← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 96

Sashe 60

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wace magana kenan?" Tashi tayi daga wurin kitson ta koma É—aki.

"Auren Taj da Salwa. Alhaji ya ce baya son a wuce wata guda. Naga har an cinye sati."

Azkar É—in tunkarar shugaban da kake tsoron cutarwa daga gare shi Inna ta karanto wannan karon kafin tayi magana.

(Allahummak finihin bima shi'ta)

"Wane Taj ɗin wai? Nawa dai sati biyu kenan da aurensa. Bani kuma da labarin zai ƙara wani."

Mami tayi kwafa a hankali tana raya duk za su zo hannu ne. Da ta san haka za ta yi mata tun farko ma da ta karɓo laya.

"To ki tambayi maigidan naki. Sai mu yi magana daga nan."

Inna ce ta fara kashe wayar. Ta dinga karanto addu'o'i. Me yasa duk wata rigimar gidan akan Taj take kunno kai? Istigfari tayi da sauri sannan ta fita ta tafi ɓangaren Alhajin. Dama yana gida. Girkin Umma ne. Inna tayi sallama ta shiga falon bayan Umma ta amsa ta iske shi yana cin abinci.

"Alhaji me nake ji daga bakin tsohuwar matarka?"

Karo na biyu kenan da Inna tayi masa magana babu kyautata kafazi. Yana namiji sai da yaji wanibabu a ransa. Maganar Hajiya na neman tabbata da ta ce masa kada ya ƙure haƙurin Abu don mai haƙuri bai iya fushi ba.

"Wani abin ne ya faru?" Ya tambayeta kamar bai sani ba.

"Ka fini sani Alhaji. To amma ina so ka sani ka gama yi min hawan karkatacciyar kuka. Wannan juya min yaro da kake yi ya isa haka."

"Haba Inna. In ranki ya ɓaci kada ki bari hankalinki ya gushe mana. Da mijinki fa kike magana." Umma ta ankarar da ita don muryarta tashi take sosai.

"Me ya rage min? Yau ko agola ne Tajuddin ai iyakar abin da mijin uwa da baya sonsa zai yi masa kenan. Wai ni matar nan za ta kira ta ce ya maganar auren Taj da Salwa?"

"Me?" Umma ma ta É—aga murya ba tare da tunani ba.

"Ah to, kema kya faÉ—a. Wai da Alhaji su ka yi magana."

Ya fa manta da maganar nan. Duk a zatonsa idan Ahmad ya faÉ—a mata yadda su ka yi za taji haushi ta ce basa so. Daga ranar da su ka yi maganar ko tunawa bai sake yi ba saboda rashin mahimmancin zancen a wajensa.

Umma ta dube shi "Alhaji wai haka?"

"Eh. Mun yi magana da mijinta ya bawa Taj Salwa. SharaÉ—ina kenan idan ba zai saki Æ´ar gidan Habibu ba. In ba haka ba kuwa..."

"Kana son ya saketa kafin auren ya wuce wata uku ko? Ahmad, ɗan halak ya faɗa mana" Inna ta ƙarashe masa.

"Tunda kun sani sai ku sa ya zaɓi ɗaya. Na gama magana."

"Ahaf. Ai babban kuskurenka da ka bari aka yi auren nan Alhaji. Shi ne mai wuyar. Ko yanzu ba abin mamaki bane ace Hamdi tana da juna biyu."

Ba Alhaji da ya kusa ƙwarewa da ruwan da yake sha ba, Inna ma zaro idanu tayi.

"Kai Umma?"

"Auren yanzu da ake yiwa yara bayan duk sun ƙosa. Ko mu nan nawa ne ƴaƴanmu su ka haihu wata tara ko goma da aure? Indai an bada sadaki ai magana ta ƙare. Don ma ba lafiya gare shi ba."

"Ai kuwa sati mai zuwa za ta tare." Inna ta faÉ—i sannan ta dubi Alhaji "ka faÉ—awa tsohuwar matarka ta nemarwa Æ´arta miji tun wuri."

Inna na fita Alhaji ya tsare Umma da tambaya. Shi fa daina gane komai ya yi daga inda ta ce bashi da lafiya.

"Ciwo ne da Taj É—in?"

"Typhoid yake da maleriya. Satinsa guda ko aiki baya zuwa."

Ransa a ɓace ya ce "Kuma shi ne aka rasa wanda zai faɗa min?"

"Taj ne fa. Ka damu da ciwonsa ne dama?"

"Me kike nufi?"

"Wai abin da ido ya gani baki ke faÉ—a."

Ta jima da fita daga É—akin ta bar Alhaji da tunani. Me yasa sai akan Taj iyalinsa su ke yi masa irin wannan? Sai kuma maganar Salwa. Bai san har yanzu Mami bata da cikakken hankali ba. Ai da maimakon hannunka mai sanda sai ya fito musu a mutum kawai.

Yana wannan lissafin tuni Mami ta garzaya wajen toshe ɓarakar da take hangowa. Magana ta yiwa Alh. Mukhtar. Ya kuma aiwatar duk da baya so.

Alhaji sai waya kawai yaji. Ganin sunan mai kiran ya hanzarta É—auka domin ya kashe maganar Salwa. Sai dai kafin ya ce komai Alh. Mukhtar ya yi masa dabaibayi.

"Akwai wasu ƴan uwana mazauna Kano da muka yi magana mutum biyar. Ɗaya ma ƙanin mahaifina ne uwa ɗaya uba ɗaya."

"Wani abu ne ya same su?" Alhaji ya ƙosa yaji ƙarshen zancen ko ya sami damar yin nasa.

"Lafiya ƙalau. Dama don a sama muku sauƙi ba sai kun taho har nan ba. Shi Baffan namu na sanar dashi za ku zo neman aure da biyan sadaki. In kun saka rana sai ka sanar dani. Na tura musu lambarka ma dai."

Alh. Hayatu mai baki sai yaji yawun bakinsa ya ƙafe. Ta ina zai fara cewa ya fasa? Abin da kamar wuya. Girmansa zubewa zai yi. Idan matansa su ka san halin da yake ciki ya tabbata dariya za su yi masa.

"Idan na saka ranar zan sanar da kai."

"Yauwa to nagode." Ya đan numfasa "don Allah kada a ja lokacin. Nima na gama shiri."

"To"

Alhaji ya gyaɗa kai. Kuma har zuciyarsa sai yaji yana tausayin Alh. Mukhtar ɗin. Shi da zai iya dafa littafi mai tsarki ya yi rantsuwar matansa basa biye biyen tsibbu ashe a aljanna yake. Gudun faɗuwar girma ya janyo ya kasa kyautata musu akan abu guda da su ke buƙata daga gare shi.

*

Inna na dawowa daga ɓangarensa taci karo da wasu rantsattsun akwatuna manya manya guda huɗu a tsakiyar falo. Ƴan gidan an haɗu ana ta murnar yaushe gamo da Amma. Rabonta da shigowa gidan yayan nata an jima.

"Takwara oyoyo" Umma ta ce daga bayan Inna da ta kasa magana.

"Yauwa Takwara" Amma ta ce, ita da su Mama su ka bi Inna da kallo.

Murmushin dole tayi musu gami da yiwa Amma sannu da zuwa sai ta shige ɗaki. Ta manta da mai kitson sai da ta ganta zaune tana jiranta. Kuɗin kitson ta bata sannan ta ce ta tafi za ta nemeta daga baya. Matar bata matsa ba don ta lura Inna bata cikin nutsuwa. Uwar ɗaka ma ta shige ta rufo ƙofa. Wayarta ta ɗauka ta kira babban wanta. Tana jin muryarsa ta fashe da kuka.

"Me yake son ya mayar da rayuwar yaron nan? Shi ba fasiƙi ba, ba ɓarawo ko ɗan fashi ba. Amma ace duk wani abu dake nuni da ba a son mutum akansa yake ƙarewa?"

Rarrashinta ya yi sannan cikin kuka ta labarta masa abin da ya tunkaro su kuma.

"Ina jin lokaci ya yi da zan nunawa Hayatu bai fi ni zafin kai ba. Turo min lambar baban ita matar Taj É—in. Sati na sama in sha Allahu za ta tare. Idan ya kuma barazanar rabasu kuma ni da kaina zan É—auki mataki."

"Yaya ita kuma tsohuwar matar tasa fa?"

Dariya ya yi ta manyan dattijai "kinsan Allah, barazana ce kawai. Hayatu da wuya yake yar da abu ya waiwaye shi. Abin da ya raba shi da Habibu kenan tun farko. A yanzu kuwa ban hango zai taɓa yarda babar Ahmad ta zama surukarsa ba. Rabuwarsu ba ta daɗi bace."

Nutsuwa ta samu da wannan wayar. Ta fito falonta don zuwa wajen Amma ta gansu duka zaune. Umma ta faÉ—a musu abin da ya faru. Su ka haÉ—u suna bata baki. Tun bata son nuna ai É—an cikinta Alhaji yake yiwa haka har ya kai ta fito tana faÉ—a da bakinta.

Su ka haɗu da Amma su ka bata baki. Auren ƴar Mami kuma ko Taj ne ya kwaso da kansa ba za su yarda ba. Suna wannan tattaunawar Alhaji ya shigo ɓangaren nasu. Ganin babu kowa ya tambayi ina su ke. Aka ce su na ɗakin Inna. Juyawa ya yi bakinsa alekum ya fice, musamman da yaji cewa Amma ta zo. Sake hargitsasu za ta yi ta zuge su tas. Ƙarshenta in bai yi da gaske ba sai anyi sa'in'sa a gaban mutane idan ya ce zai nemasu yanzu.

***

Sai washegari Taj ya sami ƙwarin fita sosai. Jiya da su ka yi waya da Hamdi ya ce zai je Happy Taj ta ce ya bari ya ƙara hutawa.

"Kin isa matar Happy. Dama tunda Happiness ya yi tafiya na san ba wani daÉ—in wajen zan ji ba sosai. Da ni É—an gata ne dai sai ki zo ki tayani zama." Yayi maganar a hankali.

"Naƙi wayon. So ka ke Abba ya tsireni? Yana wajen sai na zo na wuce."

Marairaicewa ya yi "A misali da ba zai yi faÉ—a ba za ki zo? Uhmm? Allah naji jiki fa. Ga rama."

"Kullum fa ina kiranka."

"Kira daban, gani da ido daban. Kin san fa babu jinya mai daÉ—i kamar kayi a gaban matarka."

Hamdi tayi dariya. Da alama Taj kallon yarinya yake yi mata. Shi ne zai yi mata wayo.

"Allah ko? Saboda me?"

"Ana yi ana petting É—in mutum. Ga pecks here and there. Sai ka manta ma da ciwon." Ya bata amsa yana jin dama so samu ne.

Baƙuwar kalmar da taji ta tambaye shi.
"Meye kuma pecks?"

Taj na jin haka ya tashi zaune yana Æ´ar dariya. Ashe ma wayon da take ta zillewa zai yiwu.

"Peck É—in ne baki sani ba? Ko dai kin faÉ—a ne?"

"Allah ban san shi ba. Pecks naji ka ce."

Da fatan kada ta É—ago shi ya ce "Da yawa ne pecks. Gashi akwai nauyi da na É—auko miki."

"Idan da rabo sai na gani watarana."

Duk a zatonta wani abu ne da ido zai iya gani kuma hannu zai É—auka.

Dama ce ta zo wa Taj bayan sun gama wayar da yamma. Mama ta kira Yaya ta sanar da ita za su zo washegari ita da su Amma. Wasu daliliai sun janyo suna son ayi biki sati mai zuwa. To dama su ma suna ta É—an shirinsu don ba a zauna haka ba.

Yaya sai ta kira Hamdi ta ce ta tambayi Taj ko gidan Sajida ne gobe ta tafi.
Chapter 60 · 0% Book details