Sashe 34
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan Alhaji ya amince za ka yarda a É—aura goben?" Taj ya tambaye shi kafin su fita. Shi ko a fuska bai nuna damuwa ba da Abba yake ta maganar su daina zancen.
Shi dai Abba ya gama gajiya da zancen. Sannan ya matsu su tafi saboda so yake ya fice ya koma gida su shawarta da Yaya.
"Me zai hana? Waye zai ƙi jinin Yaya Hayatu ko ma in ce zuri'ar Alh. Sule?"
Jin wannan ya kwantarwa Taj hankali. Ya san Alhaji ba shi kaÉ—ai bane shamakinsa. Shi kan shi Abba za a sha fama da shi.
***
Salati Yaya ta fara yi kafin ta fashe da kuka. Zaune su ke a cikin wani ɗan falo ƙarami na ɗakin Abba. Ita da shi da kuma Baba Maje, Inna Luba mahaifiyarta da kuma ƙaninsa Abdulƙadir.
FaÉ—an kukan Inna Luba ta fara yi mata kafin ta koma tausarta.
"Indai ku ka nunawa yarinyar nan cewa kun karaya na tabbata ciwon da za ta ji sai yafi na fasa auren."
"Yaron nan ya cuce mu" cewar Abdulƙadir.
"Na dai cuce mu. Rayuwar da na zaɓa ce ta zo tana bibiyar ƴaƴana" Abba ya faɗi da raunin murya.
"In ka amince kuma kana jin Sajida ba za ta ƙi ba, yanzu zan kira Baballe ya zo gidan nan a rufe magana. Gobe ya auri ƙanwarsa bakin kowa alekum. Ko kuwa?"
Abba ya nuna farincikinsa da godiya.
"Zan so haka. Amma Maje ka tuna lallai akwai haƙƙi tsakaninmu da yaran nan. Aure ba a son yi masa shigar sauri. Yanzun nan sai ya jagwalgwala abin da ake son gyarawa."
Baba Maje ya dage harda cewa "indai ba kuma rowar Æ´ar za ka yi min ba ka amince kawai. Ba don ni na haife shi ba amma Allah yaro ne mai biyayya. Ina sa rai in Allah Ya so ba zai bamu kunya ba."
Yadda ya matsa É—innan sai Inna Luba ta ce a kira yaron. Ba a mayarda hannun kyauta. Kuma Allah kaÉ—ai Ya san dalilin faruwar wannan al'amari.
Cikin farinciki Baba Maje ya kira Baballe a gabansu. Allah Yasa baya nesa sosai ya ce gashi nan zuwa. Ita Iyaa da Siyama suna can wajen biki. Uwar baƙin hali kuma an tafi bikin ƙawa kamar yadda ta shirgawa Iyaa ƙarya.
Kowa ya yi zugum ana jiran isowar Baballe. Baba Maje ya takura masa da waya saboda basa son Æ´an biki su fara dawowa. An gargaÉ—e su lallai kada su wuce takwas a waje har amaryar.
Baballe ya iso hankalinsa duk ya tashi. Irin wannan kira da wayar bai saba dasu daga mahaifinsa ba. Shi yasa ya dinga tunanin ko wani abu ne ya faru. Kafin ya iso sai da ya kira Iyaa yaji lafiyarta da ta Siyama. Ummi kuwa bata É—auki wayar ba don kada a ce ta dawo gida. Sam ba ya raga mata akan halayen da ta tsiro musu da su a gidan.
Tiryan tiryan haka Baba Maje ya labarta masa halin da ake ciki a gaban kowa. Wanda shi Abba ya so su keɓe. Don idan Baballe zai ƙi, ba zai ji nauyin idanuwansu ba.
"Baba don Allah ko za mu koma soro mu yi magana" abin da ya ce kenan da Baban nasa ya matsa masa akan ya bada amsa.
Gabansa sai da ya ɗan faɗi. Yaran yanzu ba a ci musu laya. Ya gama yabonsa shi ne yake son watsa masa ƙasa a ido.
"Nan dukansu amsar da ka bani dole zan dawo musu da ita. Saboda haka gara ma kawai ka faÉ—a a gabansu."
"Baba don Allah" ya faɗi yana cije leɓensa na ƙasa. Shiru ba zai amfane shi ba a wannan lokacin. Shi yasa yake son faɗa masa dalilin da ya sa ba zai iya auren Sajida ba.
"Ka je ka saurare shi don Allah. Share ire iren waɗannan abubuwan fa don mun isa su ne su ke zama dalilan yaji ko mutuwar aure. Allah Ya kiyaye." Inna Luba ta faɗi tana nuna musu ƙofa.
Ba don ya so ba ya tashi su ka fita. Ransa duk ya ɓaci don Baballe bai saba yi masa haka ba. Yaro ne shiru shiru mai sauƙin kai. Tsayinsu kusan ɗaya don ma shi shekaru sun ɗan durƙusar da shi. Fuskar Iyaa ma'abociyar fara'a ya ɗauko. Ga shi kyakkyawan matashi mai zuciyar nema. Banda aikin da ya samu ƴan watannin baya akwai shi da buga bugar neman halak. Bai san zama ko kaɗan.
"Ina jin ka. Kada ka ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa min ƙasa a ido ba." Baba Maje ya ce a kausashe.
"Ba haka bane Baba" Baballe ya ce a ladabce "ƴar uwarta nake so. Na ɗan jinkirta faɗa mata ne saboda wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ƙanwarta so na aure." Ya ƙarashe kai a ƙasa.
Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ƙofar cikin gidan.
"Danƙari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faɗa mata ba ai ba zan yi wannan karambanin ba."
"Idan zai bani ƙanwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta komai tunda ban shirya ba." Baballe ya furta da hope ɗin baban zai amince.
"Dama ko wace ai zan faÉ—a musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su ka yi da Ummi a makaranta?"
Da sauri Baballe ya ce "Zeenatu ce ba Hamdi ba."
"Wace Zeenatu kuma?" Baba Maje ya ce don kansa ya ƙulle.
Baballe ya yi murmushi "Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ƙarshen shekara idan ta gama na san lokacin na ɗan yi tari. Sai na gabatar da kaina."
Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce "banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai kaji ana batun an kawo kuÉ—i."
Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba musu ido. Baba Maje ya É—an rissina kai na jin kunyarsu ya faÉ—a musu yadda su ka yi da É—ansa.
"Alhandulillahi ai duk gida ne." Cewar Abdulƙadir.
"In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a ɗaura nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ƙare karatunta."
"Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faÉ—a musu."
In ji Inna Luba.
*
Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba ta kira su har Halifa É—akin Abba ta faÉ—a musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma É—akinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana.
"Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta."
"Ita kaÉ—ai?" Ta share nata hawayen.
"Wata damuwar tana buƙatar kaɗaicewa kafin zuciya ta karɓe ta. Idan tana buƙatarmu da kanta za ta neme mu."
Zee ya kalla da ta faÉ—a kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai.
"Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?"
Inna Luba tana shafa mata baya ta ce "Ja'ira. Ashe kukan ba na ƙin mijin bane. To ai da sauƙi. Yayyenki kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake."
"Mijin ma bana so Inna." Ta ce tana ƙara sautin kukanta.
"Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi maƙota za ki tara mana ko me?" Yaya ta faɗi cikin fushi.
Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da take yi, bata so a wulaƙanta su.
Hamdi ce ta riƙe Zee su ka koma ɗaki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma'anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai goshinta ƙasa wurin Allah.
Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiɗa abin sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun ɗazu. Don lokacin shaɗaya ma ta kusa. Alƙur'ani kowacce ta ɗauka ta buɗe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha'awa. Yayinda ta ƴan uwan biyu ke nemawa kawunansu zaɓin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu'ar zaɓin alkhairi. Tana fata kowacce ta sami aminci a ƙaddarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka.
Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi alƙawarin sake haɗuwarsu ko jin muryar juna sai in sun haɗu bisa kuskure. Ba za ta ɗauka ba balle ace ta kasa haƙuri da wanda babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban.
***
A ɓangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu'a kawai. Roƙon Kamal ya yi akan ya kai shi gidan Yaya Babba ya ce babu ruwansa.
"Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi maka bata shige ka ba."
"Don Allah Abba bai baka tausayi ba?"
"Ya bani, amma addua ce kaɗai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka haƙura da auren Hamdi ni kuma nayi maka alƙawarin auren Sajida."
Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na haƙura da ita ba. Wannan tsiwar yake son ƙurewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faɗo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ƙafar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat ɗaya ba.