← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 96

Sashe 86

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duka su ka rufar masa. Yaya Kubra ta tashi zata koma mota don motar likita ba ta rabuwa da kayan bada kulawar gaggawa.

"Dawo ki zauna." Alhaji ya tashi ya dafa kafaÉ—ar Kamal "akwai Allah kaji ko." Ya dubi Abba "ka haÉ—a muku kaya kai da Kamal akwai jirgi gobe. Yanzu zan sa Ahmad ya sayi ticket ku tafi Saudiyya."

"Alhaji ni fa? Me zan yi?" Bishir ya tashi tsaye da zafin nama yana goge ƙwalla.

"Tare zamu bisu jibi da Ahmad. Bana son iyayenku su gane komai. Kawai zan ce musu Umra zamu ni da yarana maza."

"A nan za ku barni Alhaji?" Yaya Kubra ta soma sabon kuka.

"Kina da visa ne?" Da sauri da amsa cewa akwai "ki tattaro komai na asibitinsa a wajen Dr. Mubina jibin sai mu tafi. Ki san me za ki faɗawa iyayenki tunda kin ƙware a rufa-rufa." Kai ta sunkuyar.

"Me zan faÉ—awa Taj?" Kamal ya yi tambayar ga Alhaji.

"Zai yi zargin baka haƙura ba shi yasa baka haɗa da shi ba." Inji Bishir.

Alhaji wayarsa ya É—auko daga aljihun gaban rigarsa ya dubi lokaci. Yayi wuri ya kira mai sabon aure. Sai ya ce da Kamal,

"Ka faÉ—a masa zamu je Umra amma ba da shi ba. Yaje ya yiwa matarsa passport a nemi visa a sanar dani sai su tafi daga baya."

Da ya fita ya kulle musu ƙofar ɗakin sai ya sami damar barin zazzafar ƙwallar da ya danne a gaban ƴaƴansa saukowa. Sau ɗaya ya haɗa ido da Kamal yaga yayi masa murmushi na wanda ya karɓi ƙaddararsa hannu biyu.

"Ya Allah ban isa ba. Ba iyawata bace ta bani ƴaƴan nan. Allah nagodewa ni'imominKa gareni. Da rauni da gazawata na zo gareKa cikin ƙanƙantar da kai. Ka ceci rayuwar ɗana Ya Ubangijina." Bayan shekaru masu ɗimbin yawa ya sami kansa da fashewa da kuka mai ciwo da cin zuciya. Yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Waɗanda ya rasa a ɓari da biyu da su ka tafi da ƙananun shekaru har yau yana jin abin a ransa.

Tsayuwarsa ya yi a wajen yana neman nutsuwa amma idan ya tuna haƙuri irin na Kamal sai yaji zuciyarsa tana zafi. Duk gidan shi ne yafi kowa damunsa akan maganar Taj. A dalilinsa ya haƙura ya bar iyalinsa suna mu'amala da Taj ɗin. Domin da fari niyarsa ya yanke shi daga jikinsa gabaɗaya.

Ƙofar ɗakin Yaya Kubra ta zo da shirin fita taji sautin da mahaifinta yake dannewa. Bata san lokacin da ta koma da baya ta ɗora kukan ba. Abba da Bishir su ka kara kunnuwa su ka ji. Kowa ya koma ya zauna da kuka. Shi kuma ya koma ciki ya shige ɗaki ya rufe ƙofa.

"Magana ake ta Kamal yana da rai har yanzu. To me hwaru?" Kamal ya faÉ—i yana dariya.

"Ni ban taɓa tsanar wannan kalmar ba sai kamar yau." Abba ya sha kunu.

Yaya Kubra tayi murmushi "dole ka sako wasa kafin Taj yaji wannan maganar."

"Don Allah ki bar tayar min da hankali. Da me kike so in ji? Ciwon ko tararrabin abin da zai zo yayi?"

***

"Siyama kin tabbatar duk abin da Iyaa ta faÉ—a min gaskiya ne?"

Yadda Baba Maje ya É—auki zafi sai da gaban Siyama ya faÉ—i. Ta dai san cewa ba gulma ta kawo ba tunda cutar da mutum taji za ayi take son hanawa da ikon da Allah Ya bata.

"Da gaske ne Baba."

"Kirawo min Ummin"

Tashin muryar iyayen nata ne ya fito da ita daga ɗaki inda taji Baba Maje na rantsuwar sai ya karya Ummi. Iyaa kuma tana tare shi. Da ƙyar ta samu ya nutsu shi ne ta ce masa,

"Taurin kai gareta ka sani. Idan baka bi komai a hankali ba wallahi ko me zai faru ba faÉ—in gaskiya zata yi ba."

Bai daina faɗan ba sai dai ya haƙura da zancen zuwa ya tasheta da duka. Hankalin Siyama sai ya tashi shi ne ta fito yake tambayarta.

"Ita hayaniyar nan bata tasheta ba?" Ya faɗi yana girgiza ƙafa da kallon ƙofa.

"Yanzu zan taso maka ita. Amma don Allah ka bi komai a sannu."

Ɗakin nasu Iyaa ta shiga ta taso Ummi. Har ta fara kiran bacci bai isheta ba Iyaa ta daka mata tsawa. Haka ta biyota tana zumɓura baki. A zatonta aiki ne za a saka ta. Sai gata tayi ido huɗu da Baba da su ka sauko ƙasa.

"Ke Siyama hau sama ki É—auko min wayar Ummi."

Firgigit duk wani baccin iya shege da hammar ƙarya su ka gudu.

"Wayata Baba? Ke tsaya Siyama."

Siyama ta dakata. Baba ya zaro mata idanu ta kama bin bene ba shiri.

"Baba me nayi? Don Allah kada ka duba min waya." Ummi ta juya za ta hau benen.

"Ki ka kuskura ki ka hau benen nan sai nasa Baballe ya karyaki."

Cak ta tsaya "Baba me nayi?"

Bai kulata ba don bata cancanci hakan ba har Siyama ta sauko ta bashi wayar.

"ÆŠakinku É—aya. Ki faÉ—a min gaskiya, akwai wata ko babu?"

Mugun kallo Ummi ta watsawa Siyama. Ita kuma jikinta ya É—an yi sanyi.

Iyaa ta ce "Baki ji me aka ce miki bane?"

"Akwai"

"ÆŠauko min."

"Baba don Allah..." Ummi ta zube a ƙasa tana magiya. Abubuwan dake cikin wayar dake ɗakin sun fi ƙarfin me wayar. Dukkan wata mu'amalarta ta waje da fitintinunta suna ciki.

Ba jimawa Siyama ta sauko saboda a ƙasan filo Ummi ta ajiyeta da ta raba dare tana dannata jiya.

"Zan saurari Habibu don nayi imanin indai wani abu ya faru gidan ƴaƴansa ba zai ɓoye min ba. Idan abin da Siyama taji kina ƙullawa ya tabbata to ki kuka da kanki. Sannan in ki ka saka ƙafa a ƙofar gida to kada ki dawo na yafeki." Ya kalli Iyaa da Siyama "duk wanda ya bata aron waya ba da yawuna ba."

Wayoyin ya kashe a gabanta ya tashi ya shige nasa ɗakin. Ummi ta rasa gane kuka ya kamace ta ko me. Abin da yake taso mata yafi ƙarfin hawaye ko kalaman da take jin tana son zazzagawa Siyama.

***

Ahmad ya so ƙwarai ya kira baban Salwa akan ya turo a ɗauketa. Da wannan niyar ya shiga ɗakinta inda ya mayar da Mami bayan tafiyarsu Anti Zabba'u ya shiga da ya gama wayar. Ɗakin wari yake yi mai ɗauke numfashi. Ya yi mata kallo ɗaya ya juya. Nan ya barta tana so tayi kuka amma bakin ma ya karkace sai dai hawaye kawai. Kallon da yayi mata na takaici ne da baƙincikin halin da ta saka kanta kuma su ma ta jefa su.

Mami bata da kowa sai ƴan uwa waɗanda ta jima da barranta kanta daga garesu saboda abin duniya. Bata zuwa sabgar kowa sai dangin dangiro da abokan arziƙi masu kuɗi. Jininta dai ta datse zumunci da rashin mutumci saboda ita tana gidan mai kuɗi. Yau ga ranar ƴan uwa amma babu wanda zai nema ya taimaka masa da kula da ita. In ya ɗorawa Zahra wankin kashi da fitsarinta ba ƙaramin rashin adalci hakan zai zama ba. Yau da gobe sai Allah. Gashi Mamin a baya bata nuna mata ƙauna saboda akwai wadda ta so ya aura. Wannan tunanin yasa shi fasa neman Salwa ta tafi. Ita ce mace kuma dolen Mami. Zai saka mata ido kafin ya sami wadda zai dinga biya.

Shawarar da ya yanke ya faɗawa Zahra. Ta bashi goyon baya da alƙawarin za ta dinga taimakawa ita ma.

"Ni ban san me yasa ka damu da komawarta ba tun farko. In don Taj ne ina ganin yanzu ai ta haƙura."

"Ke dai ayi shiru kawai. Allah Yasa ta haƙura ɗin. Ni dai duk ranar da ta fita daga gidan nan idan bana nan ki kirani."

"In sha Allah"

Taɓe baki Salwa tayi. Zancen ba a bayan idonta ake yi ba. Tana kitchen kuma suma sun san tana jinsu. Ba za ta nuna ɓacin rai don an barta zaman jinyar Mami ba. Za ta kwantar da kai ta bi Ahmad sau da ƙafa domin zamanta a gidan shi ne babban hujjarta da rufin asiri a Kano. Kafin nan dai da lokacin aurenta da Taj dole tana buƙatar gidan zama. Idan yaso in tayi aure sai taga wanda Ahmad zai ɗorawa aikin Mami idan ba Zahran ba.

Wayar Ummi ta sake kira bata samu ba. Ta doka tsaki ta ajiye wayar ta cigaba da wanke wanke.

***

Tsaye tayi a ƙofar banɗakinta dake cikin ɗaki tana kallon sauyin da gadon ya samu. Taj ya canja bedsheet ya gyare gadon. Halin da take ciki na ciwo da zazzaɓi bai hanata yaba kyawun setin american bedsheet da duvet ɗin da ya shimfiɗa ba. Navy blue da red flowers ne a jiki wanda kalar farkon ta dace da ta labulen ɗakin nata. Ita kam me za ta ce da Inna? Duk wani abu da uwa za ta yiwa ƴa ita ma anyi mata na gata. Akan sayen zannuwan gadon Inna da kanta ta kira Yaya ta faɗa mata sun saya a wadace. Indai ba akwai wanda ta tanada ba tuntuni to kada ta sayawa Hamdin wasu. Bayan wannan wayar sai ta turo aka kawo guda shida. Duvets biyu, normal bedsheets huɗu ta ce a rabawa Sajida da Zee. Sajida ta dinga murna kuwa da taga sunan dake jikin ledar.

"Ni fa a instagram nake following É—inta (@nafs_beddings). Ashe zan ga kayanta zahiri."

"Kyau garesu ko me?" Cewar Zee da bata san murnar me take yi ba.

"Kyau ma ai faɗar ɓata baki ne. Ki je shafinta ki gani. Ina maganar quality ne. Ki taɓa ki san kin haɗu da kayan ƙwarai ba jabu ba. Yadin sam ba ya tashi ki ga yayi kurajen nan kamar pimples a fuskar budurwa."

Hamdi bata manta yadda su ka dinga dariya ba. Sai yanzu ta gane ashe dai da gaske ne maganar Sajida. Zama tayi tana shafa laushin duvet É—in tana jindaÉ—in mallakarsa. (Kamar kullum ni É—in ganau ce don har baby Ahmad na sayawa baby set a wajenta. Kayanta speak for themselves. Don Allah ku nemi Nafisa Tofa 08034581454 ku rabu da jabon zannuwan gado.)
Chapter 86 · 0% Book details