Sashe 16
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kalli Uncle B ya yi wani irin murmushi mai ciwo sannan ya É—aga waya ya kira É—an yayarsa police. Makarantar ya kwatanta masa.
"Ku taho yanzu don Allah."
"Yallaɓai da ka bari an kira masa ƴan sandan dake kusa da nan. Ka san kowanne laifi ana shigar dashi a unguwar da ya faru."
"A kira su. Shi wannan É—ana ne saboda haka ina jiran zuwansa saboda ina son komai ya tafi da jagorancin wani nawa."
Suna wannan zance Uncle B ya matsa gefe yana ta bige bigen waya da hargagin iska. Bayan ya gama ya cigaba da masifa yana doka teburin Principal.
"Baki san ko ni waye ba a garin nan wallahi. Ina da damar sanyawa a rufe makarantar nan baki É—aya a yau idan na so."
"Ka daɗe baka aiwatar ba. Mutumin banza. Girma da matsayinka basu ƙara maka komai ba sai sanya hannu wajen ɓata tarbiyar yaran mutane."
A cikin minti talatin motar Æ´an sandan da VP ya kira ta iso makarantar aka yi awon gaba da Uncle B. Baba Maje da Ummi da VP É—in su ka tafi tare dasu. Principal ta sanar da malamanta wajibcin neman iyayen yara a kurkusa domin tattaunawa da gujewa maimaicin abin da ya faru.
Hamdi da Abbanta su ka fito tare fuskokinsu babu walwala sosai. Shi yana cikin damuwar halin da abokinsa ya sami iyalinsa, ita kuma tana cike da kunyar ya san irin matsayin da ta ajiye shi a matsayinsa na uba. Hannunsa ta riƙe ganin yana raɓewa gefe guda.
"Abba in kai ka ka ga ajujuwanmu?"
"A'a Hamdi." Ya zame hannunsa.
"Ba ka yafe min ba ko?" Idanunta su ka kawo ruwa.
"Ban taɓa fushi dake ba. Ba dai na son sake bar miki abin faɗi a cikin abokan karatunki." Ya ce a sanyaye.
Wannan furuci nasa ya sanyata kuka sosai. Ta roƙe shi da ya jirata a nan inda yake za ta dawo bayan ya hanata kukan. Tana tafiya ta samu ɗalibai na dinning hall ana cin abincin rana. Duk da yadda take wasiwasi amma da ta tuno da maganar da Principal tayi mata sai taji zuciyarta ta daina tsoron komai.
"SS3 A" ta ƙwala kira da ƙarfi.
Tashi su ka yi wasu kuma su ka amsa da baki.
"Ku zo ku gaisa da Abbana."
Ai kusan rabin hall É—in ne su ka fita a guje. Aka kasa controlling É—in su. Tana gaba har inda ta barshi tsaye. Kawar da kai taga ya yi tayi murmushi ta zaga gabansa.
"Abba an zo gaishe ka."
Tunda yake kullum yaransa su ka zo gida da ƙawa basa taɓa cewa a gaisa da shi. Ƙawayen ma bai san kowa ba sai na dangi ƴaƴan ƴan uwa.
Ya juya suna ta ina wuni shi kuwa ya kasa amsawa saboda kada jin muryarsa yasa a yiwa Æ´arsa dariya.
"Abba ka amsa mana" Hamdi ta ce tana dariya kamar ba ita ba. Yarinyar da kullum take cikin ƙunci da damuwa.
Ya buɗe baki ya dinga amsa musu. Ƴan matan nan maimakon nuna ƙyama sai yake ganin kamar ya burgesu. Wasu basu taɓa ganin ɗan daudu a kusa haka ba. Kamar wani abin sha'awa su ka dinga girmama shi. Kan Hamdi ya kumbura suntum saboda daɗi. Ranar da taimakon malamai aka ƙora su duka har ita cikin makaranta sannan ya samu ya tafi wajen Baba Maje.
***
Ganin su Inna ya yi saurin É—aukewa Taj damuwar da ya shiga. Sai gashi ya zage yana ta hira kamar ba shi ba. A cikin hirar ne ya tambaye su ko akwai wani abu a tattare dashi da zai sa ayi masa kallon namijin da bai cika ba.
Ya naÉ—e hannun rigarsa har saman kafaÉ—a irin yadda yara su ke yi.
"Saboda son burge Alhaji har gym nake zuwa ina motsa jiki. Yanzu wannan..." ya nuna dantsensa "bai isa a kirani namiji ba?"
Kamal kula ya yi da Salwa da ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci da yadda tayi saurin ɗauke ido daga kallon hannun Taj. Shi kuma gwanin ya kama ƙasan riga zai ɗaga wai ya nuna musu packs ɗin ƙirjinsa. Gudun kada ɗan uwansa ya kunyata shi ne ya kai masa duka a hannun.
"Dalla malam rufe wannan sandar raken."
Taj da yaji zafi ya rama dukan "ɗan baƙinciki in ka isa ka buɗe naka mai kama da taliya."
"Mama kina dai jin abin da yake faɗa min ko?" Kamal ya faɗi yana miƙewa tsaye.
"Laifinka ne fa Kamal. Kai ka fara dukansa" Mama ta goyi bayan Taj.
"Saboda ya dawo daga America za ki nuna min wariya? Ke fa ki ka hana raini tsakaninmu."
Su Hajiya sai dariya su ke yi. Taj ya sami goyon baya ya cigaba da tsokanarsa.
"Ka ci sa'a ban auro baturiya ba da kaga asalin wariya. In taho da Æ´an Æ´aÆ´ana farare su na Mom...Dad...who is this black man" ya nuna Kamal aka sake tuntsirewa da dariya. Ya cigaba da tsokanarsa "Duk Æ´an uwa su taru a kansu ana son burgesu. Kai kuwa naka sai dai kaji ana cewa 'Sule maza tafi wurin babarka ta goge maka majina' "
"Banza ƙazami. Wai majina kamar tashin Soron ɗinki. Kuma don wulaƙanci ba ma Sulaiman ba Sule zan haifa?" Kamal ya faɗi yana shure shi da ƙafa.
Taj dariyar da ya san za ta ƙular dashi ya cigaba da yi.
"Sule Kamalu Hayatu Sule. Irin ƴan chubby yaran nan masu ɗan ƙaton ciki ba."
Ba ka jin komai a falon sai dariyar iyalin ta farinciki. Salwa da take ganin duk motsin Taj wani salo ne daban mai tafiya da zuciyarta ce kaɗai ta ƙare da murmushi.
Kamal da Taj su ka gaji da wasansu na dambe da girma bai hanasu yi ba su ka koma cin abinci daga plate É—aya su na hirar da babu mai ji.
RAYUWA DA GIÆI 9
Batul Mamman💖
***
Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station É—in da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta Æ´an matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar É—an yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo da ita gida daban.
Abin baƙinciki shaiɗanin tsohon najadun da yafi kowa hure mata kunne Uncle B ashe makanike ne. Matansa biyu da ƴaƴa goma sha uku. Sau ɗaya ake ɗora tukunya a gidansa. Irinsu Ummi ke cinye ɗan abin da yake samu. Ita da yake tunanin raba hanya da ita saboda rashin bashi haɗin kai tuntuni ashe silarta asirinsa zai tono. Sai da ya yi sati guda a ƙulle kafin a yarda a bada belinsa. Shi ma kuma an haɗa masa da muguwar tarar da zai ji jiki wajen biya.
Hantara da kyara su suka marabceta daga dawowarta gida. Ta zama mujiyar da bahaushe yake kira mai baƙin jini. Iyayenta ba su dake ta ba don ciwon abin da tayi ya kai maƙura. Yayanta Baballe ne dai ya kasa zama bayan yaji kukan Iyaa yayi yawa a waya da tana labarta masa. Ya niƙi gari ya taho Kano ya sakar mata ƙarfinsa. Zaneta ya yi ciki da bai babu wanda ya hana shi. Sai ma dare da jikinta ya yi mugun tsami ne Iyaa ta tada ta zaune.
"Sau nawa ki ka zubar da ciki Ummi?"
Duk soyewar zuciyarta da ya hanata kukan dukan da ta sha wannan tambaya sai da tayi sanadin zubar hawayenta. Hannu ta É—ora akan bakinta tana danne kukan.
"Iyaa? Ciki kuma?"
"To Ummi meye abin mamaki a ciki? Samarin da su ke kashe miki kuɗi ƙannen uwa ne ko na uba da za a ce zumunci suke yiwa?"
Hawaye take ita ma ga tsoron kada Ummin ta amsa zargin da su ke yi mata ita da Baba Maje.
"Wallahi Iyaa ban taɓa yarda na bada kaina ba."
"To me ki ke basu ko me su ke samu a madadin kuÉ—insu? Don dai bana jin shaiÉ—ancin naki ya yi tsamarin da za ki asircesu su dinga bin umarninki."
Shiru Ummi tayi. Hankalin Iyaa ya sake tashi ta dinga kai mata duka da hannu ta ko ina.
"Ki faÉ—a min gaskiya kafin zuciyata ta buga."
"Iyakarsu tattaɓani amma bana yarda da..."
Da sauri Iyaa ta tashi don bata son kuma jin ƙarshen zancen.
"Ya isa. Kin yiwa kanki."
Fita tayi ta bar Ummi tana kuka. Kuma duk wannan abu bai zama ishara ya tuna mata yadda ta dinga cin zarafin mutane dole rana irin ta yau ta zo ba. Sunan Hamdi kawai ke yawo a zuciyarta. Ko harararta aka yi laifinta take ƙara gani. Musguna mata da ta dinga yi a makaranta ai bai shafi komai na karatunta ko rayuwarta ba a tunaninta. She was just having fun. Ba ita kaɗai bace senior mai yi wa na ƙasa da ita hawan karkatacciyar kuka, saboda haka bata ga dalilin da zai sa ita kaɗai ce rayuwarta ta kife irin haka ba. Da me ake so ta ji? Sanin waye Uncle B ko fitowar sirrinta? Ko kuwa rabata da makaranta a matakin ƙarshe da iyayenta su ka yi don ta ɗauki bidiyon ɗan daudu?
"Wallahi sai na rama Hamdiyya. Babu wanda ya isa ya saka ni kuka ban saka shi ba."
Da wannan kalaman ta goge hawayenta a fusace ta kwanta tana shure Siyama da ƙafa don ta ɗan matso ɓangarenta cikin bacci.
***
Kwanaki sun ja inda a farko farkon watan August É—aliban sakandire su ka kammala jarabawar fita. An yi WAEC har ta fito kafin a gama NECO. Da taimakon Allah da kuma dagewar karatu Hamdi ta sami kyakkyawan sakamako.
Kwana biyu bayan kammala jarabawar makaranta ta shirya gagarumin taron sallamar ɗalibai. Iyaye da ɗaliban suna shiryawa wannan rana wasu tun farkon shiga SS3. Ɗinkin ankon wata shuɗiyar atampa su ka yi mai adon fari da yellow. Tun kafin hutu aka fitar amma lokacin Hamdi bata ƙarɓi ƙyallen ba. Saboda ko kusa bata sa ran zuwa. Sai bayan faruwar lamarin nan taji a jikinta ta daina ɗararewa. Allah Ya taimaketa kafin a gama jarabawar lokacin visiting da Sajida da Zee su ka zo mata ta basu.