayan shigar Kamal ciki sai ga Mubina. Da sauri ta shiga asibitin tana magana a waya. Bayanta Alh. Hayatu yabi da sauri. Tana shiga cikin asibitin tayi hanyar emergency inda ya ga fitowarsu É—azu ya kirata da kakkausar murya.
"Dr. Mubina"
Cikinta ya ba da wani mahaukacin sauti domin ta riga ta gane muryarsa. Ta juyo kamar mara laka a tsorace.
"Kai ni wajen yarona."
Gaba tayi ya bita a baya har É—akin. Ta buÉ—e da sallama. Nos É—in da ya taya ta aiki da daddare yana tsaye akan Kamal dake kwance babu riga. Juyawar nan da Kamal ya yi da yaji motsinta sai idanuwansa su ka sauka a cikin na Alh. Hayatu Sule Maitakalmi.
RAYUWA DA GIÆI 30
Batul Mamman💖
Kuna neman reliable data ba cuta va cutarwa? Ku saya a baku na kowane layi cikin aminci da rahusa?
Look no further. Contact MKdataservices for your data, airtime, tv subscription and nepa bills.
08038258489
https://www.mkdatasarvices.com.ng
Sayen nagari....mayar da data gida!
~~~~~
Ya yunƙura zai tashi ba shiri don ya san yau ɗin abin da zai fuskanta sai ya gwammace kiɗa da karatu. Alhaji ya yi masa alama da ya koma. Ya sake yunƙurawa dai sai Alhajin ya kalle shi yana mai buɗe masa idanu. Dolensa ya koma ya tada kai da filo.
Mubina dake tsaye da tasar allura tayi wiƙi-wiƙi da idanu ya duba "Ƙarasa ki duba min shi mana."
Tayi sauri ta isa gaban gadon. Ido Kamal ya rufe don allurar akwai zafi. Alhaji yaji wani irin tausayinsa ya tsirga masa. Kujerar gaban gadon yaje ya zauna. Ya kama hannun Kamal na dama ya riƙe. Irin riƙon ƙarfafa gwiwa da rarrashi.
Dama yaya lafiyar kura? Duk wani emotion na rauni da Kamal yake adanawa tun farkon rashin lafiyar a lokaci guda ya fashe. Ya ƙara ƙarfin riƙon hannun mahaifinsa yana kuka mara sauti. Tsananin tausayinsa yasa Mubina taya shi. Nos ɗin ma kawar da kai gefe yayi. Shi kuwa Alhaji dakewa ya yi duk irin yadda hankalinsa ya tashi.
"Kuka a gaban mace Kamal kamar wani mace? Ni fa ka san ba shiri nake da rago ba."
Hawayen ƙaruwa su ka yi. Ya dawo da kansa saitin Alhaji kawai ya cigaba da abinsa.
Alhaji yayi murmushi "matana basu taɓa ganin hawayena ba duk shekarun nan. Kai kuwa ka saka mace a gaba kana abin kunya. Ko batun alaƙar taku shi ma ƙarya ku ka yi min?"
Girgiza kai Kamal ya yi. Alhaji ya dubi Mubina da allura a hannu tana kallon ƙasa. Allurar ya ce tayi tunda da alama akan lokaci ake buƙatarta. Ba don haka ba ya san Kamal ba zai fito da asuba ba. Bayan anyi allurar wadda yadda yaga an soka ta ciki ya ƙara kiɗima shi sai ya tambayi Nos ɗinnan abin sallah. Gari har ya soma haske basu yi asuba ba. Daga kan gadon Kamal ya bi shi sallar. Bayan sun idar suna zaune su biyu, Alhaji yana zaune akan abin sallah ya tambaye shi game da ciwon.
"Lalurar dake damunka a hanyar fasiƙanci ka same ta ne?"
"A'a Alhaji" ita ce amsarsa.
Muryar Alhaji ta karye domin a tsorace yake Allah Ya sani. Kamar kada ya idar da sallah ya yi tambayar tun farko.
"To me yasa? Mene ne dalilin ɓoyewar?"
"Saboda maganin ba mai samuwa bane Alhaji. Ƙoda nake buƙata kuma ..."
Yana son yin faɗa amma ya san cewa abin da zai sa Kamal yi masa ɓoyon ciwo ba ƙaramin abu bane.
"Gani, ga ƴan uwanka mutum ashirin da bakwai amma ka kasa faɗa? Bayan na san karamcin da Allah Ya yi min a gidana. Yau ko babu ni babu mahaifiyarka ina da yaƙinin cewa sauran uwayenka za su tsaya maka ka samu a jikin ƴan uwanka ko da kuwa ƴaƴan cikinsu ne."
Nan dai Kamal ya yi masa bayani akan matsalar da aka samu. Bai gamsu ba sai da Mubina tayi masa fashin baƙi. Amma duk da haka zuciyarsa fafur taƙi amincewa. Ana bayanin yana jin zufa a duka jikinsa. Gabansa kuwa faɗuwa kawai yake yi.
Yayi salati yafi a ƙirga. Kamal ya yi mamaki domin faɗa yasa rai zai yi masa.
"Alhaji baka yi min faÉ—a ba."
"Wane irin faÉ—a kuma Kamal? Ta yaya ma za ka yi tunanin zan maka faÉ—a? Halin da zuciyarka take ciki na firgicin ciwon ma da ina da iko wallahi zan raba ka dashi. Da ace akwai yadda zanyi cikin ku babu mai yin atishawar da zai ji a jikinsa. Baka ganin dalilin ciwo na dawo da É—an uwanka? Ta yaya kai kuma zan yi fushi da kai?"
"Kayi haƙuri."
Tare su ka fito bayan allurar ta saki Kamal. Alhaji ya dage sai dai ya bishi a motarsa. Zai turo a É—aukar masa tasa.
"Kawo muƙullin to.." ya miƙa hannu zai karɓa. Alhaji ya hana.
"Da Æ´aÆ´ana da jikoki kake tunanin zan yarda kana rabin mutum ka ja ni?"
Suka yi dariya sannan su ka shiga Alhaji ya ja su. Jifa jifa su kalli juna su yi murmushi don su kwantarwa juna hankali.
"Alhaji don Allah maganar nan.." Kamal ya fara roƙonsa da su ka isa gida.
"Shiga ciki Kamaluddeen" Alhaji ya katse magiyar da ya so yi masa akan ya yi shiru da maganar.
Bayan Kamal ɗin yabi ya same shi yana yiwa su Taj ƙaryar abin da ya fitar da shi da asuba. Murmushi yayi musu bayan ya amsa gaisuwarsu. Su huɗu yau su ka kwana a ɗaki guda kamar wasu yara ƙanana.
"Yaya kan naka?"
Abba ya wani turo Taj gaba "taɓa shi kaji Alhaji. Jikin da sauƙi. Ai jiya bamu yi bacci ba saboda yi maka gadinsa."
"Nagode Sulaiman. Yau ni ne abin tsokana ko? Ko da yake girmanka ne baban Hayatu."
Aka saka dariya sannan ya haye sama ya kira Ahmad. Taj ne kawai ba ya sakin jiki ya yi dariyar saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa gaskata wai shi ne a gida.
***
Rabon da Abba Habibu yaga rigimar Yaya irin wadda ya gani tun bayan dawowarsa a daren jiya ya manta. Ta nuna masa rashin jindaÉ—inta sosai. Da mitar ta kwana ta tashi.
"Amma dai kin san ba dawa taje ta kwana ba."
"To mene ne maraba? Gidan surukan da bata riga ta tare ba saboda Allah. Salon a sami abin goranta mata nan gaba."
Kwanciya Abba ya gyara don bacci sam bai ishe shi ba. Ya yi dare a waje sannan rikici ya hanasu bacci sosai.
Yaya ta haÉ—e rai "kwanciya ma za ka yi?"
"Da fa? So ki ke muyi ta É—aga murya a sami abin goranta mata da yawa?"
Saukowa tayi don kanta da taji me yace "amma ka san damuwata. Ina gudun kada ace bamu saya mata mutumci ba."
"Akwai mutumcin da ya wuce auren da aka É—aura mata? Kuma na nanata miki cewa ba Taj bane ya ce ta zo su tafi. Yaya Hayatu ne ya ce ta bi mijinta."
"Zancen nawa dai ya fito. Ya ce ta bi shi saboda yana ganin ya isa. Ni bana son wani ya rainaka ne." Ta faɗi da ƙanƙanuwar murya.
"Nayi zaton kin yi min sanin hagu da dama ashe ba haka bane? Wallahi kuɗi ko muƙami ba zai sa na wulaƙanta ƴata ba. An riga an ɗaura aure. Bai kamata na nuna mata bijerewa umarnin mahaifin mijinta garesu daidai bane. Ko har kin manta matsayin da muka haɗu da Taj tsakaninsa da babansa?"
Jikinta sai ya sake yin la'asar. Ta kama bakinta bayan ta bashi haƙuri. Bawan Allah dama ba riƙo gare shi ba. Nan da nan ya kashe wancan zancen ya sako maganar kai amarya tunda ya san dole za a dawo da Hamdi daga gidan Alh. Hayatu. Sai da su ka gama tsara komai ya koma ya kwanta ita kuma ta fito falo.
A firgice ta sami Zee tana kai kawo. Zee ɗin na ganinta tayi maza ta rufe ƙofar falon kada kowa ya ji.
"Yaya kada ki tada hankali idan ki ka ji me zan faÉ—a."
"Allah Yasa dai lafiya Zee."
"Jiya Hamdi bata dawo gidan nan ba."
Da gangan Yaya ta ce "kai haba?"
Zee ta sake kwantar da murya "Wallahi kuwa. Nayi ta kiran wayarta bata É—auka. Sai da asuba tayi min message wai tana gidan su Ya Taj."
"Indai haka ne ai babu damuwa."
Zee kasa ɓoye mamakinta tayi. Da tsammanin faɗa ta zo sai ta samu ba haka ba. Yaya ta gama tsokanarta sannan ta taimaka tayi mata bayanin me yake faruwa. Su ka gama dariya da tunanin me za su ce da mutanen da suka kwana idan aka fara cigiyar amarya.
***
Hajiya, Umma da Mama sai da safe Inna ta sanar dasu duka abubuwan da su ka faru a gidan da daddare, har ma da baƙuwarsu. Murna a wurinsu ba a cewa komai. Dawowar Taj abin farinciki ne da shi kaɗai ya cancanci ayi ƙwarya ƙwaryar walima saboda farinciki.