← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 96

Sashe 83

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aure dai nayi...idan mutum yaji haushi wata asabar É—in mu kai shi É—akin doctor"

"Maimakon ka zo mu zanta yadda za ayi a shawo kanta tun kafin Æ´an kai amarya su watse ka zauna tsokana."

"On a serious note kana ganin abin da take so zai samu yanzu? Alhaji fa take so ya canja yadda yake yiwa Abba. Bata san na fita son hakan ba ta É—auki fushi dani."

Shawarwari Kamal ya soma bashi sai dai a yau ko kusa zancen ba shigarsa yake ba. Ya riga ya san da me zai kama Hamdi a hannu. Damuwarsa yanzu canjin da ya gani tattare da Kamal mai yawa tsakanin jiya da yau. Happiness is hiding something. Yana ji har cikin ɓargonsa. Ko maganganun da suke yanzu yana hango pain ɗin da ɗan uwansa yake ƙoƙarin ɓoye masa. Dole zai yi wani abu a kai. Kamal bai fi shi wayo ba.

*
Wannan asabar ta kafa tarihi mai girma a gidan Alh. Hayatu. Yinin bikin Taj da aka shirya yi a gidan wan Inna sai ya dawo gidan mahaifinsa. Ƴan uwa na kurkusa da su ka san me ya wakana tsakanin uba da ɗa sun taho harda maza irinsu dattijon arziƙi Yaya Babba su ka yi fatan alkhairi su ka tafi tare da Alhaji. Aka dinga kiran ƴan biki cewa venue ya canja last minute. Ƴaƴa, surukai da jokokin Marigayi Alh. Sule Maitakalmi sun gwangwaje cikin farinciki. Inna da ƴan uwanta su Hajiya anko su ka yi da Amma uwar goyon Taj. Ango ya fito tsakiyar dangi babu shayi ko tararrabi gwanin ban sha'awa.

Wai aka ce taɓa kiɗi taɓa karatu. Da yake a gida suke matashin ɗan Yaya Kubra ne yayi musu DJ. Ba kunya ita da kanta ta ce masa ya kunna musu waƙar da ta faɗa masa tun a gida. Ta sanya autar Alhaji Surayya tayi coordinating komai. Layi aka yi a jere tun daga Yaya Hajiyayye har ita Surayyan. Dukkaninsu sanye da anko iri ɗaya na shadda light brown. Ɗinkin mata irin ɗaya, haka ma na mazan. Daga kan Yaya Hajiyayye kuma ta jere Inna, Umma, Mama da Hajiya a gefe da gefen juna.

DJ ya saki waƙa su ka dinga bi.
Hurry hurry come carry your baby go
Come and see my mother ahh....

Kowa sai ya bar abin da yake yi ana kallon zugar gidan Alh. Hayatu. Babu wanda bai yi rawa ba idan an zo kansa, har Ahmad da tun safe yake cikin ƙunci. Sai yanzu da yaga Kamal yana walwala har yafi Taj rawar ma ya sake. Bayan sun gama matsawa su suka koma gefe suna nuna uwayensu ana ta dariya.

Wani abin burgewa shi ne da Taj ya taka har gaban Amma yana nunata da hannuwansa biyu yana faɗin come and see my mother. Bata san lokacin da ƙwala ta zubo mata ba. Ya rungumeta a wurin yana ɗan dukan bayanta.

A wurin kowa har angon wannan wunin is the best event. Kowa yaji daÉ—i. Ana la'asar Mama ta ce ayi haramar É—auko amarya a kaita gidanta.

*

Ƙarfe biyar da rabi motocin kai amarya su ka cika layin gidan Abba Habibu. Motoci na alfarma da kece raini. Taj bashi da wasu abokai na a zo a gani sai cikin ƴan uwansa. Su ne kuma su ka cika wurin ƙwai da kwarkwata. Kowa ya zo ɗaukar amaryar Taj.

Su ma biki suka yi sosai. Gidan Abba Habibu babu masaka tsinke. Abinci da abin sha sai mutum ya ture.

Ƙarfe uku aka shige ciki da amarya. Kayan gyaran jikin da Amina Meens_insense take yi Hairat matar Halliru ta saya domin yau. Ba don nisa ba da ita da kanta za ta sake yiwa Hamdi gyaran nan kafin a kaita. Sake scrubbing jikin tayi ta turarata sosai. Bayan an gama ta sanyata ta tashe jikinta da kwalacca ɗin meens ɗin. Sannan tabi gaɓoɓi da oil ɗin scentmania. Ita kanta Hamdi duk kukan rabuwa da gida da ta fara sai da ta dakata ta shaƙi ƙamshin sosai.

"Hamdi kada ki yi wasa da ƙamshi. A jikinki da gidanki. Rahama ne shi babba kuma abokin yaƙi da nasarar kamo zuciyar maigida. Mace mai wayo bata bari mijinta yaji wari a jikinta."

"Ba za ki amsa ba uwar miskilanci? Ana baki darasi kin wani haÉ—e rai." Cewar Sajida tana harararta da gefen ido.

"Idan na amsa ace bani da kunya. Nayi shirun kuma ban tsira ba. Me ya hanaki yi min kara ki ce to?" Hamdi ta rama hararar.

"Ba laifinki bane. Gidan miji za ki kwana yau, dole ki min rashin kunya."
Sajida ta faÉ—a da rawar murya.

"Kinga kin saka ta kuka ko?" Zee ta matsa jikin Sajida ganin har ta soma zubar da hawaye.

Jiki a sanyaye Hamdi ta matsa kusa dasu "ni me na ce don Allah. In ranki ya ɓaci ki faɗa min mana. Meye na kuka?" Ita ma sai ƙwalla.

"To ni wa zan rarrasa cikin ku?" Zee ma ta kama kuka.

Rungume juna su ka yi suka kama kuka haiƙan. Ta tabbata yau su uku kowa makwancinta daban. Aure abin so kuma abin alkhairi ya rabasu.

Hairat fita tayi ta basu wuri. Ana ganinta a waje aka fara tambayar ko Hamdi ta gama shiri.

"Yaya leƙa ɗakin." Ta ce da Yaya.

"Ga iyayensu nan..." Yaya ta faÉ—i cikin kunya.

Hairat kuwa ta ce ita ya dace taje. Ƴan uwan nasu ma su ka goyi baya. Tana shiga ta samesu su uku suna sharɓar hawaye. Da su ka ganta wajenta su ka ƙarasa kowacce kukanta ya ƙaru. Ta fara yi musu nasiha sai gashi tabi sahu. Sai da aka ji shiru aka biyo bayansu. Inna Luba da kanta da sanya Hamdi a gaba ta saka kaya. Riga da zani na leshi mai ɗan karen laushi. Fuskarta babu makeup sai hoda da kwalli da ɗan pink lipstick sama sama. A haka ma tayi kyau sosai.

"Har a fita ban yarda ki sake sanya min ƴa kuka ba. Ki daure ki riƙe hawayenki don Allah."

"Haba Inna? Ba ma ta ni kike yi ba sai Yaya?" Hamdi ta kyaɓe fuska.

"So so ne Hamdiyya..." cewar Inna Luba tana dariyar tsokanar jikar tata.

"Amma son kai yafi ko? Naji da ana cewa wai mutane sun fi son jikokinsu akan Æ´aÆ´a."

Inna Luba ta kaɗa baki ta ce "Duk ƙarya ne."

"Ai kuwa sai na faÉ—awa Yaya ta daina jin babu daÉ—i idan kina shareta."

"Zo nan don ƙaniyarki" Inna Luba ta yafito ta ta gudu.

Matar Kawu Abduƙadir ƙanin Abba Habibu ce ta zauna da Hamdi bayan ta gama shirin ta bata kayan gyara ba mata da sati guda kenan ana bata ta shanye.

"Ki kula da abincin da kike ci da tsafta. Wannan sinadari ne. Kada ki dinga yi musu shan ƙoshi don Allah. Komai saisa-saisa yafi"

Sunkuyar da kai tayi har ta gama yi mata bayani ta tashi. Daga nan gida ya kaure da guÉ—ar shigowar dangin Taj. Cikin Hamdi ya yamutsa da wata irin fargaba. Kukansu ita da su Zee ya dawo sabo fil. Aka fita da ita ko Abbanta da taci burin gani bata sanya a ido ba. Yadda ya bar gidan ranar kai Sajida ita ma haka yayi mata. Ba zai iya ganin fitarsu ba.

A motar Kamal aka sanya amarya. Mummy matar Yaya Babba da uwargidan Alh. Lurwanu wan Inna su ka saka ta a tsakiya. A gaba kuma wata Anti Zinatu ce.

Rantsuwa kala kala Kamal ya yiwa Yaya Kubra akan lafiyarsa kafin ta bari ya fito. Tana barazanar za ta tona masa asiri yayi dariya.

"Ni za ki lallaɓa kafin na tona naki asirin. Alhaji da Yaya Ahmad sun san da ciwon. Na rufa miki asiri ne dai kawai..."

"Alhaji ya sani? Kamal ka kyauta kenan? Idan ya san nima na ɓoye ka san me zai min?" Ta katse shi a tsorace.

"Shi yasa nace ki barni na fita kada na janyo miki" dariya ya yi mata ta bashi hanya da zai fita ya ce "ba maganarki ce bana ji ba, sai dai ina so ki min haƙuri don ban sani ba ko wannan ne abu na ƙarshe da zan yiwa Taj."

Haka ya fita ya barta tana share hawaye. Ta gama ƙarar da duk basirarta da waɗanda za ta nema amma ba a dace ba.

***

Gidan amarya ko yaya yake sai kaji ana son barka. Balle kuma gidan Tajuddin da Hamdiyya. Duk wanda ya shiga da santin gidan yake fita. Kayan ƙawa da ƙyale ƙyale an saka amma masu aji wanda basu cika waje sannan basu fiye ƙyalƙyali ba. Harkar girma da girma kawai. Inna da masoyanta waɗanda su ka goya mata baya sun yi rawar gani sosai. Haka zalika Abba Habibu da Yaya. Basu kwanta anyi musu komai ko don gudun raini da wulaƙanci.

Da sunan Allah a baki da zuci iyaye su ka kai Hamdi ɗakin aurenta. Aka kuma umarci ƴan uwanta da su bar kuka haka nan saboda ta sami nutsuwa. A gidan aka yi sallar magariba sannan aka soma tafiya. Yan matan dangin amarya da ango kowa da irin salon nasiha da shaƙiyancin da yake yiwa amarya a kunne. Da aka watse ya rage Sajida da Zee sai Siyama da sa'aninsu daga ƴaƴan ƴan uwan Abba Habibu. Sun zage sun sake gyare komai kafin shigowar angwaye. Iyaa bata bari Ummi ta bi su ba.

*

Taj ya haɗuwa da Alhaji kafin su fita. So yayi su gana su kaɗai ya ƙara yi masa godiyar dawo dashi cikin ahalinsa da yayi. Sannan yana so ya faɗa masa yanayin Kamal da baya yi masa daɗi. A ƙarshe ya roƙe shi ya matsawa Kamal ɗin ya sanar dashi damuwarsa. Tunda ya san ba zai kalli idon Alhaji ya yi masa ƙarya ba.

Da Ahmad su ka shiga wajensu Hajiya. Kowanne É—aki idan yaje sai anyi masa addu'a. Sisters É—insa su ka kama koke koke. Ahmad ya haÉ—asu manya da yara ya dinga faÉ—a.

"Auren ku ke yiwa kuka?"

"Kwanansa É—aya a gida fa zai sake tafiya."

"Sai ka koma basu gaji da ganinka ba" cewar Ahmad yana haɗe rai don baya son ɓata lokacin da ake yi.

Taj ya kanne ido É—aya ya kawar da kai gefe "ni dai Hamdi"

"Lahhhh"
Chapter 83 · 0% Book details