Sashe 23
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sarai ya ji ɓacin rai a cikin muryarta. Ya kalli Kamal yana neman agaji. Shi kuma sai ya raɗa masa a kunne cewa ya faɗa mata zai je Abujan su fara fahimtar juna. Haka kuwa ya faɗa mata. Nan da nan sautin muryarta ya koma daidai. Ta dinga shi masa albarka. Bata ga laifin Hajjo ba da take so wa jininta Taj. Da tana da sauran ƴa ma kafin Hajjon tayi masa tayim Anisa za ta haɗa su. Abu guda ne dai ta ajiye a ranta. Idan yaje yace baya so to fa dole a haƙura. Don sun riƙe shi bata so ayi amfani da hakan a matsayin dalilin yi masa tilas. Zai zamana ba don Allah su ka taimaka masa ba.
Dariyar mugunta Kamal ya dinga yi bayan Taj ya gama faÉ—a masa yadda su ka yi da Hajjo.
"Salwa kuma fa? Ko har yanzu ba fahimci ta mato maka ba?"
"Hmmm, ai baka san me tayi min ba..." ya sake kwashe labari ya sanar dashi.
Kamal dariya harda faÉ—owa daga kan gado. FaÉ—an da su ka manta dashi kenan aka koma hirar masoyan Taj.
"Yanzu dai da gaske Abujan zamu je."
"I'm not interested Happiness. Ina tsoron kada naje su zata na amince."
"Sai mu yi mata bayani mu nemi haÉ—in kanta" ya É—an kalli Taj É—in "akwai wadda ka ke so ne?"
Kamar ya faÉ—a sai ya tuna reaction É—in Kamal akan Abban Hamdi kawai ya fasa. Shiryawa su ka yi su ka tafi site tare. A hanya
"Na fa yi maka laifi Happy. Naje na sake lalata chance ɗin Mal. Habibu ya karɓi aiki da kai."
Ana kukan targaÉ—e, ga karaya ta zo. Taj ya gama sauraron Kamal ya ma rasa abin da zai ce.
"Kayi shiru" Kamal ya furta yana satar kallonsa.
"Ka san bana ganganci da rayuwata. Ba don haka ba duka zan maka."
"Sai da naje nake ganin kamar ban kyauta ba. Amma ni yadda ya É—auki zafi da jin sunan Alhaji yafi damuna. Kana ganin ko shi ma yadda yayi maka haka yayi masa? Naji Yaya Hayatu ma yake kiransa."
Da daddare Taj ya kira Hajiya ya tambayeta game da Abba Habibu. Don kada ta zargi komai sai ya ce,
"Hajiya don Allah mece ce alaƙar Alhaji da Habibu ɗinnan?"
"Me yasa kake son sani?"
"Don na kiyaye. Kada na taɓa bari girki yasa nayi koyi da irin tasa rayuwar"
Hajiya na jin haka kuwa tayi masa bayanin da yake nema. Alhaji ya so Habibu tamkar ƙaninsa na jini. A rayuwarsa kamar yadda ƴaƴansa su ke gani yana son kyautatawa duk mai mayar da hankali a harkar ilimi. To Habibu sai dai ace masa gifted. Kana faɗa yake kwashewa. Sai ka rasa wace irin ƙaddara ce ta karkata masa rayuwa ta mayar dashi ɗan daudu. Gashi a lokacin daudancin mafi akasari ba a raba shi da kawalci da sauran alfasha mai zubar da mutumci.
"Da ya dawo daga Saudiyya yayi ta bibiyar Alhaji yana neman ya taimaka masa da jari ko ya ɗauke shi yaron shago. Amma waccan ƙyama da yake masa tun farkon fara daudun tasa yayi masa kora ta wulaƙanci."
Jikin Taj ya yi sanyi sosai. Idanunsa su ka kaÉ—a su ka yi ja.
"Bai taimake shi ba?"
"Inaaa. Ka san shi da kafiya. Tunda ya juya masa baya bai ƙara waiwayarsa ba. Ni dai ƙarshen labarinsa da naji ance ya buɗe shago yana abincin sayarwa."
Shiru taji ya yi da tana magana. Ta rage murya,
"Taj ba za ka sauke naka ƙudurin kayi yadda yake so ba?"
"Hajiya ba haram bane. Ki cigaba da sani a addu'a. In sha Allah ba zan taɓa yin abin da za ku yi baƙincikin zaɓina ba."
***
A cikin wata guda mamallakiyar Luciousbites.ng wato Hauwa ƙawar Anti Labiba ta san tana tare da haziƙar ɗaliba. Duk snack ɗin da su ka wuni koya to in sha Allah washegari idan Hamdi tayi kuskure ba zai yi yawa ba.
Ita babu ƙiwa ko ha'inci, ɗaliba kuma mai ƙoƙari. Aikin nasu yana tafiya yadda ake so. Wasu dama ta ɗan iya sai dai yanzu ta koyi hanyar da ta dace da zamani wurin inganta saninta. Sannu a hankali ta ƙware wajen yin doughnut, samosa, meatpie, springrolls, chinchin irin na ƴan gayu, gashin nama da kifi kala kala. Da kuma uwa uwa haɗaɗɗen plain youghurt, coconut infused youghurt da yogo fura.
A gida irin farincikin da Anti Labiba ke gani a tare da ita har mamaki take bata. Mijinta ma sai da ya ce wai gani yake kamar an canja ta da wata. Yaran gidan kuwa tunda an yarje mata gwada abin da ta koya, sun kwashi gara ba kaÉ—an ba. A ci a gida kuma aje makaranta.
***
Wannan wata gudan harda ƴan kwanaki a ɓangaren Taj cikin wahala su ka zo masa. Kacokan ya ajiye aikinsa bayan ya wayar nan da ya yi da Hajiya. Ya karkata akalarsa zuwa ga son lallai sai Abba yayi aiki tare da shi. Kamal da yaga ba zai iya hana shi ba sai ya bashi goyon baya.
Ranar farko tun safe ya shirya yaje ƙofar gidan Abba. Bai aika a sanar da zuwansa ba. Ya yi zamansa a cikin mota har Abban ya zo fita sannan ya tare shi. Ai kuwa yana ganin shi ya sauya fuska.
"Baka sami saƙona a wajen ɗan uwanka ba?"
Gaishe shi Taj ya yi. Bawan Allah yana faÉ—an ya tsahirta ya amsa sannan ya cigaba.
"Bana son rigima da mahaifinku. Ban san me ku ka ji game dani ba. Amma ko ma mene ne nufinku ni da Allah na dogara."
"Don Allah ka saurareni. Da alkhairi na zo maka."
Cikin gida Abba ya koma. Bai ƙara fitowa ba har la'asar. Taj ya tafi amma bai karaya ba. Washegari ma ya sake zuwa. Ranar Abba ko sauraronsa bai yi ba ya wuce ya yi tafiyarsa. A haka su ka cinye sati guda. Wasu kwanakin duk sammakonsa idan ya zo zai samu Abban ya fita kafin ya zo.
A kwana na tara Taj sai ya canja tsari. Tare su ka zo da Kamal wanda ya ce zai bada haƙurin abinda ya yi kwanaki. A zatonsa ko shi yasa Abban yaƙi sauraron Taj. Yaro ya tura ya ce a faɗawa Abba su Taj sun zo kuma wallahi yunwa suke ji.
Sajida ce kaɗai a gida da Yaya. Halifa da Zee suna makaranta. Sajida tana jin saƙon yaron ta figi mayafi ta fita. Yaya tana ta kiranta taƙi dawowa. Abba kuwa ƙwafa ya yi.
"Bawan Allah zamu haÉ—aka da Æ´an sanda wallahi. Bar ganin kuna da kuÉ—i" ta harare su duka "wallahi muna da masu tsaya mana mu kara daku a hukumance."
"Ki yi haƙuri ƙanwarmu. Aiki kawai ƙanina yake son yi tare dashi. Shi ma sana'ar girki yake."
"To ya ce baya so. Ai.ya faÉ—a mana ko ku su waye." Ta ce da tsiwa.
"Ɗan tsaya mu yi magana" Taj ya ce bayan ta gama magana. Tsayuwar tayi tana karkaɗa ƙafa ita a dole ranta ya ɓaci.
Tarihinsa ya bata a taƙaice.
"I believe yadda nake son in dawo da ƙimata a wurin Alhaji haka Abbanku zai so mutane su yi masa uzuri su karɓi sabuwar rayuwar da ya gina."
Cikin mutuwar jiki ta ce "haka ne."
"Ina son yin aiki da Abba amma a setting da ya bambanta da wanda ya saba. A inda maza masu yin komai na maza su ke girki. Burina idan an kwana biyu rayuwarsa tayi daidai ta yadda masu aibata shi a bayansa za su ji kunyar abin da su ka yi."
Ƙwalla ta saukowa Sajida "zai yiwu? Kana ganin wannan abubuwan na mata za su barshi?"
Kamal ya sanya baki "Allah aka ce. Ba yadda za ayi ka bar kowa ka kama Shi sannan kasa rai da ganin ba daidai ba. Taj only wants to help."
"Mece ce ribarsa idan ya taimaka masa?"
"Mutane su fahimci akwai sana'o'in da basu keɓanta ga mata ba kawai. Sannan ƙyama ba ita ta dace da irin wanda ya yi rayuwar Abba ba. In an bi hanyoyin da su ka dace shi ma zai karɓu a cikin mutane kamar kowa" Kamal ya sake bata amsa.
Abin nema ya samu Sajida ta koma gida da murnarta. Abba na ganin hawayenta ya tashi.
"Me su ka yi miki?"
Ta fashe da kuka "don Allah Abba ka sauraresu. In sha Allah wannan wahalar neman wurin hayar zai ƙare."
Fita ya yi ya sallame su. Taj sai ya ƙi motsawa.
"Zan sa a nemo min mahaifinka ya zo ya tafi da kai."
"Zan tafi amma don Allah ka bani abinci. Yunwa nake ji."
Abba ya kallesu. Duk sun yi laushi.
"Ba ku karya bane?" Ya tausasa murya. Sai muryar tasa ta sake yin ƙasa.
"Ni dai na sha tea. Happy kuma bai ci komai ba."
Abba ya kalli Taj da mamaki "Happy kuma?"
"Eh. Sunansa kenan" Kamal ya bashi amsa.
"Yana sallah kuma?" Abba ya tambaya harda matsawa baya.
Me kuwa za su yi banda dariya. Taj yana yi ya riƙe ciki. Abba ya sami kansa da yin murmushi bayan sun yi masa bayanin sunayen nasu.
"Innza ku ci ko indomie ce sai na karɓo a shago Sajida ta dafa muku."
"Don Allah abinci muke so. Wanda ka girka." Taj ya ce da sauri.
Girgiza kai Abba yayi yana É—an murmushi.
"Ku jira nayi muku iso a ciki."
Sajida ce ta leƙo ta kira su bayan ya shiga ciki. Aka yi musu shimfiɗa a tsakar gida. Yaya ta fito da lulluɓi su ka gaisa. Taj ya dinga kallon gidan yana ayyana wai fa a nan yarinyar nan da ya gani take rayuwa. Yana son tambayar ina take amma dole ya kama bakinsa.
Abba ya shiga kitchen suna iya hango duka motsinsa ta tagar dake tsakar gidan. Kai kawo kawai yake yi cike da ƙwarewa. Yaya da Sajida kuma suna jansu da hira jefi jefi. Kamal ne kaɗai yake amsawa. Hankalin Taj ya yi kitchen. So yake kawai yaga yadda Abba yake aiki.
Yaya ce ta lura da hakan ta yiwa Abba magana. Yaran sun burgeta saboda babu girman kai a tare dasu.
"Nace ko za ka bari ya shigo ciki ya taya ka?"
"A'a, nagode."
Taj ya tashi "gani kawai zan yi. Ba zan saka hannu ba."