← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 96

Sashe 48

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsar Hamdi ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba. Kai tsaye ta faɗa mata magana ta rama wadda tayi mata. Tana so ta ce mata ita da kanta za ta auri Taj amma gani take faɗin hakan zubar da aji ne sai ta gimtse fuska cike da takaici.

"Ni ba Æ´ar gidansu bace."

"Ikon Allah. Kuma naga ya yi saving sunanki da Sister Salwa? Cousin É—insa ce ke kenan?"

"Sister Salwa???" Baƙinciki ya mamaye zuciyar Salwa a lokacin da take nanata kalmar "haka ya rubuta?"

"Uhm, da capital letters."

Tsanar Hamdi ta sake ruruwa a zuciyarta yayinda ta bata amsa.

"To ko ma dai mene ne kada ki saki jiki don ba zan zauna da kishiya ba."

"Lahhhhhhh, ko ke ce wadda ta suma ranar aurenmu?"

Salwa ta haɗiyi yawu da ƙyar saboda jin da alama suna da yawa masoyan nasa "suma kuma? Shi ya ce miki akwai wadda ta suma a kansa?"

"Ba ke bace kenan." Hamdi ta faɗi da rashin damuwa "Allah Sarki. Kada ki damu fa. Ni bani da matsala ko ya ce zai ƙara aure don na san a danginku dole a bashi wata. Tunda na samu na shiga sai dai in ce Allah Ya bawa mai rabo sa'a. Mu kwana lafiya."

Katse kiran tayi ta ajiye wayar a kusa da tata tana murmushi. Za ta so ganin idanun Salwan nan. Irin yadda taji tana sauke numfashi da tana bata amsa ya kusa sanya ta dariya. Ta riga ta san mahaifinsa baya sonta. Abba kuma ya faɗa mata mahaifiyarsa tana maraba shi yasa ma ta nemi ganinta. Duk da haka ba sakin jiki zata yi ba. Dole dama ta sa rai da ganin wulaƙanci kala kala kafin ta bar musu danginsu. Ko banza dai bata bari an ƙuntata mata ba ta ce a ranta tana faɗaɗa murmushinta. Zee ta kalla tana ta sharar bacci. Ina ma idonta biyu. Yau da sun mannawa wannan cousin ɗin hauka. Don Zee dake sakandire ma ta fita sanin irin waɗannan abubuwan. Zamani na turawa, na baya suna zuwa da wayo da dabarun da waɗanda su ka gabacesu basu taɓa sani ba. Bata san lokacin da tayi bacci ba saboda yadda abin duniya ya dameta daga baya. Shin ƴan mata gare shi ko kuwa a dangi ake son aura masa daidai da shi? Zuwa gidansu jibin nan kuwa shawara me kyau ce?

Da kuka Salwa ta kwana. Ba kuma na auren Taj ba wannan karon. Yadda yarinyar da ta raina ta ɓata mata rai ba tare da ta rama ba ne yake damunta. Wai bata da matsala ko zai sake aure. Kenan ma alfarma za ta yi mata ta bari a aurota.

Ƙwafa tayi "sai zaman gidan Taj ya gagareki indai ni ce."

***

Da Abba zai fita kamar yadda ta faÉ—awa Taj ta bashi wayar. Ya dubeta da kyau ganin fuskarta shar babu damuwa a tare ds ita.

"Hamdi kada ki manta da maganarmu. Bana son abu ya yi nisa Alhaji yasa a ɗora miki zawarci mai ciwo. Gara ma ace ba kya son shi zai fi miki sauƙi."

"In sha Allahu Abba" ta faɗi tana mai sunkuyar da kai don ta san jiya dai bata wani taɓuka abin kirki ba.

"Garin yaya ya manta wayar?"

"Ina jin daga aljihunsa ta fito. Sai bayan tafiyarsa na gani."

"To shike nan. Ki kula dai. Sai na dawo." Tsayar da ita ya yi kafin ta koma ciki "wannan hijabin Hamdi gaskiya ko dai ki haƙura dashi ko kuma kada ki yarda wani baƙo ya ganki da shi."

Da sauri ta kalli jikinta "Abba wani abin ya yi?"

"Ki duba madubi."

A dawo lafiya tayi masa a soron da su ke tsaye su biyu sannan ta koma ciki. Hannu ta ɗora a ka da ta ƙarewa kanta kallo. A haka fa ta fita wurin Taj jiya. Da ta tuna an ɗauke wuta ne ma ta sami nutsuwar kama aikinta na yau. Zee ce da girki idan ta dawo daga makaranta. Ita kuma wanke wanke da shara. Halifa kuma kullum shi ne da wankin banɗakuna da sharar tsakar gida zuwa soro da harabar gidan. Duk wanda ya san gidan Abba ya shaide su da tsafta. A kansu Anti Labiba ta ƙara gane cewa babu wata ƙwaƙƙwarar alaƙa tsakanin talauci da ƙazanta. Kowanne zaman kansa yake yi.

*

Yana cire lock É—in wayar abin da ys fara gani shi ne (save - discard) na recording call. Ya san da wuya Hamdi ta iya yin kira da wayarsa tunda yatsansa ne mabuÉ—in wayar. Amma wa ya kira shi ta É—auka har su ka kwashi waÉ—annan mintuna suna magana? Saving ya yi sannan ya shiga call log. Nan ya tarar da missed calls É—in Salwa kafin wanda aka É—auka.

Da saurinsa ya nemo recording ɗin ya shige office ɗinsa ya kunna. Shi kaɗai ya dinga dariya. Hamdi bata da dama. Ta kuma burge shi. Bata cikin irin ƴan matan nan da su ke zama a taka su son rai su shiga ɗaki su yi kuka. Nishaɗi fal zuciyarsa. Salwa ce ma yaga dacewar ya taka mata burki kafin ta kai su ga ɓacin ran da wani zai ji su. Kiranta ya yi kamar tana jira ta ɗauka. Ƙin magana tayi gudun maimaicin abin da ya faru jiya. Sai da ya yi sallama ta saki rai ta amsa ta gaishe shi.

"Kin kirani jiya ashe. Hope ba matsala bace?"

"Eh wallahi." Ta gyara zama tana murmushi "babu wata matsala. Kira nayi kawai mu gaisa. Faɗa maka tayi na kira?" Ta ƙarashe maganar a hankali.

"No, missed calls É—inki na gani. Sai kuma naga alamun kun yi magana da Babe É—ina har na kusan five minutes. Lafiya dai ko?"

Wai Babe? Siririn tsaki tayi kuma yaji. Ba don yana son a yau ya daƙile komai nata ba da ya ajiye wayar.

"Na ce lafiya ko?"

"Naga kwana biyu baka nema na ne."

"In ce miki me Salwa? Muna gida É—aya nayi aure ki kasa yi min fatan alkhairi."

Tsayar da zuciyarta tayi wurin daina kwana-kwana a kansa.
"Ohhh, wai har kana saka wannan a jerin aure Ya Taj? Ba ance babanta É—an ..."

"Yes, É—an daudu ne a da. And one of the most wonderful people alive today. Mamanta kuma is physically challeged. Polio ya yi affecting posture É—inta sosai."

"Ta faɗa min jiya" ta ce don bata ga amfanin maimaitawar ba. Mutane irin waɗannan mene ne abin tinƙaho dasu? Idan iyayenta ne za ta yi bakin ƙoƙarinta wurin guje musu don ma kada ace ta san su.

"Ina sake faÉ—a miki duk da na fahimci kin sani ne don ki gane cewa duka waÉ—annan abubuwan da wasu ke gudu ni su ne su ka sa Hamdi ta zama the most special girl alive. I love her Salwa. Bana kuma son duk wani makusancina ya dinga ganin kamar wannan abu ya isa dalilin da zai rageta a matsayin mace. She is everything I want."

"Kirana kayi ka ci min mutumci saboda ina son ka? To my face ka ke faÉ—a min kana son wata?" Salwa tayi magana da rawar murya.

"To your ears dai. Amma in kina so zan maimaita miki in mun haÉ—u. Ba ke kaÉ—ai ba kuma, duk family É—in Maitakalmi, babu wanda zan ragawa akan mutumcin matata."

Iya wuya ran Salwa ya gama ɓaci. Za ta iya rantsuwa basu taɓa wata doguwar hira da Taj a waya ba idan ta kira shi kamar wannan. Saboda ƴar gwal ta kai masa gulmar wayarsu ta jiya.

"Abin da Yaya Ahmad ya ce Alhaji da bakinsa ya gaya masa wata uku ya bawa babanta ya kashe auren don ka koma gida. Na san akan mace ba za ka zaɓi dawwama a haka ba" Ta faɗi kai tsaye don da alama kukan ba zai kaita ko ina ba "Ya Taj zamu yi aure kuma za ka bani haƙuri akan wulaƙanta soyayyata."

Ita ta fara kashe wayar ta barshi da wani irin sanyin jiki. Bai taɓa zaton yayan nasu zai ɗauki sirrinsa ya faɗawa ƙanwarsa ba. Kowa matsayinsa daban. Maganar da ko Kamal bai samu ya faɗawa ba saboda rashin lafiyarsa. Su Innarsa da Amma da sisters ɗinsa duk basu sani ba. Shi ne zai sanar da Salwa? He felt disappointed and betrayed. Tun farko abin da ya yi ta gudu game da ita kenan. Tunda baya so dole yayan nasu ya sami ɓangare guda da zai fi tausayawa. Sai ya musgunawa ɗayan kuma? Duk da haka ya ƙudurce ajiye abin a ransa har ya gano yadda aka yi taji zancen.

Bayan sun kammala wani emergency order na taro an fitar da abincin ya tafi wurin Kamal. Mutumin da kullum idan ya shiga shagon nasa har mita yake masa na rashin hutu yau a zaune ya same shi yana gyangyaɗi. Ya kan ce masa mene ne amfanin ƴan zaman shagon dake nuna kaya da waɗanda ke wurin biyan kuɗi. Shi kaɗai ya yi nan, ya yi can. Sai gashi hayaniyar kwastomas bata hana shi baccin ba. Yana zuwa hannu ya kai ya taɓa wuyansa da goshi. Abin da ya farkar da Kamal ɗin da sauri don ji ya yi kamar an ɗora masa ƙanƙara. Tsigar jikinsa har tashi tayi ya buɗe ido a firgice.

"Happiness kaji jikinka kuwa? Tashi mu koma asibiti" Taj ya ce yana kai hannu gefe ya É—auko masa wayarsa.

Hamma Kamal É—in yayi "bacci ne fa. Bari na shige ciki na kwanta" ya nuna nasa office É—in.

"Kada ka raina min hankali mana. Bacci ne yake kawo zazzaɓi? Muje don Allah."

Wasa ya mayar da maganar ya ce "Sai dai in kai ka. Dama na faÉ—a maka yau É—anin motarka zanyi. A adaidaita sahu ma na taho saboda son banza."

"In ka bari mu ka je asibiti Allah zan yarda mu yi musanye. Saboda na san kai mayenta ne na saya."
Chapter 48 · 0% Book details