← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 96

Sashe 87

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanciya tayi ta rufe jikinta. Bata ji motsin Taj ba. Ta dai yi tunanin ƙila yana nasa ɗakin. Gara ya yi zamansa a can. Bata son abin da zai sake janyowa su haɗa ido. Tashinta da yayi da asuba ma don babu yadda za ta yi ne. Zancen zuci ta cigaba da yi wanda gabaɗaya ya ƙare akan baƙuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki jiya. Taj ya nuna mata so da ƙauna kamar ya haɗiyeta. Wata zuciyar ta ce mata ya kuma saka ki kuka kamar zai ƙarar miki da hawaye ba.

Tunaninta na kaiwa daidai nan ya buɗe ƙofar da sallama ya shigo. Da sauri kuwa ta sake yin ƙasa da kanta ta rufe ko ina.

Taj murmushi ya yi ya je bakin gadon ya soma buɗe lulluɓin da tayi. Bata bari ya gama ba ta kama duvet ɗin da nata ƙarfin. Sai ya saki, ya hau gadon daga gefenta ya turata ciki ta hanyar matsawa yana rufa shima.

"Matsa min, matsa min" ya dinga faÉ—i har su ka koma tsakiyar gadon sannan ya daina turata.

"Me ya hana ki bacci? Ko jirana kike yi?" Ya yi maganar yana rungumota gabaɗaya a ɓangaren damansa.

Hamdi ga tsoro ga tsiwa, ta haÉ—a biyun ta ce, "In jira ka kayi min me?" Da rawar murya.

Taj ya yi dariya "Hamdiyya matar Malam Tajo. Maida wuƙar ni ba wani abu nake nufi ba."

"Waye kuma Tajo? ÆŠan uwanku ne?" Ta harare shi.

"Ni ne shi, shi ne ni." Ya nuna kansa.

Hamdi ta yamutsa fuska "A'a gaskiya."

"To ke ce shi, shi ne ke?"

"A'a fa." Ta ƙara da tura baki.

Abin ya burge shi ya kwanta a jikinta "To ya abin yake?"

Murmushi tayi na kunya "Ni ce kai, kai ne ni...shi kuma Tajo bamu san shi ba."

"Taj ɗin ma in kin ce baki san shi ba sai a siyo rago a saka min sabo." Ya faɗi maganar da wani shauƙi dake kwasarsa saboda shagwaɓar Hamdi "duk yadda kike so haka za a yi Mrs Happy."

Wani sabon shafin ya so a buÉ—e ta ce sam bata san zance ba indai ba sumar da ita zai kuma yi ba. Ya dinga yi mata dariya. Su na Æ´ar hirarsu har bacci ya sake kwashe su. Ba su su ka farka ba sai da aka kira Taj.

Ƙanwarsa ce wadda a jerin haihuwarsu bayan Kamal sai shi sai kuma ita Rawda. Abincin amarya da ango na sati guda ta ɗauki nauyi saboda gidanta yafi na kowa yin kusa da na Taj. Kullum safe, rana da dare take turo yaron gidanta ya kawo a babur. Amarya da ango su ka sake samun lokacin shaƙuwa da sabo da juna.

Taj ya bar Happy Taj a hannun yaransa. Sai Abba Habibu dake zuwa amma ba kullum ba. Taj yayi yayi ya ɗauki hutu amma yaƙi.

Wata irin soyayya Taj da Hamdi suke yiwa juna wadda bata da shamaki ko basaja. Sak su ka fitowa juna tun farko, shiyasa alaƙar tasu tayi saurin ƙulluwa. Jin junansu suke yi tamkar tare da soyayyar juna su ka tashi. Ga Taj gwanin zolaya wadda a sati gudan nan Hamdi ta koya. Duk baƙon da ya shigo gidan sai ya fita da murmushi saboda nishaɗin da zai samu daga masoyan.

Abu biyu ne su ka so damun Taj amma dalilai sun sa basu yi tasiri ba. Na farko tafiyar su Kamal Umra bagatatan ko haÉ—uwa basu yi ba. Yayi mita kuwa kamar ya ari baki. A ranar da su ka tafi wadda ta kasance kwana biyu da tarewar Hamdi, da yamma ya tafi gida bayan wayar sallamar da Kamal ya yi masa daga cikin jirgi.

Cikin farinciki su ka gaisa da su Umma kafin ya hau sama da aka yi masa iso wajen Alhaji. Gaishe shi ya duƙa yayi Alhaji ya miƙa masa hannu yana girgiza kai.

"Kai ka san ba haka nake gaisawa da Æ´aÆ´ana ba."

Da sauri Taj ya tashi ya ƙarasa gaban Alhaji ya miƙa masa hannu. Alhaji yayi murmushi sannan su ka zauna.

"Ina matar taka?"

Kai a ƙasa yana susar ƙeya Taj ya ce "tana gida. Ta ce na gaishe ku."

"Ina amsawa idan da gaske kake."

Rantsuwa Taj ya fara sai yaga Alhaji yana murmushi. Da alama dai yayi furucinsa da zolaya ne. Sannan babu shakka yana sane da abin da ya yiwa Abba Habibu ya ɓata ran Hamdi. Ba dai zai ɗauko zancen ba saboda ba shi ya kawo shi ba. Yana da mahimmancin da shi ma zuwa da zama na musamman ya dace da shi.

"Alhaji maganar Kamal ce ta kawo ni."

"Kayi aure Taj. Bai kamata ka zauna kana ƙunƙuni don ya tafi ba tare da kai ba. Ya dace ka fara sanin ragamar rayuwarka da ta ƴar mutane ce a wuyanka yanzu. Ba dole bane Kamal ya daidaita tafiya da kai ba."

"Ba haka nake nufi ba" cewar Taj

Tausayi ya bawa Alhaji yadda ya yi maganar. Shi kuma ya katse shi ne kawai saboda baya son hankalin Taj ɗin ya kai ga abin da ake ɓoye masa.

"To ina jinka."

Shiru Taj yayi. Alhaji ya sami kansa da yin murmushi. Yayi matuƙar kewar Taj da halayansa. Idan kayi masa faɗa alhali bai yi laifi ba, haka zai yi ta marairaicewa sai ka koma rarrashinsa ko babu niyya.

"Ashe baka canja hali ba har yau? Mijin aure fa kake."

"To ai ba maganar tafiyar nazo yi ba. Duk da dai naji haushi. Ko ba a je dani ba da sai a faɗa min. Ɗan Adam ba ya rasa buƙatu a wajen Allah."

"To ka roƙa mana a inda kake. Allah Yana ko'ina."

"Amma dai ba kamar idan ana shafa Ka'aba ana ambaton suna na da buƙatuna ba ko Alhaji."

Sake faÉ—aÉ—a murmushi Alhaji ya yi. Ya dubi Taj ya ce "welcome home."

Tsabar daÉ—in da Taj yaji bai san lokacin da koma kusa da Alhaji ya rungume shi ba. Alhaji ya gama basarwa amma a ransa daÉ—i yake ji.

Da ya nutsu ne ya faÉ—a masa ainihin abin da yake tunani. Yana magana Alhaji shiru kawai yayi. Daga dawowa gida, bayan kwana biyu da tarewar matarsa ya zai yi idan yaji ciwon da yake damun É—an uwa mafi soyuwa a gare shi?

"Baka yarda da ilimin Dr. Mubina É—in bane har kake tunanin wani ciwon ne yake damunsa?"

"Ba haka bane Alhaji. Ban sani ba ko idanuna ne amma har wani kumburi naga yayi rannan. Yanayin bai yi kama da ƙiba ba."

Shi da baya son ɓoye abu bai san dalilinsa na son bawa Taj ɗan lokacin samun farincikin aurensa ba kafin ƙwai ya fashe.

"Yanzu mece ce shawararka?"

"Idan kun tafi don Allah ka tilasta masa zuwa asibiti. Idan da kai ne dole zai je ayi masa thorough check up."

Alhaji ya yi murmushi don ya ɓoye halin da yake ciki.
"In sha Allahu zamu je."

"Nagode." Ya dinga faÉ—i har ya fita. A zuciyarsa yana mai fatan Allah Yasa babu komai.

To tafiyarsu Alhajin ne kuma sau biyu ya sake samun kansa a yanayi na ɗaukewar jin ƙamshi da ɗanɗano. A na biyun da ƙyar ya iya ɓoyewa Hamdi ya shiga ɗaki yayi ta bulbula turare kafin daga baya abin ya daidaita. Ranar da ya tasar masa na ukun kuwa ana gobe za su yi sati ne. Saboda tsabar tashin hankali, yadda yaga rana haka yaga dare. Cikin tsananin kiɗima ya zame jiki daga wajen Hamdi ya koma falo ya kira Kamal a waya.
RAYUWA DA GIƁI 33

Batul Mamman💖

This page is sponsored by spicesbyMrsghaleetk....yep, MRS GHALEE TK. Nace ba, wai kina cikin masu cewa girki da spices baya daɗi? Ko kuwa kin saba saya kina bari ya siƙe a kitchen saboda baki gane ɗanɗanon da yake bayarwa ba?

Albishirinki, Mrs Ghalee TK dai za ta yi Ramadan promo. Dama ce ta samu gareki wajen sayen ingantattun kayan girki masu tallafawa cefane musamman a wannan marra ta tsadar kayan abinci. Ke dai Æ´ar uwa, harma da É—an uwan da ya saba taimakawa iyayensa ko matarsa, ko kuma mai son burge iyali, ku yi tanadi don Mrs Ghalee TK ta zo da rangwame domin gyara tukwanenku. Ku sai ku garzaya ku nemeta akan wannan layin ta manhajar whatsapp ko kiran waya 08032834178.

Taku ce Batul Mamman, ganau akan kayayyakin da nake tallata muku.

***

A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya buɗe idanu ya miƙa hannu zai ɗauki wayarsa. A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman. Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi kaɗai ne a ɗakin. Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin. Tafiyar just ƙafa ke kawo su. Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an buƙaci duka baƙi da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya. Kwanaki goma aka bashi ya gama shan magani da allurai kafin a fara dialysis.

"Happy lafiya dai ko?" Ya ce cikin bacci da firgici domin kuwa ukun dare harda kwata lokacin.

Kamar an tsunkuli Taj ya É—aga kai ya kalli kyakkyawan agogon bangon falon. Baki ya buÉ—e gami da girgiza kai.

"Don Allah Happiness kayi haƙuri. Kasan Allah ban duba time ba. Ashe past one. A nan uku ta wuce ko?"

Kamal ya gyara zama ya ce "Eh...mene ne ya faru? Haka kawai ba za ka manta lokaci ba."

"Gobe sai muyi magana in sha Allah. Am very sorry." Taj ya ce har zuciyarsa.

"Taj" Kamal ya kira shi da ɗan ƙarfi "me ya faru?"

Roƙonsa Taj ya fara yi akan ya jira safiya don har ya katse kiran amma ya sake kiransa. Su ka ɗan yi ja'inja ɗinsu sannan Taj ya faɗa masa abin da yake faruwa dashi game da ɗaukewar ɗanɗano da jin ƙamshi ko wari wasu lokutan.

"Zuciyata tana bani Covid ce. Nayi browsing naga ɗaukewar sense of smell da taste suna cikin symptoms ɗinta. Ni bana mura amma bayan magrib ina ƙirgawa sau bakwai Hamdi tayi atishawa."

Kamal yayi Æ´ar dariya "sannu Doctor."

Taj ya ɓata rai "Happiness its not funny."

"Na sani. Shi yasa nake mamaki da kana zaune a gida ka yankewa kanka cutar dake damunka."
Chapter 87 · 0% Book details