← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 96

Sashe 31

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya buɗe office ɗin ya shige ya rufe ƙofar don kada wani ma ya ganshi. Ya faɗa toilet yayi alwala. Rigar uniform ɗinsa ta chef dake fitar da ƙamshin kitchen ya ɗan tattaro ya kara a hancinsa. Guntun tsaki ya yi ya ɓalle maɓallan da su ka ƙawata ta daga wuya har ƙasa, daidai saman cinyarsa inda yake daura apron. Wurgi ya yi da ita kan cushion chair ɗin da ta bashi baya ya nufi closet inda yake da irinsu spare har goma sha ɗaya. Kowacce set ce farar riga da farin wando. Jerin round maɓallen ne kawai baƙaƙe. Wata rigar ya ɗauko, ya zare ta daga hanger ya mayar da wandonta.

Baccin Hamdi ya soma nauyi don ta fara mafarki mai daɗi taji wani abu ya faɗo a fuskarta. Ƙamshin turare mai ɗan karen daɗi ta fara shaƙa sai kuma taji na girki. A hankali ido har lokacin a rufe ta sake danna rigar a hancinta. Ta soma murmushi ita kaɗai sai kuma ƙwaƙwalwarta ta farka ta tuna a ina take. Bata san lokacin da ta ture rigar da sauri ta kuma ƙwalla salati da ƙarfi ba. A tsorace ta tashi ta kallo bayan kujerar.

Taj ma saitinta ya kalla da riga a hannu. Allah Ya so shi akwai vest a jikinsa wadda ya yi tuck-in da ita a cikin wandon.

"Abbanaaaaaa" Hamdi ta faɗi tana kai hannu ta ɗauki throw pillow ɗin kujerar ta jefa masa. Sakin rigar ya yi ya cafe pillon yana cigaba da ƙarasowa inda take. Kallo ɗaya ya yi mata ya ganeta. Mamakinsa dai me take yi a office ɗinsa kamar aljanna?

Da hannu ya dinga yi mata alamar tayi shiru amma taƙi.

"Shhhh, zan miki ihu nima."

Kama bakinta tayi ta ɓame. Sannan ta lura da bashi da riga. Ba shiri ta ɗauki wadda ya wurga kan kujerar ta cilla masa.

"Ya Salam!" Ya ce da sauri don ya ma manta yanayin da yake. Ya koma ya ɗauki wadda ya fiddo yanzu ya saka. Baya su ka juyawa juna daga inda su ke tsaye har ya gama ɓalle maɓallan.

"Uhmm" ya yi gyaran murya "how did you get here?"

Muryarsa kamar yadda ta tuna ta ba ta mata bace. Irin deep masculine voice É—innan wadda sautinta yake ratsa zuciyar mai saurare.

Gwanar a tsiwace ta amsa. Ba don zuciyarta ta so hakan ba. Sai don kawai tana son yakice shi daga ranta. Saninsa bashi da wani amfani. A dalilinsa yau wanda bai san Abbansu ba ma ya sani. Kuma ta tabbata haka za a tafi ana cewa É—an daudu ne.

"Wani Kamal ne ya kawoni da ina jin jiri."

"Subhanallah, kin ji sauƙi yanzu? Ko a je asibiti?" Taj ya ce da kulawa.

"Na warke."

"Alhamdulillah. Allah Ya ƙara sauƙi. Da alama kema ba kya son gatherings. Ni kaina da zan iya da zamana zan yi. Taron mutane indai ba costumers bane bana so."

"Allah Sarki. Amma ni ina son taro, ciwon kan na gajiya ne" Hamdi ta yi magana tana yamutsa fuska.

Taj yana lura da ita. Bai san dalilinta na yin hakan ba. Uzurin rashin lafiyar kawai ya yi mata.

"Bari nayi sallah na baki wuri."

"Hhhhh" ta buÉ—e baki tana kallon agogon office É—in. Biyar saura minti uku. Kamar za ta yi kuka ta ce "ban yi sallar ba nima."

Toilet ya nuna mata. Ta tsaya turus tana kunyar shiga banÉ—aki a gaban shi. Murmushi ya yi kawai ya fice. Ita kuma tayi alwala ta fito tayi sallah. A kullum idan sallah ta kama ta a waje tana yiwa Allah godiya da Yasa iyayensu tilasta musu shiga da mutumci. Idan ka gansu dole su burge ka. Ga kyau ga sanin darajar kai.

*

Magariba Taj ya so taro ya watse sai gashi kamar a lokacin ake tuttuɗu mutane. Shi da ma'aikatan sun gama kaiwa maƙurar gajiya. Tun suna dafawa a marmace har idan sun ga sabuwar oda sai su ji kamar su ce ba za su karɓa ba.

"Don Allah ku saka CLOSE sign a ƙofar restaurant ɗin." Cewar Taj yana fiddo wayarsa daga aljihun wando. Shugabannin bakery da masu nama ya kira ya ce idan sun gama da mutanen dake gabansu su fara shirin rufewa. Yana gama wayar Abba ya ce masa da ya sani bai ce a sallami mutane ba.

"Albarkar da muke nema ce ta samu kake neman ture ta?"

Taj ya sadda kai "ba manufata ba kenan Abba. Naga gobe za mu fara aiki officially. Idan bamu sami isasshen hutu ba zamu iya farawa a ga gazawarmu."

"Ko kusa. Dagewar yau ita za tasa ma'aikatanka su gane aiki ka ke so ba wasa ba. Maimakon a sallami mutane mu bari komai na yau ya ƙare. Babu yafi daɗi akan mun tashi."

Taj yaji daɗin shawarar Abba. Shi yasa ake cewa tafiya da gwani da akwai daɗi. Sannan iyawa kaɗai ba ta tafiya daidai sai an haɗa da experience. Tsarin wasu ƙasashen ya sani akan harkar restaurant. Abba kuwa ya jima cikinta a gida Nigeria kuma garin Kano.

Suna haka aka dinga kiran Abba amma yaƙi ɗauka. Aikin gabansa yake son kammalawa. Taj sai ya ƙarba. Haƙuri yaji ya bayar da alƙawarin an kusa tashi. Da ya gama ya dubi Taj yana murmushi.

"Hamdi ce uwar rigima. Wai in fito mu tafi tana jin bacci."

Taj sai yaji babu daÉ—i. Tara saura amma kamar yanzu aka fara aiki.
"Shi yasa nace a tashi. Dare na ƙara yi."

"Kada ka damu, muna fita za mu sami adaidaita sahu. Bana son su tafi su kaÉ—ai ne dai tunda duhu yayi. Nayi zaton zamu iya gamawa da anyi magariba."

"Bari na kira Kamal ko sun gama. Motarsa ai za ta ishe ku ko?"

Abba ya yi dariyar jin ana tambayarsa ko mota za ta ishe su "Adaidaita É—aya ma yana isar mu. Zee a sama, Halifa a kusa da direba. Mu uku a tsakiya."

"A sama kuma? Saman nan dai na bayan seat?"

"Eh mana."

Abin ɗaure masa kai ya yi ya ce "Ninke ta za ayi ko lanƙwasawa?"

Abba ya dinga dariya. Har su ka gama Taj na mamakin zancen zaman sama. Da su ka fito sai yaga har gara wurinsu. Boutique ɗin Kamal ya cika da samari da ƴan mata. Muƙullin motarsa ya karɓa ya ce masa zai kai su Abba gida.

"Za ka iya dawowa kuwa?"

"Me ka mayar dani ne? Zan dawo mana."

Kamal ya yi dariya "a dinga haÉ—awa da in sha Allahu dai."

Da ya fita shima Abba tambayar da ya fara yi masa ita ce ko zai gane hanyar dawowa. Ya nuna babu wata matsala sai su ka tafi. Abba na gaba, ƴaƴansa na baya. Hamdi tana ta faman kumbure kumbure don ita bata son ma a gaba ace suna cin arziƙi.

Waya Abba ya gama da Yaya ya sanar da ita suna hanya. Ya duba missed calls.

"Ashe kin yi ta kira bayan wadda na É—auka Hamdi? Ban ji ba ne."

"Ai Abba ƙiris ya rage ka fito kaga tana kuka. Ka san yadda bata son zuwa taro."

Saurin kallon madubi Taj ya yi kamar ta sani kuwa ita ma ta kalla. Maimakon taji kunyar ƙaryar da tayi masa sai ta juya idanu ta murguɗa baki.

"Kin yi kyau." Ya furta idanunsa har lokacin a kanta ta madubin.

"Wa?"

Abba ya faÉ—i yana kallonsa. Su Sajida ma duk sun zuba masa ido su na jiran amsa.

"Wata mota ce ta wuce yanzun nan. Ba don motata ta kusa isowa ba da ita zan saya."

A haka zancen ya mutu. Lokaci lokaci suna haÉ—a ido ta madubi tana harararsa. Sai bai damu ba. Zuciyarsa tana raya masa tabbas ya yi mata laifi ne. Laifin da yake ganin ba zai wuce na rashin nuna mata ya santa ba lokacin da su ka haÉ—u a Abuja.

Ya kai su gida lafiya amma komawa ta gagara. Ƙarshe sai Abba ya kira saboda rashin dacewar neman ƴan mata sha ɗaya da rabi na dare. Da kwatancem Abban ya fita daga unguwar. Yana tafiya a hanya yana nanata 'in sha Allah ba zan kuma ɓata ba.'

***

Satin farkon buɗe Happy Taj lokaci ne da Taj da Kamal ba za su taɓa mantawa dashi ba. Sun sami ciniki da yawaitar al'umma fiye da tunaninsu. Taj gani yake hakan ba ya rasa nasaba da addu'ar da Alhaji ya zo ya yi musu daren da za a buɗe wajen. Da kuma ta iyaye. Sai kuma saukar karatun da su ka yi shi da Kamal da sadaka domin neman Allah Ya sanya musu albarka. Kuma Ya tsaresu da wurin kansa daga zamewa al'umma fitina.

Duk da ya yi sanarwar gama ɗaukan ma'aikata to amma fa har lokacin mutane basu fasa kawo takardun neman aiki ba. Ya rufe ido ya ƙara ɗaukar masu shara da wanke toilets. Da kuma masu wanke-wanke da shara. Irin aikinka, irin uniform ɗin da za a ɗinka maka da suna idan an ɗauke ka. Bakery ne kawai ya bar space ɗin Hamdi. Da gaske yana son yin aiki tare da ita. Ya yabawa iyawarta sannan yana kusancinsu zai taimaka masa ya sami soyayyarta.

Baya son yin garajen fara nuna mata soyayya a yanayin da ake ciki. Bai san yadda Abba ma zai ɗauki maganar ba don ya kula yana da gudun rigima. Balle kuma Alhaji. Idan ya ƙyaleta haka kuma tabbas zai ji labarin wani ya yi masa shigar sauri. Da wannan shawarar ya tunkari gidan ranar wata lahadi, ana saura kwanaki huɗu kamun Sajida.

Cikin gidan ya fara shiga su ka gaisa da Yaya. Bayan sun ɗan taɓa hira ya tashi ya ce ta turo masa Sajida. Kuma sarai ya san Sajidan bata nan. Tun zuwansa aka ce tana wajen gyaran jiki. Zee kuma ta tafi karɓo ɗinki.

"Daddawar É—aka ce kawai a gidan."

Kamar bai san wa take nufi ba ya ce "gaskiya a ƙannena babu daddawa."

"Ashe baka san Hamdi ba. Kana kallo dai tun shigowarka ta shige É—aki. In ba kiranta nayi ba kuma da wuya ka sake ganinta har ka tafi."

Daga ɗakin Hamdi ta zumɓura baki da kwance zanin da Yaya take yi mata.

"Sai ki fito don na san kina jina." Yayan ta É—aga murya.
Chapter 31 · 0% Book details