← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 96

Sashe 46

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu da sallamar Kamal ya wartsake har ya koma shagonsa. Sai lokacin Taj ya sami sukuni da nutsuwa a ransa. Kullum yana tunanin Hamdi amma damuwar Kamal ta ishe shi. Daɗinsa ɗaya da ya koma gidan Ahmad Salwa ta tafi Bauchi. Hankalinsa kwance ya soma fafutukar neman gida don Inna ta faɗa masa bikinsa ba zai ɗauki lokaci ba. Yawancin fitar da Abba su ke yi ko Bishir. Bai fiye neman Kamal ɗin ba saboda yana ganin hutu ya kamace shi ba taya shi neman gida ba. A cikin kwanakin kullum yana waya da Abba. Abban ya so zuwa duba Kamal amma da ta tuna yadda su ka yi Alhaji sai ya haƙura kawai ya kira shi. Yaya har fushi tayi. Ta nuna masa rashin dacewar hakan. Shi dai haƙuri ya bata da ƴan dabarun wayo har ta daina zancen.

Yau alhamis ta kama kwana shida da ɗaurin aurensa. Ya sami sabon gida a sharaɗa self-contain daidai me sabon aure. Mama ce ta bashi shawarar kada ya ce sai ƙaton gida. Gara ya mayar da hankali wajen gina filin da su ka saya shi da Kamal shekara biyu da su ka wuce.

Shirye shiryen biki yana ta kankama. Iyayen basu saka rana ba sai sun ci ƙarfin shirinsu. Masu haɗa lefe su Yaya Hajiyayye kuma an taso Taj a gaba ya kawo size ɗin underwear ɗin Hamdi. Ya gama zille zillensa ta biyo shi har office a Happy Taj ta saka shi a gaba.

"Kirawota a gabana ka tambaya."

"Na ce miki fa zan tambaya yau É—innan na turo miki."

"Ai na gaji da gafara sa. Kai ko irin abinnan na angwaye da an É—aura aure su fara damun amarya da fitina da alama baka iya ba"

Kunya kamar ya fice ya bar mata office É—in.
"Haba Yaya Hajiyayye. Sai kace wani É—an is**. Kunyarki ma ta kama ni."

Dariya tayi sannan ta ce "Ka kira yanzu nima jirana ake yi in faÉ—a."

Ido ya zaro "wa da wa za ki faÉ—awa? Wannan ai tonon silili ne. Kowa sai ya san girmanta saboda Allah? Sirri ne fa." Ya yi kicin kicin da fuska.

Yaya Hajiyayye me zata yi kuwa banda dariya.
"Sirri manya. Ba dai naji ance weekend za ka kaiwa su Hajiya ita ba? Tana cire mayafi zan aunata tas da ido wallahi."

"Zan fasa kawota."

"Ka ma isa?"

"To umarnin zan bata kada ta yarda ta cire mayafi...kai, hijab ma za ta saka."

"Kayi ka gama. Telan da zai yi mata É—inkunan biki ma ranar zai zo aunata." Ta ce tana kallon idanunsa.

"Tela kuma?" Ya ambata kamar yau ya fara jin kalmar "Dama har yanzu ana wannan jahilcin Yaya? Na zata yanzu mata ke auna kansu su bawa telan idan ma namiji ne."

Ganin ta same shi a hannu ta cigaba da kunna shi.

"Ɗinkunan maza ai sun fi na mata kyau. Sun san duk wani lungu da saƙo da za su auna saboda shape ya fito."

Abu ya yi tsamari. Taj harda gumi don takaicin yadda idanunsa ke nuna masa Hamdi a gaban wani ƙato yana gwadata. Mantawa ya yi da girman yayar tasa ya ce,

"Wannan dai kafurci ne ƙaɗa'an. Kamar ba a zuwa islamiyya a garin nan?"

Ta gimtse dariyarta da ƙyar "mu ne kafiran kuma yau Taj?"

"Allah Ya baki haƙuri" ya ce yana kumbure kumbure.

Dariyar da take dannewa sai da ta fito. Tayi mai isarta ta ce to lallai a yau ɗinnan take so ya tura mata kafin ƙanwarsu da ta tafi UK da mijinta ta dawo nan da kwana uku.

Tunda ta tafi yake tunanin yadda zai tambayi Hamdi. A ganinsa mai baki amma yana da kunya. Ga amaryar tasa ita ma gwanar tsiwa. Ƙarshenta daga tambaya ta fassara shi.

*

A unguwar tasu ya yi Isha tare da Abba. Ya jira shi ya sanar da Yaya zuwansa sannan ya shiga su ka gaisa.

"Kwana biyu mun tada kai tsaye. Naji kana ta yawon neman gida."

"Yiwa kai ne Yaya."

Abba ta kalla don bata daina fushin zuwa dubiya ba "Kamal bai yi fushi damu ba ko?"

Shi da ya san komai a bakin Zee ya riga ya fahimci Abba tsoron zuwa yake kada su haÉ—u da Alhaji. Nuna mata ya yi babu komai tunda ba jimawa ya yi ba. Kwana É—aya ne.

"Allah Ya ƙara masa lafiya." Ta tashi ta ce "Me za ka ci a ɗora maka? Yau abincin ana magariba da kowa ya ci aka bayar saboda zafi. Abbanku kuma ya ce a ƙoshe yake bamu ajiye masa ba."

Shi da ba wata surukuta yake yi da su ba sai cewa ya yi zai ci indomie. Abba ya miƙe saboda sabo zai tafi kitchen ɗin.

"Girkin matarsa zai ci. Don Allah zo ka tafi ka watsa ruwa ka huta."

"Au...haka ne fa" ya furta yana jin kamar ya faÉ—awa Yaya gaskiya. Baya son su fara jindaÉ—in kasancewa tare bayan ya san auren ba mai É—orewa bane.

Dariya su ka bawa Taj. Yaya ta ce ya jira yanzu za ta turo Hamdi.

*

Tana jin takun Yaya ta gyara filo ta kwanta. Dama tunda taji muryarsa ta san sai an nemeta. Ba kuma son ganinsa take yi ba. Abubuwa uku ke damunta. Haushin abin da Alhajinsa ya yiwa mahaifinta da wa'adin da ya basu, sai kuma rashin nemanta da ya yi na tsayin kwanakin nan. Na ƙarshe kuwa kewarsa ce da ta mantar da ita rashin son girkin da yake yi. Ranar da taji Kamal ne babu lafiya dai tayi masa uzuri amma sai taƙi kiransa ta kira Kamal ɗin.

"Tashi kafin ranki ya ɓaci." Yaya ta kai mata duka a cinya. Ta tashi tana sosa wurin.

"Kina fa da zafin hannu Yaya."

"Wuce ki É—an gyara fuskarki ki je ki dafawa Taj indomie."

"Indomie kuma? Ba ya iya dafawa ba? Ya tafi gidansu mana." Ta turo baki.

Hannu Yaya ta kai za ta É—alle bakin ta gudu.

"Bana son rashin É—a'a Hamdi. Kuma saura idan kin je ki kasa gaishe shi. Mara kunya kawai."

Yaya na fita tayi saurin cire kayanta ta saka riga da wando na bacci ta É—ora hijabin da ya wuce gwiwarta kaÉ—an. Fita ta zo yi Zee ta kama kiran Yaya.

"Zo kiga a yadda za ta fita."

Saurin rufe mata baki tayi "gulma dai haramun. Ina ruwanki?"

"Babu ruwana amma dai a matsayina na mai jin maganar iyaye zan so Æ´ar uwata ma tayi hakan."

Harara kawai ta gallawa Zee ɗin. Ta koma gaban ɗan madubinsu ta fesa body spray sannan ta shafa hoda da man leɓe. Dama niya tayi taje masa tana hamma ta ce bacci take ji.

"To uwar iya...haka yayi ko kuwa sai na cire hijabin?"

"Da yafi bada citta don wallahi har laɓe sai nayi muku."

Hamdi ta tafa hannuwa "gulmawiya, shi yasa naga kin yi saving sunan Baballe da Sadiq a wayarki? Wato É—an zuwan nan da yake yawan yi har ya kwance miki hadda. Kin manta kukan bakya so É—in da ki ke yi."

Zee taji kunya sosai. Sai ta cije don Hamdi ba za ta rabu da ita da wuri ba.

"So muke mu rigaku haihuwar da Ya Taj ya ce ku za ku fara yi."

"Na shiga uku. Zee zancen haihuwa yayi miki? Da wa zai haihun?"

Zee ta ƙyalƙyale da dariya "Hamdiyya Habib mana"

Tana faɗin haka ta fice daga ɗakin. Hamdi ta gama jimamin maganar ta fito da ƙudurin fara cika umarnin Abba. Za ta cigaba da nunawa Taj bata son girki da ma wasu abubuwan da take jin za su taimaka wurin ɓata masa rai.

*

Danna waya yake su na chatting da abokinsa Wakili da su ka yi karatu tare a Indiya ta shigo. Sallamar nan ciki-ciki da gaisuwar.

Taj ya yi kamar bai ji ba yaƙi amsawa. Sai da ta shigo cikin falon ya ɗaga kai ya kalleta.

"A dinga sallama Æ´an mata."

Ta juya idanu "Ai nayi."

"Banji ba." Ya faÉ—i lokaci guda ya shagala da kallonta. A garajen fitowarta hijabi ruwan madara ta saka mara kauri. Da kaÉ—an ya wuce babu a jikinta. Rikita masa lissafi yaga tana neman yi ya wayance da cewa "ba za ki iya sallamar bane in tafi?"

Ta turo bakin nan "to Assalam alaikum."

"To wa alaikum salam."

"Guda nawa kake ci?"

"Me?"

"Indomie É—in mana."

"Oh, ki kimanta." Ya gyara zama abinsa.

Tana son tambayarsa ko me da me za ta saka a ciki amma bata son yawaita yi masa magana. Fita tayi ya ajiye wayar da dama amfaninta rage masa kallon ƙurillar da yake yi mata.

Ita kaɗai ta kama tsaki da ta tuna yanzu ƙila fa duk yadda za ta dafa zai ji bata yi ba saboda sabo da girki. Yanke shawarar yinta normal kawai tayi. Ta ɗauko attaruhu da albasa za tayi grating amma bata san gejin cin yajinsa ba. Ƙarshe dai guda biyu ta saka da ƙaramar albasa. Ta raba jajjagen biyu sai taga kamar yayi yawa. Kaɗan ta saka ta dafa indomie ɗin dashi. Sai ta kuma soya wani da curry da ɗan maggi cikin mai daidai suyar ƙwai. Yana fara ƙamshi ta juye ƙwai uku da ta kaɗa a kai. Ƙamshinsa har falo. Ta kawo cucumber ta yanka rabi a zagaye ta jera a gefen plate ɗin mai ɗan zurfi kaɗan ta tsakiya. Indomie ɗin tana ƙarasawa da sauran ruwa mara yawa ta juye sannan ta rufe kanta da ƙwan. Yadda bata son ci da sanyi shi yasa tayi gaggawar kai masa.

Tana ajiye tray É—in ana É—auke wuta. Taj ya kunna torchlight É—in wayarsa ya hasketa tayi saurin rufe ido.

"Hamdi da zuciya É—aya kika dafa min dai ko?"

"Me ka gani?"

"Wuta aka É—auke. Kin san mu a India yanzun nan sai mu fassara abu."

Murmushi tayi don ta fara gano tsokanarta yake da zancen Indiyan nan.

"To Shah Rukh Khan. Da me ka fassara É—auke wutar?"

Taj ya haɗiye abincin da ya kai bakinsa ya ce "Da lokacin waƙa cikin duhun dare mana. Muna bin bango muna rawa."

Toshe bakinta tayi ta kama dariya. Abin nasa azimun. Wai bin bango. Ganin ya tsura mata idanu amma bai fasa cin abincin ba shi ne ta ce.

"Bin bango kamar wasu ƙadangaru."
Chapter 46 · 0% Book details