← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 96

Sashe 17

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abba fa ya bar sana'arsa Hamdi. Ki haƙura kawai a kawo miki ko cikin kayan sallarki ne." Zee ta faɗi bayan ta gama kallon atampar.

Mangareta Sajida tayi "Yaya bata gargaÉ—eki akan faÉ—a mata ba?"

"Gaskiya fa na faɗa mata don kada ta sa rai." Zee ta bata amsa tana ƙunƙuni.

"Ya Sajida me yake faruwa? Ba don saboda ni ya daina ba?" Hamdi ta tambaya hankalinta na tashi.

Bayanin abin da ya faru su ka yi mata. Sannan Sajida ta ce kada ta damu in sha Allahu za a saya a É—inka kafin ranar.

"Na haƙura." Hamdi ta ce a sanyaye tana tuhumar kanta a matsayin wadda ta kasa godewa mahaifinta a lokacin da yake yi musu.

"Anti Labiba ce ta bani kuÉ—i da zan taho. Allah zan iya saya miki." Sajidan ta bata amsa tana dariya.

Daga nan su ka koma wata caftar mai daɗi. Sajida tayi saurayi a Abuja daga zuwa taya cousin ɗinsu zaman jego. Mutumin da gaske yake. Yana aiki da rufin asirinsa. Ƴan maza zar su ke da mijin Anti Labiban (ƴa a wurin babbar yayar Abbansu Anti Zinatu).

Ƴan matan uku su ka haɗa kai su na ta murna kamar ma anyi auren an gama.

Zee ce ta dakatar da shewar tasu "Kin dai yi masa bayanin Abba ko?"

Fari Sajida tayi da idanu tana faÉ—aÉ—a murmushinta "Kada ku damu. Ya ce sai da su ka yi magana da mijin Anti kafin ma ya yi min magana. Yanzu dai ku sa rai da zuwansa nan da wata guda. Lokacin ma kin dawo gida ko?"

"Su Ya Sajida an fara kashe murya a waya kenan." Hamdi ta tsokaneta.

"Zan É—auko rahoto kafin ki dawo. Dama bata yi na gani ba don kada na fesawa Yaya."

"Kin fa raina ni Zee. Ni da na raineki."

Dariya Zee da Hamdi su ka yi. Ita Zee SS2 take don tsiransu da Hamdi babu yawa.

***

Aikin gini ya soma kankama son Taj ba ɓata lokaci ya zo yi ba. Shawarar Amma ya karɓa ya yi ginin a iya restaurant da shaguna ƙalilan. Wani Architect ya kwatantawa abin da yake so. Nan da nan aka zana masa plans kala uku. A ciki ya zaɓi ɗaya. Shi da Kamal kullum sai dare su ke komawa gida. Shi ya tafi gidan Ahmad, Kamal kuma ya koma don muddin ya kwana zai gamu da fushin Alhaji.

Tsarin da aka ɗauko ya bada ma'ana sosai. Gini ne da aka yi ɓangare uku manne da juna. Na tsakiyar yafi girma da faɗi kuma shi kaɗai ne aka ɗorawa bene. Na hagu anyi kitchen ƙato da komai domin aikin fulawa. Cake, doughnut, meatpie, samosa, pies da dangoginsu. A wadace yake sai dai babu wurin zama a ci a ciki. Idan mutum baya son fita akwai ƙofa da za ta sada shi da tsakiyar wato ainihin restaurant ɗin. Ɓangaren dama wanda shi dama za a fara tararwa shi kuma kana gani za ka san na masu gashin nama da kifi ne. Ko yanzu da ake matakin gini kaɗai kana gani zai burge ka. A tsakiyar sama gabaɗayansa kujeru da teburan zama ne. Sai wasu ɗakuna biyu domin masu gudanar da taron da zai iya cin mutane hamsin. Meeting, seminar, reunion da sauransu amma banda biki. Ɗakunan ɗaya normal ne ɗaya kuma VIP. A ƙasa ma da wurin cin abincin sai ɓangaren masu haɗa natural juice da za ayi bayan kayi order. Saii kuma makeken kitchen ɗin Taj da ma'aikatansa. Har ila yau a farfajiyar wajen an keɓe wani waje da aka soma tayar da garden. Za a ƙawata wajen da liluka da wajen guje guje da wasan yara. Sai kuma cikon alƙawarin da ya yiwa kansa. Zai gina madaidaicin boutique da gininsa zai kallon restaurant ɗin ya bawa Kamal amma bai faɗa masa ba.

Yau sun bar wurin duba aikin da wuri sakamakon zazzaɓi da ya rufarwa Taj gadan gadan. Kamar wasa ya ce kansa na ciwo, sai gashi kafin su isa gidan Ahmad yana rawar sanyi. Ɗauke hanya Kamal ya yi su na cikin tafiya. Taj ya ɗago kansa da ya yi nauyi da ƙyar ya dubi hanya.

"Sayar dani za ka yi don kaganni haka Happiness?"

Kamal ya yi murmushi "kwantar da hankalinka. Ai an taya kuma naji ba tsada za ka yi ba."

"Ka ci bashi don sai na rama."

"Allah Ya baka haƙuri. Yadda nake jin yunwa idan kayi fushi dani da alama Salwa ba za ta bani abinci ba yau."

Wani irin kallo Taj ya yi masa na neman alaƙar fushinsa da cin abincin Kamal amma ya kasa ganewa.

"Wani abu ne ya haÉ—aka da ita?"

"No" Kamal ya bashi amsa mischieviously.

"Meaning?"

"A bar zancen sai ka warke."

Taj bai matsa ba. Kansa kuɗa yake kamar zai cire. Asibiti Kamal ya kai shi duk turjiyarsa. Abu ya kai da ƙarin ruwa don likitan ya ce jikinsa babu kuzari. Gashi sakamakon gwaji ya nuna yana da malaria da thypoid duk shi kaɗai. Sun haɗe da rashin hutu sun kayar dashi lokaci guda.

"Amma ba kwana zan yi ba ko?"
Ya tambayi likitan bayan an gama saka masa canula a hannu.

"Ka godewa Allah da ka iya shigowa nan da ƙafafunka. Your temperature is abnormally high."

Da Kamal ya barshi ya rufe ido don ya gaji sosai. Bayan fitar likitan da Alhaji yaji Kamal ɗin yana waya. Ya sanar dashi halin da yake ciki. Ƙaguwa ya yi yaji me Alhajin zai ce don kamar ya ƙwaci wayar a hannun Kamal. Ya dai daure har su ka gama. Shiru bai ji Kamal ya isar da saƙon Allah Ya ƙara sauƙi ba.

Sai da ya bari ya gama waya da su Inna da Ahmad sannan ya tambaye shi.
"Bai ce komai bane?"

"Yana hanya ne da alama ba ya ji na sosai" Ita ce kalmar da Kamal ya ƙirƙiro ya faɗa masa.

"Hmmm"

Kamal ya dawo kusa da shi "Happy kayi haƙuri sannan mu cigaba da addu'a."

Abinka da ƴan dangi. Lokaci ƙanƙani asibitin ya fara cika da ƴan uwansu. Kowa ya zo faɗan rashin hutu yake yi masa.

*

Don son tabbatar da zarginsa, Kamal kiran Salwa ya yi ya faÉ—a mata bayan ya sanar da Ahmad. Tunda yaji ya ce baya gida shi ne ya kirata. Ai kuwa abin da ya yi tsammani yaji. Rikicewa tayi ba tare da ta sani ba.

"Ya Kamal yana iya magana?"

Ya yi murmushi "eh, ko in bashi ne?"

Da sauri ta ce "a'a" kunya na lulluɓeta da ta fahimci za ta bada kanta. Awa guda bayan sun yi wayar ta kasa sukuni. Jira take Zahra matar Ahmad tayi maganar zuwansu dubiya tunda tayi arba'in yanzu amma taji shiru. Bini-bini ta ɗaga waya ta duba lokaci. Da ta kai matakin da ba za ta iya haƙuri ba sai ta tambayi Zahran.

"Anti Zahra na ce ko sai Hayat ya taso in an kai shi islamiyya za mu wuce asibitin?"

Zahra ta zaro idanu tana laluben wayarta "ba ki da lafiya ne Salwa? Ina yake miki ciwo? Bari na faÉ—awa Daddy."

"Ƙalau nake Anti. Dama maganar duba Yaya Taj ne."

Zahra tayi murmushi "lahhh kada ki damu. Daddy ya ce zai biyo muje yanzu. Ke kuma ki zauna saboda Hayat."

"In zauna?" Salwa ta ce ba shiri.

"Ina jin babu lallai ya kwana tumda yace min suna ta waya da Kamal. Meeting ne ya hana shi fita da wuri."

Rasa bakin magana tayi ta fita kawai. Zahra ta bita da ido ba tare da kawo komai a ranta ba.

Da Ahmad ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Zahra ya ce ta fito bayan la'asar. Kafin ta gama shirya Aisha Salwa tayi saurin fita wajensa.

"Ya Ahmad kana ganin daga gida ba za su fassara rashin zuwana duba shi ba ace don ba É—an uwana bane?"

"Ke, gidanmu babu irin wannan kin ji. Bana son Hayat yayi missing islamiyya shi yasa nace ki zauna."

"Naga kamar zamu iya dawowa kafin ya taso."

Wani irin kallo mai tattare da tuhuma ya yi mata.

"To ko mu zauna ke ki je?"

Diriricewa tayi don bata tsammaci furucinsa ba. Ta ce "Haba Yaya ba haka nake nufi ba."

Su na tafiya ta sake kiran Kamal ya ce mata jikin Taj da sauƙi. Don ya ƙara rura wutar da ya fahimci ta soma cinta ya ce
"Yanzu dai ya gama amai wallahi. Ya galabaita sosai don ko zama ya kasa. Amma dai da sauƙi za a ce."

"Kace ina masa sannu don Allah" ta ce da muryar kuka.

"Ban gane ba. Ba za ki zo ba?"

Da sanyin murya ta ce "Ya Ahmad ya ce na zauna."

Tausayi ta bashi ya daina ɗorata. Yana ajiye wayar ya yi murmushi "shege Happy. Daga zuwa ya yi ɓarna a zuciyar ƴar mutane."

Wasa wasa sai da Taj ya yi kwana biyar aka sallamo shi. Kuma tun washegarin kwanciyar tasa kullum sai Salwa ta je. Duk wani motsinta Ahmad ya kafa ya tsare har ya tabbatar da zarginsa. Hankalinsa kuwa ya tashi don yana jiye mata abubuwa da dama.

***

Takarda ce cikin foolscap Hamdi take ta karantawa tun wajen kwana uku tana son haddacewa. Speech ne malamar English ta bata wanda za ta yi ra ranar taron. Cikinta har ƙullewa ya yi yau da aka kira assalatu saboda tana da tsoron yin magana a gaban mutane. Har aka gama yayin monitoci da mataimakansu da ma prefects bata taɓa karɓa ba. Komai na mutane gudu take. Sai gashi wannan karon Principal da kanta ta ce a bata. Wai jawabin godiya ne a matsayinta na overall student ta makaranta. Da shawarwari ga ƴan uwanta ɗalibai akan hanyoyin bi domin samun nasara.

Ga dai takarda ko daga bacci ta farka za ta iya kawota tas da ka, amma da zarar tayi tunanin mutanen da za ta fuskanta sai taji kan ya koma fanko. A haka ta janyo jiki ta zo wajen taron tamkar mara lafiya. Ana tsakar gabatar da shirye shirye ta tashi kafin a zo kanta. Bayan Admin block taje ta sami wuri ta zauna tana ta bita kamar mai zuwa musabaqa.

*
Chapter 17 · 0% Book details