← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 96

Sashe 6

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin faÉ—a ya ce mata gidansa babu maza da yawa. A cikin mata ashirin da uku a rasa me yin girki sai maza? Shi yasa yake sanya ido sosai saboda idan ya yi sake tabbas mazan za su iya jin cewa kwaikwayon yayyensu mata ba laifi bane. Ko É—ankwali ya gani a hannun É—ansa ya dinga faÉ—a kenan.

"Da irin wannan sakacin wani yaro a unguwarmu ana ji ana gani wallahi ya zama cikakken É—an daudu. Gidansu akwai mazan ma amma daga sai ga Habibu ya koma Simagade a unguwa."

Gashi dai faÉ—a yake yi amma faÉ—in wannan suna sai da ya sanya Hajiya da Mama yin Æ´ar dariya. Umma da Inna dai a murmushi su ka tsaya. Ai kuwa sun janyowa kawunansu sabon faÉ—a. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Musamman Mama da a yau tayi nadamar amsa sunan uwar maza a gidan.

"Dole ki yi dariya mana tunda ba ɗanki bane. Da alamu da gangan ma ki ka nemi ɓata min rayuwar yaro saboda baki san daɗin haihuwar namiji ba."

Ba ita da ya yiwa gori ba, dukkaninsu hankulansu tashi su ka yi. Mama ta saka kuka, Umma da Inna su na taya ta. Hajiya kuwa fiƙe idanu tayi ta ɗauki ragamar girmanta.

"A'a fa Alhaji. Akan ƴaƴanka ba za mu lamunci irin wannan ba. Kai ka koya mana zama da juna. Tunda mu ka kai yanzu kuwa wallahi ba za mu yarda ka haddasa mana rigimar da bamu yi da ƙuruciya ba."

"Ba akan ƴaƴana za ki ce ba. Ki fito fili ki faɗa min cewa akan Taj ba za ku yi min biyayya ba." Ya dubi Inna ya cigaba da sababi "wato sai da ki ka ga lamari ya lalace sannan ki ka ankarar dani riƙon sakainar kashin da ake yiwa ɗana don kawai ana ƙyashin kusanci na da shi."

"Na shiga uku. Alhaji yaushe mu ka yi haka?" Ta faÉ—i a É—imauce ganin Æ´an uwanta sun zuba mata ido.

Shi a ganinsa babu dalilin da zai sa taji wani ɗar a zuciyarta. Ya riga ya santa da kawaici saboda haka don ana yabon ɗanta a tunaninsa bai isa dalilin maganarsu ta ɗazu ba. Tabbas ganin rayuwarsa ta ɗauko hanyar gurɓacewa a hannun uwar riƙonsa shi yasa tayi magana.

Su Hajiya ficewa su ka yi aka rasa mai tambayarta abin da ya faru ma. Tana kuka ta tashi za ta bisu domin kwance wannan É—auri da maigidan ya yi mata ya hanata fita. Dama girkinta ne. Sai kawai ya ce idan ta fita daga É—akin ba da yawunsa ba.
RAYUWA DA GIƁI 4

Batul Mamman💖

***

Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa baƙo ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare ɗaya ana gab da samun gagarumar ɓaraka.

Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da ɗora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai ɗakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo ɗakin tare. Kai a ƙasa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya.

"Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu Æ´an uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake É—aukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba."

Umma ta kalleta babu wannan fara'ar ta kodayaushe
"To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?"

"Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran Æ´aÆ´an musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi."

"Maganar girkin fa?" Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai.

"Yadda ba ku É—auke shi laifi ba nima ban É—auka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?"

Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta.

"Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ƙara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daɗi. Saboda haka zance ya wuce."

Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga É—akin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya.

"Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan."

Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi.

Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ƙasar India inda yake haɗa degree ɗinsa a fannin Computer Science. Zaɓi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaɓa cikin ƙasashen da su ke cibiyar kasuwanci.

"Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya." Cewar Taj.

Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce "ni dai Dubai."

Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaɓinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta ɓangaren karatun da zai rabasu na ƴan shekaru.

"Anya kuwa Happy da Happiness za su iya rabuwa na shekara huɗu? Ku dai sake shawara ku zaɓi waje ɗaya."

Kamal ya kalli Taj da sanyin jiki. Ya ɗauka sun gama magana akan za su zaɓi Dubai. Burinsa ya koyo larabci banda karatun da za su yi. Sannan idan da faraga ya sami wani balaraben malamin ya danɗaƙi haddarsa da kyau ta ƙara zama. Kuma lafiya ƙalau Taj ɗin ya amince har da cewa shi ma zai yi. To me ya kawo wannan sauyi?

Alhaji bai ce musu komai ba amma ya fahimci akwai matsala tsakanin yaran. Sai bayan kwana biyu ya kira kowannensu gefe don jin me yake faruwa. A yadda ya fahimta zaɓinsu bai zo ɗaya ba. Kuma kowanne yana so ɗan uwansa ya bi ra'ayinsa. Kamal sai daɗa kwaɗaitawa Taj koyon larabci yake. Shi kuma duk da yana so amma haka kawai zuciyarsa tafi kwantawa da India. Sulhu ya yi musu da alƙawarin kowa zai sami inda yake so.

Harka ta kuɗi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci an gama yiwa kowa cuku-cukun samun gurbin karatu har ana shirin tafiya. Iyayensu mata su ka sha kuka kamar lokacin tafiyar Ahmad. Ƴan uwansu hatta na gidan miji don an fara aurarwa a gidan duka aka haɗu a filin jirgi wurin rakiya.

Alhaji da kansa zai kaisu makaranta. Dubai su ka fara zuwa saboda karatun Kamal saura kwanaki a fara. Ya biya komai ya tabbatar ya yi settling sannan su ka wuce India. Ahmad ya taho Mumbai ya tarbesu su ka rankaya Hyderabad tare. Gari daban za su zauna da Taj amma haka ya zauna da shi aka gama komai. Bayan sun raka Alhaji filin jirgi ya sake bin Taj har hostel É—in makarantarsu, Osmania University ya tabbatar babu matsala sannan ya wuce makaranta.

***

Washegari Taj ya fita ganin gari. Karatunsu sai nan da kwana goma masu zuwa. Yana cikin yawo ya ci karo da wani katafaren ginin gidan abinci na alfarma. Mutanen dake shige da fice a wajen ba za su ƙirgu ba. Murmushin takaici ya yi. Ina ma iyayensa sun bashi goyon baya. Da watarana idan Allah Ya albarkaci nemansa zai iya mallakar wuri irin wannan.

Baya tare da yunwa amma yana son ganin wurin. Musamman kitchen da masu girki. Wurin shiga ya lura layi ake bi. Gashi ginin hawa biyar ne amma ko ina ka kalla tunda zagaye yake da gilas kana hango cikowar mutane. Da kansa ya haƙura da shigar ya kama zagayen ƙayataccen ginin yana mai son ganin iya faɗinsa. Ƙamshin girki mai tada kwantacciyar yunwa gami da muryoyi da ƙarar kayan kitchen yaji yana cikin tafiya. Da sauri kuwa ya manna goshinsa da gilas ɗin wajen yana ganin yadda ake kai kawo a wani makeken kitchen cikin tsari duk a ƙoƙarin ciyar da kwastomomi. Zuciyarsa a take ta soma harbawa. Yaji saukar nishaɗi da farinciki a ransa. Bai san minti nawa ya kwasa yana bawa idonsa abinci ba sai da yaji an taɓa kafaɗarsa an yi magana da yaren punjabi, guda cikin yarukan ƙasar.

Da sauri ya juya yaga wani ɗan dattijo sanye da t-shirt da wando ya ɗaure ƙugunsa da apron mai tambari da sunan gidan abincin. Kansa wata irin hula ce kamar ta wanka amma ita mai laushi ce. Ana amfani da ita domin hana zubar gashi cikin abinci. A shekaru a ƙiyasin idonsa zai yi sa'an Alhajinsa.

Daburcewa Taj ya yi ya matsa baya a tsorace yana cewa "I'm sorry. Sorry. Sorry."

Hanyar komawa yake nema don tsoronsa É—aya kada mutumin ya haÉ—a shi da security a ce me ya kawo shi nan.

Murmushi mutumin ya yi ya ce "hungry?" Don dama ita ce tambayar da ya yi masa da farko.

"Come inside" ya umarce shi da yaga yana neman guduwa.

"Am sorry Sir. Please. I won't come again." Ya ce zuciyarsa na faman lugude a ƙirjinsa.

Ko sauraronsa mutumin bai yi ba ya riƙe hannun ƙofar da ya biyo ya fito zai koma. Buɗewarsa ke da wuya wani jibgegen mutumi ya tare ƙofar ya yi magana da yarensu yana kallonsa.

Dattijon sai ya amsa da turanci yana yiwa Taj kallon in kuma ka musa babu ruwana. Nunawa ya yi ciki za su shigo da shi sannan ba laifi ya yi masa ba.
Chapter 6 · 0% Book details