Sashe 9
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Indai ni zan yi maka izini to ka sani har abada ba zan taɓa yarje maka ka sake tsayuwa gaban murhu ba. Allah Ya yi min rufin asirin da ko mata cikin tsatsona ba za su nemi kuɗi da girkawa wasu abinci ba balle kuma namiji."
Ƙwalla mai zafi ta shiga saukowa Taj a yayinda yake jin kamar da gayya mahaifin nasa yake tauye shi. To amma ko zai hana saboda baya son a haɗa ɗan cikinsa da sana'ar girki me yasa ba zai duba cewa rashin zuwansa zai salwantar da mafarkin cigaban ɗan marayan da bashi da gata ba.
"Alhaji ka yiwa Allah..."
"Na gama magana" Ya furta da izza sannan ya fuskanci Ahmad "ka canja mana booking idan akwai jirgi mu tafi yau da ƙanin naka. Takardunsa kuma ka tsaya ka karɓar masa."
Hankalin Taj tashi ya yi ya miƙe da sauri "Alhaji na rantse maka ba don ni zani ba. Idan ban je ba za ayi disqualifying ɗinsa."
"Wannan nauyin sai ya zame maka darasin rayuwa a gaba ta yadda ba za ka sake marmarin saɓawa umarni na ba."
Inna da Mama har ma da Ahmad saka baki su ka yi wajen lallashin Alhaji akan ya amince amma ya yi biris da su. Taj kuwa kuka yake tamkar yaron goye. A wannan yanayin wayar Wakili ta shigo masa. Alhaji da kansa ya ce ya É—auka kuma ya faÉ—a masa ba zai je ba.
"Happy Taj yi haƙuri na kira ka da sassafe." Ya yi magana da ɗan jin nauyi.
"Kada ka damu na riga na tashi."
Wakili ya yi Æ´ar dariya "jiya wanda mu ka gaisa ka ce yayanka ne ko?"
"Eh." Ya amsa da sanyin murya.
"Breakfast na haÉ—a masa nake neman address É—in ka. Na rasa da me zan karramaka. Ko a wannan matsayin mu ka tsaya kai ne sila. Zan so yin aiki tare da kai nan gaba." Ya sake dariya "kana burgeni ne. Ina son koyon girki kamar kai."
Kasa cewa komai Taj ya yi sai ruwan hawayensa da ya ƙaru. Daurewa ya yi ya ce da Wakili zai tura masa address ɗin yanzu. Bayan ya ajiye wayar ya dubi Alhaji da ya gama jin komai.
"Ka gani ko Alhaji? Yana da kirki kuma maraya ne. Cutar shi zan yi idan ban je ba."
Gajiya Alhaji ya yi da magiyar dukkaninsu ya É—aga murya ya ce ce "Ku fitar min daga É—aki gabaÉ—ayanku."
Iko da izzarsa ba tun yau su ke damun Mama ba. Amma wannan ya fi ɓata mata rai. Wace irin zuciya ce da shi da za a dinga roƙonsa akan tallafawa rayuwar wani ya turje a kai. Sannan da girmansu ya haɗa su da ƴaƴan cikinsu ya yi musu kora irin wannan ta ƙasƙanci. Ta dubi hawayen Inna wanda ko ba a faɗa ba ta san na son share damuwar ɗanta ne. Bata cewa kowa uffan ba ta fita ta koma ɗaki inda ta baro wayarta. Kimanin minti goma ta ɗauka wurin yiwa mijin yayarta wanda ya kasance babban wa ga Alhaji ta fayyace masa komai.
"Zan kira shi yanzu. Kashe wayar." Kawai ya ce bayan ya gama jin bayaninta.
Da ta koma ɗakin yadda ta fita ta barshi haka ta same shi. Saboda halin da Alhaji ya sanya jama'ar ciki hatta iskar ɗakin bata daɗi. Shigarta ke da wuya Alh. Jafaru ya kira shi kamar yadda ya yi mata alƙawari.
"Hayatu."
"Na'am" ya amsa da ladabi domin ya yarda da aka ce babban wa uba, musamman wanda ya riƙe matsayin da gaskiya da amana irin yayansu.
"Ni Jafaru na bawa Tajuddin izinin fita yaje ya ƙarasa abin da ya fara. Sannan ina mai umartarka da ka zauna har a sallame su daga makaranta ku taho tare."
"Yaya Babba?"
"Idan ban isa ba kana iya take umarnina ka É—ora naka."
Bai bashi damar sake cewa komai ba ya kashe wayarsa. Alhaji ya kalli Mama da wani irin ɓacin rai mara misali. Sanin bata da gaskiya sai ta sadda kanta ƙasa kawai.
"Tashi kaje wurin gasar."
Iya abin da ya ce kenan ya fice daga ɗakin ya barsu. Taj bai ma gane dashi ake ba sai da Mama tayi masa magana. Ya kalli agogo yaga takwas saura mintuna ƙalilan. Gashi da ƴar tafiya zuwa makarantar. Tunanin wanka ko kusa bai zo masa ba ya fita da gudu-gudu ya sauka neman abin hawa. Ya isa tara saura minti bakwai. Har an gama shirya komai sauran teams biyun sun tsaya suna jiran lokaci. Wakili kuwa shi kaɗai ne a can gefe yana ta baza idanu cikin tashin hankali.
Taj na shiga wurin aka kaure da ihu da tafi. Ashe ba Wakili kaɗai ke jiransa ba. Masu mara musu baya da dama sun shiga fargabar makomarsu da aka ga bai zo ba. Tara daidai aka buga wata ƙatuwar ganga wadda ta bawa participants ɗin damar farawa.
RAYUWA DA GIÆI 6
Batul Mamman💖
***
Kyakkyawan envelop Yaya Babba ya miƙawa Alhaji ya kuma bishi da kallo a tsanake don son karantar yanayinsa. Kamar yadda ya yi tsammani duk wani annuri da walwalar da yake tare da ita a farkon zamansu tsaf ya kau. Duhun da yake zuciyarsa ya sami damar nuna kansa a fuskar. Disappointment ɗinsa akan Taj ya kashe masa jiki da zai yi magana.
"Kawo maka ya yi?" Da Yaya Babba ya gyaÉ—a kai sai ya ce "to me yake so?"
Kallon tausayi Yaya Babba ya yi masa. Mutum mai kafiya irin ƙaninsa yana da wuyar sha'ani. Wani zubin ya tabbatar yana sanin cewa ba a kan gaskiya yake ba amma don kada ya sauya baki sai ya cigaba da riƙo da hujjojinsa masu rauni. Sai dai a yau ya ƙudiri niyar amfani da girmansa karo na biyu ya tanƙwara ƙanin yadda yake so.
A nutse yadda zai fahimta ya labarta masa zuwan Taj gidansa kwanaki uku da su ka wuce. A lokacin sun kusa wata biyu da dawowa daga India. Sakamakon gasar girkin nan ne Wakili ya taho masa da certificate ɗinsa na ɗaukar na ɗaya. Sannan ga admission letter kamar yadda aka yi alƙawari. Shi ne ya kai masa ya gani amma ya roƙe akan kada ya sanar da kowa domin ko iyayensa mata bai nuna musu ba. Ya kawo ne saboda ya nuna masa godiya akan shige masa gaba da ya yi har ya sami damar ƙarasawa. Sai kuma Wakili da ya nuna son zuwa ya gaishe da iyayensa kafin ya wuce Minna. Shi ne ya kai masa shi inda aka yi masa tarba mai kyau. Da yaji daɗi har mahaifiyarsa sai da ya haɗa da Yaya Babba su ka gaisa.
Alhaji ya gama jin zancen da bai gamshe shi ba ko kusa ya ce "mece ce manufar nuna min tunda ya ce baya son na sani?"
Yaya Babba dakewa ya yi babu alamun wasa ya ce "ina son ka sanya masa albarka ne domin idan Allah Ya kaimu lokacin fara karatun ni zan mayar dashi da kaina."
"Kada mu yi haka da kai Yaya."
Alhaji ya furta da ƙaramar murya yana jin wani irin yammm a sassan jikinsa. Yana matuƙar ƙaunar Taj sannan burinsa a duniya yaron ya gaje shi. Idan hakan bai samu ba ya yi zarra a duk sana'a ko aikin da ya nema amma banda GIRKI. Yadda rayuwar Habibu ta sauya salo a kan idanunsa ba zai taɓa lamuncewa ɗansa ya faɗa wannan hanyar ba. Shi fa ko duk jikinsa kunnuwa ne ba zai yarda girki ba wani nau'i bane na daudanci.
"Idan Allah Ya bamu yara masu biyayya, amfani da ƙarfin iko wurin hanasu farinciki ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba Hayatu."
"Haka ne."
"Ka amince?" Yaya Babba ya tambaye shi yana murmushi.
"Ai ka ishe shi uba Yaya Babba. Ba za ka taɓa faɗin magana na musanta maka ba in sha Allahu."
Da zuciya ɗaya Yaya Babba ya miƙa masa hannu su ka yi musabaha cike da farinciki. Bai san cewa magana ce mai harshen damu Alhaji ya yi masa ba.
"Allah Ya ja kwana baban Tajuddin. Nagode da karamcin nan da kayi min. Da yardar Allah sai mun yi alfahari da zaɓinsa."
"Uhmm" kawai Alhaji ya iya cewa don bakinsa ya bushe kamar an shanya a rana. Samu ya yi ya bar gidan kamar babu abin da ya riƙe a ransa.
Bayan fitarsa Yaya Babba ya kira Mummy (ÆŠaharatu) matarsa kuma yaya ga Mama ya sanar da ita anyi nasara. Ta kama murna tana cewa hakan shi ne daidai.
"A neman haram ake yin fito na fito da burin ƴaƴa. Yadda Taj ya rame ya sanya abu a ransa ko ya zauna ba daɗinsa za su ji ba. Allah Yasa matakin nasara da samuwar alkhairi mu ka ƙulla."
"Amin" Yaya Babba ya faÉ—i yana gyara zaman gilashinsa.
Duk cikin zuri'arsu shi da wata ƙanwarsu Jamila ne ake yiwa laƙabi da ƴan boko. Matarsa ɗaya da yara biyar waɗanda huɗu sun yi aure saura namiji ɗaya. Mutum ne da ya yarda da displine ɗin yaron da ya kauce hanya amma sam bai yarda a tauye haƙƙinsu ba. Ita kuwa ƙanwar tasu da yara ke kira Amma likita ce. Sai da ta gama karatu tayi aure har ana ganin da gangan taƙi yi tun farko. Mijin mazaunin Amerika ne a can yake aiki. Bayan aurensu da ta bi shi ita ma ya sama mata take aikinta a wani asibiti. Yaransu biyu mata.
***
Ɗaki Alhaji ya kira Taj bayan ya koma gida. Ya yiwa ɗan nasa kallo na ka bani kunya sannan ya miƙa masa envelop ɗin. A take kuwa jikin Taj ya kama rawa.
"Ba da wata manufa na kai masa ba Alhaji."
"Ka ji na ce wani abu ne?"
"A'a."
"Madalla" ya gyara zama "Yaya Babba ya ce ka haÉ—a kayanka ka koma gidansa kafin lokacin fara karatun naku."
"Wane karatun? Ba service zamu tafi ba?" Ya tambaya da faÉ—uwar gaba.
A ransa Alhaji gani yake rainin wayo ne kawai Taj yake son yi masa amma ya san komai. Ƙarshenta ma shi ya roƙi Yaya Babban da ya taimaka masa ya sami komawa makarantar.
"Idan ka dawo sai ka zo kayi service É—in. Ina yi maka fatan samun nasara da alkhairi. Allah Ya yi maka albarka. Tashi ka tafi."