Sashe 67
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗakin Mamin suka fara zuwa. Yana karanto surorin neman tsari ya watso duka kayan cikin wardrobe ɗinta da kowacce durowa. Sun tsinci ƙulle ƙulle da wasu ƙwarya da tarkace guda biyar. Aka koma ƙasan gado nan ma akwai. Daga nan sai ɗakinsa. Abu ya ƙazanta. Kansa har ciwo ya dinga yi saboda tashin hankali. A ɗakin ƴaran gidan ne dai ba a sami komai ba. Kitchen ma Bushra ta nuna wani ruwa da ta kan ga Mami ta tsiyaya musu a girki. Ya ɗauka ya tuttular. Kit ɗinta inda take ajiye abubuwa masu mahimmanci ya ɗauka ya muƙa da ƙasa sai gashi ya buɗe. A nan ya tsinci laya mai sunansa da ake taunawa. Sai kuma masu sunan duka ƴaƴansa banda nata. Da kuma sababbi a leda ɗaya Taj, ɗaya Zainab (Inna).
"Wallahi Baba wannan take sakawa a baki ta ce kayi mana abu kuma sai kayi. Ko ranar da ka ce in na kuma fita zance za ka tsine min da ita tayi magana."
Haƙuri ya bawa ƴar tasa. Ya rasa matakin ɗauka na gaba. Ita ta bashi shawarar su ƙona komai. Ya ce kada ta taɓa. Da tsintsiya da abin kwasar shara ya tattara komai ya tara a tsakar gida. Ya kawo fetur ya zuba sannan ya kira Mami ya ce su dawo.
"Har maganin ya fita?"
"An fasa, sai gobe."
Masifa ta yi masa na katse mata baccin yamma sannan su ka taho gida. Ana buÉ—e musu gate ta hango shi daga shi sai Æ´ar shara a jikinsa ya sanya wasu tarkace a gaba. Su ka fito daga mota ta taho inda yake. Jikinta ne ya saki lokaci guda da ta gane mene ne a gabansa.
"Alllll....hhhhajjii? Mmmmene nee wannnnan?"
Haɗe rai ya yi sosai ya tura mata ashana da ƙafarsa.
"ÆŠauki ki cinna musu wuta."
Jikinta rawa ya kama yi sosai. Tana ta gumi ta rasa abin yi.
"ÆŠauki mana!" Ya daka mata tsawa.
Ta kasa motsi sai ƙullewar ciki. Salwa da taga halin da babarta ta shiga ita ma tsorata tayi. Tunda bata san kayan mene ne ba durƙusawa tayi ta ɗauki ashanar.
"Baba ni bari na ƙona."
Kafin Mami ta iya tare ta har ta ƙyasta ashana. Tana cillawa kuwa kayan nan su ka yi wata mahaukaciyar ƙara tamkar tashin gurneti. Mami tayi zaman daɓaro a ƙasa tana ihu.
"Kin kashe ni. Salwa kin kashe gidan nan."
Da faÉ—a Alh. Mukhtar ya ce "ta dai kashe ki ke kaÉ—ai banda gidana."
"Mami kayan meye?" Salwa ta tambayeta ganin kuka take haiƙan. Bata sami amsa ba sai daga bakin babanta.
"Nagodewa Allah da Ya turo Alh. Hayatu gareni ya farkar dani mugun baccin da nake yi. Sai yau na gane ashe zaman waÉ—annan abubuwan muke yi ba aure ba."
Mami kuka kawai take yi da gurnani. Hankalinta ya kai ƙarshen tashi. Idan ya saketa bata da tudun dafawa. A zaune ta ja jiki zuwa inda yake za ta kama ƙafarsa ya janye da sauri.
"Ka rufa min asiri."
"Ki rufawa kan ki dai" ya dubesu ita da Salwa dake tayata kuka "yauwa, Alh. Hayatu ya ce in faÉ—a miki ki warware abin da ki ka yiwa É—ansa har su ke rigima da matarsa. Idan ba haka ba kuma ki jira martani daga gare shi." Ya wuce ciki.
Mami ta zauna tana tumami da kuka kafin ta tashi ta bishi ciki da sauri.
"Wane É—an? Taj? Wallahi ban yi masa komai ba."
"Ki daina saurin kama sunan Allah tunda baki san shi ba. Da idona naga laya da sunansa."
Mami ta kwantar da murya "Ayyaaa Alhaji, bamu yi amfani da ita ba. Dama na ajiye ne sai sun yi aure da Salwa. Ai ban baki ba ko...."
Ta juya babu Salwa babu dalilinta.
"Salwa? Alhaji ina Salwa?" Tayi maganar kamar wata zararriya. Tsoro take ji kada ƙona kayan nan ya janyowa ƴarta wani abu. Don dai tabbas malaminta ya sha yi mata kashedi akan kada ma wani ya gani balle a taɓa.
ÆŠakunan gidan ta duba bata ganta ba. Tayi wajen gate tana faman kiranta ko kallon titi bata yi. Bata yi aune ba mota ta É—ebe ta tayi sama ta dawo. Maigadin Alh. Mukhtar da ya biyota yana son faÉ—a mata Salwan ta fita ne ya koma ya sanar dashi abin da ya faru. Ya fito su ka wuce asibiti tare da mai motar da ya bugeta.
Salwa kuwa tunda taji saƙon babanta hankalinta ya tashi. Indai Alhajinsu Taj ne ya yi waccan maganar kenan asirin ya kama su. Matsalar kawai tunda ake zargin Mami a hankali zsi gano ita ce. In haka ta faru kuma zai hana Taj aurenta idan su ka fara soyayya. Tasha ta wuce tunda da atm a jikinta ta ciri kuɗi sai Kano. Wurin Ummi za ta je ta taimaka mata da wanda za a rufe bakin Alhaji.
Motarsu ko fita gari bata yi ba Alh. Mukhtar ya kirata ya faɗa mata abin da ya sami Mami. Don baƙinciki sai da tayi kuka. Haka ta sauka daga motar ta tafi asibiti.
***
Mai shawara aka ce aikinsa ba ya ɓaci. Duka abubuwan da Inna ta sa Taj yi ya rungumesu hannu bibbiyu. Ƙuncin zuciyarsa ya ragu sosai. Duk da ya kan ji haushin Hamdi yana taso masa lokaci zuwa lokaci tunda fitar asiri sai a hankali, amma a zuciyarsa ya sani cewa ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba kamar yadda ya dinga ji a kwanakin baya. Banda yawan addu'a, Inna ta sa yanzu ya ware plate goma na abinci kullum sai sun bayar sadaka. Ba wai ragowar na mutane ba. Mai kyau da an gama dafawa ake packaging. Ranar farko ma na mutum ɗari biyu su ka yi aka kai asibitin gwamnati. Kusan zai rantse ma daga ranar ya fara jin canji sosai. Ciyar da mabuƙata ba ƙaramin abu bane.
Duka wani jere da gyaran gidan amarya an gama shi a farkon sati. Duk wanda ya shiga kamar kada ya fito. Hatta kayan da za su saka Kamal ya kai wa Hamdi nata ana jibi fara biki. Bayan ta shiga gida ta gwaggwada ta dawo ta same shi. Ta faɗa masa babu wanda yake buƙatar gyara. Sai kuma tayi godiya sosai.
"Yanzu yaya kike ji game da É—an uwana?"
Kai ta sunkuyar tana murmushi. Da ya sake yin tambayar ta ce "Alhamdulillah."
"Kina ganin faɗa ya ƙare? Za ku iya zama babu tashin hankali?"
"Ban sani ba ko daga wurin shi." Ita ce amsar da ta bayar da ƙaramar murya.
"Nayi magana da shi. Ke nake tambaya kuma."
Kunya ce ta isheta ya ce gara ma ta daina domin tunda ta shigo danginsu ta sani cewa bayan shi yanzu ta sami ƙarin ƴan uwa. Kuma kowa zai tsaya mata idan Taj ya yi nufin cutar da ita.
"Zan iya in sha Allah."
"Alhamdulillah. Kamar yadda na faɗa masa ku bi komai a sannu. Kada ku ce dole a yau ko gobe ku ke son ganin alaƙarku ta dawo kamar da. Wannan zai janyo muku too much expectation, wanda kuma rashin samunsa zai sa ku zama disappointed."
"In sha Allah zan kiyaye."
"Hamdiyya"
Mrs Happy ya saba kiranta. Shi yasa Hamdiyyar ya faÉ—ar mata da gaba.
"Na'am Ya Kamal."
"Don Allah ki riƙe min Taj amana. Abubuwa da yawa sun same shi. Yana buƙatar inda zai sami kwanciyar hankali."
ÆŠan murmuhi tayi "ai kana nan Ya Kamal sai mu dinga shawara. Ka fini sanin abin da ya dace da shi."
Murmushin da Kamal ya mayar mata mai matuƙar rauni ne. Da ace idanunsa ma take kallo za ta ga sun kaɗa.
"Yanzu ke ce mafi kusa dashi."
"Ba zan shiga tsakaninku ba in sha Allah" ta faÉ—i da sauri.
"Rayuwa da yau da gobe za su iya shiga. Ni dai na baki amanar Happy. Please Hamdiyya, give him the happiness he deserves."
Har ya tafi tana juyayin maganganunsa masu kama da sallama. Anya lafiya kuwa?
***
Idan ka ji yara na waƙar gobe Juma'a, kuturu dariya yake ko zai sami ɗan kwabo to lallai ranar ta kama Alhamis. Ta wannan satin ita ce ranar Kamun amarya Hamdi wadda iyayen ango Taj su ka yi rawar gani wurin tsara taro na burgewa. Biki ne na ƴan kasuwa kuma ƴan boko. In baka yi bani wuri. Sun tsara abinsu na yau ma mata kawai. Mazan gidansu ko mutum ɗaya ba a yarje masa zuwa ba. Daga DJ ɗinsu kuwa har mai hoto da MC duka mata ne. Daga cikin wani katari da Alh. Hayatu ya sake yi a rayuwa harda dacewa da kyakkyawar tarbiyar ƴaƴansa akan sunnar Fiyayyen halitta SAW. Ba dai a rasa nono a ruga, wani dole sai ya bauɗe. To amma dai majority a gidan sun ginu da wannan tarbiyar ta iyayensu mata. Wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Alhaji ya kan kasa yiwa wanda ya kuskure uzuri. Shi fa kusan komai Allah Ya bashi. Bai san wani nau'i bane na gwajin rayuwa. Idan ya ƙanƙantar da kai ya yarda rahama ce daga cikin taskar Ubangijinsa sai Allah Ya ƙara masa da lada mai gwaɓi. Idan kuwa girman kai da jin cewa isarsa da iyawarsa ne su ka bashi kamar yadda ya tsinci kansa yanzu, to dama Allah barin mutum yake da iyawar tasa.
Ƙarfe ɗayan rana mai kwalliya ta zo ta fara rangaɗawa Hamdi bayan tayi sallar azahar. Jiki ya sha gyara na gaske saboda haka in ka ganta sai ka ƙara kallo. Ga ƙamshi wanda da kanta ta ce a bar turara mata jiki haka nan saboda kada ta fara ɗaukar zunubi a cikin mutane.
Tana idar da sallar la'asar ta saka kaya aka ɗaura mata ashoke. Da ta fito daga ɗaki Yaya tashi tayi ta bar wajen. Bata son kowa yaga ƙwallar da ta cika mata idanu. Yau ita ce Allah Ya nufi ƴarta da auren gata irin wannan. Da bikin Sajida abin bai yi armashi sosai ba saboda tangal tangal da auren ya soma yi tun kafin a ɗaura shi.