← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 96

Sashe 21

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Salwa kin fini sanin rigimar Mama tunda a gabanta ki ka tashi. Ke shaida ce irin yadda ta fitini Abbanku. Abubuwan da take yi bana jin akwai wanda Alhaji bai sani ba. Tun da in naso zuwa wajenta hutu baya son bari saboda yana gudun kada na koyo abin da zai haÉ—a rigima a gidanmu."

Hawaye ta goge da mayafinta. Da muryar da kuka ya gama dusashewa ta ce "To ni yaya zan yi? Ba ni na É—orawa kaina ba"

"Kada ki yi komai sama da neman zaɓin Allah. Sai kuma tsare mutumci da darajarki ta mace. Ke kin sani da ina nan ko ɗakinsa ba za ki shiga ba. Ba kuma don ban yarda dashi ba. Amma wankin underwear...haba Salwa? It was totally wrong."

Daga ƙarshe rarrashinta ya yi da jaddada mata lallai kada ta ƙwallafa rai akan Taj domin indai Alhaji bai amince ba da wuya ya aureta.

***

Hutu yana ta daɗi. Hamdi ta zaga gari sosai da Anti Labiba da yaranta. Basu da ƴan uwa sosai a garin sai abokan arziƙi. Shi yasa yawon nasu yafi ƙarfi a wuraren shaƙatawa da ciye ciye.

Wata rana sun dawo da yamma liƙis Anti Labiba ta ce da Hamdi ta ɗora abinci. Tayi tuƙi ta gaji ga bebinta na ta tsala ihu. Ɗaki ta shiga domin yiwa yarinyar tsarki amma har ta fito Hamdi bata ɗora komai ba. Gyaran kitchen ɗin take yi saboda ana gama cin abincin rana su ka fita.

"Hamdi baki ji na ce ki É—ora jallof É—in macaroni ba?"

Murmushin ysƙe tayi "Anti Labiba don Allah ki ɗora. Duk wani yanke yanke zan miki."

Ƙanƙance ido Anti Labiba tayi. Sai kuma ta tuna wata hirarsu da Sajida lokacin da ta zo mata zaman biƙi. Tabbas ta faɗa mata a duniya babu abin da Hamdi taƙi jini bayan namijin da ya iya girki kamar girkin kanshi. Ita duk abin da za ta ɗora akan wuta mai suna abinci zuciyarta bata son yi. Ba kuma komai ya janyo ba illa tsohuwar ƙiyayyar da take yiwa sana'ar Abbansu. Kuma fa da yake a wurinsa ta koya da wuya ka ci abincinta baka yi santi ba.

"Baki iya girkin bane ko me?"

"Idan na dafa ba lallai na iya ci. Don Allah ki É—ora kinji Anti..."

Sosai abin ya bawa Anti Labiba mamaki. Hamdi bata taɓa yi mata ƙiwar aiki ba. Ga iya sammako ta gyara gida tun zuwanta. Amma fa duk cikin aikin nata bata taɓa yin girki. Ita kuma Anti Labiba bata damu ba saboda mijinta baya son cin girkin mutane musamman a gida.

Abincinta tayi ta gama. Hamdi sai taji babu daɗi don sai da aka matsa mata taci abincin. Bayan sun gama ta bita ɗaki ta bata haƙuri.

"Ni ban yi fushi ba. Kawai ina mamakin yadda aka yi ki ka zafafa akan harkar girkin nan."

"Idan ina yi sai Abba ya dinga faɗo min a rai. Wallahi Anti Labiba bana son ganin shi a kitchen kwata-kwata. Yanzu ma ina ta fatan Allah Yasa ya sami wata sana'ar tunda an karɓe gidan abincin." Magana take yi muryarta tana rawa.

Anti Labiba ta saƙala hannunta a kafaɗarta.
"Nayi zaton kin daina abubuwan da ki ke yi da naga yanzu kullum sai kun yi waya dashi."

"Ni me nake yi?" Ta tambaya da zumɓura bakin.

"Babu komai." Ta shashantar da zancen "snacks da pastries fa? Su ma kamar girki ki ka É—auke su?"

"Don ban iya bane amma ina so."

"Saboda basa cikin girkin da Abba ya koya mu ku ko?"

Sunkuyar da kai Hamdi tayi a kunyace. Ita kuwa Anti Labiba sai wani tunani ya ɗarsu a zuciyarta. Ba dai za ta ce komai ba sai ta tuntuɓi ƙawarta Hauwa gobe. Idan Hamdi tayi sa'a za ta koyi small chops da youghurt from one of the best a garin Abuja.

***

Kwana biyu Taj ya yi baya zuwa site ɗin aiki. Idan Kamal ya zo sai ya ce kansa na ciwo. Abu ya taru ya dami Kamal sosai. Lokacin tafiyar Taj na gabatowa amma ya sanyawa ransa wani abu daban. Shi kuma yafi son ko zai tafi ya zamana aikin da ya rage ba mai yawa ba. Gara aci ƙarfin komai a gaban mai wurin.

Yau da ya bar gidan Ahmad wucewa ya yi gidan Abba Habibu. Bai wahala wurin gane gidan ba. ShaÉ—aya na safe ta É—an wuce. Ya tura wani yaro ayi masa sallama da shi. Wata budurwa ba wadda ya gani a zuwansu na farko ba ce ta fito ta gaishe shi.

"Abba ya fita amma yanzun nan zai dawo. Ba nisa ya yi ba."

"Ke ma ƴarsa ce?" Kamal ya kasa daurewa sai da ya tambaya. Ita da ta rannan da ya riƙe Zee aka kirata su na kama sosai. Kyawawan ƴan mata ne masu nutsuwa.

"Eh."

"Yaya sunanki?"

"Sajida." Ta amsa masa.

Kujerar roba ta kawo ta ajiye masa a soron ta koma ciki. Kimanin minti goma a tsakani sai ga Abba ya dawo.

Mamakin ganin Kamal ya yi sosai. Su ka gaisa sannan Kamal ya É—an rissina kai.

"Na san za ka yi mamakin dawowata bayan yadda nayi a wancan zuwan namu."

"Babu komai. Allah dai Yasa lafiya."

"Alhamdulillah"

Shiru ya kuma biyo baya har sai da Abba ya sake tambayarsa sannan ya yi magana. Da farko ya fara da bashi labarin burin Taj tun ƙuruciya da duk wani abu da ya biyo baya.

"Wallahi ban hana shi don ƙyama a gareka ba. Amma indai Alhaji ya sami labarin kuna tare bana jin zai zai yafewa Taj."

Kallonsa Abba ya yi sosai yana jinjina kai "to amma a ina mahaifin naku ya sanni."

"Soron É—inki. Shi ma mutumin cikin gari ne."

A karo na uku Abba ya sake ƙurawa Kamal idanu na wasu ƴan daƙiƙu sannan ya yi murmushi.

"Yaya Hayatu ne mahaifinku?"

Da sauri Kamal ya kalle shi "ya akayi ka gane?"

"Da gaske ku ƴaƴansa ne?" Abba ya kuma tambaya yana miƙewa tsaye.

"Ƴaƴansa ne." Ya faɗi yana gyaɗa kai.

Jiki a matuƙar sanyaye Abba ya ce. "Ka faɗawa ɗan uwanka kada ya sake zuwa gidan nan. Kai ma ka tashi ka tafi."

Kamal bai jidaÉ—in yadda Abba ya koma ba. Da alama ba mutum bane mai son hayaniya. Amma jin waye mahaifinsu ya canja yanayinsa. Hannu ya sanya ys fiddo dubu É—arin da ya tanada tun a gida.

"Ga wannan ka ƙara jari don..."

"ÆŠauke kuÉ—inka yaro. Bana so ko da wasa Yaya Hayatu ya yi tunanin da gangan na kusanci rayuwarku."

Ciki ya shige ya bar Kamal riƙe da kuɗin yana fargabar yadda za su kwashe da Taj idan ya sami labarin zuwan nan nasa.
RAYUWA DA GIƁI 12

Batul Mamman 💖

Wannan shafin yana ɗauke da tallan _LUCIOUSBITES_ gidan kashe ƙwalama. Mazauna garin Abuja ga taku ta fito da kanta ba saƙo.

Taron biki, suna, conference, seminar ko reunion ne? Ko kuwa sha'awar kashe kwaÉ—ayi ce ta tashi? To ku sha kuruminku. Hauwa aka luciousbites.ng ta fito domin fitar daku kunya a ko ina.
Domin ƙarin bayani kuna iya tuntuɓarta a kan wannan layi 08174821831.

***

Da gaske ciwon kai ke damun Taj saboda bai iya sanya abu a rai ba. Ya so ƙwarai ya ja Abban Hamdi a jiki. Ba don neman soyayyarta ba, wannan da kansa zai yi ba ya buƙatar taimakon kowa sai Allah. Mahaifinsa yake son nunawa a rayuwa kowa da ƙaddararsa. Kuma a kowacce sana'a indai ba addini ne ya haramta ta ba, akwai mutumin banza da nagari. Don al'ada ta ƙyamaci wani abu ba shi yake nufin yinsa laifi bane. Sannan uwa uba akwai uzuri ga ƴan Adam domin ba kowa ke dawwama cikin saɓo ba.

A ganinsa rashin aikin Abban Hamdi wata hanya ce ya samu da zai iya sako shi cikin tasa sana'ar. Idan Allah Ya sanya musu albarka kasuwa ta buɗe Alhaji zai iya fahimtar kowanne bawa akwai hanyar arziƙinsa. Sannan ko iyaye ba sa so indai Allah bai haramta ba sannan ɗan bai kasance mai saɓawa kowa ba, albarka za ta iya binsa duk inda yake.

Ƙarar wayarsa ce ta tashe shi daga kwanciyar da ya jima yana yi. Sunan Salwa da ya gani ya sanya shi yin tsaki. Ita bata san gudunta yake yi ba? Har yau yana mamaki da bata yi tunanin kamar yadda mata ke killace kayansu na ciki haka kowanne namiji da ya san mutumcin kansa yake yiwa nasa ba. A iya saninsa ƙiwa da rashin son aikin namiji ba zai sa ya bawa ƙanwarsa shaƙiƙiya wankin ƙananan kaya ba. Ballantana kuma wadda babu wani abu da ya haɗasu.

Bari ya yi kiran ya katse sannan ya kirata.

"Don Allah ka buɗe min ƙofa na manta muƙullina a ciki."

Falo ya fito sanye da dogon wando na sanyi ruwan toka da farar shirt. Ya buÉ—e mata jamlock É—in ya juya zai koma É—aki sai ta kira sunansa.

Tun ranar da ta gyara masa ɗaki da faɗan da Ahmad ya yi mata ta rage kuzari da karsashi a komai. Fargabarta ita ce ɓacin ran da ta gani tare da Taj da kuma shawarar da Ahmad ɗin ya bata akan ta cire shi daga ranta. Da za ta iya da tun kafin ta zubar da ajinta ta cire shi ta ƙarfin tsiya tunda ta fahimci bata gabansa ta fuskar da take so.

Sake kiransa tayi da bai juyo sosai ba.

"Ya Taj don Allah ka yi haƙuri akan abin da ya faru rannan. Na fahimci kuskurena."

"Ya wuce, kada ki damu."

Fasa tafiya ya yi da ya tuna ƙanwar Ahmad ai ƙanwarsa ce shi ma. A matsayi guda duk su biyun su ke zaune a gidan. Shi yasa yaga dacewar ya bata shawara.

"Ko don gaba ki kiyaye irin wannan. Ba ni ba, ko Yaya ki ka wankewa undies bana jin za ki burge shi." Kai ta sunkuyar sai ya yi murmushi "ku mata ba kwa son a taɓa koda jakarku. So just imagine ace ni nayi miki wannan karambanin. Will you realy be happy that I helped?"
Chapter 21 · 0% Book details