Sashe 28
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita Salwa banda ƙawa har Maminsu ta san irin soyayyar da take yiwa Taj. Da fari ta nuna rashin goyon baya saboda ɗan tsohon miji ne. Sai da taji ta kuma ga waye Taj a wani bidiyon girkinsa a youtube da Salwan ta nuna mata tayi mubaya'a. Matashi ne mafarkin duk wata budurwa. Burin duk wata uwa da take son ƴarta da arziƙi. Ko da wasa girkinsa bai zo ranta ba balle ya dameta. Yana da kuɗi kuma ta san asalinsa. To me ya rage?
"Kada ki yarda ya manta dake. In ya tafi ki dasa kanki a cikin rayuwarsa."
"Ta yaya? Ko sau ɗaya bai taɓa nemana ba da kansa."
Mami tayi dariyar manya "wannan ai duk ba wata matsala bace. Ke ki dinga bibiyarsa. Gaisuwa safe, rana da dare. Ƴan abubuwan nan namu na mata ku baku iya ba. Sai a zauna sakato ana jiran namiji ya yi komai."
Salwa ta sunkuyar da kai "Mami idan mace tana bin namiji fa wulaƙanta ta yake yi."
Taf...taji saukar duka a kafaɗa. Rai a ɓace Mami ta ce "banda shashanci dama ai ba da soyayya za ki bishi ba. Kulawa kawai. Ko kissar ma sai na koya miki?" Ta harari ƴarta.
"Na fahimta Mami."
"Ko ke fa."
Da haka Salwa ta kafa masa ƙahon zuƙa. Waya da saƙwanninta babu wani abu da zai bada ita har yasa Taj gudunta. Yayana sama Yayana ƙasa ne dai. Gaisuwa, bibiyar ayyukansa da yi masa fatan alkhairi. Tun yana sharewa har dai bisa shawarar Kamal ya soma amsa mata a mutumce.
"Ba'a san inda rana za ta faɗi ba. Ka daina wulaƙanta duk mai nuna damuwarsa a kanka."
"Kada ta sa rai ne Happiness."
Dariya Kamal ya yi "kai ma kamar wani ɗan yaro in kayi wani abin. Ai yadda ta zo maka a ƙanwa haka za ka je a matsayin yaya. Tunda baka so ta bijiro da zancen soyayya sai ka toshe ƙofar."
"Kamar ya?"
"Ka dinga bata labarin wata a matsayin budurwarka. Wataran ka ce ma tana gaisheta."
Girgiza kai Taj yayi kamar yana gaban Kamal É—in "ba zai zama cin fuska ba kuwa?"
"A ƙanwa fa tazo maka. Kuma dai kayi mata hannunka mai sanda taƙi ɗaukar haske. Ba sai ka bita ba kawai a tafi a haka. Ya dai fi akan ka dinga shareta wanda za ta fassara a matsayin wulaƙanci."
A haka suke ta tafiya. Ya Taj da ƙanwarsa Salwa.
A ɓangaren Anisa kuma bai san wane tudu wane kwarin aka bi ba sai ji ya yi Amma ta tado masa da zancen ko za su fara haɗa lefe kafin su koma gida.
"Lefe kuma? Na wa?" Ya tambayeta kai tsaye babu mamaki a tare dashi.
"Kada ka raina min wayo Taj. Ya ku ka yi da Anisa?"
"Anisa kuma?"
Amma ta ɗaure fuska "Allah idan na sake magana ka ce min 'kaza kuma?' Sai ranka ya ɓaci."
"Yi haƙuri Ammana." Ya yi mata murmushi.
Mayar masa tayi sai kuma ta sake shan kunu.
"Ka san sau nawa Daddy yana yi min maganarku? Sai dai nayi ta kame kame saboda ka ƙi cewa komai."
Yadda su ka yi da Anisa da Hajjo ya faÉ—a mata.
"Ni na zata mun gama magana tunda ta fahimceni."
Yanayin Amma duk babu wani kuzari ta ce "Maganar da aka fara daga sama ai a can ya dace a ƙare ta. Me yasa ba ka faɗa min ba?"
Ya yi shiru. Ba zai iya ce mata yaga kamar tana so ba shi yasa ya kasa sanar da ita ba.
Anti da kanta tayi mata waya tana cewa wai ta kira tayi mata murna Æ´arta ta sami miji. Anisa da Taj sun daidaita.
Da murna Amma amsa mata da "cewa zaki yi na cigaba da tari. Allah Yasa damu za ayi."
"Amin amin" Anti ta amsa da farinciki.
Da su ka yi waya da Daddy ma zancen kenan. Har yana cewa idan su ka dawo da kansa zai yiwa Alhaji magana. Ƙudurin Taj na aure bayan ya koma gida ba abin a kawo ido a zuba masa bane. Dole su za su yi nasu ƙoƙarin a yanzu da Taj ya zama successful su mayar dashi gaban mahaifinsa.
Ya gama tsare tsaren hanyoyin da zai bi domin bawa Alhaji haƙuri ya janye fushinsa. Wanda hakan ya yiwa Amma daɗi sosai. Shi ne ta tayar masa zancen shi kuma ya nuna ba haka aka yi ba.
"Ni yanzu ya kake so in yi Taj?"
Ta ma rasa ta inda za ta ɓullowa lamarin. Idan ta nuna bata so a yanzu da maganar ta fito daga bakin kishiyarta da mijinta kowa ita zai zarga. Za a ce ita ce bata so. Sannan ga dukkan alamu ma dai gadar zare Hajjo take neman ko ma a ce ta ƙulla mata. Kuskure guda zai sa a ce tana gudun ƴar kishiya. Ko kuma a gorantawa Taj rufin asirin da aka yi masa. Ta san Hajjo sarai. Idan abu bai tafi yadda take so ba to mutum ya shiga ɗari ba ma uku ba.
"Kasan me nake so da kai?"
Ya girgiza kai "ko mene ne zan yi miki Amma."
"Kada ka nuna musu komai ta waya yanzu. Don Allah ko da wasa kada kayi abin da Anisa za ta sami maganar da za ta kaiwa Hajjo. Idan mun koma gida sai ayi maganar a gaban kowa. Yanzu ko me zamu yi a waya babu mai fahimta."
Ko da Daddy ya zo lokacin da za ayi mata send-off party na retirement basu nuna komai ba ita da Taj. Lafiya lafiya yake waya da Anisa su gaisa. Idan bata kira ba sai ayi sati biyu bai nemeta ba. Bisa shawarar Anti da Hajjo da su ka kitsa wancan zance na amincewarsa duk da Anisan bata so haka ba take yawan kiransa ko ta tura saƙo ta whatsapp.
Wata gomq sun ƙare kamar ƙifta ido da buɗewa. Duk wani shiri na komawarsu gida ya kammala. Catering services ɗinsa na Happy Taj ne dai bai rufe ba. Duk lokacin da buƙata ta tashi zai iya komawa ya yi aikinsa ya dawo gida.
Zuciyarsa a ranar da za su tafi tana cike da É—okin sake ganin Hamdi. Ba tare da saninta ba, duk wasu abubuwa musamman wanda su ka shafi samari yana sani a wajen Æ´an uwanta. Zee akwai surutu. Ita ke faÉ—a masa irin abin da Hamdi take yiwa samari idan sun zo.
"Ni fa ina ganin kamar akwai wanda take so" ta taɓa faɗa masa watarana.
Murmushi yayi shi kaÉ—ai da ya ji muryar Hamdi tana cewa Zee "gulmammiya, yau kuma faifaina aka buÉ—ewa Salman Khan? Ki gama Yaya tayi mana shari'a don ba yarda zanyi ba."
Zee ta diririce, wayar da bata gama ba kenan ta tashi tana bata haƙuri.
Ita kuwa kaza huce kan dami tayi. Mutumin nan na Abuja da bata san sunan shi ba ta riga ta cire shi a rai, tana kuma jin haushin yadda ya jirgata ta hanyar nuna kamar ya damu da ita.
***
Dogon tsaki mai madda da gunna Ummi ta saki a lokacin da Iyaa take duba katunan bikin Sajida da Yaya ta kawo da kanta.
"Allah Ya shiryeki Ummi. In Allah Ya so ba zan taɓa aibata ki da bakina ba balle ki fi haka."
"Me kuma nayi? Yanzu mutum bai isa ya yi tsaki ba sai an fassara shi?"
Tashi Iyaa tayi ta bar falon. Idan ta zauna tabbas za ta ƙare da dukan Ummi da duk abin da ya zo hannunta. Haka su ke ta fama tun bayan dawowarta daga makaranta. Ummi ta kangare fiye da tunaninsu. Maganar aurenta da aka sa ran yi da ta gama makaranta tabi ruwa. Mijin dama na gida ne. Duk shaiɗancinta tana masifar son sa kamar rai. Zancen duniya da baya ɓuya sai gashi mahaifiyarsa da su ke ƴan maza zar da Baba Maje sannan ƴar mace da namiji da Iyaa ta zo har gidan neman ƙarin bayani.
Yayinda Ummi take ta tsula tsiyarta a makaranta bata taɓa tunanin akwai idon sani da za su iya kawo zancenta gida ba. Sai gashi a hawan hawa maganar bullying ɗinta da haura katanga tana bin samari yawo ta dawo. Maganar ayi ƙarya ko kwaskwarima ma ba za ta yiwu ba. Dole su ka faɗi gaskiya da roƙon rufin asiri.
"Maganar nan ba za ta taɓa fita daga bakina ba in sha Allahu. Amma fa aure babu shi Fisabilillahi"
Baba Maje ya kalli Æ´ar uwarsa, sai dai bai ji haushinta ba sosai. Ko shi ne zai iya yin haka.
Washegari ya mayar musu da kuÉ—in aurensu. Kayan kuma su ka ce a barsu. A ranar babu wanda ya runtsa a gidan. Ummi kusan hauka tayi musu tuburan. Kuka da magiya harda barazanar tana son auren.
"Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Ke ki ka haƙawa kanki wannan ramin. In kina da hankali sai ki canja tsarin rayuwarki don gujewa maimaici."
Tana gunjin kuka ta ce "yanzu Baba akan É—an daudu da Æ´arsa ka gwammace rayuwata ta zama haka? Baka barni nayi jarabawa ba sannan auren ma ka kasa hana a fasa shi?"
"Ɗan daudun ne kuma yake ta fafutukar ganin kin koma makaranta ba." Ya ce da faɗa "amma da yake kin daɗe kina taɓa mutumcin mutane Allah Yana yi miki talala yanzu ai kin ga ishara. Duk ƙoƙarinsa abu yaƙi ci yaƙi cinyewa. Ni kuma da hannuna ba zan sake kai ki wata makarantar ba."
Gidan da su ka barta basu tsira ba. A hankali ta tsiri fita yawo. Idan ta dawo ayi faɗan, dukan da nasihar duk a bayan kunnuwanta. Shafawa idanunta toka kawai tayi tana abin da ranta yake so. Cikin watanni kaɗan ta ɗashe fata ta koma fara tas. Ga magungunan da take sha na supplement masu ƙara wasu sassan jiki. Halittarta duk ta sauya ta koma wata daban. Duk inda ta ratsa maza ke bibiyarta suna kashe mata kuɗi. Wayo da dabara irin nata yasa taƙi yarda ta bada kanta. Amma fa tana bari su fanshi wahalarsu ta hanyoyi daban daban. Hukuncin faɗa da duka ya ƙare. Sai nasiha da addua tsakaninta da iyayenta.