← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 96

Sashe 51

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi Æ´an uwansa É—aya bayan É—aya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaÉ—ai sun ishi juna gayya.

"Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu." Yaya Kubra ta faÉ—i.

Tana cikin waɗanda Hamdi ta riƙe sunansu saboda kana kallonta kaga ƴar gayu ajin ƙarshe. Gashi ance likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna.

Kai ta gyaɗa har lokacin ta kasa buɗe fuskarta da kyau. Hira ce ta ɓarke kowa da irin tambayar da yake yi mata.

"A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah."

"Hajiya ai so muke ta buÉ—e bakinta."

"Baki zai buÉ—e ne babu abinci?" Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara É—auko kwanuka.

"Yau bamu ci komai ba muna jiran amaryarmu. Me za ki ci?" Wadda tayi maganar ta fara buÉ—e food flask. Akwai fried rice wadda taji kayan haÉ—i da hanta, tuwon shinkafa da miyar agushi, waina (masa), coleslaw, pepper chicken, farfesun kayan ciki da kuma nau'ikan lemo na kwali da ruwan roba. Abu kamar taro, kodayake taron ne tunda yawa garesu.

Kai a ƙasa ta ce "Na ƙoshi."

"Kada na sake jin zancen ƙoshin nan Hamdiyya. Don Allah ki saki jiki don a gida kike. Girkin yau dukkaninmu uwayenki sai da muka saka hannu." Umma tayi magana tana hararar ƴaƴan nasu "daga cewa za ki zo gaishemu duk su ka baro gidajensu saboda fitina. Ai gashi nan kun cika mata ido ta kasa sakewa."

Dariya aka yi. Aka gama ajiye tarin kayan abinci kamar na biki sannan aka shiga zuzzubawa. Hamdi ta lura kusan sa'anni ake haɗawa a tray guda. Firdaus ta nace a haɗasu a tray guda amma fir aunties ɗinta su ka ƙi. Wai matar aure ba sa'arta bace. Basu san ita babu yadda za ayi ta ci abinci da kowa a zuwan farko ba. Kuma ƙila na ƙarshe.

"Idan ba za ki iya ci su ba a zubo mana tare."

Wani irin shiru falon ya yi na wucin gadi kowa na kallon Inna kamar ba ita tayi maganar ba. Kafin kuma su kwashe da dariya suna hailing É—inta. Harda masu karambanin É—auko plate za su zuba musu.

Da wani irin sauri Hamdi ta matsa tray mafi kusa da ita harda gyara murya ta ce "Bismillahir Rahmanir Rahim."

WaÉ—anda basu yi dariya da farko ba ma sai da su ka yi yanzu. Cikin ruwan sanyi Inna tayi musu maganinta. Inna ma murmushi tayi.

Abinci ya yi daɗi. Ba don gidan surukai bane tabbas cin da Hamdi zata yi sai yafi wanda tayi na baƙunta. Su na ci ana kiran sallar la'asar. Ɗakin Mama aka ce a kai ta tayi sallah a can. Suna tafiya da Firdaus ne ta tambayi Salwa. Don duk abin da ake hankalinta bai bar kallon ƙofa ba.

"Gidan nan kowa nada kirki Firdaus. Da ina shigowa na haÉ—u da wata Æ´ar uwar taku ma a bakin gate mu ka gaisa. Naga kamar ta tafi."

"Kai anya kuwa. Kowa na nan fa."

Ba don bata riƙe sunan ba ta ce "sunanta Salma ina jin."

"Salwa ko?" Sai kuma ta kalli matan dake zaune ta ce "Ina Anti Salwa ne? Sai yanzu na lura bata nan."

Cigiyarta aka fara yi ana kiran Anti Zahra ko ta san inda ta tafi saboda bata cewa kowa za ta fita ba. Ita dai jikinta sanyi ma ya yi. Dama tun a gida da ta rangaÉ—a wannan uwar kwalliyar hankalinta bai kwanta ba.

"To ku kira ta mana. An duba banÉ—akuna? Ko bacci ya É—auketa a wani É—akin?" Cewar Hajiya.

Hamdi ta tabbata ko ma mene ne babu hannun Æ´an gidan nan, duba da yadda su ka shiga ruÉ—anin ina ta shiga. Firdaus ta ce musu ai Hamdi ta ce taga fitarta.

"Tambayata sunan wadda su ka gaisa a waje tayi shi ne na kula ita ce bata nan."

"Da shirin fita ki ka ganta?" Anti Zahra ta tambayi Hamdi.

Murmushi tayi don tambayar da take jira kenan dama.
"A'a, cewa tayi za ta je wajen shi..."

Yaya Hajiyayye ta ce "shi wa?"

"Ke kuma komai sai anyi miki gwari gwari ne? Taj take nufi ko Hamdiyya?" Yaya Zulaiha ta tambayeta.

Ta sake yin murmushi kawai. Kunyar inda take ba za ta sa ta bari Salwa ta sami biyan buƙata ba. Tayi kaɗan! A yadda tazo mata da raini da isa shi yasa za ta hana ruwa gudu matsawar da igiyar Taj a kanta. Ko sun rabu Salwa ta aure shi ba za ta ce ita ce sila har taji daɗi ba.

"Ku kira min ita. Ko Kamal. Ta dawo ciki" Anti Zahra ta faÉ—i hankalinta a tashe.

Yadda tayi yasa kowa kallonta da ayar tambaya. Sai ta wayance wai taga Salwan daga tafiya ta dawo ko abinci bata ci ba su ka fito. Nan kuwa tsoronta kada taje tayi abin da zai zubar musu da mutumci. Domin duk abin da Salwa za ta yi dole a danganta ta da Ahmad. Ita kuwa bata son abin da zai taɓa mutumcin mijinta akan wata shirmen soyayyar da babu aji a ciki.

Kamal É—in aka kira ya ce sun fita da ita da Taj amma ba jimawa za su dawo.

"Ya za ku fita da ita babu wanda ya sani?" Umma da ta kira wayar ta tambaye shi.

"Gamu nan Umma. Mun kusa gida ba in sha Allahu."

Sallah aka tafi yi. Wasu kuma suna ta aikin kwashe kwanuka. Masu aikin gidan dai za su aikatu da wanke wanke. Don ma ba da plate suke ci ba, haÉ—awa ake yi.

Hamdi ta đauro alwala ta tada sallarta a inda aka shimfiɗa mata abin sallah.

Shigarta ta kamala ta burge Mama. Taƙi jinin lokacin sallah ya yiwa mata a waje su dinga aron mayafi ko hijabi saboda nasu bai dace da tsayuwa gaban Allah ba. A ganinta rashin daraja addini ne yake sa mata fita da suturar da ba za ta musu sallah ba. Su kansu sun san hakan bai dace da tarbiyya da ma ɗa'a ga addini ba.

Da ta idar sake gaishe da Mama tayi bayan ita ma ta idar.

"Hamdiyya ina son mu yi magana. Matso kinji."

Gaban Hamdi ya É—an faÉ—i. Ko faÉ—a mata zata yi ta fara shirin zama bazawara?

"Ina fata kin san komai game da Taj yanzu da alaƙarsa da mahaifinsa?"

"Na sani" ta amsa kai a ƙasa.

Mama ta numfasa ta ce
"Kullum burinmu shi ne ƙila idan ya tashi aure su daidaita. Sai Allah Ya ƙaddara masa aurenki. Wannan ma ya ishi mai hankali tunani." Ta kamo hannunta ta riƙe "a halin yanzu mutumci da martabar mahaifinki da ta mijinki suna hannunki Hamdiyya. Hali da ɗabi'ar da za ki nuna mana ita za ta tabbatar da ɗorewar rigimar Alhaji ko kashe gobarar da ta tashi babu gaira babu dalili."

Jin an taɓo Abbanta ne yasa ƙwalla cika mata ido. Wani ɓangare na zuciyarta yana ƙara tunatar da ita laifin mahaifinsu ne da su ke fuskantar wannan abu daga ita har shi. Yayinda wani ɓangaren kuma yake kare Abba a matsayin đan Adam ma'asumi wanda ya cancanci duniya tayi masa uzuri idan ya bayyana tubansa.

Da ƙaramar murya ta ce "Me ya kamata na yi?"

"Na san ke yarinya ce amma tunda na ganki naji bani ds haufi akan zaɓin da Allah Ya yiwa Taj." Mama ta faɗi tana yi mata murmushi "Alhaji yana son mutane jajirtattu. In kin kula yaran gidan nan kowa baki gare shi. To ƙuruciya su ke samun wannan ƙwarin gwiwa ta rashin gazawa daga gare shi. Saboda haka kada ki yarda ki zama sokuwa. Ko laifi aka yi miki yafi son ki gwada ƙwatarwa kanki ƴanci. Sai abin yafi ƙarfinki ya amince ki nemi wani. Abu na biyu kuma ki kasance a kodayaushe cikin nuna hali na kyakkyawar tarbiyya. Zan so ya gani kuma ya shaida cewa ƴaƴan Habibun da yake ganin ya kauce hanya ya sun cika ƴaƴa ta kowacce fuska. Na ƙarshe kuma ki so mahaifinki da mijinki. Ki nuna masa ke kina ƙaunarsu dasu da sana'ar da Allah bai haramta musu ba. Kina alfahari dasu kuma hakan bai rageki da zama ƴar da shi ko wani zai kasa ƙauna a matsayin suruka ba."

A rayuwa akan ce wanin hanin daga Allah baiwa ne. Hamdi ta fahimci haka a yau. A shekaru irin nata ko ma fi wata ba za ta gane mene ne ainihin abin da Mama take so ba. Saboda duka maganar a ɗan dunƙule take fita. Amma yau da gobe saboda tashi a gaban Abba yasa ta gane. Magana da iya zuba zance a wajen cikakken ɗan daudu yana daga cikin alamomin da ake ganesu ma. Ya rage nasa ne nesa ba kusa ba da ya gane yana daga cikin abubuwan dake saurin saka a gane tsohuwar rayuwarsa.

A taƙaice Mama so take ita Hamdi ta saye zuciyar Alhaji da halaye masu kyau ta yadda zai gane Habibun da ya raina bai gaza ba wurin tarbiyyar ƴaƴansa. Sannan sana'ar Taj bata cikin dalilan da mutum zai yi fushi da ɗansa.

Godiya tayi mata da alƙawarin kamantawa da yardar Allah.

"In kin kula gidan nan babu ƴan ubanci tsakanin ƴaƴanmu. Duk da Alhaji ne ya ɗora mu akan turbar zaman lafiya to amma fa akwai ƙoƙari matuƙa daga Hajiya. Daga cikin irin zaman ne alhakin kula da kuma tarbiyar ƴaƴa maza ta dawo hannuna. Ba don Allah Ya tsare ba da tuni a sanadiyar korar Taj komai ya rikice mana. Ni kaina ina ɗorawa kaina laifi domin kuwa ni na ƙarfafa masa gwiwar girki. Fatana da raina da lafiyata in ga lokacin da Alhaji zai shigo da Taj ya damƙawa mahaifiyarsa."

Kowane gida akwai nasu kalar damuwar. Tana ganin kamar duk duniya sun fi kowa sai gashi gidan da tun shigowarta komai na jama'ar ciki yake burgeta su ma da nasu.
Chapter 51 · 0% Book details