← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 96

Sashe 7

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙuttt ya haɗiyi yawu sannan kamar mai taka iska ya bi su ciki. Ƙofar na rufewa gabansa ya sake faɗuwa. Sai dai duk wannan tsoron ya kau lokaci guda da ya ƙarewa kitchen ɗin kallo na kurkusa. Aiki kowa yake yi da sauri-sauri ga magana ana yi wadda ya fahimci karanto odar masu jiran abince ce ko bada umarni. A gefe guda kana iya ganin wasu suna ta jere plates ɗin da aka gama haɗawa a wani abin turawa za a fita da shi. Ga masu girki sun duƙufa suna yi. Wuta da mai da cokula sai chuu...chauuu su ke. Ganinsa ya ƙare akan masu yanke yanke kamar inji. Wasu su na yanka albasa, caras, da ma nau'ikan kayan lambun da bai taɓa gani ba. Wani haɗaɗɗen murmushi ya saki sai ga ƙaton mutumin ya dawo da tray shaƙare da kwanukan abinci.

"Eat."

Mutumin tsoro yake bashi amma duk da haka ya faÉ—a masa gaskiya "Am not hungry."

"Taste our food and we talk, okay?"

Juyawa ya yi yaga dattijon farko ne ya yi magana. Musu ma wuri yake samu. Karɓar tray ɗin ya yi babu shiri ya zauna a inda aka nuna masa. Ƙamshin abincin ya tafi da tunaninsa. Shinkafa ce da kaza. Ga kuma wani haɗin albasa, cucumber da tumatir da wani ganye mai tsami tsami da daɗi kamar kunne zai fita. Wani ɗan kwano mai zurfi a gefe kuma miyar naman sa ne wanda ya dahu ya yi luguf. Sai wani abu kamar bread ko gurasa mai faɗi. Abu ɗaya ya kula shi ne babu cokali. Ya ɗaga kai ya tambaya dattijon nan shi kuwa ya ce masa.

"We eat with our hands here."

Taj ya gyaɗa kai ya miƙe yace zai wanke hannu. Sink ya nuna masa ya wanko ya dawo. Yana zama ya yi Bismillah ya fara ci. Miyar ya ɗauka zai zuba a shinkafar da wani ɓangaren nata ya yi jaja-jaja, wani fari-fari, wani kuma yellow. Mutumin ya nuna masa ai gurasar nan ake ci da miyar. Shinkafar kuma ya zuba salad ya dinga haɗawa da nama. Ya tambayi sunan abincin aka ce masa chicken biryani ce da kuma chappati da beef curry (miyar).

Tunda ya saka hannu bai cire ba sai da abincin ya rage ɗan kaɗan. Yana ture plate kawai yaji mutanen kitchen ɗin suna ihu harda masu rungume juna. Ashe duk sun ankara da tsayuwarsa tun farko. Shi ne ogansu mai wurin ya shigo da shi. Farincikin fuskarsa a matsayinsa na wanda su ke da yaƙinin ranar ya fara cin abincinsu ne yasa su murna.

Sai da kowa ya nutsu aka cigaba da aiki sannan mutumin ya tambaye shi sunansa da dalilinsa na leƙensu.

"Kenan kana son girki" ya tambaye shi da turanci bayan ya yi masa bayani a taƙaice.

"Sosai."

"Ka taɓa yin makarantar girki ko ka koya daga wani professional?"

"A'a."

"Muna da makarantu a nan inda za ka iya yin degree."

Taj ya yi murmushi da ya hango fuskar Alhaji idan ya je gida da kwalin degree a fannin girke girke. Sanar dashi ya yi cewa karatu zai fara kuma banu damar canjawa.

"Idan ka tabbata kana da ra'ayi ni zan iya koya maka a nan. Ka je ka duba tsarin karatunka. Ranakun da baka da aji ka zo nan kayi aiki."

Baki ya buÉ—e da tsananin mamaki.

"Aiki?"

"Baka so ne?"

Da sauri ya ce yana so. Ya dai yi mamakin samu ne kafin ya nema.

Ƙaton mutumin nan ya sakar masa fuska ya ce.

"Dukkaninmu a haka yake ɗaukar mu aiki. Ra'ayin yi kawai zai gani daga gareka sai ya ɗauke ka yaronsa. Wurin nan nasa ne. Idan ka bada himma tabbas za ka ji daɗi. In kuma yaga baka da ƙwazo a wata ɗayan farko zai sallame ka."

Kamar wasa daga wannan rana Taj ya fara karatu kuma yana zuwa koyon aiki a ROYAL CUISINE. Abin farinciki shi ne kasancewar dattijon da ake kira Paaji (ɗan uwa ko yaya) musulmi. Yawancin ma'aikansa musulmai sun fi yawa ma. Komai na wurin halal ne. Sai da ya yi wata guda cur babu abin da ake koya masa a kwana ukun da yake zuwa duk sati sai sanin sunaye da amfanin kayayyakin abinci da kayan ƙamshi (spices). Hancinsa ya aikatu don ko abu na kama da ɗan uwansa idan bai tantance ba maimaici za ayi ta yi. Wasu abubuwan kuma a ido su na kama amma a zahiri ɗaya nada amfani ɗayan kuma guba ne. Dole suma sai ya gane bambancinsu don kada a bashi a kasuwa ya cutar da masu sayen abinci.

Bayan nasararsa a wannin fanin kuma aka koma koyon ɓare tafarnuwa da yankanta ƙanana. Kan kace meye wannan hannunsa ya cika da plaster. Irin wannan yankan na mugun sauri ake so ya iya. Da ƙwararre a wurin aka haɗa shi. Daga nan aka koma albasa. A haka, a haka ya ƙware a yankan kayan lambu da kayan marmari. Yankan nama ma zaman kansa yake. Sai da ya koyi haɗa mince meat ko babu na'ura da wuƙa kawai da ƴar muciya. Shekara guda ko mai ba a taɓa bari ya soya ba sai da ya zama zakara a fannin ƙananan ayyukan da su ne ƙashin bayan kowane girki.

Bayan an dawo hutu wanda yaje gida ya yi da kyakkyawan sakamakon ƙarshen shekara ta farko aka kai shi gaban wuta. Zo ka ga farincikinsa da na abokan aikin. Mutane ne ƴan asalin garin Punjab masoyan duk wani abu na farincikin al'umma. Su dai ayi nishaɗi a zauna lafiya. Shi yasa Taj ya saje cikinsu. Happy Taj su ke kiransa tun ranar da ya yi skype da Kamal su ka ji yana kiransa Happy. Da yake anfi samun ƴan ƙabilarsu mabiya addinin musulunci a Pakistan, shi yasa Paaji duk inda ya sami ƴan uwansa musulmi yake basu aiki. Taj da wani Uygur Chinese (wata ƙabilar musulmai a China) Aynur kaɗai ne baƙi.

A cikin shekara ukun farko Taj ya ƙware a girke girke da dama na yankin Asia. Banda na Indiyawa an koya musu na Larabawa da duk wani yankin Asia da su ka yi fice ta fannin abinci. Duk kuma wannan badaƙala ko sau ɗaya Ahmad bai taɓa sani ba har ya gama ya koma gida. Taj ya ci karensa babu babbaka ya haɗa riba uku a zaman nasa. Bai manta da ƙudurinsu na bitar hadda ba shi da Kamal shi yasa ya shiga wata makarantar ƙarshen mako da ake yi a masallaci. Kamal ne kaɗai ya san me yake ciki kuma ya bashi goyon baya tare da nanata masa mahimmanci barin abin a matsayin sirri.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Taj da Kamal sun ƙarƙare karatunsu a cikin shekara uku da ƴan watanni. Kowanne akwai taron convocation da za ayi a makarantarsu. Kamar yadda aka fara kai Kamal, ranar nasu taron ta zo sati uku kafin na su Taj. Alhaji sai ya ɗauki Hajiya da Umma su ka tafi Dubai. Satinsu biyu a can su ka koma gida tare da Kamal ɗin. Bayan kwana huɗu ya juya da Ahmad, Mama da Inna zuwa India.

***

Gagarumar gasar girki ce Culinary Academy of India ta saka domin samun zakarun da za ta bawa tallafin yin karatun degree na tsahon shekara uku a fannin Catering Technology and Culinary Arts. Makarantar reshe ce ta Jami'ar da ya kammala wato Osmania University. Kuma ɗalibanta ta buɗewa gasar masu ra'ayin girki waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba. Paaji na samun labari ya saka shi a gaba a gaban kwamfutar restaurant ɗin nasu ya cike komai online. Abokan aikinsu su ka yi ta murna domin da fari har ya soma yi musu sallamar komawa gida da zarar an yi convocation.

A kwana biyar za ayi komai a gama. Taj bai san da tahowar su Alhaji ba kamar yadda Kamal bai san ya shiga gasa ba. So ya yi ya yi surprising ɗan uwan nasa. Wanda kuma da ya faɗa masa zai gargaɗe shi da tahowar tasu. Duk wayarsu da gida ana ta ɓoye masa don an san ba ƙaramin farinciki zai yi ba idan su ka zo. Tahowar Ahmad kawai ya sani saboda zai zo registration na masters tunda ya gama bautar ƙasa.

Sun iso ƙasar awa guda kafin a shiga gasar a rana ta huɗu wadda ta kasance alhamis. Zuwa yanzu team ɗin Taj da aka haɗa da wani banufe ɗan Nigeria mai suna Wakili su ne su ke jan ragamar muƙami na biyu. Wasu wa da ƙani ƴan Indonesia kuma a sahun farko. Wayarsa Ahmad ya kira ya faɗa masa sunan hotel ɗin da su ka sauka.

"Yaya ka daure ka ƙaraso Uma Nagar cikin Culinary Academy." Ya ce da farincikin isowar ɗan uwansa.

Don dai yau É—aya yana ganin ba komai bane idan an sani. A tunaninsa nasararsa ta karatun da Alhaji yake so za ta sa ya bashi damar cika nasa burin.

"Me ake yi?"

"Gasar girki na shiga."

Gefe Ahmad ya matsa hankali a tashe.

"Ashe ba ka da hankali Taj? Tun yaushe Alhaji ya soke maganar nan?"

Da yanayi na ban tausayi Taj ya ce "Yaya ina so wallahi. Domin neman amincewarsa na dage sosai a makaranta. Kana ganin yanzu ba zai sauko ba tunda nayi karatun da yake so?"

"Baka da hankali." Ahmad ya sake faÉ—i yana jin zufa na karyo masa.

Duk abin da yake yi hankalin Alhaji dake magana da su Inna yana gare shi. Sauke wayar daga kunnuwansa ke da wuya yaji ya ce masa,

"Me ku ke ɓoyewa da har za ka tashi ka dawo nan?"

"Babu komai Alhaji. Ya ce min baya hostel ne."

Rashin gaskiya ya gani ƙarara a fuskar ɗan nasa shi yasa ya ce,
"Kai ni inda yake!"
RAYUWA DA GIƁI 5

Batul Mamman💖

"Alhaji..."

"Zan saɓa maka."
Chapter 7 · 0% Book details