Sashe 76
Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon nutsuwa Alhaji ya yi mata sai tayi saurin kawar da kanta gefe amma bai kasa gane tana cikin ɓacin rai ba. Bata so tayi kuka a gaban mutane. Cigaba da tsayuwarta a nan kuwa tana ganin yadda Abbanta yake takatsantsan hatta wajen yin motsi sai taji duk ta tsargu. Auren ya zo mata wuya har tana tunanin makomarsa. A haka ma bata da labarin alaƙarsu da juna kafin a haifeta. Ba a son ranta su ka shiga ciki har likita ya zo ya buƙaci ya shiga office ɗinsa.
Ko da Alhaji ya tayar dashi za su shiga wajen likitan can jerin kujerun baya inda ta zauna ya kalla yana sake nazartarta. A take kuma wata irin kunya ta saukar masa. Hamdiyya bata ce komai ba amma yanayin komai nata a yanzu yana yi masa nuni da cewa anyi mata abin da bata ji daÉ—i ba. Ba tare da tsawaita tunani ba ya san waye da wannan aikin.
'Lallai Habibu ya haihu' ya faɗa a ransa. Yayinda duniya take ƙyamar irinsu har ta kasa karɓar uzurinsu in sun tuba, ƴarsa ta ture girma da yawan arziƙin gidan aurenta tana mai nuna ba za ta lamuncewa taka darajarsa ba. Abin da bai taɓa zato bane yaji a ransa. Hamdiyya ƴar Habibu ta burge shi har wani sashe na zuciyarsa yana kamanta wannan hali nata da abin da yake tsammata daga jininsa.
RAYUWA DA GIÆI 29
Batul Mamman💖
***
Wata doguwar allura Mubina ta zare daga tsakiyar cikin Kamal ta ajiyeta akan kwanon tasa daidai girmanta. Ta koma gefe ta haɗa yatsunta na hagu da dama ta sarƙesu, sannan cikin dabara ta cire gloves ɗinta. Duk abin da take yi kwata-kwata taƙi yarda ta haɗa ido dashi. Umarni kawai take bawa Nos ɗin da ya taya ta aikin akan abin da zai yi. Shi kuwa yana ta kallonta har ta gama bai ce uffan ba. Canjawar yanayinta ya sanya zuciyarsa tsirgawa don ya san bashi da nasaba da kasancewarsa babu riga a wajen.
Baya ta bashi yana daga kwance ta harɗe hannuwanta a ƙirji.
"Sauƙin da za ka samu yanzu ba mai ɗorewa bane. Daga shi sai dialysis wanda shi ma tasirinsa ba ya wuce lokacin da za a sami ƙodar da za a dasa."
Numfashi kawai yaja da ƙarfi yana mai rufe idanuwansa. Zuciya da jikin nasa duka sun gaji. A ƙoƙarinsa na ganin bai ɗagawa kowa hankali ba yayi exhausting ɗin kansa. Duk wata lakar jikinsa mutuwa tayi sakamakon jin abin da tace. Tashi ma sai ya gagare shi. Ji yake kamar lokaci zai cimmasa yanzu yanzu. He badly needed a shoulder to cry on. A ɗan rarrashe shi a bashi baki. Sai yanzu yake nadamar ƙauron bakinsa. Sunan Happy yake kira a zuci domin shi ne zai iya bashi shawarar yadda za su fasa ƙwan a gida.
Shirun da ya yi ya sanya Mubina yin gyaran murya.
"Bari na baka wuri ka shirya."
Da sanyin jiki ya yi mata magana kafin ta fita.
"Kada ki tafi Mubina. Bana son zama ni É—aya don Allah. Not when you just told me I don't have much time left."
Tsayuwa tayi amma bata ce komai ba har ya mayar da rigarsa ya sanar da ita. Ta juya a hankali ta dube shi. Idanunsa sun kaɗa sun yi ja sosai. Sai wata ƙwalla da take barazanar wanke masa fuska. Koma mata ɗan yaro ya yi mai jiran rarrashin uwa. Komai nata da ya danganci juriya a take ya ƙwace. Jikinta ya kama rawa a yayinda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.
"Yaya za ka yi da haƙƙina da ka ɗauka Kamal?"
Idanunsa ko buÉ—ewa da kyau basa yi ya É—aga kai ya kalleta.
"Me nayi miki kuma?"
"Ka san baka da burin rayuwar duniya me yasa ka bari na kamu da son ka? Me yasa kake azabtar dani ta hanyar nuna min kanka a yanayin ciwo amma ka ƙi bani haɗin kan nema maka magani?"
"Ashe kina sona..." Kamal ya tattaro ƙarfin hali yayi murmushi gami da komawa ya kwanta "kinga har naji ƙarfi a jikina. Bari na huta sai na tafi."
Wani irin kallo Mubina tayi masa "ka san ƙarfe nawa kuwa? Ko ka manta za a sake allurar ƙarfe shida na asuba?"
"Kada ki damu zan dawo in sha Allahu."
Mamaki ya bata. Ta zata gaskiyar da ta faɗa masa mai ban tsoro za ta sa ya soma tunani da yin abin da ya dace. Rai a ɓace ta ce
"You are simply unbelievable! Me za ka je yi a gidan bayan dare ya raba? Kai da ka zo a sume ne kake zancen zuwa gida."
Ya za ayi ya manta? Dama dauriya ya dinga yi a wajen dinner É—in. Taj na fita da Hamdi ya kirata. Lokacin ta kusa gida ma tunda ita ma taje dinar. A asibiti su ka haÉ—u sai dai kafin ta iso ya suma a mota. Wurin parking ta dinga dubawa har ta gano motarsa tasa aka É—auko shi.
"Zan fa dawo da gaske. So nake in sanar da Alhaji lalurata. Ko ba haka kike so ba?"
"Kada ma ka faÉ—a mana. Ni ina ruwana? Na daina damuwa."
Kamal ya yi murmushi "to wallahi ki canja taku don soyayya babu nunawa juna damuwa bata da armashi. It won't even last."
Ƙwalla ta goge da ƙasan mayafinta ta harare shi "kai ɗin lasting zaka yi balle soyayyarka?"
"Ahhhh, abu na Allah...ki ka san ta inda sauƙi zai zo min? In warke muyi aure. Duk shekara na raka ki labour room ɗin can naku na sama."
Ba lokacin wasa bane amma sai da Happiness ya sanyata murmushi sannan su ka fito daga É—akin.
*
Alhaji bai yi mamaki ba da bincike ya nuna banda jinin Taj da ya hau babu wani abu da likitan ya iya gani da zai zama silar ciwon kai mai tsanani irin wanda yake fama dashi. Ya duba ido da kunne har ma haƙoransa domin ciwonsu kan jawo ciwon kai amma duk ƙalau suke. Kuma ya ce yana bacci.
"To ko stress É—in biki ne?" Likitan ya tambaya da damuwa.
Miƙewa tsaye Alhaji yayi "kada ka damu doctor. Kawai ka rubuta masa pain reliever mu tafi." Idan sihiri ne ba a asibiti za a gani ba.
Rubutawar ya yi su ka fito. Taj yana mai ƙara jin mamakin mahaifin nasa. Yadda yake abubuwa kai ka ce babu abin da ya taɓa faruwa a tsakaninsu.
Kowa tasowa yayi da ganinsu banda Hamdi. Da farko tana ganin ƙofar ta buɗe ta tashi da sauri. Tana haɗa ido da Alhaji sai ta koma ta zauna ta kama kallon gefe. Kama kanta tayi don kada ya faɗi abin da zai sake damunta.
Taj ɗin ma ƙin kallonsa tayi wanda Alhaji ya karanci yadda hakan ya dame shi. Da alama kasancewarsa a wajen ce kawai ta hana shi ƙarasawa gareta. Ita ma kuma dauriya ce da taimakon fushin da tayi tun a hanya ya hanata ko da satar kallonsa.
Murmushi Alhaji ya yi ba tare da ya sani ba. Wannan yarinya anyi rigimammiya. Wato ita nan maganarsa ce har yanzu ba ta haƙura ba. 'To ai shikenan. Na san maganinku daga ke har Taj ɗin.'
"Abba zo ka kaisu gida sai ka taho da motar Taj É—in."
Zumbur ta miƙe tayi gaba. Taj ya auna yaga idan ya bari ta fita fa akwai matsala a gaba. Kai ya ɗan sunkuyar yaƙi kallon Alhaji da Abba ya ce,
"Ina zuwa Alhaji."
"Ina za ka je?"
Hamdi da ta kusa ƙofa kuma taji maganganun da suke yi sai ta tsaya cak. Kuka kawai take son yi. Wato umarnin kada ya bita aka bashi yanzu kuma. Bata juya ba ta sake ɗaga ƙafa ita ma Alhajin ya tsayar da ita.
"Kema ina za ki je a daren nan kike ƙoƙarin fita ke kaɗai?"
"Tafiya za mu yi Alhaji. Dare ya raba sosai." Abba Habibu ne ya bashi amsa.
"Ai na san daren ya yi shi yasa nace Abba ya kai ku gida kai da wanda ya tuƙo motar."
Ba shiri Hamdi ta juyo. Taj ma dai Alhajin yake kallo.
"Ku kuma ku wuce mu tafi gida."
"Mu su wa?" Taj ya yi tambayar a gaggauce.
"Kai da matarka mana. Ko kana tunanin a daren nan zan bari ka tafi gidan Ahmad ka tashe su?" A zahiri kuwa baya son yaje ne ya sake haɗuwa da Salwa ta ƙulla wani abin. Bai ga abin da zai sa ya bar Taj ya kwana nesa da gida ba yau ɗinnan.
Furucinsa Halliru mai tuƙo mota ne kaɗai bai bawa mamaki ba tunda bai san komai ba. Fuskokinsu su duka abin dariya don dai ma Alhajin yana gudun raini a gaba da ya dara. Idanun Hamdi ƙara girma suka yi. Na Abbanta kuwa da Taj sun yi micimici kamar ya ce zai yanka wani.
Taj baya son saka rai a banza sai cewa ya yi "ban taho da muƙullan gidan ba."
"Naku gidan ba da gayyar mata ku ke shigarsa ba?" Alhaji ya ce yana tafiya har ya wuce Hamdi ya fita.
Bata iya tafiya ba sai da Taj ya ƙarasa inda take ya riƙo hannunta. Suna zuwa bakin ƙofa ta ƙwace hannun ta fito. Abba Habibu dai ya shiga duhu dole ya nemi ƙarin haske.
"Alhaji ina za su je ne?"
"Gidana." Ya amsa kai tsaye.
Hankalin Hamdi sai yanzu ya yi asalin tashi. Ta dubi Abbanta tana girgiza kai kamar zata cire shi.
"Bishir muƙullin motar yana wajenka ko?"
Nuna masa muƙullin ya yi shi kuma kai tsaye ya yi gaba ko jiran wani ya yi magana bai tsaya yi ba. Ya sakar musu bomb ya barsu da hayaƙi.
"Abba don Allah ba za ni ba" cewar Hamdi harda hawaye.
Taj kuwa kai ya girgiza masa cike da murna "Abba ku tafi sai da safe."
"A yi haka?"
"Abba kana ji fa Alhaji da kansa ya ce in zo gida na kwana ba roƙa nayi ba." Ya kalli Hamdi, kallo na girmamawa "albarkacinki naci. Wallahi albarkacin aurenki ne. Nagode Hamdi."
Shi ma Abba sai lokacin ya fahimta sosai. Ya riƙe hannuwan Taj su ka yiwa juna murmushi na farinciki.
"In sha Allah daga yau waccan magana sai dai a tarihi kuma. Allah Ya cigaba da toshe dukkan ɓaraka."