← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 96

Sashe 3

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dole zamu dinga canjawa with current trend. Idan ban yi shi da girma ba chanjin zai dinga bani wahala. Maybe wani ya saye space É—in kusa dani in rasa hanyar expansion. Sannan yin babba da zan iya bada hayar shops for diverse businesses zai taimaka. Idan mutum bai je don cin abinci ba maybe yaje wurin tailors, grocery shopping, wasan yara and the likes."

Taƙaita masa bayanin tayi ta hanyar nuna masa ta gane. Yana son yi mall mai ɗauke da shaguna daban daban amma na brands da suka yi suna. A haka nasa ɓangaren wato wurin abinci ko bai yi kasuwa sosai ba zai dinga samun kuɗin haya daga waɗanda suke ciki. Burinsa talaka da maikuɗi kowa ya ɗanɗana ababen more rayuwa a ƙasarsa cikin jindaɗi. Goyon baya ta bashi amma ta yi masa hannunka mai sanda akan tsoron da take ji da kuma ƴan gyare gyare.

"Kamal jininka ne. Kuma na san irin shaƙuwar dake tsakaninku. Amma kada ka manta mutane irinmu da yawa living in diaspora (ƙasar waje) muna fuskantar matsala guda. Sai mu tura kuɗi gida domin wani aiki musamman gini. Idan mun koma mu tarar babu aikin babu kuɗi. Kuma family su nuna basu yarda muyi ƙarar wanda ya cucemu ba."

Da rashin jindaÉ—i ya ce "Amma Happiness ne fa."

"Shi ɗin fa. Ka tafi gida ayi komai a gabanka. Sayen fili, kafa foundation da dukkan wani abu da ya dace ka sani. Daga cikin abubuwan da su ke durƙusar da business harda rashin kulawar wanda ya samar da shi. An bar komai a hannun ma'aikata. Sai abu ya lalace a zo ana complain."

Sai kuma ta bashi shawarar maimakon mall ita dai tafi son ya yi ƙaton restaurant tunda da girki ya yi fice. Idan an gina sai ya ware wurin wasan yara domin janyo mutane. A ɓangare guda ya yi wurin da masu gashin nama ko tsire zasu iya haya. Da kuma inda masu kayan fulawa kamar cake da su meatpie zasu yi nasu. Maimakon mall indai akwai wurin da aka keɓe domin yara to fa tabbas iyaye za su zo. A ƙarshe ta ce ya tabbatar wurin an yi shi yadda zai burge mai kuɗi sannan bai yiwa talaka tsadar zuwa ba.

Sosai yaji daÉ—in shawararta. Ya ce zai sa a sake yi masa wani zanen. Amma fa dole zai samarwa Happiness wurin da zai kafa nasa shagon. Addu'a tayi masa da fatan Allah Ya É—orar da zumuncinsu shi da yayan nasa. Sai da su ka tabbatar sun daddale komai ya ce,

"Ni fa nafi son mu tafi tare."

"Ya kamata kaje gida uwayenka su ganka haka nan."

Tashi tayi ta juya masa baya amma bata tafi ba.

"Tajuddin ka sani cewa if your intension is not honourable (idan niyarka ba mai kyau bace). Ina nufin in kana son fara business ɗin nan ne kawai domin ka nunawa Yaya Hayatu cewa kayi nasara duk da yadda ya nuna ƙiyayyar sana'arka, to lallai Allah zai kunyataka. Domin Ya karrama darajar iyaye. Saɓanin fahimta da rashin goyon baya daga garesu ba dalili bane da zai sa mu nuna musu raini."

"Korata fa ya yi" jijiyar kansa da idanu su ka firfito a lokacin da yake maganar.

"Shi kuma Allah Ya zaɓa maka a matsayin uban. Ya kuma rayata haƙoƙin junanku a kan ku. Idan ya take nasa kada ka kuskura kayi nufin binsa da ƙulli. Wallahi duk wahalarka ta shekarun nan sai ta tashi a banza."

"Amma..."

"Ka tsaftace niyarka Taj. Everything will just fall into place. Goodnight"

Juyowa tayi ta sumbaci goshinsa sannan ta ɗauki wayarta ta shige ɗaki ta bar shi a tsaye yana kai gwauro da mari. Maganarta a kullum umarni ce a gareshi. Ta san yana yi mata biyayya gwargwadon iyawarsa. Me yasa bayan tsayin lokacin nan don zai tsaya da ƙafarsa za ta ce ya tafi gida?
RAYUWA DA GIƁI 3

Batul Mamman💖

Masu tambaya littafin ba na kuÉ—i bane.

***

Auren Habibu da Jinjin ba na son zuciya bane kamar yadda Æ´aÆ´ansu suke hasashe. Yar mahaifinsu da suka fi É—orawa alhakin saboda sunanta da Zee tace wato Anti Zinatu ma ba laifinta bane. Abu ne na karamci da sanin darajar wanda ya kiyaye taka darajar.

Aure ne na zumunci domin kuwa kamar yadda Iyaa da Baba Maje suka fito daga zuri'a ɗaya su ma iyayensu mata shaƙiƙan juna ne. Mahaifiyar Habibu ita ce babba. Tayi aure a Kano da ƴaƴanta maza uku da mata biyu. Shi ne na biyu. Ita kuwa mahaifiyar Jinjin a garinsu Ɓatagarawa dake Katsina tayi aure. Bata sami haihuwar ba da wuri sai akanta. Ta haifota kyakkawa mai kama da dangin mahaifiyar. Idan ka ganta da ƴaƴan Inna Batulu za ka rantse ita ta haife su duka. Sunanta Khadija amma ake kirantan Jinjin (jinjinniya don ƙauna). Soyayya da gata gwargwadon hali ta taso tana gani wurin uwa da uba kafin Allah Ya jarabceta da cutar shan inna tana da shekara biyu da rabi. Lokacin da iyayen su ka farga ƙafar ta mutu ba ƙaramar damuwa su ka shiga ba. Idan tana tafiya kafaɗa da ɓangaren ƙirjinta na dama sai ya ballaƙo waje. Wannan abu ya tsayawa uban a rai. Har ta kai indai yana wajen da ta miƙe zai ce,

"Don ubanki koma ki zauna. Kina faman tafiya kamar wata tsuntsuwa babu kyan gani."

Ko ya ce "wannan da ma ciwon tafiya ya yi dake kika huta. Meye haka don Allah?"

Da bata da wayo uwar ke kuka idan yana wannan rashin albarkar. Ƙarshe ma yayi aure shi da matar da lafiyayyun ƴaƴan da su ka haifa su ka taru su ka mayar da rayuwar Jinjin ƙuntatacciya. Yanzu ita ke kukan uwar na rarrashi. Watarana Inna Batulu ta kawo musu ziyara ta tarar da ƴaƴan kishiyar ƙanwarta suna dukan Jinjin. Abin takaici uwarsu da ƙanwar na kusa amma wai kawaici ya hana ta ƙwaci ƴarta. Garin cangala ƙafa ta kifar da garin masarar tuwon dare. Kuma gudu ma take saboda an biyota za a ci zali.

Inna Batulu na gani tayi kukan kura ta damƙo yaran nan su uku ta bi kowa ta feffela musu mari. Ta ƙare musu zagi irin nasu na Katsinawa.

"Banda raini ba yayarku bace?" Ta juya ga ƙanwarta "shiga ki haɗo min kayanta yanzu zan wuce da ita tunda ba kya so."

"Ba haka bane Yaya."

Da takaici takalleta "kunyar marasa kunya asara ce Luba. Gidan nan kaf har mijin naki ban ga wanda ya dace ki ragawa akan kyautar da Allah Ya yi miki ba."

Jijjiga Jinjin tayi a gabanta ta ƙara da cewa "don bala'in gidan nan ƴar shekara goma sha uku ji ƙirjinta kamar anyi daɓen siminti."

"Kai Yaya Talatu?"

"Allah kuwa. Zuwa yanzu ai yaci ace an fara ganin..."

Da ɗan gudunta Jinjin ta bar wajen don bata son ƙarasa jin hirar iyayen.

Kamar wasa maigidan na dawowa Inna Batulu ta sauke masa nashi kwandon masifar ta ce kuma jiransa take a bata Æ´a.

"Gata nan har abada da gaban abada na bar miki." Ya furta ko ajikinsa.

Luba sam bata ji daɗi ba amma haka ta shirya mata kaya su ka tafi. Bata da wani farinciki ko nishaɗi a gidan idan ba Jinjin take gani ba. Da ita take hira tunda miji ya juya mata baya. Sauƙinta ɗaya ta san cewa yanzu za ta sami ƴanci ta wataya kamar sauran yara.

A Kano tabbas taga gata da soyayyar da tasa har take manta da nakasar dake tare da ita. Inna Batulu da maigidanta harma da yaransu sun mayar da ita Æ´ar gata. Matsala guda ta kula akwai a gidan ita ce ta yayanta Habibu. Lokacin yarintarsu tana iya tuna shi da yawan wasa da dariya. Yanzu kuwa kullum iyayensa cikin kukan sabuwar É—abi'arsa suke yi.

Shi ne tafiya yana rangwaÉ—a da karairaya jiki kamar mata. Ga uwa uba muryarsa da bata san ya aka yi ta motse ba. Idan ya yi magana sai ka rantse wata budurwar ce. Duk wasu take taken daudanci yake nunawa. Indai zai yi sallama a gidan daga su Inna Batulu har Æ´an uwansa basu da nutsuwa.

A yau da take da kusan wata biyu a gidan sallamar wata matashi suka ji a gaggauce. Babu kowa a gidan sai Jinjin da ta dawo daga makarantar islamiyya. Fita tayi ko kaya bata cire ba ta sami wani mutum da bata sani ba. Da gani magidanci ne ya sha shadda wagambari da ɓakar ɗara a ka.

"Inna Batulu ko Baba nake nema" ya ce kafin ta gaishe shi.

"Duk basa nan."

Kallonta ya sake yi ya tuna sun taba shiga gidansu wurin iyayensa da Inna Batulu tace ƴarta ce daga Ɓatagarawa. Shi yasa kawai ya faɗa mata abin da ya kawo shi.

"Ki ce musu Habibu na gani a gidan abincin wasu Æ´an daudu yana girki a kasuwa."

Rasa abin cewa tayi don fuskar mutumin tayi nuni da matsanancin ɓacin ran da ganin hakan ya janyo masa.

"Kin fahimci abin da nace kuwa?"

"Eh, zan faÉ—a musu in sha Allahu."

Juyawa ya yi babu sallama zai tafi ta tambaye shi wa za ta ce musu.

"Hayatun gidan Alh. Sule."

Sunan da taji bayan tafiyarsa ya dawo mata da hirar da ta taɓa tsinkaya daga mutan gidan. Akwai gidan wani mai kuɗi nan kusa dasu wanda aka ce ɗansu Hayatu ya ɗauki Habibu tamkar cikinsu ɗaya. Saboda ladabi da ƙoƙarinsa a shekarun baya ya kasance duk wata lalurar karatunsa Hayatu ya ɗaukarwa kansa. Irin abin nan na maikuɗi ya cicciɓi talaka domin inganta masa rayuwa. Ance da Habibun ya fara canja akalar rayuwa Hayatu ya shiga ɓacin rai sosai. A son sa yaron ya ginu ya zama mutum amma kullum ana yi masa faɗa yana daɗa kangarewa. Me za ayi da namiji mai girki a ƙasar hausa? Har dukansa taji ya taɓa yi watarana da ya ganshi da ɗaurin zani a ƙirji ya fita. A ƙarshe ya ce masa zai iya tsaya masa ya koyi girkin harma ya mayar dashi sana'a amma sai ya ajiye duk wani abu da yake kamanceceniya da mata. To Habibu dai ana faɗa ta kunnen dama zancen na ficewa ta hagu.
Chapter 3 · 0% Book details