← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 96

Sashe 79

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma banda abin Alhaji me zai sa ya taho da Hamdiyya bayan tare da mahaifinta su ke?" Umma ta faÉ—i bayan sun É—an nutsu da murnar.

"Kema dai Jamila kamar baki san halin mijin naki ba. Ƙarshenta gani ya yi kamar Taj ya damu shi ne zai taho masa da ita don ya kwantar masa da hankali. Son ƴaƴa kuma a wajen mutumin nan ai ba a magana." In ji Mama.

Wata uwar guÉ—a su ka ji daga falo. Dama suna É—akin Mama ne. Inna ta sallami kowa ta bar Hamdi saboda baccin da ya sake É—auketa bayan tayi sallar asuba.

Fitowa su ka yi iyaye, Æ´aÆ´a da jikoki. Ashe Amma ce tayi fitowar sassafe ko wanka bata yi ba. Hijabi kawai ta É—ora akan rigar baccinta ta fito. Tana ganin matan gidan, musamman Inna sai ta kama kuka.

"In da na san aure ne zai dawo da Taj gida ai da ko kwana guda ba zai yi a matsayin É—an da uba ya kora ba. Kai, Allah mun gode maKa."

Waɗanda basu sani ba duk sun ji a lokacin. Murna da farinciki kamar me. A wajen Taj ta sami labari tun daren. Nan falon nasu su ka kira Kamal ya shigo da Taj. Sai abu ya koma kamar ranar kowa ya ƙara ganinsa tun tafiyarsa ta farko. Waɗanda basu kwana a gidan ba ma duk an kira su. Kafin bakwai sun cika gidan. Taj murmushi kawai yake yi. Yana cikin farinciki fiye da kowa. Ciwon kan ma ya tafi gabaɗaya ya tafi. Zuciyarsa kamar yau aka dasa masa ita. Babu damuwar komai a ciki. A gaban ƙafafun Amma ya zauna akan kafet tare da ƴan uwansa. Baka jin komai sai hamdala da ake yawaita yi.

"Kai ku duba min Hamdiyya ko ta tashi."

Hajiya ce tayi maganar tana mai duban ƙofar ɗakin Inna. A take mutum uku ƴan mata da wasu biyar cikin jikoki su ka miƙe a guje kowacce tana cewa ita za ta duba.

"Mijinta na zaune wa ya aike ku?" Mama tayi musu tsawa. Sai kuma ta kalli Taj "tashi kaje mana."

"Ina?" Ya tambaya don bai san kan gidan ba yanzu.

"Tana É—akin Inna" cewar Firdaus.

Tashi ya yi kafin yana waige "wanne ne?"

Yayinda wasu ke nuna masa, masu hankali wannan tambayar fami tayi musu. Inna mai yawan kawaici sai gata ta duƙar da kai tana share hawaye. Ace ɗan halak bai san ɗakin mahaifiyarsa ba a gidan ubansa! Tabbas wannan abu akwai ciwo.

Yana ganin halin da su ka shiga ya yi saurin barin wajen domin baya son ayi ɗa kwance uwa kwance. Murnar kowa za ta koma kuka. Abin da ba zai so ba. Tafiyarsa kuwa tsokanar ƴan uwansa ta janyo masa. Aka yi ta masa dariyar shaƙiyanci. Hakan sai ya hana koke koken da iyayensu su ka fara.

*
Hamdi ta fi minti goma sha biyar tana son fitowa amma tana kunyar mutan gidan. Na farko bata san lokacin da kowa ya fita ba saboda bacci.....'bacci a đakin uwar miji don abin kunya' shi ne abin da ta fara faɗawa kanta da ta farka. A saman kayanta na jiya kuma taga an ajiye sabuwar doguwar riga an cireta daga leda amma da tag. Da ta ɗaga wani irin ƙamshi ne mai daɗaɗa ruhi yake tashi a jikinta. Babu makawa turara ta aka yi. Ga wata ƙaramar ledar an saka sabon brush. Ta san ita aka ajiyewa. Banɗaki ta shiga tayi wanka a gurguje ta fito. Bata son kowa ya shigo ya ganta. Musamman Inna. Gaban dressing mirror ta zo ta tsaya ta shafa man da Innar ta nuna mata jiya. Daga nan bata sake taɓa komai ba ta saka rigarta mai kyau ta yafa ƙaramin mayafin ta fita falon ɗakin. Nan ma babu kowa shi ne ta dinga zuwa ƙofar fita tana dawowa.

Buɗe ƙofar taji anyi tayi saurin gyara zama a zatonta Inna ce. Sallamar da ya yi ce ta sake tada mata hankali. Idan wani ya shigo ya gan su a ɗakin fa? Idan Inna....

"Baki amsa min sallama ba kin tsaya kina yaba Salman Khan daga sama har ƙasa." Taj ya faɗa yana zama a kan kujerar da take.

Da sauri ta tashi tsaye tana kallon ƙofa ta ce "Ni ba kai nake kallo ba" da ƴar tsiwarta saboda ba wai ta manta abin da ya yi bane jiya.

"As if..." sai kuma ya koma kallon falon yana inhaling ƙamshinsa kafin ya miƙe tsaye "Wanne ne ɗakin baccin Inna?"

Da hannu Hamdi ta nuna masa. Yadda ya dinga tafiya ne ya taɓa mata zuciya. Ta bi bayansa har ciki. Nan kam har lumshe idanu ya dinga yi saboda yadda ƙamshin ɗakin yake nutsar masa da zuciya. Irin ƙamshin da ya dace da Innarsa. Mai sanyi, daɗi da kuma kama waje ya zauna a ran wanda ya shaƙe shi.

Juyawa tayi za ta fita ta bashi wuri sai kawai taji ya janyota ya rungume ta baya. Duƙar da kansa ya yi daidai kunnenta. Wani nau'in ƙamshin ya shaƙa mai daɗi. A ransa ya ƙudurta neman sunan mai sayarwa a wajen Inna don ba za a bar matarsa da gidansa a baya ba.

" Yau ma arziƙinki na ci aka ce na shigo ɗakin Inna kamar yadda Alhaji ya barni na shigo gidan nan domin ki. I owe yoy big time Hamdi. Thank you."

Tausayinsa taji kamar daren jiya ta ce "Na taya ka murna Happy."

"Kin dai taya mu." Ya juyo da ita suna fuskantar juna.

"A'a fa. Ni dama tun farkon zuwana Alhaji bai koreni ba."

"Sai ni uban Æ´an taurin kai ko?"

"Ni dai ban faÉ—a ba" tayi murmushi.

"Kin ayyana a ranki na sani." Ya kama hannuwanta yana murmushi.

"Ka dai tsargu kawai saboda baka da gaskiya"

Janta ya yi wajen gadon "Zo mu É—ana gadon Inna."

"Ni kaza?" Hamdi ta ce a firgice "kada ka janyo min abin faÉ—a har jikoki mana."

Zillewa tayi ta fita daga É—akin ya bita falo kafin ta fita.

Haƙuri ya bata akan maganganum Alhaji ga Abba jiya.
"Abin da nayi jiya har yasa ki fushi was for you Hamdi. Na san baki ji daÉ—i ba amma ina so muyi clearing issue É—in kafin anjima."

Da ya san amsar da za ta fito daga bakinta da bai tayar da wannan maganar ba. Kallonsa tayi. Kallo mai tarin ma'anoni. A wajenta kuwa da manufa É—aya tayi shi...(na san abin da nake yi).

"Uba uba ne Ya Taj. Nagode da baka barni na yiwa Alhaji rashin kunya ba da yanzu ina nadama don ba tarbiyar gidanmu bace. Amma ina so ka sani cewa WALLAHI ba zan taɓa sakin jiki a gidanka ba sai Alhaji ya ɗauki Abbana da darajar da Allah Ya bashi."

"Me kike nufi?" Taj ya tambayeta da yaji komai nasa ya fara kwancewa.

"Aurena kayi ba sadaka aka baka ba. Allah Ya sani ba zan iya É—auke kai ina gani ana yiwa mutum mafi girman daraja a wurina irin haka ba. Sai in ga kamar nima na yarda bai kai a girmama shi ba."

"Amma ni wane irin girma ne bana bashi?"

Abin da bata son farawa don kar ta kasa dainawa ne ya zubo. Hawaye. Hankalin Taj ya sake tashi. Ya matso ta matsa baya.

"Ba da kai nake ba. Ba kuma faɗa nake da Alhaji ba. Amma kai ma ka san irin matsayin da ya bashi daga maganarsa ta jiya. Kana gani ko zuwana nan ba shawartarsa ya yi ba duk da dai an ɗaura aure. Ko don ya taɓa yin daudanci ne?"

A lokacin ya gane Hamdi bata da labarin ainihin abin da yake tsakanin iyayensu maza. Bata san sanayyarsu ta wuce ta zaman unguwa ɗaya ba. Akwai sauran rina a kaba kenan. Amma da ta buɗe ƙofa ce ta kawo ƙarshen zancen.

Sam bata nuna musu taji maganganunsu na baya bayan nan kuma ta fahimci inda suka dosa ba. FaÉ—an hana Hamdin fitowa tayi masa.

"Abinci za ta ci a mayar da ita gida."

***

Wayar Alhaji ce ta tayar da Ahmad daga baccin da ya koma. Kamar yadda dalilai daban daban su ka hana yawancin mutan gidansu bacci, shi ma haka Salwa tayi sanadin wargaza nasa zaman lafiyar da ta gayyato Anti Zabba'u gidansa.

Ana kiran assalatu da ya tafi masallaci su ka tattara za su bar gidan ko tsinke basu gyara ba daga ɓarna da almubazzarancin da su ka yi da daddare. Suka taɓa ƙofa su ka ji a garƙame. Ya sanya kwaɗo ta waje da zai fita. Anti Zabba'u ta dinga ruwan ashariya tana cewa tafi ƙarfin Ahmad ya wulaƙanta ta.

"Mu gyara gidan nan kawai kafin ya dawo. Ni bana son rigima." Wata a cikin Æ´an matan ta ce.

Rai a ɓace Anti Zabba'u ta ce "An faɗa miki saboda shara ya rufemu? Nuna isa ne kawai da cin mutumci irin na uwarsa."

"Duk da haka gara mu gyara. Zan fi son mu fita salin alin kafin ya fahimci halin da waccan mara kunyar take ciki."

Da wannan maganar su ka duƙufa. Gyaran dai sai a hankali amma dai yafi babu. Duk abin da su ke yi kuwa Anti Zahra tana jinsu tayi zamanta a ɗaki. Mami ma taji komai tana cike da takaicin ba za ta iya ɗaukar mataki ba.

Da ya dawo don kansa ya ce su bar aikin saboda yadda su ka tasarma damalmala gidan. Ruwan mopping wannan klin aka zuba masa kuma ba a bari ya narke ba aka matse mop ɗin sama sama aka soma yaɓawa a ƙasa.

"Ga gidanka nan za mu fita amma wallahi Ahmad bashi kaci. Wannan wulaƙancin sai kayi nadamarsa."

"Boka ne fa ki ke taƙama dashi. Ni kuma da wanda ya busawa bokayen rai na dogara. Ki ajiye makaman kawai ayi zumunci Fisabilillahi."

Ƙwafa tayi. Ranta yana tafarfasa. Mutumin da ta bawa kuɗinta kuma aiki bai ci sai ya yi nadama shi ma.

Sun zo fita Ahmad ya ce "ina Salwa?"

Kamar jira suke kuwa yana magana su ka fice gabaÉ—aya a gurguje. Bai tsaya tambayarsu ko lafiya ba ya shiga É—akin ya ganta a zaune a kan kafet da kumburarriyar fuska tana kuka.

"Tunda bugun fanke kaÉ—ai su ka yi miki ki taso ki gyara gidan nan yanzu yanzu."
Chapter 79 · 0% Book details