← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 96

Sashe 56

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hamdi bata san yazo ba. Wata shirt mai gajeren hannu ta saka da zani ta fito ko ɗankwali babu. Fuskarta fayau sai idanu a kumbure saboda kukan da tayi. Babu abin da ke tashi a jikinta sai wani irin ni'imtaccen ƙamshin body oils ɗin Scentmania. Gwaji kawai tayi tunda dama tun kafin fitarsu ta so sakawa amma sanin rashin dacewar haka a addinance yasa ta fasa. Wurin ƙarfe goma na safe taga saƙon Yaya Kubra ta whatsapp. Ashe tun jiya ma ta turo. Bata yi mamakin ganin sunan ba saboda Firdaus ce ta zauna tayi ta kiranta da lambobin ƴan gidan tana mata saving.

Bayanin sirrin dake tattare da ƙamshi ga matar aure ta turo mata wanda ainihin mai turarukan Scentmania ta tura mata. A ciki ta gane ƙamshi ba ƙaramin tasiri gare shi ba idan ana amfani dashi ta hanyar da ya dace. Musamman idan mace tayi katarin sani da sayen body oils ɗin da ita dai Hamdi bata taɓa jin ƙamshi irin nasu ba. Har shawara take bayarwa cewa yana da kyau mace ta samu wani ƙamshi da za ta yawaita amfani dashi wanda miji zai ganeta dashi. To ko makamancinsa yaji a waje ita zai fara tunawa ya sami nutsuwa. Gashi wai har classes tana yi. Sannan packages ɗin ba dai arha ba. Dole ma ta faɗawa su Sajida idan ta huce daga fushin yau. Don tana ta hango su ana can ana raha banda ita. (07065525409 - Scentmania by Sana)

A ƙofar falon ta tsaya don kads Yaya tayi mata magana akan idonta.

"Yaya me za a dafa na dare?" Tayi magana muryar nan na nuni da har yanzu ranta ba a sake yake ba.

Daga ciki Yaya ta amsa mata.
"Abincin daren za ki ɗora tun yanzu? Ƙarfe biyu ma bata yi ba."

"Gara na gama tun yanzu."

"Ai fa yau tunda na hanaki fita sai abin da hali ya yi. To shigo ki gaishe da mijinki da jiki. Baya jindaÉ—i."

Labule ta ɗaga tana cewa "waya ku ka yi?" Sai ta ganshi a zaune ya jinginar da kansa a jikin kujera. Ciwon kan ke neman dawowa harda zazzaɓi. Da baya ta fara tafiya za ta koma.

"Ina kuma za ki? Fita zan yi gidan Gwaggo Dela in duba ta."

Ta gaban Hamdi ta zo ta wuce abinta. Tana fita tsakar gida ta ja kunnen Halifa akan kada ya shiga falo sai Taj ya tafi. Dariyar shaƙiyanci kawai ya yi. Tana jiyo shi ta ce

"Ɗan banza." A ranta kuwa gani take in ba wajen matarsa ba yanzu ina zai je in bashi da lafiya. Uwa ce dai tafi cancanta yaje ya narke mata da shagwaɓa da rakin maza. To kuma babu dama.

Sai da Yaya ta fita daga gidan sannan Hamdi ta yarda ta ƙara kallon Taj. Yana daga zaunen ya nuna mata kusa dashi da hannu amma bai yi magana ba. Ta juya ta kalli bayanta sai ta girgiza kai.

"Please. Bani da lafiya fa." Taj ya faÉ—i yana lumshe idanu.

Shahada tayi kawai ta biye masa duk da kafin yazo da ta gama fushin rashin amsa wayarta da ya yi. A hankali ta isa bakin kujerar amma taƙi zama. Ya miƙa hannu ya janyota gefensa.

"Bani da ƙarfin ɗaukanki saboda wani irin weakness da nake ji. Da tun daga bakin ƙofar zan taroki."

Rumgumota yayi a gefensa. Ƙamshin jikinta mai sanyi ya buge shi. Bai san lokacin da ya sanya fuskarsa a tsakanin wuyanta ba. Ta fara noƙewa taga kamar ma angiza shi take sai ta haƙura.

"You smell..." ya kai hancinsa bayan kunnenta ya ja numfashi ya sauke a hankali "relaxing and sweet."

ÆŠumin da taji a fuskarsa dake bin wuyanta yasa ta daina mutsu-mutsu har ta tabbatar ba normal É—umin jikin mutum bane.

"Zazzaɓi kake yi haka?" Ta faɗi tana janye jikinta don su fuskanci juna.

"Uhmm." Ya amsa da rashin kuzari "harda kaina."

Juyawa tayi ta taɓa goshinsa. Ya ɗora hannunsa akan nata. Cike da kasala ya ce,

"Ba don bana jindaÉ—i ba da na nuna miki yadda shigar nan taki tayi min kyau."

Hannunsa dake tracing ƙaramin hannun rigarta ta riƙe tana mamakin yadda yake tunanin wani abu daban da zazzaɓin jikinsa. Sake janyota yayi ya mayar da kansa kafaɗarta yana ƙara rungumeta.

"Ina zuwa."

Fita tayi ta barshi. Ya runtse ido don kan nasa ba da wasa yake ciwo ba. Duk yadda aka yi zirga zirga da rashin hutun kwanakin nan ke tambayarsa.

Abinci tayi niyyar kawo masa sai tayi tunanin babu lallai ya iya ci. Ta É—auko gasara ta dama masa kunu da tsamiya kaÉ—an saboda yaji daÉ—in bakin. Da ta koma falon idonsa a rufe ta same shi. Ta zuba kunun a kofi ta zauna a gefensa.

"Ya Taj?"

A hankali ya buÉ—e idonsa. Ta nuna masa kofin. Ya buÉ—e bakinsa.

Ƙofa ta kalla "Yaya fa za ta iya dawowa."

"Ba kya tausayina? Allah I am sick. Amma dai kawo. Zan rama idan na warke."

Yana shanyewa ko magana bai yi mata ba ya miƙa mata wayarsa bayan ya buɗeta.

"Kira min Happiness. Kaina..."

Hankalinta a tashe ta kira.

*

Tun dare bayan gidan nasu ya watse, ƴan uwa duk sun tafi Kamal ya soma jin jikinsa yana neman dawowa. Ya sha magungunansa ya shige ɗaki ya rufe ƙofa. Rashin kuzarin dake tattare da ciwon gami da ciwon jiki da wahalar numfashi ya soma ji. Ya dinga juye juye akan gado har Allah Ya kawo masa bacci. Da gari ya waye ya ɗan ji sauƙi amma ba sosai ba. Ya lallaɓa ya tafi boutique ɗinsa ya shige office ya kwanta. Idan yana gida damunsa za ayi da tambayar ko lafiya. Nan kuwa yaransa ba za su neme shi ba sai ya zama dole indai ba da kansa ya fito ba.

Yana kwance cikin ciwon nan ne Hamdi ta kira shi. Ya sani sarai ciwon wasa ba zai sa Taj nemansa ba. Haka ya tashi ya lalubi muƙullin motarsa. Kafin ya kai ƙofa amai ya taso masa. A cikin office ɗin ya fara da ƙyar ya ƙarasa toilet. Tun yana yi a tsaye sai da ya yi zaman dirshan a ƙasa. Kusan minti sha biyar kafin yaji dama-dama ya tashi yasa tissue ya goge duk inda ya ɓata a office ɗin sannan ya fita. Wayar Taj ya kira domin yaji jikin tare da bashi haƙuri akan rashin fitowa da wuri.

"Ya naji muryarka a shaƙe? Allergy ɗin ne? Me ka ci?" Taj ya manta da ciwonsa ya tashi zaune da kyau.

"Ƙwarewa nayi. Baka ganni ba harda amai saboda tari."

Komawa Taj ya yi ya sake kwantar da kansa "ai kaƙi jin magana akan shan abu kana surutu."

"Ba za ka yi min sannu ba to?"

"Sannu ba don halinka ba."

Kowannensu ya yi maganar cikin dauriyar ciwo. Su ka yi sallama Kamal ya cigaba da tuƙi. Yana son faɗawa Taj lalurarsa amma mene ne amfanin sanya shi cikin damuwa?

Da nasa ciwon ya ƙarasa gidan Abba ya ɗauke shi. A soro ya yi sallama da Hamdi don ya ce turarenta hijab ɗin da ta ɗora ma bai hana shi mara lafiya ji ba.

"Allah Ya baka lafiya."

"Amin."

"Za ka kirani idan kun gama da asibitin?" Tayi magana tana kallon ƙasa.

"Dole na. Ko don na baki haƙuri."

"Haƙurin me?"

"Wanka da shirin tarbar maigidan da ki ka yi mana. Ni kuma nazo na haÉ—aki da jinya. Maimakon na yaba miki da kyau tunda babu kowa a gidan. Mtswww, Allah ban jidaÉ—i ba."

"Allah Ya shiryeka." Ta tura shi.

"Ya shiryemu dai Hamdi. Ni dake idanunmu iri É—aya ne."

"Wane iri?" Ta tambaya don bata gane ba.

"Zan miki bayani a gaba."

Motar Kamal ya shiga su ka tafi asibiti aka yi masa allura da bashi magani. Bai ga komai a tattare da Kamal ba domin ya daure sosai yana danne nasa ciwon saboda yadda yaga Taj.

***

Da wuri Yaya Kubra tayi clearing schedule É—inta ranar litinin. Ta tabbatar bata da sauran aiki na gaggawa a asibitinsu sannan ta fita domin ganawa da Dr. Mubina. Hankalinta a Æ´an kwanakin da su ka gabata sam ba a kwance yake ba. Tana dai daurewa ne kawai saboda kada kowa ya gane. Ta dai sakawa Kamal ido fiye da koyaushe. Duk wani motsinsa tana bi. Zuwanta biyu Happy Taj ma tana siyayyar dole duk don ta sami ganinsa. Bata son kiransa ta É—ora masa wahalar zuwa gidanta ko asibiti.

A reception ta bada katinta ta ce don Allah a miƙawa Dr. Mubina idan tana nan. Matar ta karɓa ta duba.

"Tun É—azu ta ce idan kin zo a nuna miki inda take. Bismillah."

Babu mamaki ko kaÉ—an a tare da Mubina da zuwan Yaya Kubra. Wannan yasa da ta shiga office É—in ta ce ,

"Allah Yasa ban ɓata miki lokaci ba. Naga kamar jirana kike."

"Na san yanayin aikin. Ina da niyyar jira har zuwa dare ko za ki zo." Ita ce amsar da bata sannan su ka gaisa.

Yaya Kubra ta É—ora ledar kwalin maganin akan tebur tana fuskantarta.

"Na sami saƙonki. Amma mene ne dalilinki na breaking doctor-patient confidentiality? Laifi ne babba kin sani."

Murmushi Mubina tayi "domin mu ceci Kamal kamar yadda ki ke tunani. Sannan ban karya doka ba. Magungunan ba a same su a nan ba shi ne nayi masa order daga India. Da su ka iso ni bana nan ina wajen conference a Ghana. Za ki iya duba date É—in. Na kira shi bana samu. Kuma ban san numbar kowa nasa ba, sai sunanki da na asibitinki. Shi yasa na tura."

"Kema kin san dai ba zan yarda da wannan zancen ba."

Mubina ta dage taƙi bari fuskarta ta nuna ta san bata kyauta ba. Dags ƙarshe dai ta ce,

"Tura miki kawai nayi. Ban san za ki buÉ—e ba."

Dariya Yaya Kubra tayi. Da alama babu yadda za ayi ta kama wannan matashiyar likitar da laifi.

"Ki yi min bayanin ciwon Kamal baki da baki ba abin da nake zargi daga magani ba."

"Ƙoda ce. Duka biyun. Idan ciwon ya sake tashi sai dai mu fara dialysis. Shekara guda kenan yana fama. Kusan duk wani magani da na sani mun gwada. Amma they are barely functioning." Mubina ta faɗi da rawar murya.
Chapter 56 · 0% Book details