← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 96

Sashe 89

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya suka yi sannan ya barta ta koma bakin aikinta. Kowanne ganye ta kunna shi ya soma tafasa kaɗan sai ta kashe ta tsane ruwansa tas. Ta haka ne miyar ba za ta yi ruwa ba yadda take so. Sannan kalar za ta fi kyau. Manja ta zuba a tukunya ta kawo garin daddawarta na annurfoods ta zuba a ciki. Ta zuba tumatir, albasa da attaruhu da tayi blending sama-sama. Ya fara suyowa ta ƙara da wata albasar da ta yayyanka mai ɗan dama. Ita ma tana yi mata daidai ta juye ruwan naman nan a kai ta ɗanɗana. Abin da bai ji ba ta ƙara ta bari ya haɗe jikinsa sannan ta fara zuba ganyen ugu da shuwaka ƴar kaɗan wadda Yaya da kanta ta wanke masu a gida ta busar. Jiķata kawai tayi da ruwan zafi ta taso. Ƙamshin girkin har falo. Ta zuba alayyahun da ugun yayi yadda take so sannan ta ƙara da kifin da ta riga ta gyara. Ta zuba garin crayfish ta rufe tukunya. Bayan minti biyar ta kashe ta saɓa murfin tukunyar.

"Zuba min nawa yanzu." Firgigit ta juya don bata ji shigowarsa ba.

"Ka bari su iso mana tunda sun ce a nan za su yi azahar."

"Ko ki bani ta laluma ko in miki ɓarna a tukunya."

Hannunsa ta ja har bakin tukunyar ta ce ya ɗanɗana miyar. Ya zuba a plate ya ɗeɓi zallar miyar da bata yi ruwa ba ga kyau a ido ya ci.

"Mrs Happy..."

"Yes" Hamdi ta amsa da É—oki.

"Kin sami 100/100"

Mamaki ta kuma bashi da ta kama rawa tana juya ƙugu. Ya kuwa dangwarar da plate ɗin ya kwasheta. Abincin da basu ci ba kenan sai da baƙinsu su ka zo. Suma kuwa su ka yi ta santin girkin amarya.

***

Jiki na rawa Yaya ta kira Inna Luba a waya tana kuka. Innarta ta tada hankali tana ta tambayarta me ya faru.

"Ke kaɗai Allah Ya bani Jinjin. Idan kika ɓoye min damuwarki waye zai faɗa min tasa? Ko ba kya son addu'ata?"

Mijinta da kishiyarta suna tsakar gidan take wannan wayar. Su ka tsayar da hirar da suke wadda har yau basu sakata a sabgarsu suna sauraronta.

"Hmmm, ƙarshenta ɗan daudun mijinta ko ƴaƴanta ne wani ya kwaso abin kunya." Cewar kishiyar Inna Sarai.

"Ko kuma ta cangala ƙafarta a inda bai kamata ba" Malam ya faɗi yana zungura baki irin shi dai babu ruwansa ɗinnan.

Inna Luba ko ta kansu bata bi ba ta cigaba da cewa Yaya ta faɗa mata me ya faru. To dama Abba Habibu yana gefe yana dariya. Da yaji kukanta yaƙi yankewa bayan ta kira wayar shi ne ya karɓe wayar.

"Inna kada ta tayar miki da hankali. Makka za ta je shi ne take kukan murna."

"Allahu Akbar kabiran" Inna Luba ta faÉ—i da dariyarta "Habibu wa ya biya mata?"

"Ni ne Inna" Abba ya bata amsa yana murmushi.

Yaya sai ta karɓe wayar "Inna ashe yana ta tarin kuɗi ban sani ba. Yaje domin ya biya mana kuɗin sun ƙaru akan yadds ya sani. Shi ne ya ce shi ya taɓa yi ni na tafi. Inna tarinsa na tsayin lokaci amma ya zaɓi ya tura miskiniyar matarsa akan yaje" ta sake fashewa da kuka.

Inna Luba ma sai da tayi kuka. Ta dinga yiwa yayarta da mijinta Mal. Umaru addu'a. Sun ƙaunaceta, sun ƙaunaci gudan jininta. Yau gashi da ranta da lafiyarta take jin Jinjin za ta keta hazo taje ƙasa mai tsarki.

Da ta gama wayar Malam dawowa yayi gabanta ya tsaya.

"Naji kina zancen zuwa Saudiyya. Waye zai je?"

"Yarinyar nan ce mijinta ya biya mata." Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye.

"Wai Jinjin ɗin ko guda cikin ƴaƴanta?" Malam ya kasa ɓoye son abin duniyar da ya taso masa haiƙan. Idan ƴar cikinsa taje Makka tabbas ya sami abin cika baki da fankama cikin abokansa a ƙauyen. Bugu da ƙari yadda bata da rowa yasa rai da jallabiya, ɗan madina da tashi-ka-fiye-naci. Ƴar bagaruwan nan a gaban su Mal. Ya'u zai dinga ɓantara yana korawa da zamzam.

Zuciyarsa ta luluƙa birnin tunani da yaji ita ce dai mai zuwa, Inna Sarai ta katse masa daddaɗan mafarkinsa.

"Daga ji an fara biye biye kenan. Dama naji labarin auren jari aka yiwa yaran nata. Shi ne za ku fara kai mazajen ana mallakesu. To dai a dinga jin tsoron Allah."

Inna Luba ta dubeta da kallon baki ishe ni kallo ba ta kawar da kai.

"An faɗa miki kowa irinku ne? Da mallakar namiji tana gabana ke kin isa Malam ya kalle ki? Ku da malaman tsibbu ku ka dogara. Ni kuwa kin san gidan Qur'ani da hadisi na fito. Har yanzu akwai irin ɗaliban babana da ko ƙwandala ba zan bayar ba za su ban mijin naki a tafin hannu."

"Ai wallahi ƙaryarki. Malam nan gani nan bari daga ke har musakar ƴarki."

Lokaci guda ga mamakin matan nasa ya daka tsawa.

"Ba na son sakarci Sarai. Duk abin da za ku yi na kishi a daina haÉ—awa da Æ´ata."

"Jinjin É—in? Mai shan inna" cewar Inna Sarai don tana ganin kamar bai gane ba.

"Shan inna kika ce ai ko? Kowa ya san lalura ce ba ita ta É—orawa kanta ba."

Wannan furucin nasa ya sanya duka matan kallonsa da mamakin da yafi na farko. Shin mafarki suke yi ko gaske ne. Inna Sarai haɓa ta riƙe daga baya ta koma tafa hannuwa. Inna Luba kuwa ƙare masa kallo tayi ta kama hanya ta wuce ɗaki. Tana jiyo shewar Inna Sarai tana kiran Malam mai kwaɗayi.

***

Kamar kullum Ahmad yau ma da ya kira Zahra sai da ya nemi Salwa. Baya kiran wayarta saboda ya san yanzu yi masa ƙaryar taja gida ba zai bata wahala ba.

Ta gaishe shi da ladabin kura ta saurari jawabinsa. Wai ya samo asibiti sun gama komai za a kwantar da Mami.

"Ke za ki zauna da ita. Akwai wani yaron office É—inmu da nayi making arrangement dashi akan kawo muku abinci idan Zahra ta gama"

"To Yaya. Allah Ya dawo daku lafiya."

Babu wata ƙofa da Salwa ta bari a buɗe wadda Ahmad zai yi zargin wani abu. Zahra ma da su ke gida ɗaya bata ga komai ba. Duka su biyun har suna addu'ar Allah Yasa shiriya ce ta zo. Ta dawo hayyacinta. Salwan da su ka sani ce a gabansu.

Ashe kwantan ɓauna tayi musu. A ranar da yamma su ka koma asibiti ita da Mami. Bayan tafiyar Zahra rufe ƙofa tayi tayi juyin murna son rai. A nan dai Ahmad bai isa ya ce ta bawa Mami su yi magana don ya tabbatar tana asibiti. Dama ce ta samu da za ta bi kadin aikin da tayi don ayi a wuce wajen.

Bari tayi sai wuraren shabiyun rana washegari ta silla wanka ta ci ado tamkar a gidan biki take ba asibiti ba. Tayi nan tayi can tana ta shiri, Mami na aikin binta da ido. Sarai Salwa ta san tuhuma ce take mata da irin kallon da take binta dashi. Ita kuwa yanzu wannan kallon ya bar yi mata kwarjini. Mamin kanta ta jima da rasa martabarta ta uwa daga ranar da ta buɗewa Salwa sirrinta na biye biyen malaman tsibbu. Gajiya tayi da kallon da ake mata ta dubi Mamin tana mai taɓe baki.

"Naga kina ta kallona. Unguwa zanje. Ga nurses nan za su kula dake kafin na dawo."

Mami ta girgiza kai. Tana takaicin yadda ta koma babu magana kuma babu damar yi da gaɓɓai. Da ƙyar ta iya girgiza kai ta kafe Salwa da ido da kallon gargaɗi. Ita kuwa tayi mirsisi tamkar bata san me Mamin take nufi ba.

Su kansu ma'aikatan asibitin sun yi mamaki sosai da ta fito zata tafi. Wata mai shara ta kasa ɓoyewa har sai da ta magantu da Salwan ta ce su dinga leƙa daƙin kafin ta dawo.

"Baiwar Allah wace irin unguwa ce wannan da ba za ki iya jiran wani a Æ´an uwa ya canjeki ba sai ki tafi?"

"Au..." Salwa ta faɗi cikin murmushi sannan ta buɗe jakarta ta fito da wallet. Dubu biyar ta miƙawa ta kusa da wadda tayi maganar "gashi ku raba da duk wadda ta tayaki dubata. Ba wani jimawa zan yi ba."

Suna ji suna gani ta fita abinta. Wadda aka bawa kuɗin kamar ta karɓi wuta sai sannan tunaninta ya dawo. Zubar da kuɗin tayi ba shiri domin ta san dokar asibitinsu. Zuwa duba mara lafiya indai ba shara ce ta kaisu ba ba huruminsu ba. Sauran ma kowacce neman zillewa tayi. Sai a ƙarshe su ka yanke shawarar kai kuɗin wurin wata babbar metiron kafin ya janyo musu matsala. Ai kuwa tayi ta fađa da su ka je.

"Mahaifiya babu lafiya ai ko jarabawa ce da ita ta haƙura tunda babu kowa."

Su dai sub-staff ɗin babu wadda ta sake magana. Suna kallo ta tashi da kuɗin a hannu ta tafi ofishin daraktan asibitin. Shi tashi yayi yaje yaga halin da Mami take ciki. Tayi fitsari har ya gangaro kan kafet. Idanun jajir tasha kukan baƙinciki. Ƴar cikinta ce ta banzatar da ita saboda nata muradin kamar yadda ta dinga yiwa nata ƴan uwan. Barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Ko ma mene ne laifinta ne!

Darakta ya bincika yaji likitan da yake kula da case É—inta wanda aka haÉ—a da Ahmad ta waya har su ka yi magana kafin a kwantar dasu.

A matsayin wurin na asibiti, fitsarin ba shi bane damuwarsu kamar fitar Salwa wadda ita ya dace ta neme su idan wani abu ya faru. Bai ɓata lokaci ba kuwa ya kira numbar Ahmad ta Saudiyya wadda su ke magana.

"Laifi ne babba wani daga waje ya biya ma'aikatanmu su yi masa personal aiki kuma a cikin asibitin. In asibitin ne bai yi muku ba kuna iya ɗauke patient ɗin. Amma ba za mu yarda da negligence daga gareku ba tunda patient ɗinku mai buƙatar kulawa ce 24/7 sannan daga baya azo ana kuka damu."

Ran Ahmad yayi matuƙar ɓaci. Ya bawa likitan haƙuri da alƙawarin za a gyara. Wayar Salwa ya shiga nema ba ji ba gani.
Chapter 89 · 0% Book details