Sashe 47
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin ci sa'a yunwa nake ji da na tashi na gwada miki yadda ake yi."
"Bana ma son sani" ta zare wayar fitila daga inda aka jona chaji ta kunna. A take haske ya wadata a falon. Ta buÉ—e fridge ta É—auko ruwan sanyi ta É—auko da kunun ayan da Yaya ta haÉ—a da rana.
Ta kawo gabansa ta ajiye a gefen tray É—in sannan taje ta kawo kofuna guda biyu ta dire masa. Kujerar nesa dashi taje ta zauna
"Nagode" ya ce bayan ya gama. Abincin kaÉ—an ya rage.
Hamdi ta kalle shi da wutsiyar ido "banlbu daÉ—i ko? Ba irin haka ka saba dafawa ba?"
"Ke dai ki ce kina son in yaba miki. To nayi. Yayi min daÉ—i sosai."
Bata yarda dashi ba "duk iya girkinka?"
"Girkina daban, na matata Hamdiyya ma daban. Zan dinga taimaka miki a kitchen amma ba kullum ba. Ina son in dawo gida kamar kowane namiji in ci abincin da matar gidan ta dafa."
Yana lura da yadda maganarsa tayi mata daɗi. Ba dai ta son nunawa ne. Shi kuwa indai tana da kunnuwa to ba zai fasa faɗin maganganun da za su yi tasiri a zuciyarta ba. Tashi yayi ita ma ta miƙe.
"Bari na ƙarasa gida na huta kuma."
Tray ɗin ta duƙa ta ɗauka ya ce "na faɗawa Yaya ranar asabar zan zo mu je gidanmu."
"Gidanmu ko gidanku?" Ta ce a tsorace.
"Saurin me kike yi? Gidan iyayena ba gidana ni da ke da Æ´aÆ´anmu ba"
Ya ƙare maganar yana kashe mata ido.
"Sai da safe" tayi masa fuskar shanu. Hira dashi tana yi mata daÉ—i amma biyewa zuciya ganganci ne.
"Oh, don Allah ɗauko min underwear ɗinki na sama da na ƙasa ana son ganin size."
Tray ɗin hannunta ta kusa saki da taji me ya ce. Bata ankara ba taji hannuwansa sun damƙi nata. A karo na biyu su ka ji wannan yanayin da ya bambanta da in sun taɓa kowa. Zame nata hannun tayi ta bar masa tray ɗin.
Taj ya ce "yauwa yi sauri. Kuma don Allah wankakku."
Wata uwar harara da ta banka masa ba shiri ya ajiye tray É—in a inda ta É—auka.
"Ai gaskiya ce. Naji an ce Æ´an mata maimaici su ke na sati biyu ko ma fi kafin su wanke."
Kamar za tayi kuka ta ce "Don sharri? To ba zan bayar ba. Idan ma bokanka ne yake so kace masa na hana. Ya turo aljanu su satar masa."
"Dare ne dai kuma babu wuta. Ki cigaba da kiraye kirayen abubuwa. In su ka zo..." ya faÉ—i a hankali yadda zancen zai shigeta.
Ai kuwa bayanta ta kalla da sauri ta ɗan matso kusa dashi. Tausayi ta bashi. Duk tayi wiƙi wiƙi da idanu.
"Yayata ce ta ce na tambayeki fa."
"Size ake tambaya ai. Ya za ka ce in baka?" Hamdi ta ce da mamakin irin nasa tunanin.
"Don kada ki faÉ—a min ba daidai ba. Nafi son komai accurate."
"To ba zan bayar ba. Ka kamanta yadda ya dace." Ta ɗora hannuwa a ƙugu.
Taj ya san bata da masaniyar shigar da tayi. Da bata yi wannan tsayuwar a gabansa ba.
"Don't dare me Hamdi. In ki ka yi wasa da hannuna zan kamanta."
Da sauri ta koma bakin ƙofar falon har tana tuntuɓe saboda gigitar kalamansa.
"Matsoraciya."
"Naji."
"Za ki turo size É—in ko in sa Zee ta É—auko min na tafi dasu?"
Zai aika ta sani yanzu. Tunda ya iya faÉ—a mata zasu riga haihuwa ai komai ma is possible yanzu.
"Zan turo." Ta ce a hankali.
"Good girl. Sai jibin ko?"
Kada azo tafiya ya ce su biyu kaÉ—ai shi yasa ta ce masa da Zee za su je. Shi kuma ya ce a'a don yanzu matar aure ce. Sai ta ce to da Halifa.
"Haka kawai sai in ɗauke ki da ƙato a mota?"
Hamdi ta ɓata rai "Halifan ne ƙato?"
"Yanzu duk duniya daga Abba sai ni sai Alhajina ne kaɗai normal maza a wajenki. Sauran kowa ƙato ne."
"Kaima ƙaton ne kuwa."
"Mijin ƙatuwa ba."
Dariya yake yi da yayi maganar. Sai gata tana murmushi. Fushi dashi ma da alama ɓacin lokaci ne. Sai da safe ya yi mata ya tafi. Ta tattare kwanukan ta tafi kitchen tana wankewa hirarsu na dawo mata. Da ta gama gidan tsit yayi mata. Yau ko inji Halifa bai fito ya kunna ba da aka ɗauke wuta. Bata san Yaya ce ta hana ba. Wai ƙarar za ta dami Taj.
Ƙaramin table ɗin da ta ɗora masa tray taje ɗaukewa sai taga wayarsa. Ta ɗaga ta juyata a hannunta. Dole masu iphone su ke jin kansu. Wayar a hannu ma daban take. Abba ta yanke shawarar bawa da safe don da alama yau sun yi baccin wuri.
Kimanin rabin awa da tafiyarsa taga kira daga wani suna an sa Anti Zahra. Sai da aka kira na biyu sannan ta ɗauka. Muryarsa taji ta saki ranta. Ya ce ta ajiye wayar zai zo ya karɓa washegari.
"Zan bawa Abba ya taho maka da ita."
"To nagode. Goodnight."
*
Famfo iya famfo Mami ta yiwa Salwa. Tunda ta koma gida da ramar kwana biyu amma kamar tayi jinya hankalin Mamin ya tashi. Ta kira Ahmad ta ƙare masa tanadi. Harda kiransa wanda baya kishinta.
"Aure kuma tunda tana so ko uban naku bai isa ya hana ba."
"Mami kin fi so ta kai kanta inda ba a sonta? A ƙarshe ta dinga fuskantar wulaƙanci."
"Rufe min baki. Matan gidanku sun gama cinye maka zuciya baka iya taɓuka komai. Arziƙin Taj kai kana da rabinsa ne?"
"Kowa rabonsa yake ci Mami. Don Allah ki daina biyewa Salwa."
Cikin faɗa tayi masa tsawa "Salwa za ta dawo. Ina so ka yiwa Alhajin naku maganarta don na san yana ƙaunarta. Ita wadda Taj ɗin ya aura na riga na samu bayani akanta. Bata da wani abin nunawa balle ta kara da jinina."
Ta inda take shiga daban da inda take fita. Ran Ahmad ya gama ɓaci da su ka gama wayar. Yana jiran dawowarta ya nuna mata kuskuren sanya Mami tayi masa irin wannan faɗan.
Bayan Mami ta gama dashi kan Salwan ta koma tana yi mata nata faɗan na rashin ɗaukar shawararta. Kissa ba ƙaramar makami bace a wajen mata.
"Ki bari sai kamar shaÉ—ayan dare ki kira shi ki gigita shi da kalamai masu daÉ—i."
Sunkuyar da kai tayi tana murmushi.
"Ki nuna masa yafi kowanne namiji ba tare da kin zubar da ajinki ba."
Sai da ta gama kwasar huÉ—uba sannan ta shige É—aki. Ta gama komai da wuri ta zauna jira. ShaÉ—aya da kwata na dare kuwa ta doka kira wayar Taj.
RAYUWA DA GIÆI 21
Batul Mamman💖
This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ƙamshi babu ruwansa da gari ko ƙasa. Wuyarta ciniki ya faɗa. Za ku sami undiluted oil perfumes ɗinku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haɗa kwalabe daban daban ki gigita waɗanda ya halatta su ji ƙamshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ƙarin bayani a tuntuɓeta a wannan layin 07065525409 .
***
Da farko da taji ƙarar wayar cikin baccin da ya fara ɗaukarta tsorata tayi don ta manta da ita. Niyyarta ta barta ta gama sai ta kashe, ko waye ya kira da kansa. Ita ba mai son amsa wayar mutane bace. Wani kiran ne ya sake shigowa immediately bayan na farkon ya katse. Ta daure ta wartsake idanu ta kalli sunan mai kiran SALWA B. Wani irin tunani ne ya shiga karakaina a ƙoƙon ranta. Meye ma'anar B ɗin? Bichi, Bunkure? Ba dai brother bane tunda sunan mata ne. To ko dai baby yake nufi? Ko bestie? Haba! Zuciyarta tayi wani irin kumburi ta taso mata har wuya. Harda wani ɗaci-ɗaci kamar ta tsotsi flagyl. Mantawa tayi da maganarsu da Abba a karo na biyu yau ta amsa kiran ido rufe. Garin sauri harda _record_ ta danna a rashin sani da ta mannata a kunnenta.
"Ya Taj na tasheka ko?"
Salwa tayi magana da sassanyar murya da ta sha kwaskwarima domin yin tasiri a zuciyar wanda ake yiwa.
"Ayya ba shi bane. Ya manta wayar ne." Hamdi ma ta mayar da zuƙaƙƙiyar murya.
Ba shiri Salwa ta zabura ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi. Da ta gama shirin yadda za ta dinga mirginawa hagu da dama saboda daÉ—in murya da hirar da za su yi da Taj.
Gabanta na faÉ—uwa ta ce "Wace ce ke?"
Tana buÉ—e murya normal, Hamdi ta gane wannan wayar ba ta Æ´ar uwa bace. In ma Æ´ar uwar ce to tabbas cousin ce.
"Suna na Hamdiyya." Ta ce a kunyace "manta wayar ya yi a wajena É—azu."
Tsakin Salwa taji wanda ya yi mata ciwo matuƙa kafin ta ji ta ce,
"Wai Æ´ar gidan É—an daudun da ya aura last week ce?"
"Laahhh, ashe kin sanni."
Hamdi ta amsa da sauran fara'a a muryarta kamar gaske. Bata so tayi saurin kwafsawa kuma ya kasance Salwan Æ´ar gidansu ce.
Cikin huÉ—ubar Mami harda kada ta ragawa yarinyar da ya aura. Tunda ance musu sakandire ta gama sun tabbatar babu wayo da wayewa a tare da ita. Tsorata ta da nuna mata ita É—in ba komai bace zai taimaka sosai wajen samawa Salwa Æ´anci idan ta shiga gidan Taj.
"Da alama kina da rawar kai. To amma ba zan hana ki ba. Lokacinki ne. Ki dai sanya a zuciyarki cewa nan ba da jimawa ba wadda ta fi ki son Taj za ta shigo rayuwarsa."
Hanci Hamdi ta ja kamar mai shirin kuka "Anti Salwa nayi muku laifi ne har ku ke son bashi wata daga aurenmu? Ita wadda za ku bashi É—in bana jin ta kai ni son shi. Don dai bamu haÉ—u bane da kema sai kin yaba min. Tarbiyya da iya kula da miji duka É—an daudu da miskiniyar da su ka haife ni sun koya min."