Sashe 61
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan baki je yanzu ba aka fara biki za ku kwana biyu baku haÉ—u ba."
DaÉ—i ya kama Hamdi. Tana ta murna ta kira shi. Sai ya ce ta shirya shi zai zo ya kaita.
Shi ne fa yau ya shirya yau cikin nishaɗi. Happy Taj ya fara zuwa. Akan idon Alh. Usaini ya wuce. Nan da nan ya kira Ummi ya ce aikinsu zai iya yiwuwa yau. Da alama Taj ya dawo aiki. Tunda suna ta kula da shige da ficensa tun bayan sun gama shirinsu. Sai dai bai ƙara zuwa ba sai yau ɗin.
Kai tsaye Salwa Ummi ta kira. Don dama Alh. Usaini bai yarda Salwan ta san shi ba. Ko ta kwaɓe sai dai su ƙare tsakaninsu da Ummi. Tana zuwa Ummin ta bata turarukan da Alh. Usaini ya bayar. Guda biyu ne masu wani irin ɗan karen ƙamshi. Ɗaya a yadda Ummin ta faɗa mata zai haddasa faɗa tsakanin Hamdi da Taj. Ɗayan kuma zai haɗa ƙaƙƙarfar soyayya tsakaninta da shi.
"Amma me yasa ki ke taimaka min Ummi?" Salwa ta tambayeta bayan ta karɓi turarukan.
"Saboda ba zan taɓa sanya ido Hamdi ta zauna a gidan miji alhali ni ta hana ni aure ba."
Da farinciki Salwa ta ce "Allah Ya bani ikon taimaka miki nima a duk lokacin da kike buƙata."
"Amin"
Bayanin yadda zata saka turaren Ummi tayi mata. Ta fito za ta tsallaka ta shiga Happy Taj sai taga motar Taj ɗin yana fitowa. Hankalinta ya tashi. Ummi ta ce kada ta damu. Su jira zuwa la'asar domin indai ya shigo ko ya fita da wahala a rufe wurin baya nan. Jin haka sai ta sami wuri ta zauna su ka cigaba da ƙulla yadda za ayi bikin Salwa da Taj bayan sun yi nasara.
***
Zee ce ta yiwa Hamdi light make up sannan ta shirya. Doguwar rigar atampa ta saka wadda take fitted daga sama. Sai kuma aka buɗeta daga ciki har ƙasa. Turarukanta na scentmania tabi ta shafe jikinta dasu.
"Don Allah Ya Hamdi a dinga ragawa Salman Khan."
"Wallahi zan miki rashin mutunci akan kiransa Salman Khan."
Zee ta dinga dariya. Suna gama ɗaurin ɗankwali ya kirata. Yaya tana son yi mata ɗan gargaɗin manya amma kuma ta rasa me ya dace ta ce. Miji da mata wane gargaɗi kuma za ayi musu wanda ba zai shiga hurumin shari'a ba? Ƙarshe dai sai cewa tayi,
"A kula da kai dai. Banda yin abin da bai dace ba."
Tunda ta fito ya kasa ɗauke ido daga kanta. Yana mamakin yadda ya mallaki wannan yarinyar da ya taɓa gani tana practicing speech. Ganin farko ta kanainaye masa zuciya. Ita ce first true love ɗinsa. Ya kuma yi sa'ar zama mijinta.
Daga ciki ya buɗe mata ƙofa. Sai da ta zo shiga ta fara jin faɗuwar gaba. Ta kasa gane ta murnar ganinsa ce ko ta tsoron fitinarsa, ko kuwa ta wani abin daban da bata sani ba?
Zama tayi ta rufe ƙofar sannan ta gaishe shi. Tana yi tana kawar da kai daga kallon fuskarsa. Ta san yanzu yana ganin kwalliyarta zai ce kama tsokanarta.
"Mrs Happy yau kuma ƴar ɓoye fuska ce? Irin yanayin nan da Indians..."
A gaggauce ta É—aga fuska su ka haÉ—a ido.
"Kada ka ƙarasa. Ka bar Indiyawa su sarara don Allah."
Lumshe ido ya yi ya buÉ—esu akan fuskarta.
"Na barsu. Yau ko su basu da kalaman da zan yabawa Hamdina." Yatsa É—aya ya É—aga a gaban fuskarsa "In ce awwnnn sau É—aya don Allah?"
Riga shi tayi harda fari da idanu "awwnnnnn"
Taj ya sanya hannayensa duka a saitin zuciyarsa "yarinyar nan za ki kashe ni. That was just too cute."
"Tunda kaga ba kai kaÉ—ai ka iya ba don Allah ka daina."
"Ban yi alƙawari ba. Atleast zan cigaba kafin na samu wani abin tsokanar taki."
Tuƙi ya fara a hankali suna tafiya Hamdi ta sake yi masa sannu da jiki.
"Ka rame da gaske fa."
"Sauron garin nan wasa ne? Jiya na kira mai kula da gidanmu na ce su duba duk wata ƙofa ko window a saka net." Don jin me za ta ce ya ƙara da cewa "ko mu je ki gani?"
"Allah Ya baka haƙuri. So kake Yaya ta ce a biyoni da kayana kada na dawo gida yau?"
"To ba shikenan ba. Kowa ya huta."
Cewa tayi bata yarda ba. Ya ce sai ya kaita. Dama ya kamata su gaisa da Amma. Tunda tana can da su Umma kafin su je wajen Yaya sai su haɗu. Hamdi ta rikice sosai don ya đauke hanya daga inda ta kwatanta masa gidan Sajida. Ya gama janta sannan ya ce Happy Taj za su fara zuwa.
Narke masa fuska tayi "so dai kake dole yau nayi laifi ko?"
"Ba zama zamuyi ba. I just realllyyy need to show you that peck."
Zazzaro masa idanu tayi "da ka bari ma kawai..."
Taj ya kama dariya "yau wata za ta yiwa Abba bayani. Ki ka ce min baki sani ba."
"Muna gama waya na duba a google." Ta bashi amsa da ƙaramar murya.
"Wannan fassarar google ce. Ni dai sai na nuna miki."
"Don..."
"Shhhhh. Ba a faɗa miki babu kyau roƙo ba?"
Wanda baya jin magiya biye masa kawai ake yi. Daina zancen tayi ta karkata zamanta ta zuba masa idanu yana tuƙi.
"Mene ne?"
"Jira nake muje ka nuna min peck É—in nan."
"Haaa, shi yasa nace kalarmu É—aya. Ni dake duk fitinannu ne. Allah dai Ya shiryemu."
Juyo da abin kanta ya yi ya dinga tsokanarta har su ka isa akan idon Salwa don ta riga Ummi ganin motar tasa. Nan gabanta ya cigaba da faɗuwa kada su haɗu da Abba. Taj ya buɗe mata wata ƙofa ta baya wadda directly office ɗinsa za ta kai mutum.
"Emergency exit ce for naughty people like us."
"Banda ni."
"Kin ganki fa." Ya janyota ya rungumeta a jikinsa gabaÉ—ayanta "ke da aka ce ki tafi gidan yayarki kin biyo miji office."
"Laifin wa don Allah?"
"Naki mana" ya soma magana a hankali. Ƙamshin jikinta ya tayar masa da kewar sati guda "I miss you so much."
Idanunta sun soma raina fata don akwaita da tsoro ta ce "ka zo mu tafi."
"Uhm uhmm" peck É—in da ta ce bata sani ba ya soma sauke mata a fuska.
"Happy" ta daure ta kira shi. Tsoro ne fal a zuciyarta. Na zuwa wajen da kuma na shi kan shi mijin nata.
"Mrs Happy"
Daidai lokacin su ka ji an ƙwanƙwasa ƙofar. Hamdi ta ƙwace daga hannunsa a firgice. Shikenan, idan Abba ne ta gama yawo a wurin Yaya ba shi ba.
Muryar wani yaronsa yake ji yana rantsuwar baya nan. Sai kuma ta mace da ya tabbatar Salwa ce tana cewa taga shigowarsa. A buÉ—e mata ta jira shi. To da yake yaron ya santa sai ya ce ta bari ya É—auko spare key.
Ita Hamdi ko maganganun bata ji da kyau. Ƙofar kawai da taji an riƙe yasa ta neman toilet.
"Stay with me please. Ba Abba bane."
Ta girgiza kai ta gudu. Idan ba Abba bane ai dai zai iya samun labari.
Tana shigewa Taj ya buɗe ƙofar. Salwa ya gani a tsaye yau ita ce da mayafi a kafaɗa ɗaya ɗan mitsitsi haka?
"Ya Taj" ta kira sunan shi tana murmushi.
Baya ya yi don ta samu ta shigo saboda kada ta faɗi abin da zai kunyata shi. Tana sanya ƙafarta a ciki ta rufe ƙofar.
"Salwa me ya kawo..."
Faɗo masa tayi a jiki kafin ya gama tambayarta. Hannunta hagu da dama kowanne da turaren da Ummi ta bata. Wuyansa ta riƙe da hannayen saboda ance lallai ta taɓa fatarsa da turaren ba kaya ba.
Ya sanya hannuwansa zai cire nata sai dai kuma duka hannuwan ta shafesu suma. Saboda haka yana taɓawa abin ya sake shigarsa.
"Sake ni Salwa" ya ce yana jin wani irin abu na shigarsa.
"My Taj..." ta sake yunƙurin rungumarsa.
Fincikota taji anyi ta baya don bata ji lokacin da aka buɗe ƙofar banɗakin ba. Ta juya za ta yi magana Hamdi ta tsinketa da mari.
"Ke! Ni za ki..."
Rai a matuƙar ɓace Hamdi ta sake marinta sannan ta saka hannu ta rabata da Taj.
"Fita."
"Nace ki fita ko na tara miki mutane. Banza kwartuwa."
"Ya Taj warn this girl." Salwa ta ce tana Æ´ar dariya "ko na kashe maka jiki ne?"
Shi fa jiri ne ma yake É—aukarsa. Amma idanun Hamdi sun rufe da ganin da tayi musu. Me zai sa ya bari Salwa ta rungume shi na tsayin lokaci har ta fito.
Ƙofar office ɗin Hamdi ta buɗe ta kamo hannun Salwa ta janyota. Inda ta sami ƙarfin hali da na jiki ma bata sani ba.
Ita kuwa dariya ma take yi ta ce "Baki ga komai ba Æ´ar É—an daudu. Sai na zo har gida." Ta yi murmushi ta fita.
Idanu a birkice Hamdi ta juyo ta kalli Taj. Kan da yake riƙewa ma a wajenta ba komai bane illa pretense.
"Abin da ka kawoni ka nuna min kenan?" Tayi magana tana hawaye masu zafi.
"Hamdi ba haka bane."
"Dama ku maza munafukai ne."
"Ni ne munafukin? Ni?" Zuciyarsa ta harzuƙo da wani irin ɓacin rai.
"To ko É—ayan zan kira ka? Wanda ya dace da mazan dake neman matan da ba nasu ba?" Ta faÉ—a kai tsaye.
Rufe bakinta ke da wuya kuwa ya É—aga hannu zai mareta.
"Bismillah. In baka mareni ba baka haifu cikin uwa da uba ba."
Tassss.
Shi da yayi marin da ita da ya mara su ka kama zubar da hawaye lokaci guda. Komai na jikinsu da zuƙata yana nuna musu illar kalamansu ga juna da abin da su ke yi. Amma kuma wani abu daga gefe yana ingiza su da jin haushin juna na ban mamaki.
RAYUWA DA GIÆI 25
Batul Mamman💖