← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 96

Sashe 80

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya baka ganin fuskata ne?" Ta sauke mayafinta yadda zai gani da kyau.

"Allah Ya ƙara. Maza ki fito ki gyara gidan. Amma ki fara duba ko Mami tana buƙatar wani abu."

Kwanciyarsa kenan Alhaji ya kira. Dama ya tsorata saboda yayi wuri mutum ya amsa waya. Hankalinsa sai ya nemi barinsa bayan ya faÉ—a masa me Salwa tayi da kuma babban abin wato ciwon Kamal. Muryarsa kuma rawa take yi sosai.

"Ban faɗawa kowa ba sai kai. Ina buƙatar ka zo mu yi shawara Ahmad. Zan iya rasa Kamal a kowacce daƙiƙa."

"Kayi haƙuri. In sha Allahu zamu sami mafita. Gani nan zuwa."

"Ka taho da Salwa."
RAYUWA DA GIƁI 31

BATUL MAMMAN💖

YA HAKIMU gwanin Sarkin

***

"Salwa kuma Alhaji? Wani abu tayi?"

Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal kaÉ—ai ya isa ya gigita Alhaji. Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan?

Gwiwa a sage ya tambaye shi "Laifi tayi ko?"

"Kai dai ka taho min da ita."

Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon ƙodar Kamal bai hana shi nemanta ba. A kitchen ya same ta da himilin kwanuka kamar a gidan ake taron biki. Ko tausayi bata bashi ba don taurin kai da kafiya gami da son zuciyarta ne ya jawo mata. Abu guda ne dai. Ya sanyawa ransa sai ya bi kadin dukan da aka yi mata a cikin gidansa. Su Habitti ba a ci bulus ba. Muƙullin mota ya ɗauka ya ce da Zahra kiransa ake yi a gida game da bikin Taj ya fice.

Da ya kira Salwa su tafi ba ƙaramin rawar jiki ta dinga yi ba. Bata san ina za su je ba amma hankalinta duk ya tashi. Tayi zaton ya canja shawara ne zai kai ta tasha ta koma gida. Ta dinga bashi haƙuri da magiya. Bata san damuwarsa ta ninka duk wani abu da ya shafeta ba. Ciwon Kamal ya ɗaga masa hankali sosai.

Haƙurin da take bayarwa kamar ba shigarsa yake ba. Shi ne ta koma barazana
"Yaya Ahmad kada ka ɓata kuɗinka. Ba zan tafi ba domin na tabbata Taj zai zo gareni da ƙafafunsa. Ko mun je Bauchi zan shigo wata motar na dawo."

Ko ci kanki bai ce mata ba. Bashi da wannan lokacin. Ita kuwa bata sam ta shiga one chance ba sai da ta gane hanyar ina su ke bi. Ta zaro idanu da su ka ƙanƙance cikin kumburarriyar fuskarta. Ta kama ƙofa a tsorace tana kokawar buɗewa a titi.

"Me za ka kaini ayi min? Yaya Ahmad buÉ—e min na fita."

A haukace take dukan gilas tana neman yi masa ɓarna. Ya juyo ransa yana suya ya daka matsa tsawar da ta gigita ta. Saboda tsorata da tayi a lokacin da za a tambayeta sunanta da wuya ta faɗa farat ɗaya.

"Salwa!!!"

Laƙwas tayi a kan kujera har su ka isa. Su ka shiga falon tare ya sami gidan a cike fam. Zuciyarsa a take ta faɗo ƙasa daga ƙirjinsa saboda mummunan tunanin da ya zo masa. Allah Ya taimake shi su na ganinsa aka soma bashi labarin abin farincikin da aka wayi gari dashi a gidan. Idanunsa su ka sauka akan Kamal zaune a tsakiya. Wata irin ajiyar zuciya yayi mai ƙarfi sannan ya sami damar sakin ransa ya shiga cikinsu. Ko gaisawa basu gama yi ba Alhaji ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya kira shi.

"Ahmad kai fa nake jira."

Da saurinsa ya tashi har yana tuntuɓe. Kamal ya sha jinin jikinsa. Ƴar hira da dauriyar da yake yi ya kasa jurewa. Ɗakinsa zai koma kawai kafin Alhaji ya neme shi. A hanyar fita ya yi kiciɓus da Salwa. Da yake bashi da masaniyar me yake faruwa sai bai canja mata ba.

"Salwa? Ashe tare kuke ki ka tsaya a nan?" Ya kalli fuskarta "me ya same ki haka a fuska?"

Yuuuu idanu su ka dawo kanta. Jiki a mace kamar magen da aka tsamo daga lamba two ta ƙarasa ciki tana raɓe raɓe. Ƴaƴan gidan dai babu sauyin fuska amma iyayensu ko kallonta basu yi.

"Zamewa nayi."

"Allah Ya sauwake" ya ce ya fita.

Ita kuma ta ƙaraso aka gama yi mata sannu sannan ta matsa gaishe da su Inna.

"Hajiya ina kwana?" Ta durƙusa a gabanta.

"Lafiya" ita ce taƙaitaciyar amsar da ta samu ba tare da sakin fuska ba.

A ranta tayi tsaki. Ai dai ba ita ce ta haifi Taj ba take wani sha mata kunu. Ko ita Innar bata fi ƙarfin a kai sunanta gaban malam ya ƙulle mata baki ba. Nan gaba ma wajen malamin Ummi za ta je domin da alama zai fi na Mami iya aiki. Muskutawa tayi ta ƙara matsowa ciki.

"Mama..."

Mama bata jira ta gama gaisuwar ba ta tashi abinta tana duban Amma.

"Uhmmm, Jamila duba ki ga me Taj da Hamdiyya suke yi a É—akin nan har yanzu shiru."

Jin furucinta yasa gaban Salwa ya faÉ—i, ya sake faÉ—uwa. Baki ya kama rawa kamar mazari ya ji kiÉ—a. Dama ga fuska a kumbure. Sai tayi wani irin yanayi mara kyau duk suna gani.

Umma tayi dariya "kema dai Mama da rigima kike. Ba kya ko tsoron me za a buÉ—e a tarar? Sabon aure basa son sa ido fa. In ba haka ba kuwa sai aji kunya."

Inna tashi tayi zumbur ta bar musu wajen. Su ka dinga dariya banda Amma da bata gane manufarsu ba.

"Takwara me ki ka mayar min da É—a ne? Ki ka sani ko bacci ya samu tana yi?"

"Sai ya zauna korar mata sauro ko?" In ji Hajiya.

Umma da Mama sai shewa harda tafawa. Ƴaƴan na gani amma su ma basu san me ake yi ba.

Ita dai Amma tashi tayi ta barsu suna kallon suman zaunen Salwa a fakaice. Ta zubawa ƙofar ɗakin Inna da Amma ta nufa ido tana jiran ganin da gaske Hamdi za ta fito daga ciki ko yaya? In tana ciki me ya kawota gidan da sassafe? Ko dai ita ma murnar ta zo taya shi? Ai kuwa da an kira iyayenta marasa kamun kai. Me zai hana su jira ido na ganin ido? Don baƙin naci an biyo shi har gida a lokaci irin wannan da yake buƙatar ahalinsa.

*

Duk da ba komai Amma ta ji ba amma iya maganganun da su ka shiga kunnuwanta sun fahimtar da ita me yake faruwa. Akwai wani abu da Alhaji ya yiwa mahaifin Hamdi. Jikinta kuwa ya yi sanyi sai dai wayewa da sanin yau da gobe yasa ta je musu da fuskar rashin sani. Bayan ta gama ɗorawa Taj laifin hana Hamdi zuwa cin abinci, sai ta shiga ta riƙo hannunta.

"Sai da na shigo nake jin ashe jiya rigimar babanku ta haɗa dake." Hamdi ta sunkuyar da kai kawai tana murmushi "Zo ki ci abinci in kai ki gida in kuma bada haƙuri kada ace ba za a bamu ke anjima ba."

Sake yin ƙasa Hamdi tayi da kanta cike da kunya. Balle da Taj ya ce shi zai kai ta.

Ya ce da Amma "Akwai maganar da za mu yi da ita."

"Fita idona Taj." Ta harare shi.

"Please mana Ammata."

"Don ƙaniyarka ka san irin bikin da ake ta yiwa Hamdi a falo?"

"Ni kuma?" Hamdi ta fito da idanu.

Amma kuwa sai dariya ta sami damar tsokanarta domin a yanayin fuskokinsu ba za ta so su fita ba. Gidan akwai manya da masu experience da yawa. Yanzun nan za a harbo jirginsu a gane da matsala.

"Harda masu cewa ko a biyo ku da abincin nan idan ya so sai muje mu karɓo miki kayanki a gida."

"Ya Rabbi, to ya zan yi? Ko kada na fita?"

Kai da ganin idanunta da jin muryarta ka san hankalinta ya nausa da nisa. Kunya, tsoro da jin nauyi sun cika mata ciki. Da Taj ya dubeta sai da yaji kamar ya kamota a gaban Amma ya ɓoyeta cikin jikinsa. She looked so cute and innocent kamar ba bakinta bane ya gama zaro masa zantuka ɗazu.

"Wasa take yi miki. Ko Amma?" Ya rage murya shi ma É—in ba son jin wata magana babba yake yi a bakin Æ´an gidan nasu ba.

Dariya Amma tayi musu. Tana yi musu fatan alkhairi a zamansu. Sun dace sosai da juna. Sweet young Hamdiyya and Charming Happy Taj. Za ta cigaba da sanya musu ido a fakaice ta gani ko za su shirya ba tare da tsoma bakin manya ba tunda ta kula basa so a sani. Idan basu daidaita ba sai ta shiga tsakani kafin ƙaramar magana ta zama babba.

Hamdi ce ƙarshen fitowa daga ɗakin bayan Amma da Taj. Salwa ta kasa ɓoye baƙinciki da kishinta a fili. Wata irin zabura ma tayi daga zaune. Numfashinta ya nemi yankewa. A zatonta turaren jiya sake janyo ɓaraka zai yi tsakaninsu. Me Hamdi take a gidan?

Wata zuciyar ta kwaɓeta da sauri. Ko dai har an sami matsalar? Maybe shi ne aka turo su gida sulhu. Munafukar dariya tayi a zuci. Ta miƙe tsaye domin ta nunawa kowa matsayinta a wajen Taj. Kashe murya tayi tana kwarkwasa.

"Ya Taj"

Ai fa ta zo gidan yawa. Idanu sun fi goma a kanta. Hamdi wani malolon abu taji ya mata karan tsaye a wuya. FaÉ—i take tana nanatawa In sha Allahu ba za ta sake kiransa da Ya Taj ba. Sunan ko daÉ—i babu ashe, bata sani ba sai yau.

Taj kuwa Hamdi kawai ya kalla tayi kamar bata jinsu. Murmushi ma take yi abinta da ƴan uwansa suke ta nuna mamakinsu akan kwanan da tayi basu sani ba. Aka dinga yiwa ƴan kwanan ɗakin Inna surutu. Su ka ce ita ta sanya su yin shiru saboda kada su tashi Hamdin da hayaniyarsu. Shi da ya san akan tsini yake ba zai yi kuskuren sake ɓata mata rai ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ji ba. Yana gudun me zai faru idan ya amsa. Ta sake shaƙa har wuya. Abinci ƴan uwansa su ka kawo wa Hamsi shi ne ya samu ya fita wajen Kamal.
Chapter 80 · 0% Book details