Sashe 37
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja motar Ahmad su ka tafi da Bishir. A hanya Ahmad É—in duk wata yayarsu ta kusa da ta nesa ya kira ta ya sanar da ita. Bishir aka bari da kiran sauran. Duk wadda ta sami hali ta taho gidan Ahmad. Amma banda na cikin gidansu su uku. Idan aka kirasu dole a zargi wani abu. Yadda shawara ta kaya za su haÉ—u su je gida wuraren biyar na yamma.
*
Kamal na tuƙi ya ɗan kall Taj "Yanzu ka fahimci me yasa nace ka bar maganar auren nan Happy? A gaban jama'a kana ganin yadda Alhaji ya tasarma wulaƙanta Abba."
Kamar bai ji shi ba sai ya yi masa tambaya.
"Me yasa idan na zo da abu baya bani zaɓi Happiness? Sai dai ya bari nayi sannan ya ɗauki hukunci mai tsauri a kai."
"Saboda baka tsayawa kayi hangen me zai je ya dawo. Har cewa nayi zan auri Sajida duk don ka haƙura da gaggawar nan amma ka ƙi."
"Ko bana son Hamdi ba zan yarda ka auri Sajida ba. Yadda ya sallama ni haka zai yi maka. Sannan kuma ya É—ora laifin naka a kaina."
Kamal ya haÉ—e gira "akan me zai É—ora maka?"
"A dalilin kafi kowa kusanci dani mana." Taj ya bashi amsa.
Tunanin bai zo masa ba a baya sai yanzu. Tabbas da ya yi auren laifin su biyu Alhaji zai rabawa. Yana ma mamakin da ya ƙyale shi ya buɗe boutique a wurin Taj. Bai zaci zai sami goyon bayansa da wuri ba.
Taj ne ya yi magana bayan dogon shirun da su ka yi.
"Happiness, ba fa zan bari ya wulaƙanta Abba ba. Ni ban ga dalilin da zai sa mu dinga kasa yiwa mai tsohon laifi uzuri ba. Hakan zai iya sawa su koma ga laifin."
Tausayinsa Kamal yake ji. Sai dai kuma yana ganin kamar harda taurin kan Taj. Da zai sauke nasa kambun ya yiwa Alhaji biyayya da tuni an jima da wuce wannan wajen.
"Na sani. Amma akwai hanyoyin samun lada da yawa sama da zaɓar wanin mahaifinka."
Idanun Taj sai da su ka yi ja kafin ya bashi amsa.
"Baka ji me nace bane? Happiness, Alhaji bai taɓa bani zaɓi ba. He just pushes me away and gets angry when I comply (ingiza ni yake yi kuma ya yi fushi idan nayi yadda yake so). Auren nan ina faɗa bai wani ja ba ya amince min. In baka manta ba certificate kawai naje na nunawa Yaya Babba shi kenan ya koreni. Da cewa ya yi in zaɓi girki ko zaman gidansa kaima ka san ba zan taɓa barinku ba. Ba don Amma..."
Zaro idanu ya yi waje ya shiga karanto Innalillahi hankalinsa a tashe. Ya kai hannu ya damƙi hannun daman Kamal dake riƙe da sitiyari tunda yafi kusa da shi.
"Kamal...ya zan yi? Amma. Ya Rabbi." Ya faÉ—i cikin tashin hankali.
"Me ya same ta?" Kamal É—in ma duk ya gama ruÉ—ewa.
"Ya za ta ɗauki zancen nan? Ga maganar Anisa. Kada hakan ya janyo mata matsala da Daddy." Ya kuma faɗi, damuwarsa na ƙaruwa.
Har su ka ƙarasa gidan Ahmad suna jimamin yadda za su tunkari Amma da zancen nan. Kamal ya ƙara tayar masa da hankali da ya ce ya tabbata cikin kawunnansu ba za a rasa wanda zai faɗa mata ba.
"Kenan ba a bakina za ta fara ji ba? Shinenan. Na gama yawo."
Yadda ya marairaice Kamal dariya ya yi masa.
***
Falon gidan Ahmad ya cika ya tumbatsa da Æ´aÆ´an Alh. Hayatu. Duk wadda take cikin garin Kano ta na zaune a wurin.
Yaya Zulaiha ce ƴa ta biyu a gidan. Ita ta karɓe girman daga hannun Hajiyayye don ta fi ta zafi. Ta yiwa Taj faɗa sosai.
"Don kana son taimako bai dace ka dinga yin abin da zai cigaba da ɓata masa rai ba. Mahaifi ne fa."
Haƙuri ya bata da alƙawarin zai yi ƙoƙari a nasa ɓangaren yaga al'amura sun daidaita. Ya ƙara da nanata musu cewa abin ne ya zo akan gaɓa. Yana son Hamdi tun farkon haɗuwarsu. Ya yi haka ne saboda sanin halin mata tunda cikinsu ya tashi. Idan ta kuskure musu, tsaf za a goranta mata wata rana.
Babbar yaya Hajiyayye tana jin an kashe wancan zance sai cewa tayi,
"Ya maganar lefe? Ya kamata kafin a soma zancen tariya mu haÉ—a wanda zai fiddo darajar gidanmu."
"Kai jama'a, Ya Hajiyayye ana ga yaƙi kina ga ƙura. Wa yake ta lefe alhalin uwayen ango basu san anyi auren ba?" Wata yayar tasu ta ce.
Duk sai su ka kama dariya. Hajiyayye dai ta fuske abinta ta ce a samo takarda tayi list. Tunda dai an riga an ɗaura auren sannan bata fatan ace saki ya biyo baya ai kuwa zancen lefe ya zama tilas. Ƴan son biki irinta su ka goya mata baya. Daɗi ya isheta domin ƙannen nata wani sa'in tamkar ƴaƴanta ta ɗaukesu.
"Sai ka tambayar min ita size É—in takalmi da undies. In su Mama sun bamu goyon baya da wuri kaga ba sai an yi wani jinkiri ba."
"Ya Hajiyayye ki bar min sayen undies ɗin. Jibi tafiyarmu UK da Abban Farouq. Kin san na ce miki sati biyu kawai za mu yi." Wata ƙanwar tasu ta faɗi da zumuɗi.
Taj ya rasa me ya kawo wannan zance a cikin mutane haka. Kunya sosai ta kama shi don bai taɓa tunanin yin irin wannan maganar da Hamdi ba. Da su ka farga da discomfort ɗinsa kuwa su ka dinga yi masa shaƙiyanci.
***
Kamar kullum idan magana tana da mahimmanci a wajen Alhaji, ɗakinsa yake kiran matansa ya sanar dasu. A yanzu gidan nasa ya sha gyara mai kyau irin wanda ba a taɓa yi masa ba. Idan ka jima baka shigo ba sai ka kasa gane shi. Duk da cewa fasalin shi ne dai na da, amma an sabunta tsari da kaya yadda zai shiga sahun farko na kowanne maikuɗi. Saboda yanayi na girma, ya fitarwa kansa da wani ɓangaren ta baya inda ya yi sabon sashensa manne da babban falon ƙasan gidan. Saman ya barwa ƴan matan da basu yi aure ba da jikokinsa matasan mata dake yawan zuwa su kwana.
Haka kawai Inna ta dinga jin faɗuwar gaba akan wannan kiran. Jikinta ya bata ba zai wuce akan Taj ba tunda ya zo jiya. Tana son sanya ranta yayi murnar ƙila an shirya tsakanin uban da ɗansa, amma kuma duhun fuskar Alhajin ya sare mata gwiwa.
Haka su ka zazzauna har ya gama tsakurar abincinsa na rana sannan ya dube su.
"Yau bayan sallar juma'a na É—aurawa Taj aure da Æ´ar gidan Habibu Simagade."
Isashshen lokaci ya basu zancen ya zauna musu. Cike da fargaba da tashin hankali su ke dubansa. Mama tayi ƙarfin halin tambayar ko wani laifi ya sake yi.
"Da farko dai yana aiki tare da Habibu saboda ya nuna min ban isa ba. Banda haka ko masu girki nawa ne a garin nan da har sai ya nemo Habibu?"
"Alhaji ina ganin ire iren matakan da kake ɗaukarwa Taj ba za su samar da biyan buƙata ba. Shi fa ɗa komai shekarunsa indai yana da iyaye to fa yana buƙatar laluma da ja a jiki." Cewar Hajiya.
Cikin fushi da faɗa Alhaji ya ce "an ƙi a lallaɓa shi ɗin." Sannan ya faɗa musu abubuwan da ya binciko da dalilin auren.
"Yaron da yake da hankalin son fitar da wani kunya ne zai kasa gane dacewar ya kiyaye ɓacin ran mahaifinsa?"
Umma ta ce "Kayi haƙuri. In sha Allahu za mu yi masa magana."
"Bakin alƙalami ya riga ya bushe tunda an ɗaura auren."
Sai da kowacce ta gama rarrashin Alhaji akan ya yafewa Taj shi kuma yana botsarewa sannan Inna ta dube shi ido cikin ido.
"Yanzu da ka tara mu wane hukunci ka yanke masa."
Dukkaninsu sun girgiza da kalamanta da ma yanayin fitarsu. Babu wannan ladabin da kiyaye harshe da kowacce cikinsu bata isa ta ƙetare ba.
"Abu? Da ni kike?"
Ko gezau bata yi ba ta ce "Alhaji na gaji ne. Ina son sanin matsayarka ta uba kafin na sanar da kai tawa ta uwa."
Hajiya sai ta ɗan taɓata don tayi shiru. Ita kuwa ta kafe Alhaji da ido. Mamakinta ya hana shi motsin kirki. Da yaga da gaske take ne ya iya yin magana.
"FaÉ—a min naki hukuncin. Ai kema kin isa da shi. Wata tara ai ba kwana tara bane."
Gyara zama tayi ta hakimce abinta domin a yau Alhaji ya gama kaita maƙura.
"Tunda ka aurar dashi ni kuma in sha Allahu zan yi masa biki irin na É—an da mahaifiyarsa take so kuma take alfahari da shi."
"Da kyau Inna Abu." Umma ta faɗi cikin farinciki tana tafa hannuwa. Da Hajiya ta kalleta ta kaɗa kai tana dariya. Yau ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.
"Biki? Yanzu ke sai ki yi bikin É—anki ya auri Æ´ar É—an daudu? Auren da baki ma san da shi ba sai yanzu?"
"Aure ka ce, halattacciyar alaƙa. Kuma da kake zancen ban san dashi ba ai ba laifinsa bane. Na yarda da tarbiyar da mu ka bawa ƴaƴanmu. Yaron nan bai taɓa yin wani abu gaba gaɗi kamar mara mafaɗi ba. Tunda har kai ne ka jagoranci ɗaurin auren na tabbata ba a hanya ka tsinci zancen ba."
"Haka ne" ya ce da wani irin disbelief. Wai yau Abu ce take kallon idanunsa tana faÉ—a masa maganganu irin waÉ—annan.
"Na kuma jima da sanin cewa duk abin da zai yi yana turo maka saƙo ya sanar da kai."
Bai yi mamakin yadda aka yi ta sani ba
"Shi ya faÉ—a miki ko?"
"A wayarka na gani."
"Bincike kike min?" Ya É—aga murya.
"Ni na nuna mata" Mama ta bashi amsa ita ma yau da nata ƙwarin gwiwar.
Inna ta dube shi bayan ya gama yiwa Mama nata kallon za ki gamu dani É—in.