← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 96

Sashe 40

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ma Kamal da shaƙiyanci ya ce "Shege...mutumin ya fola tsundum. Allah Yasa kada Alhaji ya kawo cikas dai kafin mu kwashi ƴaƴan love."

"Za ka yi bayani. Bari dai hankalina ya dawo jikina in mun shirya da Amma. Ko da duka ne sai ka fađa min sunan budurwarka. In kuma babu sai muje wajen Baba Malam (yayan Inna) ayi maka ruƙiyya. In ma wata jinnu ce ta ƙyasa ayi waje da ita."

"Aljana sai dai a kanka. Ni kam ƙalau nake."

"To in ba tsoro ba ka faÉ—a min. Idan kuma kasa ka aka yi ne gara na sani. Sai na baka tips na shawo kan Æ´an mata. Ka san mu masu auren nan komai mun sani."

"Daga É—aurawa? Ka rufa mana asiri dai kada Æ´ar mutane ta tare da ciki."

"Sai kace wani namamajo" Taj ya sha kunu.

"Da meye?"

Da irin wannan faɗan nasu na wasa su ka isa gidan Abba. Idan ka kallesu sau ɗaya dole ka ƙara. Alhaji ya tara arziƙi a gidansa. Ba mazan ba, ba matan ba. Shi kan shi ya san wannan.

Waya Taj ya yiwa Abba bayan sun fito daga motar. Ba a jima ba kuwa ya fito da shirinsa harda babbar riga.

"Ko shigo ciki ku gaisa da mutan gidan mana. Dama can an zama ɗaya balle kuma yanzu. Kuma mazajen ƴan uwanta ma sun zo. Sai ku san juna ko." Ya nuna ƙofar yana murmushi.

Bayansa su ka bi Taj yana sunne kai shi a dole ya shiga gidan surukai. Kamal ya faki ido ya É—auke shi a hoto ya adana domin duk ranar da ya bashi haushi ya tura group É—insu na gida.

*

Hamdi na zaune da waya a hannu tana jiran kiran Taj a É—akin Halifa ita kaÉ—ai. Falonsu kuma Safwan ne da abokansa biyu. Sai kuma Baballe da iyayensa. Ga Yaya da amare Sajida da Zee. Tsakar gidan kuwa Æ´an uwa ne na kurkusa su ke ta aikin kayan miya na girkin gobe saboda sun san dole a sake zuwa kafin Æ´an É—aukar Sajida su zo. Musamman waÉ—anda basu ji auren Hamdi da Zee da wuri ba.

Abba ya shiga falon da sallama aka amsa. Taj da Kamal su ma su ka yi. Yaya jan mayafi ta ƙara yi. Bakinta har kunne. Duk yadda take son nuna kunyar surukai abu ya gagara. Allah Ya gatance mata a lokacin da bata yi zato ba.

Musabaha su ka yi da duka mazan. Sannan su ka gaisa da Iyaa da Yaya. Abba ya sake gabatar musu da juna.

"Safwan ai ka san Taj ko?"

Safwan ya yi murmushi "sosai Abba. Tun kafin ya dawo ma ta haÉ—a mu. Abokina ne ko in ce É—an uwa ma."

Sajida ta sunne kai tana murmushi. Safwan É—in dama É—an ayi ne na gaske.

"To ina jin duka dai Baballe ne baku sani ba. Sunansa Abubakar kuma É—an amini na ne."

Baballe ya taso ya sake basu hannu.

"Ni ne dai É—an autanku. Ina fata zamu yi zumunci mai É—orewa."

Iyaa taji daÉ—in yadda É—an nata ya yi. Sai da ta yi dariya da Safwan da Taj su ka ce sun É—auki girman. Aka É—an yi raha sannan Baba Maje ya juya dama da hagu.

"Ina Hamdiyya ne? Mijinta ya zo ba za ta leƙo su gaisa ba?"

"Yi maza ki kirata Zee." Iyaa ta faÉ—i ganin Yaya ta sunkuyar da kai.

A É—akin Halifan ta sameta. Ta rasa gane zaman me take yi ita kaÉ—ai bayan ta nuna musu ita bata da damuwar auren.

"Ki zo ku gaisa da Ya Taj. Amma ki yi sauri don fita za su yi da Abba."

Kafin Zee ta gama magana ta fice da ƙaton hijabin da tayi sallar magariba. Falon ta shiga da sallama. Idanunta Taj su ke nema. Shi ma kuma ƙofar yake kallo. Su ka haɗa ido ta kasa yakice nata.

Tabbas Taj ne mafarkinta, amsar addu'arta kuma zaɓin zuciyarta. A wannan ɗan taƙaitaccen kallon makaman yaƙin neman sakin su ka fara saukowa ƙasa da kansu. Buɗar bakin Inna Luba da shigarta falon kenan sai cewa tayi.

"Mu dai Tajo idan mun zo É—akin amarya ba girkinta za mu ci ba. Ranar zagewa za ka yi ka girka min don ni ce da gidan ba ita ba."

Dawowa daga duniyar da taso mantar da ita waye Taj tayi. Ta kuwa tura baki tana kumbure kumbure. Shi kuwa dariya ma ta so bashi. Yana ta lura da rikicikin yanayin dake bayyana a kyakkyawar fuskarta. Wani irin farinciki na shigarsa. Wannan yarinyar matarsa ce. Bai san lokacin da ya yi murmushi ba.

"Ku je daga soro ku gaisa mana kafin Habibun ya fito." Baba Maje ne ya yi maganar. Hamdi bata ɓata lokacin bin umarninsa ba saboda son samun damar yiwa Taj magana.

Ita ta fara zuwa soron kafin ƙamshin Taj ya yi masa iso. Ƙasa ta durƙusa da ya shigo don so take kawai a yita ta ƙare yanzu.

"Ina wuni Ya Taj?" Ta furta cikin sabon salon ladabinta gare shi.

"Lafiya ƙalau. Tashi mana."

Ƙin motsawa tayi "dama haƙuri nake son baka akan rashin kunyar da nayi maka rannan. Don Allah ka yafe min. Wallahi ba hali na bane."

'Irin wannan ladabin na neman buƙata ne' Taj ya ayyana a ransa. A fili kuwa cewa ya yi "ya wuce. Nima ki yi haƙurin abubuwan da na ce miki."

"Babu komai wallahi." Ta ce da murmushinta.

"Uhmmm, dama...na ce...dama...wai ko za ka...uhmmm" ta dinga in'ina saboda kalmomin sun ƙi haɗuwa.

Shi yasa ta so su yi maganar a waya. A haka duk yabi ya yi mata kwarjini. Kamal ne ya fito a lokacin.

"Happy ga Abba nan. Ya ce kada lokaci ya ƙure."

Taj ya dubeta. Duk tayi laushi. Fuskarta kuma tayi fayau da alama tayi kuka.

"Zan kira ki in sha Allah. Kamar ƙarfe nawa ki ke kwanciya don kada na tashe ki?"

"Zan jira ka. Don Allah ka kira."

"Okay." Har zai fita yaji ya dace ya É—an bata assignment É—in da zai sa tayi tunaninsa ko bata so "aapna khayal rakhna."

Ai kuwa a take ta ɗinke fuska. Taj ya kalleta ya saki murmushi. A babu yadda ta iya dole ta mayar masa tunda tana da buƙata a wajensa. Da ta koma ciki maimaita kalmar kawai take yi tana addu'ar kada Allah Ya kawo ranar da zai zage ya yi rawa da waƙa kuma.

***

Kamal ne ya sanar da Alhaji zuwansu. Daga nan ya yi tafiyarsa ɗaki. A gajiye yake sosai. Ga wata yunwa da bai ma san yana jinta ba sai da ya shiga gida. Agogonsa ya kalla bayan ya cire. Ya san a ƙalla yana da minti shabiyar kafin su gama tattaunawa. Don ba zai iya baccin ba tare da sanin me zai faru da ƙaninsa ba.

Ledar wasu magunguna ya ɗauko daga ƙarƙashin gadonsa. Ya ɓalli iya wanda yake buƙata ya zuba a wata ƴar roba sannan ya fita zuwa cikin gidan domin samun abin da zai ci.

A waje kusa da gate inda Taj ya yi parking Alhaji ya zaɓi ganawa dasu. Gashi dare ne. Kuma lokacin zafi. Sannan wurin akwai shuke shuke. Saboda haka sauro ya far musu. Abba ya lura Taj a takure yake.

"Da ka sani ka barni na taho ni kaÉ—ai Taj. Yanzu haka ma Alhaji yana iya jin babu daÉ—i in ya ganmu tare."

"Idan ka ɓata amaryata ba za ta yafe min ba." Salati ya kama a jejjere "Abba tuba nake. Ba da kai nake ba."

"Kaji nayi magana?" Dariya su ka yi tare.

"Abba ko mu koma mota ne? Sauron nan yanzu sai ya tayarwa mutum da maleriya."

"Kai Taj, maleriyar ma tashi take?"

Da gaskensa ya ce "ni dai tawa tashi take. Tunda na dawo bana jimawa ban yi zazzaɓin nan ba."

Da damuwa Abba ya ce masa "kayi a hankali. Ba a sakaci da lafiya. Mataki za ka É—auka don shi dai sauro bai san mutumci ba."

Dariya su ka sake yi a lokacin da Alhaji ya doso inda su ke. Ya kuwa murtuke fuska saboda baƙinciki. Yaushe rabonsa da hira da Taj wadda za ta saka su dariya haka? Ya ma rasa da wanda zai yi sai Habibu.

Duƙawa Abba ya so yi tunda ya fuskanci Alhaji na ƙyamar taɓa shi sai Taj ya taro shi da sauri.

"Ai kun gaisa É—azu."

"Yawan gaisuwa ai yafi yawan fađa Taj." Abba ya ce sannan ya dubi Alhaji "barka da dare Yaya Hayatu."

"Hmm" kawai ya ce daga maƙoshi a matsayin amsa sannan ya ce Taj ya basu wuri.

Ba don ya so ba ya tafi. Zuciyarsa tana ta fama da wasiwasin kada ya barsu Alhaji ya sake yi masa abin da yafi na É—azu.

Gyaran murya ya yi bayan tafiyar Taj ya yiwa Abba duba na ƙyama.

"Habibu!"

"Na'am" ya sadda kai yana sauraronsa.

"Ina son Tajuddin. A cikin ƴaƴana ma ban haɗa ƙaunarsa da ta kowa ba. Abin da ya shiga tsakaninmu har na kore shi bai rage min son abuna ba."

Murmushin jindaɗi Abba ya yi "Alhamdulillah. Allah Ya ƙara kawo muku daidaito."

"Daidaito kam ana gab da samu sai ka zo ka shiga tsakani."

Hankalin Abba tashi ya yi sosai. Taj bai ɓoye masa komai game da rabuwarsa da mahaifinsa ba. Da kuma burinsa na son ya dawo gida kamar kowa.

"Indai don ina aiki a gidan abincinsa ne wallahi zan ajiye...kai na ma ajiye. Ba zan so na zama sanadin sabunta ɓaraka tsakaninku ba."

Wani irin murmushi Alhaji ya yi "idan ka bar aikin ma zai maye gurbinka da na wani. Bani da matsala da aikinka."

Fahimta ce ta É—arsu a zuciyar Abba. Ya dubi Alhaji a firgice.

"Hamdi? Ƴata ce ba ka so tare da shi?"

"Ƙwarai." Ya amsa idanunsa na kallon sararin samaniya.

Auno halin da Yaya za ta shiga ya yi. Jikinsa ya soma rawa.
" Ka taimaka min Yaya Hayatu. Wallahi nayi musu tarbiyya bakin gwargwadon iyawata. Duk da ni na haifeta amma na sani bata da wani aibu na halayya sai abin da ba a rasa ba na ajizancin É—an Adam."
Chapter 40 · 0% Book details