← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 96

Sashe 73

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigiyar da take gudu tunda ta san komai wajenta ƙannen za su zo nema mazansu da matansu aka fara yi daga rufe bakinta. Kula su ka yi falon a gyare yake. Aka tambayi masu aiki kowacce ta ce ba ita tayi ba kafin su tafi. Abin da mamaki dai.

"To ko dai Alhaji ne? Naga motarsa..."

Hamɓare bakin mai maganar Yaya Samira tayi kafin ta kai ƙarshe.

"Baban namu ne zai yi muku gyaran falo don rainin wayo?"

"Gani Mugenbo shugaban marasa kirkin duniya ko?"

Muryarsa su ka ji kafin su gan shi yana fitowa daga ƙofar ɓangarensa dake cikin falon. A gurguje masu ƙuruciyar ciki su ka yi kansa saboda sabon da su ka yi dashi. Ƴan matasan kuwa su ka shiga sunne kai.

Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj. Tsaurin ra'ayinsa bai hana shi kamanta mu'amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba. Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra'ayinsa kenan koda zuƙatansu basa son abu. Ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa.

Cikin jikokin wani É—an shekara biyar zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan.

"Alhaji ba ya yin aikin mata. Shi ba É—an daudu bane."

Tsit falon yayi. Kunya ta kama su aka rasa mai kwaɓarsa. Alhaji ya jinjina maganar musamman da ya karanci yadda kowa ya sha jinin jikinsa. Duk sai yaji babu daɗi.

Murmushi ya yi na jin kunyarsu ya dafa yaron "kwashe kaya da ninkewa ai ba aikin mata bane kaÉ—ai Amir. Duk wanda zai iya saka kaya ya kamata ace zai iya ninke su."

"Laahhh, Uncle Taj ma ba É—an daudu bane kenan ko?"

"Me yasa ka ce haka?" Alhaji ya tambayi yaron da sakakkiyar fuska don ya bashi amsa.

"Saboda duk wanda ya iya cin abinci shi ma ya kamata ya iya dafawa."

Mahaifiyar Amir kasa tsayuwa tayi saboda tsoron me Alhaji zai yi bayan jin amsarsa. Ta kalli yayyenta su Yaya Kubra tana neman ceto.

Matan gidan ne ƙarshen shigowa dama. Saboda haka daga baki bakin ƙofa suke tsaye. Hajiya tana kallon idon Alhaji ta yiwa Amir tambaya.

"Kai ka san waye É—an daudu?"

"Eh mana" ya amsa da karsashi na yaron da aka yiwa tambaya mai sauƙi "sune masu yin haka..." ya ɗaga hannuwa ya tafa da iska "ahayyyeee cass, rass... ko?"

Hannuwansa Bishir ya yi saurin riƙewa ya ce "dare ya yi, ayi shirin bacci a kwanta haka nan."

Da sauri sauri su ka dinga watsewa aka bar Alhaji a tsaye cikin tunani da wata irin kunya. Yau kuma yaro É—an shekara biyar ne ya shiga sahun masu faÉ—a masa gaskiya? Kuma wannan karon a gaban mutanen da yake jin ya isa dasu ta kowacce fuska!

"Alhaji na ce Allah Ya bamu alkhairi."

Da muryar Umma tunanin da ya fara ya kau ya dawo da hankalinsa ga matansa. Hajiya ma sai da safen tayi masa ta shige yayinda Mama tayi masa tambayar ko ya gama da kwanukan abincin dare da ta ajiye masa domin ta kwaso. Amsa ya bata sannan ya mayar da dubansa ga neman Inna don tunda su ka shigo ko tari bai ji tayi ba. Jiran ta ce masa sai da safe kamar Æ´an uwanta yake sai yaga bata wajen.

'Fushi take? Me kuma nayi? Ba na bada izinin yin bikin ba? Sai da safen ma yau ban isa ace min ba?' Ya ayyana a zuciyarsa.

"Ba tare ku ka shigo da Abu bane?" Ya tambayi Mama.

Yanayinta yaga ya sauya sannan ta ce masa ya shiga É—akin Innar ya sameta. Hankalinsa tashi ya yi don ko bata faÉ—a ba yaji a jikinsa babu lafiya. Tabbas Hajiya da Umma ma basa cikin walwalar da yayi tsammanin za su dawo da ita.

Ɗakin ya shiga kai tsaye ya tarar da ɓangarenta da ƴan kwana. Wuce na falon ya yi ya shiga ainihin ɗakin baccinta inda nan ma wasu ke ciki. Sai dai suna ganinsu su ka fita. Zai yi magana ta riga shi ta hanyar miƙa masa wannan layar.

Ya miƙa hannu zai karɓa kenan sai Inna taga ya yi baya da hannunsa da sauri yana zaro idanu.

"A'uzubillahi..."

"Ka san ko mene ne kenan?" Ta ajiye layar a wajen madubi jikinta a sanyaye.

"A ina ki ka samo ta?" Ya tambaya cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda tayi tsammani.

"Sal..."

Kafin ta kai ƙarshen sunan ya gane wa za ta ce. Ya ɗaga layar yaga sunan Taj. Ransa kuwa ya yi mummunan ɓaci.

"ÆŠana? Me matar nan ta taka da har take tunanin zan zuba ido ta mayar min da É—a mutum mutumi?"

Inna na jin haka nata hankalin ya sake tashi.

"Mugun tsafi ne ko? Innalillahi. Tun a wajen naga ya fara runtse idanu."

Maganarta sake tunzura zuciyar Alhaji tayi. Sirrin da ya sakayawa Mami albarkacin Ahmad ya dawo masa tar cikin ransa. Haƙiƙa kamar sauran matansa ita ma so ya saka shi aurenta. Ta zo da fitina da neman rigima. Kullum cikin takalar Hajiya da Mama faɗa dake gidan a lokacin take. Aka mayar masa da gida filin kai ƙara. Wani abin idan tayi shi kan shi sai ya yi mamakin mene ne abin tashin hankali a ciki da har za ta nemi faɗa. Abin mamakin ma shi ne kasancewar shi ɗin jajirtaccen namiji ne amma ko zai ari baki wajen yi mata faɗa da nasiha anjima ko gobe ma sai ta ƙara. Sannu a hankali ya shiga karantarta inda ya fahimci ashe asiri take yi masa, kuma yawan rigimarta tana yi ne domin aunawa taga ko sihirin ya ci. Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da yaga wannan layar da yaji da kunnuwansa ranar da Zabba'u ta kawo mata tana cewa sunanta Raƙumi da akala. Har tana yi mata rantsuwar idan ta tauna ko me ta umarce shi zai aikata. Burinta a lokacin tunda ta haifi Ahmad yana ƙarami ta fitar da su Hajiya.

Ƙin nuna musu ya gani ya yi. Ya kuma bari tayi amfani da ita. Ranar ta yiwa Hajiya ɗiban albarka ajin ƙarshe duk yana jinsu daga ɗaki. Zuciyarsa kamar ta fito ta baki amma ya kasa fitowa saboda a kan idonsa ta saka a bakin ba tare da ta san yana gani ba. Ta tauna ta umarce shi da ya zauna a ɗaki kada ya fito ko me zai faru.

Haka kuwa aka yi. Rigima ta kaure amma duk yadda yaso haka ya zauna a ɗaki. Don baƙinciki har hawaye sai da ya yi. Sai kuma ya shiga karanto addu'o'in tsari tunda ya gama gano illar layar. Lallai idan ya zauna da ita rayuwarsa za ta zama mara amfani.

Shigowa Mami tayi da aka gama faÉ—an tana kumbure kumbure.

"So nake ka saki Haj. Gambo yanzu yanzun nan."

Ko ɗaga kai ya kalleta bai yi ba ta sake maimaita umarnin amma shiru. Dama layar na hannunta sai ta ɗaga ta juya masa baya za ta mayar cikin bakin. Bata yi aune ba taji ya damƙe hannun ya zare layar.

"Ki je gida na sake ki saki uku."

Farat ɗaya ya faɗi maganar don kada a sami matsala. Ta kuwa dafe ƙirji a gigice.

"Haj. Gambo nace..."

Ƙarfin gwiwarsa ya dawo gare shi ya ce "ni kuma ke nace."

"Wallahi baka isa ba...wayyo Allah. Na shiga uku. Alhaji ina zani? Ina kake so nayi da Ahmad bayan ka san ni marainiya ce?"

GabaÉ—aya kamanninta sauyawa suka yi a take. Tana wannan hargagin ya kira Mama ya ce ta É—auko Ahmad duk inda yake a gidan ta goya shi.

"Idan ba ni ba kada ki bawa kowa har uwar da ta haife shi."

Mafarin da goyon Ahmad ya koma hannun Mama kenan. Ba a raba ɗa da uwa amma bai san sunan da za a kira shi ba idan ya bari jininsa ya tashi a gidan shirka. Haka ya nunawa iyalinsa cewa faɗan da ta takali Hajiya ne yasa shi sallamarta. Ya kuma yi ne don kyautata ƙimar ɗansa a gidan. Daga lokacin bai sake shiga harkarta ba sai da ta fara ɗorawa Ahmad ɗin buƙatun da su ka fi ƙarfinsa yaje ya samawa mijinta aiki. Baya son haɗa inuwa da mushiriki kuma wanda yake tu'ammali da tsibbu. Shi yasa ya nesanta kansa daga gareta. Baya bari komai ya haɗasu. To amma yau dai tura ta kai bango. Idan tana cin ƙasa lallai ta kiyayi ta shuri. Ƴarta ko ita ce autar mata kuma masoyiya ga Taj ba zai taɓa sahale masa aurenta ba.

Wayarsa ya É—aga da sauri ya kira Taj...abin da rabonsa da yi har ya manta.

***

Ƙirjin Anti Zahra dukan tara tara ya kama yi da ganin wannan rashin hankali da ake yi mata a gida. Inda su ka sami ƙarfin halin iya shigar mata kitchen su ka yi binciken kayan abinci da girki shi ne babban abin mamaki. Gashi an zuzzubar da shinkafa akan kafet. Yaran babbar ƴar Anti Zabba'u sun tattake wata a wurin. Ƙarnin kifi kuwa ba a magana. Maiƙon duk an shafe a kujeru da centre table don ƙeta. Wata ma remote ne a hannunta na daman. A hagu kuma tana riƙe da kofin da aka keɓe domin maigidan ta cika shi da juice.

Shi kuwa Ahmad Anti Zabba'u da Salwa yake kallo yana neman wadda za ta yi masa bayani. Saboda yadda ransa ya ɓaci kuwa Adam's apple ɗinsa hawa da sauka kawai yake yi ya kasa magana. Gani yake duk kalmar da za ta fito bata da ƙarfin nuna yadda yake ji a zuciyarsa.

Anti Zabba'u ko a jikinta domin da shirinta ta fito. Ta saki rai tayi musu maraba kuma bata damu ba da basu amsa ba. Sai ma kaɗa baki da tayi ta ƙwalawa ƴarta da ta tafi kitchen ƙaro musu juice tayi. Ita ce ake so Ahmad ya aura yanzu.

"Habitti (Habibty take kiranta saboda tafi ƴan uwanta kyau, sunan sai ya bita) fito ga yayan naki ya dawo." Ta kalle shi "tun ɗazu take damunmu da mitar ka ƙi dawowa."
Chapter 73 · 0% Book details