Sashe 36
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita ma takaicin ɗaga muryar tasa take yi. Ga zaƙin murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki.
"Da ka É—an rage maganar saboda Æ´an biki ba su san auren Zee aka É—aura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton..."
"Ba zato bane Jinjin. Ƴaƴan Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci ɗaya."
Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haÉ—awa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.
"Shirmen Ƴar Ficika ne. Shi da ko wurin ɗaurin auren basu je ba?"
Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ƙarfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. Ƙafafunsa sun yi buɗu buɗu.
"Yaya! Yaya!!" Ya dinga ƙwala kira kamar makaho na neman ɗan jagoransa.
"Kai Halifa lafiyarka kuwa?" Wata maƙociyarsu ta tambaye shi.
"Ina Yaya?" Ya faÉ—i yana dariya.
Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida.
"Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu" cewar Inna Luba.
Murmushi ya yi yana duban Æ´an uwansa.
"Yaya an É—aura. Duka su ukun an É—aura musu aure."
Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa.
"Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?"
"Ya Sajida da Yaya Safwan."
Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah."
Anti Zinatu ta ce "Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku."
Ya murmusa da farincikinsa "a'a, sai Ya Hamdi da Happy."
Inna Luba ta ware idanu a tsorace "Hafi? Mutum ne?"
Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau.
"Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu."
Cikin Hamdi wata irin ƙullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu.
"Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?"
"Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa É—ansa aurenki. Sadakinki fa dubu É—ari biyu. Cash in faÉ—a miki."
Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan.
Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa "Ku riƙeta...Sajida kama hannun. A'a rungumota kawai kada ta kai ƙasa."
Luuu haka taji ƙafafunta suna narkewa su kaɗai za su kaita ƙasa. Kafin ta gama faɗuwa aka tallafota zuwa falo. Akan doguwar kujera aka kwantar da ita. Ana yi mata fifita. Daga nan ba za ta iya tuna me ya faru ba.
***
Ƴan uwa da abokan arziƙi dafifi su ka yi wajen taya Abba murna a masallacin. Yadda al'amura su ka kasance maƙiyi ne kaɗai zai ce bai jidaɗi ba.
Baba Maje baki har kunne shi da Baballe. Murna yake yi, ya sami damar kyautatawa amininsa bayan abin da Ummi tayi. Don tun daga lokacin shi da Iyaa su ka ja baya da iyalin Abba. Suna masu jin kunyar abin da ƴarsu tayi. Duk rashin son fita sai ya zamana Yaya ce mai ƙoƙarin zuwa. A yawan ziyarar da take kai musu ne Baballe yaga Zee ya ƙyasa. Ashe rabonsa ce bai sani ba.
A ɓangaren Taj kuma inda mahaifinsa yake ya zauna tare da ƴan uwansa. Kawunnai ne na ɓangaren Alhaji shi kaɗai sai ƴan uwansa su Ahmad. Yadda ya hana Taj faɗawa su Inna tun jiya, haka ya tsallake ƴan uwansu maza da dukkanin abokansa.
Mutane na ragowa ya tashi da sauri ya fita. Ƙaninsa Baba Amadu ya tare shi ganin sun nufi wurin motocinsu.
"Haba Yaya Hayatu. Ba za mu tsaya mu gaisa da baban amaryar ba za mu tafi?"
"Baka gane shi bane? Habibu ne fa. Meye abin gaisawa a nan?" Ya amsa a wulaƙance
Daga nan gaban Taj ya faÉ—i. Su ka haÉ—a ido da Kamal kowannensu da tunanin da yake ransa. Yaya Babba kuwa haÉ—e rai ya yi.
"Da alama akwai manufar da ta sanyaka amincewa auren nan bagatatan. Dama nayi mamaki da ka sanar dani jiya a ƙurarren lokaci. To amma saboda Taj ne shiyasa na zo don kada sai an zo ɗaurawa ka ce ka fasa don kawai ka muzanta shi."
Alhaji ya yi murmushi "bani da wata manufa. Auren fitar da ubangidansa a daudanci daga kunyar al'umma yake son yi kuma nayi masa don kada ma a sami bakin zagina."
Kallon tsananin mamaki Taj ya bi shi da shi. Bakinsa ya mutu. Tun ba a je ko'ina ba ya gane shigo-shigo ba zurfi Alhaji ya yi masa.
"Alhaji don Allah ka tsaya" Ahmad ya roƙe shi don baya jindaɗin ganin manya su na sa'in'sa.
"Kaima ban maka izini tsayuwar ba. Yanzu ku sai ku yi musabaha da mutum irin wannan?" Ya nuno Abba da yake tahowa inda suke da Æ´an abokansa.
Abin ban sha'awa babu ɗan daudu ko ɗaya. Dama su Ƴar Ficika ne. Shi kuma tunda a gabansa mahaifin Safwan ya ci mutumcin Abban sai ya ce shi da yaransa ba za su ɗaurin auren ba don kada a sake samun matsala.
Bawan Allah bai san wainar da ake toyawa ba. Da ya iso hannu ya miƙawa Yaya Babba gami da rissinawa sosai cikin girmamawa. Har sai da Taj yaji wani iri.
"Yaya barka da rana?"
Fuskarsa shi ma a sake ya ce "Sannu Habibu. Shekaru da yawa. Gashi mun zama surukai."
Abba ya murmusa "ina ni ina surukuta da ku Yaya? Ƴa taku ce. Sai dai ace ta bar gida ta sake komawa gida."
Ragowar ƴan uwan Alhaji su ka ƙarbi musabaharsa saboda Yaya Babba ya buɗe musu hanya. Ransa fari ƙal ya sake rissinawa ya miƙa hannu ga Alhaji.
"Yaya Hayatu ..."
Kallon da Alhaji ya yiwa hannun yafi ƙarfin a kira shi na wulaƙanci. Sai dai a ce ƙasƙanci. Domin ba ma da duka ƙwayar idon ya kalle shi ba. Duniya bai ga abin da zai sa ya kama wannan hannun da ya gama lalacewa da bleaching ba. Knuckles ɗin (gaɓoɓin yatsu) duka baƙaƙe ƙirin. Ragowar hannun kuma fari da ɗigo ɗigon baƙi.
Yawu mai ɗaci Taj ya haɗiya ganin Abba ya shanye abin da aka yi masa tamkar babu komai. Hannun kawai ya mayar ya ƙara duƙawa.
"Barka da rana."
"Kaga tashi don Allah. Bana son wannan ɗabi'ar taku ta gaisuwa kamar maroƙa."
"Alhaji" Taj ya kira sunansa da ɗan ƙarfi ba tare da tunanin komai ba sama da son ya tunatar da shi me yake aikatawa a gaban mutane.
Ko kallonsa Alhaji bai yi ba. Yaya Babba ne ma ya yi masa alama da ya yi shiru kawai.
Ba tare da nuna ɓacin rai ba Abba ya miƙe yana murmushi. Zuciyar Taj ta kasa jurar ganin wannan abu. Barin wurin ya so yi. Hannun Kamal a jikin babbar rigarsa ya hana shi motsawa.
Alhaji ya ce "Ina son ganinka yau bayan Isha'i. Ai ka san gidana ko?"
"Gaskiya ban sani ba. Amma ko Taj sai na biyo in sha Allahu."
Alhaji ya yi irin murmushin nan na ɓacin rai. Yana magana ciki ciki "na manta yanzu kai ne uban. To kada ku wuce Isha dai." Ya kalli Taj "kai kuma kada ka manta dokar gidana a kanka. Da ishan ma don ni na kiraka ne."
Mota ya faÉ—a abinsa direba ya ja. Abba ya sake yin murmushi yana É—agawa motar hannu tare da faÉ—in "Allah Ya kiyaye hanya."
Hannun nasa Taj ya sauke masa ya nuna masa Baba Maje "Abba kaje ga abokinka can ina jin kai yake nema."
Sai da ya tafi ƴan uwan Alhaji su ka soma bashi baki. Baki ma kasa motsawa ya yi saboda ɓacin rai. Ya dai dinga gyaɗa kai kawai. Yaya Babba ne ƙarshen yi masa magana.
"Ina so ka sani cewa a musulunci iyaye suna da babbar daraja. Bana so abin da Hayatu yake yi maka ya zama sanadin da za ka mayar da martani. Domin idan kayi haka lallai kayi asara. Baka jidaÉ—insa ba a duniya kuma a lahira ma ba za ka sami rangwame ba."
Godiya sosai ya yiwa Yaya Babban sannan su ka tafi.
Ahmad na ganin babu sauran manyan ya ce masa "mu tafi gida mu san yadda za mu yi da matan gidan. Na san dukkaninmu ba za ta yi mana kyau ba. Ace kayi aure babu wadda ta sani."
Kafin yanzu da wannan tunanin Taj ya kwana. Amma ƙullin da Alhaji ya soma yi masa ya sa ya daina damuwa.
"Baka ji yana yi min tuni akan kada na shigar masa gida ba?"
"Ni kuma a ganina wannan shi ne lokacin da ya dace ka take wannan dokar ka shiga gidan. Rayukansu za su ɓaci. Sannan bana jin za su yarda su biyoka gidan Yaya. To a ina ka ke jin za ku haɗu har ka yi musu bayani na fahimta? Don ni ban hango sun amsa wayarka ba balle su saurareka" cewar Abba wani sarkin zuciyar.
Bishir É—an salihin cikin mazan ya ce "ÆŠauko sun dai ya dace ayi su haÉ—u a gidan Yaya ko gidan Yaya Babba."
Agogo Ahmad ya kalla. Lokaci na ƙurewa kuma ba su sami matsaya ba.
"Mu je gidana ayi shawara. Zan kira su Yaya Hajiyayye dukkaninsu yanzu a hanya. Idan ya so ko mu kaÉ—ai ne sai mu je mu yi musu bayani."