← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 96

Sashe 59

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Surprisingly daga dangin Hajiya na sami uku. ÆŠaya ne a dangin Umma. Ai jinsi baya hana bayarwa ko? Duka huÉ—un mata ne."

Mubina ta ce gender baya hanawa.
"Amma fa Kamal A negative ne. Indai ba irin nasa ba kinsan sai dai O ko AB negative ko?"

"Dukkaninsu O negative ne. Yanzu su Alhaji ya rage su sani sai a tuntuɓe su."

"Muje ki ganshi. Akwai Nephrologist da na fara magana dashi daga Port Harcourt. Idan an sami nasarar samun mai bayarwa sai naji yaushe zai iya zuwa."

Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faÉ—a. Mubina ta shige gaba zuwa É—akin da Kamal yake. A hanya tayi ta nanata mata don Allah ta daure zuciyarta idan ta ganshi. Wannan yasa zuciyar Yaya Kubra ga tsinke tun kafin su shiga.

Mubina ce ta fara shiga da sallama. Yana kwance gaɓoɓi da fuskarsa sun kumburo sosai. Shi kaɗai ya san irin azabar ciwon da yake ji. Amsa sallamar ya fara da muryarsa can ƙasa kawai sai ya yi tozali da Yaya Kubra. Ya yunƙura ya tashi zaune kafin ta ƙaraso.

Hannu ta É—ora akan bakinta don kada tayi kuka mai haÉ—e da ihu da taga yadda ya koma.

"Kamal?" Ta kira shi da rawar murya.

Ya miƙa mata hannu, kwarmin idanunsa yana ziraro hawaye ta riƙe. A gefen gadon ta zauna su ka rungume juna. For the first time tun bayan ciwon nan ya same shi ya fashe da kuka mai ban tausayi. Duk wani ciwo, ƙunci da damuwa da yake ɓoyewa ya bari ya nuna kansa a wannan lokacin. Shi ɗan dangi yana ta fama da damuwa shi kaɗai. Abin da gidansu basu saba ba.

Yaya Kubra tana kuka tana shafa bayansa da lallashi. Mubina kuwa ficewa tayi don bata son karyar masa da zuciya fiye da halin da yake ciki. Mara lafiya baya son ganin rauni a tattare da likitansa.

Tsahon minti goma zuwa shabiyar kafin yaji sanyi a ransa ya daina kukan.

"Kiranki tayi ko?" Ya tambayeta yana nufin Mubina.

Faɗa ta soma yi masa "Me yasa ka zaɓi wannan rayuwar Kamal? Bamu da mahimmanci a wurinka? Ko kana ganin ba za mu damu da lalurarka ba?"

"Irin wannan kallon kamar kina yi min sallama shi ne bana son gani. Wannan kukan zamu dinga yi kullum har lokaci..."

"In sha Allahu za a dace. Ina nan ina bincike."

"Bata faɗa miki cewa ko dialysis ba zai iya riƙeni na tsayin lokaci ba?"

"Na sani Kamal. You need a new kidney. And we'll find one in sha Allah" ta share masa hawaye da hannunta.

Alƙawarin riƙe masa sirri ya roƙeta har zuwa lokacin da za ayi bikin Taj. Sannan ƙanwarsu mai shirin haihuwa ko yau ko gobe ita ma ta sauke.

"Me yasa? Wallahi ka san ba za ka burge Taj ba. Infact ni ba zan so ganin ranar da zai sani ba. Za ku yi faÉ—a Kamal. Za ku yi faÉ—a sosai. Ko jiya da naje duba shi sai da yayi ta zancen wai ina duba maka magungunan allergy kuwa."

Jingina ya yi da pillow don ya gaji da zaman. Ya yi ajiyar zuciya.

"Na sani. Amma Happy zai tsayar da duka uzurin rayuwarsa ne. Zuwa yanzu kin san mutum ne mai sanya abu a rai. Amma kina gani saboda mu ya mayar da komai ba komai ba tsakaninsa da Alhaji. Kuma hakan fa ba ƙaramin ciwo yake yi masa ba."

"Tsakanin uba da É—a ne wannan. Ina maganar Happy da Happiness. Sai ka shiryawa duk abin da zai biyo baya."

"In ya ganni a haka kina tunanin zai iya yi min mita? Kuka kawai za mu zauna mu sha abinmu."

Yadda yake maganar kai ka san akwai tsantsar tawakkali. Yaya Kubra a nan ta wuni har tara na dare sannan ta tafi. Ta amince za ta yi shiru amma ba don Kamal ba. So take ta samu cikin dangin wanda idan ta bijiro da buƙatar ba zai ƙi ba. Maganar neman donor ta hanyar gwamnati ba zai yiwu ba. Waɗanda su ke kan list sun yi yawa sosai.

Tsakanin Kamal da Taj a waya sai ta whtsapp. Kamal ya cire simcard da sunan baya ƙasar. Wai ya tafi China odar takalma. Taj harda mitar me yasa bai faɗa masa shirin tafiyar ba. Ya ce wanda ya bawa sautu ne ya sami matsala. Gashi kuma komai ya kammala. Ana buƙatar mai kaya. Abinka da rashin sabo da yi. Taj bai kawo komai ba ya yarda. Iyaka dai in suna waya ya dinga kiran wash wash kenan don kawai yaji Kamal yana sannu kamar ya ari baki. Bai san ciwon Kamal ɗin ya ninka nashi ba.

***

Kamar yadda Anti Zahra tayi hasashe, Salwa gidan ƙanwar babanta ta tafi. Gidan da tun farkon karatunta baban ya so taje amma saboda Mami ta raina arziƙinsu ta rufe ido ta ce bata san zance ba. Wannan tafiya da tayi sai ta sami lasisin fita yadda take so tana haɗuwa da Ummi. Gwaggonta kuma bata iya yi mata magana saboda tsoron jarabar Mami.

Bayan bugun cikin da Ummi tayi mata sai ta nuna mata cewa tana jajanta mata rashin samun soyayyar Taj. Ta kuma yi mata alƙawarin za ta taimaka mata ta sami biyan buƙata indai tana so.

"Mamina ma ta gama komai har an fara maganar aurenmu" ta faÉ—awa Ummi da farinciki.

Taɓe baki Ummin tayi "in an ɗaura muku auren kina tunanin kin yi nasara ko me? Mutumin da baya sonki kuma igiyar auren tana hannunsa."

A tsorace Salwa ta ce "kuma fa haka ne. Amma ba sona bane baya yi. HaÉ—uwarsa da matar da aka aura masa Æ´ar É—an daudu duk shi ya lalata komai. Da muna waya normal."

A zuci Ummi tayi tsaki. Wannan Salwan irin matan nan ne da sakarci ya rinjayi tunaninsu. Gashi dai ta san cewa ta girmeta amma irin shirmen da take yi da sunan soyayya ita ko da wasa ba za ta yi ba.

"Ni naga sharrin Æ´ar É—an daudu. Akanta aka koreni daga makaranta sannan aka fasa bikina. Gidanmu kowa ya tsaneni akansu. Wallahi da zan haÉ—u da Hamdiyya Habib sai na rama abin da tayi min ko yaya ne."

Idanu Salwa ta zaro tana kallonta "Hamdiyya? Ai kuwa ita ma sunanta kenan. Babanta yana aiki a Happy Taj."

"Ni ban san a ina yake ba. Amma dai shi ma sana'ar girki yake yi. Kin ganta. A yadda suke matsiyata bana jin ko iskar da mai Happy Taj yake shaƙa ita ma za ta shaƙa wataran."

Hoton Hamdi ta nuna mata wanda ta samu ta ɗauka daga wayar Siyama na ranar aurensu. Salwa ta dinga sallallami gami da rantsuwar ita ce. Ita ma Ummi ta nuna nata mamakin ƙwarai.

"Indai Hamdi ce nayi miki alƙawarin zan bada nawa taimakon na raba su da masoyinki."

"Nagode. Ni kam alkhairi ne ashe ya kai ni Glory mall rannan."

Ummi sai dariyar yaƙe kawai take yi. Ita kanta duk fitinarta abin da Alh. Usaini ya tanadarwa Taj ya yi mata hatsabibanci da yawa. Ta riga ta nuna masa tana tare dashi bata da hanyar guduwa. Haka kawai take tsoron mutane irinsa waɗanda za su iya yin komai domin biyan buƙatarsu. Rashin kunyarta bata kai nan ba. Domin kuwa duk iya shegenta akwai abubuwan da take tsoron yi don kada su koma kunnen iyayenta. Tunda Allah Ya kawo Salwa sai ta bashi shawarar amfani da ita don ya cimma burinsa.

***
Jinyar sati guda Taj ya yi kafin ya farfaÉ—o sosai. Har ya faÉ—a kuwa. Abba yaje duba shi har gidan Ahmad. Kuma ya sami tarba ta mutumci daga gare shi. Wannan ya sake daÉ—aÉ—a ransa akan halin Æ´aÆ´an Yaya Hayatu. Da zai tafi ne Taj ya yi masa maganar Hamdi.

"Abba don Allah ina neman alfarma a gareka."

"Indai zan iya in sha Allahu zan maka."

"Maganar rabani da Hamdi. Don Allah ka cire komai a ranka ka bimu da addu'a."

"Innalillahi..." Abba ya riƙe kai "faɗa maka tayi? Ban san Hamdi da surutu ba wallahi."

Taj ya yi murmushi "ba ita ta faÉ—a min ba." Ya tuna maganar da Salwa tayi ya ce "Yaya Ahmad ne ya faÉ—a. Amma ya ce kada na damu in sha Allah su Inna ba za su bari ba."

"Lamari na iyaye..."

"Allah bai bawa iyayenmu damar kashe mana aure ba. Musamman idan raba auren cutarwa ne ba hanyar samun maslaha ba."

"Ina jiye maka yawan saɓanin da kuke samu dashi. Hakan ba zai haifar da alkairi ba."

"Abba ina ƙoƙarin tsayuwa akan iyakar addini kan abin da ya shafi Alhaji. Duka abubuwan da yake fushu dani a kai shi yake nuna amincewarsa sannan ya zargeni da rashin kyautawa."

Shi dai Abba gani ya yi zai shiga tsaka mai wuya. Ya yi ta nunawa Taj illar dake tattare da zama cikin fushin iyaye.

"Don Allah ka nemi sulhu dashi kafin lokaci ya ƙure."

Muryar Taj a raunane ya ce "na jima ina wannan amma yaƙi bani dama. Zan cigaba da ƙoƙari amma Abba kada ka kuma sako aurena a ciki don Allah."

Tausayi ya bawa Abban "na daina. Allah Ya kiyaye mana ɓacin rana."

"A sunnar Annabi SAW? Inaaa, Abba ai sai dai lada."

Nauyi Abba ya fara ji tun kafin Taj ɗin ya je inda bai dace ba ya ce "naga ka fara jin sauƙi. Bari na tashi."

Taj ya dinga dariya kamar ba shi ne yake kwance kafin zuwan Abban ba.

***

Inna tana falonta ana yi mata kitso aka yi mata waya. Baƙuwar lamba ta gani. Ta ɗauka da sallama su ka gaisa da matar da ta kira.

"Na san ba ki gane ni ba tunda bamu zauna tare ba. Mahaifiyar Ahmad ce. Ahmad babban É—a namiji wajen Alh. Hayatu nake nufi."

Murmushi Inna tayi. Wannan ƙalau take kuwa? A take ta cire wayar daga kunnenta ta karanto Ayatul Kursiyyu. Ɗabi'arta ce haka. Duk abin da bata gamsu dashi ba koda bata aka yi sai ta tofe shi da Ayatul Kursiyyu kafin tayi amfani dashi. Yadda Mami ta gabatar da kanta sam bai yi mata ba.

Sai da ta gama sannan su ka gaisa da ita.

"Dama naji shiru ne ina ta sa rai da wayarki amma baki kira ba. Nace bari ni na neme ki naji me ake ciki."
Chapter 59 · 0% Book details