← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 96

Sashe 94

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*
Tafiyarsu da kwana biyu shi ne lokacin tafiyar Yaya. A airport su ka haÉ—u da abokan tafiyarta. Su Hamdi su ka yi mata rakiya da mazajensu. Abin da ya bawa Taj mamaki da kuma tayar masa da hankali bai wuce ganin Dr. Mubina tana fitowa daga wajen check in ba. Ta rame sosai kamar wadda ta jima tana ciwo. Duk wasu alamun rashin kwanciyar hankali sun bayyana gareta. Da ta gan shi da farko gabanta ya faÉ—i kuma ya gani. Ta basar shi ma ya nuna bai gane komai ba. Hamdi ya kira su ka gaisa ya ce

"Ku fara ƙawance don da alama ita ce Mrs Happiness."

Hamdi sai murna ta zolayeta

"Umra za ki ko Ya Kamal za ki bi?"

Dr. Mubina tayi murmushi kawai. Taj ya nuna mata Yaya ya ce ga ƙarin abokan tafiya ta samu tunda yaga kamar ita kaɗai ce.

"Na gode kuwa."

Da aka kira su Hamdi da Taj na kallo Dr. Mubina ta haɗa akwatin ta da na Yaya tana ja. Sun ji daɗin hakan kuwa. A ƙofar jirgi inda ake nuna boarding pass Yaya za ta ɗauko nata ta haɗa da ƴar takardar da su Hamdi su ka gani wadda aka saka cikin passport ɗinta. Ita ce mai ɗauke da bayanin lalurarta da su blood group ko da wani abu na emergency zai sameta. Bata san ta yar ba tayi gaba. Mubina ce ta ɗauko mata. Tana shirin bata ta kula da bayanin da yake jiki. Zuciyarta sai da ta girgiza. Ta miƙa mata da rawar hannu.
RAYUWA DA GIƁI 36

Batul Mamman💖

***

A dalilin ba lokaci ɗaya aka saya musu ticket ba, wurin zaman Yaya da na abokan tafiyarta daban daban ne. Ɗan saurayin cikinsu Yaya tayi niyar bawa boarding pass ɗinta domin ya duba mata wurin zamanta, haka Abba Habibu ya sanar da ita tayi. Ya ceba inda mutum yake so zai je ya zauna ba. Ta ɗaga hannu za ta bashi Mubina ta riga karɓa. Ta kaita har wurin kujerar ta taimaka mata da ɗora hand luggage a sama sannan ta ɗaura mata belt. Ko ba a faɗa ba ta riga ta gane Yaya bata raɓa shiga jirgi ba.

Yaya tayi ta godiya da sanya mata albarka. Ita kuwa Allah Ya sani da biyu take yi. Kafin jirgi ya tashi bayan kowa ya zauna ta zo ta roƙi wadda take kusa da Yaya da cewa mamanta ce su ka yi musanyen seat. Wannan abu yasa Yaya jindaɗi matuƙa. Ta saki jiki da Mubina suna ta hira. Da jirgin zai tashi duk wani tsoronta Mubina ce ta dinga kwantar mata da hankali. Har aman da ta dinga ji Mubina leda ta bata sannan ta dinga shafa mata baya tana cewa ta hura iskar bakinta a ledar. A haka har su ka daidaita a iska.

"Allah Ya yi miki albarka Ya raya miki zuri'a. Ya jiƙan mahaifa."

"Amin Mama."

"Yaya yaran su ke kirana. Kema in babu damuwa ki dinga kirana da hakan."

Da murmushi Mubina ta ce "to Yaya."

Lokacin da aka kawo abinci Yaya bacci take yi. Mubina ta tasheta ta ci sannan da dabara ta sako zancen da ta zauna dominsa.

"Takardar nan ta passport É—in ki naga jininki O- ne ko?"

"Ban dai riƙe ba amma tun a gida yara ke cewa O. Wani abin ne?"

Da sauri Mubina ta girgiza kai tana mai son ɓoye zallar farincikinta sai dai Yaya ta fi ta wayo.

"Babu wata matsala. Jinin naki mai kyau ne domin babu wata lalurar da za a buƙaci wani abu na sassan jiki da ba za ki iya taimakawa ba."

"Ikon Allah. Ki ce idan na koma in nemi ƙarin sadaki a wajen Abban su Hamdi."

Dariya Mubina tayi kawai sannan ta kuma tambayarta Æ´aÆ´anta nawa.

"HuÉ—u ne."

"Kin taɓa yin ɓari?"

"Wai, sosai kuwa. Biyu nayi kafin babbar. A tsakaninsu kuma yaran na ƙara uku. Wani lokacin sai na sa rai da cikin sai ya zube."

Mubina bayani gamsashshe tayi wa Yaya game da rhesus da irin rawar da yake takawa idan aka sami saɓaninsa a tsakanin mata da miji wurin haihuwa.

"Ilimi kogi. Dole ake cewa tafiya mabuɗin ilimi. Kinga zaman abin da bai kai wuni ba amma na ƙaru." Da yake ita ɗin akwai zurfafa tunani sai ta tambayi Mubina me yaja hankalinta har take ganin farinciki a tattare da ita game da jinin.

Kunya ta kama Mubina.
"Allah ni likita ce. Yana ƙayatar da mu ganin masu abin da wasu su ke buƙata ido rufe." Tayi dariya "kada ki ce yau kin gamu da mayya."

Yaya ma dariya tayi. Sai dai kuma daga lokacin ta dinga karantar Mubina. Akwai abin da take ganin ta ɓoye mata. Kai gani ma take tana son faɗa mata amma kamar tana jin tsoro. A zuciyarta ta ce 'Allah Yasa alkhairi ne'.

***

Yau sun tashi jikin na Kamal kwata kwata babu daɗi. Anyi alluran, an saka ruwa amma duk da haka ciwo yaƙi sauka. Su Umma ke kuka Hajiya na rarrashinsu. Tun zuwansu ko sau ɗaya bata zubar da hawaye ba. Halin da ta riski Kamal a kullum gani take ba zai shiga wata sa'ar ba. Sai dare take zuwa asibitin. Kullum tana hanya daga Jeddah inda asibitin yake zuwa Makka ta wuni a Harami tana ibada. Ta zabge sosai kamar ba ita ba. Masu rarrashin nata kuma sun fita nuna rauni. Suna tausayin Kamal suna tausayinta.

"Yanzu Alhaji ace Kamal yana cikin wannan yanayi amma Taj bai sani ba? Anya kun yi musu adalci kuwa? Ka yiwa sauran Æ´an uwansa adalci? Yau ko addu'a su ke yi masa ai zai sami rangwamen ciwo." Cewar Mama tana zubar da hawaye.

"Kin fi kowa sanin cewa dukkaninsu sai sun taho. Ina gudun su zo a yanzu su haɗu wajen kashe masa ƙarfin gwiwarsa da koke kokensu."

"Ka yi haƙuri amma wannan magana fa ba hujja bace. Yaron da ya tashi a gidan gandu irin namu ace yana jinya da jama'ar da ko rabin gidan basu kai ba ai zai ji babu daɗi."

"Hajiyayye bata faÉ—a muku za su taho ba?"

"Ta faɗa. Kayi haƙuri. Na rasa me ya dace ayi ne." Ta cigaba da kukanta "ko sake auna jinin nasa za ayi a tabbatar? Ko kuma..."

"Mama ki yi haƙuri"

Kamal ne ya yi maganar yana mai runtse idanuwansa. Komai a jikinsa ciwo yake yi. Magana ma da ƙyar yake cijewa ya yi.

Muryarsa da su ka ji ce tasa su duka matsowa kusa da gadon nasa suna yi masa sannu. A lokacin Bishir ya shigo da waya a hannu yana kallon Alhaji.

"Ya Taj ne wai yake ta neman Ya Kamal. Ya tayar da hankalinsa wai tun jiya basu yi magana ba. Me zan ..."

"Kira min shi."

Inna ta hana "Kamal yanzu ba lokacin da za ka biye masa kuna hira bane."

"Bai sani ba Inna. Ki ka sani ma ko bamu da rabon sake ga.."

Umma bata bari ya gama magana ba ta ce "Ya isa. Kira masa shi Bishir."

Kiran yayi amma Kamal ba zai iya karɓa ba sai Bishir ne ya kara masa a kunne.

"In ka fara neman mutum kamar tsohuwar bazawara ta fito neman miji." Kamal ya faɗi yana murmushi da ƙyar.

Taj ya yi murmushi "Ba zan ji haushi ba balle buƙata ta taƙi biya."

"Me ka ke so?"

"Tambaya zan yi maka. Please ka matsa daga inda su Alhaji su ke."

"Na matsa. Mene ne?"

"Me Alhaji yake ɓoye mana ne Happiness? Tun tafiyarku hankalina ya kasa kwanciya. Amarcin ma na kasa sakin jiki nayi abuna yadda ya dace."

"In na yarda da kai in tafi a tsaye. Akwai damuwar da zata sa ka kasa amarci?" Yana maganar ne ido a rufe don baya son haÉ—a ido da iyayensa.

Ai kuwa hatta Alhaji sai da duka su ka yi dariya. Kamal ya nuna wa Taj lallai komai lafiya ƙalau. Ba yadda ya iya dole ya yarda.

"Mun haÉ—u da Mubina a airport da mu ka raka Yaya. Anya ibada ku ka je yi kuwa?"

Nan ma Kamal dariya yayi. Shi da Alhaji sun san da zuwanta. An kuma faÉ—awa su Hajiya. Ta ce duba shi za ta zo yi amma kowa ya san zuwan nata na sallama ne. Bakunan su ne dai ba za su iya faÉ—in abin da yake zuci ba. Sun cire hope.

"Happiness amana..."

"Me?" Kamal ya dawo daga tunani. Bai ji me Taj yace ba.

Taj ya sake maimaita cewa zai bashi amana. Ya sanar dashi lalurar da ta same shi da abin da su Salwa su ka yi. Shi ya so fara faÉ—awa amma ya gagara samunsa a waya. Hankalin Kamal ya tashi sosai.

"Ka yi min addua kafin na zo. Idan ban warke ba to ka shirya. Ni yara 12 za a haifa min kuma cin mu da sha duka wuyanka zai dawo."

"Har wasa kake yi da abu mai mahimmanci irin wannan?"

"Ina da kai Happiness mene ne zai dame ni? Amma nayi tunanin za ku j8 zancen a wajen su Alhaji fa. Sai naga da kai da su Bishir shiru. Ya Ahmad kuma kunyar nemansa nake yi."

"Da gaskiyarka. Amma na san ba zai riƙe ka a rai ba. Yana masallaci."

Suna gama wayar, Hamdi dake zaune kusa da shi tana shirya akwatin tafiyarta ya fuskanta.

"Kin san Allah, akwai abin da yake faruwa mai girma da su Alhaji. Yau kwana nawa a ce babu wanda ya faÉ—awa su Happiness abin da ya faru?"

"Maybe don kada su tashi hankalinsu tunda ibada su ka je" ta faÉ—a domin kwantar masa da hankali.

"Allah Ya kai mu gobe. Idan ma akwai wani abu zan gani."

"Me yasa ba za ka yi tunanin komai lafiya ba?" Hamdi ta sake faÉ—i.

"Saboda jikina yana bani cewa akwai problem. Kin tuna abin da ya faru daga ciwon kan da nayi a wurin dinner? Saboda damuwa gida Alhaji ya mayar dani. Sai yanzu da na faÉ—a musu hancina da harshe sun zama useless ne su ke nuna min rashin damuwar da nayi tsammanin gani."

Zungure shi Hamdi tayi tana murmushi "wannan dai rigima ce kawai da shagwaɓa. To taho in jajanta maka. Ni ai ba na kira komai naka useless ba."
Chapter 94 · 0% Book details