Sashe 70
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ki dubo waƙar I am a disco dancer a youtube. Ni kuma idan baki daina wannan kukan shagwaɓar ba in baki mamaki a gaban mutane. Ita zan yi. Kin kuma san zan iya. 80s aka yi ta ba ta zamaninku bace."
"To Baba Happy. Na ma share hawayen" ta goge idonta da kanta don barazanar Taj ba abin da za ta share bane.
"Wannan ladabin ba na gaske bane. Sai na tambayi Sajida naji ko kin ƙara yin kuka."
"Allah na daina."
"Hamdiyya" ya kirata a tausashe.
Kasa buÉ—e baki ta amsa tayi saboda kiran nasa na daban ne.
"Uhmm"
"I'll see you later."
"Bye" ta miƙawa Sajida wayar.
"Iiiiiikon Allah" Sajida ta faÉ—i baki buÉ—e "me zan gani ni Sajida Æ´ar Habibu? Hamdi? Dama rashin jin muryar mijinki ne yasa ki kuka? Shi ne ki ka É—orawa baiwar Allah Yaya. Ai kuwa bari nace mata tayi zamanta."
Da sauri Hamdi ta miƙe tana kici kicin karɓe wayar "ɗaukota fa zai je ya yi. Shi yasa ki ka ga nayi dariya."
Zee tayi dariya "anya kuwa? Naji fa kina zancen wata waƙa wai bata da hayaniya."
"Ke, kira Ya Baballe ku gaisa kema ki ji daÉ—i."
"Baballen lafiya? Sunansa Sadiq" ta faÉ—a tana kallon yayyen nata.
A tare su ka bushe da dariya sannan Hamdi ta koma ta zauna aka gyare fuskarta kamar bata yi kuka ba. Ana gamawa ta koma gefe ta buɗe youtube. Hannunta yana ƙaiƙayin ganin waƙar da Taj yake cewa zai yi. Da ta kunna ɗaya tayi kama da ta 80s ɗin daga ɗaukan ma. Ɗayar kuwa ɗaukan zamani ne. Bata ma ɓata lokacin kallon ta zamanin ba wadda ta kasance remake ɗin tsohuwar. Danna tsohuwar tayi inda kunya ta kusa sumar da ita da rawar da Mithun yake yi. Saboda raye raye nan taƙi jinin waƙe-waƙe. Idan Taj ya yi wannan girgizar da karya jikin tabbas a wurin dinar za ta tafi ta barshi.
Su Zee dai kallonta kawai suke yi. Tana duban waya da ido É—aya tana kawar da kai.
"Ta fa ci kai wannan." Sajida ta faÉ—i su ka yi dariya ko kula su bata yi ba duk da taji.
*
Da Taj ya gama wayar, ji ya yi an ture shi. Sai lokacin ya ankara ashe a jikin Kamal ya jingina da shauƙi na ɗibarsa. Ya rasa me yasa shi da Hamdi basa iya yiwa juna baƙunta. Kamar ba jiya jiyan nan da sauran ƴar rigimarsu ba. Yau kam komai ya wuce!
ÆŠaure fuska Kamal ya yi "Na ma rasa abin da zan ce maka Happy? Wato haka ake soyayyar ni ka barni ina fama da instagram da daddare?"
Taj ya kama dariya "ba dai ka tsaya wasa ba? So kake sai Dr. Mubina ta kawo maka katin aurenta ka zo ka ce min zuciyarka za ta fashe ko?"
"Allah ma Ya kiyaye. In sha Allah ba zan ga aurenta ba." Cewar Kamal yana mantawa da wa yake magana.
Wata irin juyowa Taj ya yi yana kallonsa "saboda kai za ka aureta ko kuwa ƙasar za ka bari idan ta tashi auren wani a dalilin nauyin bakinka?"
Wayancewa Kamal ya yi "likitoci na auren Æ´an kasuwa ne? Idan rabon wani ce sai in tafi China odar kaya kafin a gama bikin."
Tsaki Taj ya yi "ta nan kuma ka ɓullo? Hmmm, kai ka san yanayin aurena da matsalar Alhaji ne su ka shige min gaba. Ba don haka ba da yanzu kai ma kana kwanciya kamar gasara a ruwa idan kuna waya."
"Wannan karin magana ne ko me?" Kamal yana dariya ya tambaye shi.
"A bakin Ƴar Ficikar nan naji."
Dariya su ka yi sannan Kamal ya ce zai fita waje ya tada mota kafin Taj ya fito sai su É—auko Yaya. Æata lokacinsu faÉ—an iyaye zai jawo musu.
Yana fita Taj ya bishi da ido. Jikinsa yana bashi tabbas akwai abin da ɗan uwan nasa yake ɓoyewa. Kwana biyu ma tunda ya dawo ya gan shi a rame. Yanzu ne ma ya ɗan ciko. Zuciyarsa ta bashi ko ma mene ne ya shafi Dr. Mubina. Kuma yafi tunanin ƙila soyayyar Happiness ce bata karɓa ba. Da an gama bikin nan zai je ya sameta har asibiti ko ya nemi gidansu. Indai ba wani aka bawa ita ba zai nuna mata cewa rashin karɓar Kamal asararta ce. Happiness is a rare gem. Ko shi da ya same shi a matsayin ɗan uwa ba ƙaramin dace ya yi ba.
Ƙarasa shirinsa ya yi su ka fice daga gidan. A daidai bakin layin su ka ga motar Ahmad wanda dawowarsa kenan daga Bauchi. Horn su ka yiwa juna. Basu kula da Salwa a gaban motar da kuma Mami dake kwance a baya ba.
Kiran wayarsa Kamal ya yi yana sanar dashi kayansa wanda duka Æ´an mazan gidan zasu saka banda ango suna É—akinsa. Sun bawa Anti Zahra ta ajiye masa kafin ta tafi.
"Zan É—an makara amma. A gajiye nake."
"Wai ina ka je ne? Ance tun safe ka fita."
Ahmad ya kalli bayan motarsa ya sauke numfashi.
"Sai mun haÉ—u dai."
Da taimakon Salwa su ka shigar da Mami cikin gidan. Gabaɗaya ta rikirkice saboda ƙamshin turaren Taj da hancinta yake iya bambancewa duk inda ta ji shi. Ɗakin da take zama Ahmad ya ce su shiga da Mami.
"Bari nayi wanka naje wajen dinner É—innan. Ba zan jima ba in sha Allah. Gobe da safe sai mu tafi asibitin."
Da azama ta miƙe ita ma bayan ta kwantar da Mami "Nima bari na shirya kafin ka fito."
HaÉ—e fuska Ahmad ya yi "Salwa."
"Na'am." Sai kuma tayi murmushi "wallahi sauri zan yi Yaya."
"Ba ki da hankali ashe." Ya nuna kansa yana juya ɗan manunin yatsansa cikin ɓacin rai "wa za ki barwa Mamin da kike zancen zuwa dinner?"
Murmushi tayi "lahh, Ya Ahmad ai kai ma ka san ba zan tafi haka kawai ba. Tun a hanya nayi magana da Anti Zabba'u (ƙanwar Mami). Tana hanya ma don na faɗa mata mun shigo gari."
"Yaushe ku ka yi maganar ban sani ba?" Ahmad ya tuhume ta.
"Tun jiya ne bayan mun yi waya da kai."
Zama ya yi a gefen gadon yana matse gaban goshinsa kafin ya É—aga kai ya kalleta da takaici.
"Dama shirinki kenan shi yasa ki ka yi min ƙaryar Alhajinku ba ya kula da lafiyarta?"
"Wallahi Yaya..."
A harzuƙe ya tashi kamar zai kifa mata mari "Shut up Salwa. You are very stupid."
"Don na ce zan je bikin ƙaninka kake zagina Ya Ahmad?"
"Ba za ki ba! Ko ƙalau Mami take babu inda zaki. Haba! Yarinya kin bi kin haukace kuma kina neman haukata kowa. Taj baya son ki, kuma ko yana so ina cikin masu hana shi aurenki saboda baki san bambancin so da obcession ba."
Kuka ta fashe masa dashi. Tana jin saukar maganganunsa tamkar sukar mashi. Sai ta mallaki Taj a matsayin miji kuma akan idonsa ta ƙudurta a ranta.
Mami tana daga kwance tana ɗaga lafiyayyen hannunta akan su yi shiru. Kallonta Ahmad ya yi ya fice kawai domin dai ba a canjawa tuwo suna. Alh. Mukhtar ya faɗa masa komai da yaje ɗaukarta. Ya kuma sanar dashi cewa ya saketa sannan idan sun tafi to ta tafi kenan daga rayuwarsa. Har abada baya son sake ganinta. Ƙannen Salwa mazan suna wajensa. Ita kuma ya ce idan sun gama zaman asibiti ya dawo masa da ita domin aurar da ita zai yi. Sun gama magana da wanda zai aureta ma.
Wannan ne dalilin da yasa ya taho da ita. Ba wai ƙaryar da tayi masa ba. Don tabbas komai na buƙata Ahmad yaje ya samu suna dashi. Kawai mijin nata ne dai ya fita harkarta.
"Zan jira Anti Zabba'u ta iso kafin na tafi." Ta ce da Mami.
"Uhmm uhmm Salwa" Mami ta ce da ƙyar.
"Mami zani fa. Na san da lafiyarki ƙalau za ki bani goyon baya."
Banɗaki ta shiga ta sillo wanka. Ta fito tana cikin shiri Anti Zabba'u tayi mata waya cewa tana bakin gate. Garin saurin ta buɗe mata abu ya faɗo daga jikinta bata sani ba. Yunƙurawa Mami tayi ta leƙa abin. Sai da jikinta ya kama rawa. Sabuwar laya ce don zaren fari ne tas irin wadda take taunawa idan za ta yiwa Alh. Mukhtar magana. Zarginta akan Salwa ya tabbata. A asibiti Salwan tayi zaton bacci take ta ɗauki wayarta ta kwafi lamba. Kuma taji buƙatar da ta faɗa...tana son mallake wani. Sai yanzu ta gane malamin tsibbunta ne Salwan ta ɗauki lambarsa. Kenan duk abin da take yi ƴar na lura? Bata son inda tabi har rayuwa tayi mata wannan atishawar ƴan tsakin ita ma Salwa ta bi. Da ƙalau take duk inda ake takawa zata je domin farincikin ƴarta, amma bata so ƴaƴan su yi wannan rayuwar.
Bakin Salwa kasa rufuwa ya yi da ta buɗe ƙaramar ƙofar gate su Anti Zabba'u su ka shigo. Don ma babu motar Ahmad ta san ya tafi. Gayya guda har su shida. Ita da ƴan matan ƴaƴanta guda uku. Sai babbar bazawara da goyo. Kowacce ta bawa shabiyar baya. Ita ma Anti Zabba'un ta gaji da aure aure ta haƙura. Dama kuma ta jima tana roƙon Mami ta tilasta Ahmad auren guda cikin ƴaƴan nata amma taƙi yarda saboda kar ta san kar ne. Sai gashi Salwa ta faɗa mata halin da Mamin take ciki. Da murna ta kwaso jiki. Ko Ahmad yana so ko baya so sai ya auri ɗaya kuma ya saki wannan mai dara daran idanuwan.
Ita dai Salwa bata san Mami taga layarta ba. ÆŠaukewa tayi ta tura a jaka. Ta gama shirinta tsaf ta haÉ—a da turaren wajen su Ummi ta fita. A rashin sani turaren aikin Alh. Usaini ta É—auka tunda shi ne aka ce mata zai kawo soyayya tsakaninsu.
A daidaita sahu ta samu har event centre É—in. Motoci ko ta ina. Ta zo bakin gate tayi turus don babu kati!
***
Shafawa ido toka Taj ya yi da ya shiga ciki ya ce da Abba ya roƙi da Yaya ta fito su tafi saboda abin da Hamdi ta ce. Yayan da Inna Luba suna zaune a wajen.
"Ayi haka Taj? Muna da gefe bai fi ba?"