← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 96

Sashe 74

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga cikin kitchen ɗin aka ƙwala ihu duk wai na murna sannan wata ƴar tsumburburar budurwa ta fito da sassarfa cikin farinciki. Sanye take da matsatsen wando skin tight wanda daga gani a can ƙasan dilar gwanjo aka samo shi. Ta ɗora masa wata yarbatsulan riga mai rawa a jiki da wasu irin igiyoyi. Sai da ta tabbatar ta haɗa ido da Anti Zahra sannan ta buɗe hannuwa.

"Yaya Ahmet oyoyo."

Saurin shiga tsakaninsu Anti Zahra tayi don ta kula Ahmad bashi da niyar kaucewa.

"A gabana? Baki da hankali da alama." Cewar Anti Zahra cikin fushi "nayi miki kama da matan da za su É—auki wannan É—abi'ar ta wasan banza tsakanin cousins?"

Da wani salon shagwaɓa Habitti ta ce "Ya Ahmet kana jin matarka ko?"

Ko kallonta bai yi ba balle tasa ran yaji ƙorafinta. Hankalinsa ya tattara ya dubi matarsa.

"Me yasa ki ka shiga tsakaninmu Zahra? Da kin barta ta ƙarasa abin da tayi niyya."

Anti Zahra taji wani abu ya soki zuciyarta. Ita kuwa Anti Zabba'u har ta fara murmushin ƙeta sai taji ya cigaba da magana.

"...ni kuma sai na nuna mata idan tana taƙama ta sha nonon hauka to nima na tsotsa tunda duk tushenmu ɗaya."

Siɗe hannu Anti Zabba'u tayi da sauri ta miƙe tana taro zanin da ta kwance domin taji daɗin yin lodi.

"Ahmad ni ce mahaukaciya?"

"Kin ji na ambaci sunanki?!"
Yayi magana muryarsa a sama. Yau da yarinya ce tayi masa haka da wahala idan bai zane ta ba.

Ita da Æ´an matan duka jikinsa sanyi ya yi don ba haka su ka zata ba.
"Rashin kunya za ka yi min don na zo gidanka jinyar mahaifiyarka?"

"Jinya ki ka zo? Wa ya kira ki?" Ya buÉ—e mata wuta.

Anti Zahra sai da taji babu daɗi ta ɗan taɓa hannunsa "ƙanwar Mami ce fa. Ka sassauta harshenka a kanta."

"Kin fini saninta ne?" Ta girgiza kai da sauri don bata taɓa ganin fushinsa irin wannan ba. Anti Zabba'un ya sake kallo "cikin wađannan ƴaƴan naki babu wadda za ki je gidan aurenta ki yi wannan abin ba tare da mijinta ya yi muku kallon rashin nutsuwa ba. Kin kuma sani amma shi ne ni ki ka yi min saboda ga karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ko?"

Hankalinta sake tashi ya yi don yau tv ta sayar daga lokacin da Salwa ta kirata ta haÉ—a kuÉ—in aikin da aka yiwa Habitti.
"Saboda uwarka tana kwance shi ne za ka ci min mutumci?"

"Idan da ƙalau take ba ki isa ki shigo gidan nan ba wallahi. Yau nayi aure? Ƴaƴana biyu fa! amma ko sau ɗaya babu ke babu waɗannan abubuwan..." ya nuna matan da jikinsu ya gama laƙwas sama da ƙasa.

Babbar ce ma Hansatu ta ɗan taɓuka abin kirki ta tashi tsaye "idan ka cigaba da faɗawa mamanmu magana fa ba za mu yarda ba."

Da wutsiyar ido ya kalleta sai gata tayi tsit ita ma. Ya juya ga Salwa da ko tari bata yi ba tun shigowarsu. Babu shiri tayi ƙasa da kanta ta kama hanyar ɗaki za ta wuce sumsum.

"Idan kin wuce ciki wane mahaukacin ne zai yi min bayanin me yake faruwa da gidana? Ban soke batun zuwan nasu kafin na fita ba?"

"Yaya..."

"Ina raga miki ne kawai saboda ke mace ce, ba don haka ba da tuni na sauke miki abin da yake damun ƙwaƙwalwarki. Shashasha wadda bata san ciwon kanta ba."

Rasa da me za ta ji tayi. Da ɓacin ran Ahmad wanda bata saba gani ba, ko kuwa da ganin da Innar Taj tayi mata dumu-dumu a wajen dinner akan abin da take shirin yi? Haƙuri ta buɗe baki za ta bashi ya ɗaga hannu ya dakatar da ita.

"Ku haÉ—u ke da su ku kwana a É—akin da ki ke. Gobe da safe..." ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye akan centre table yana kallon su Anti Zabba'u "ku É—auki wannan ku yi kuÉ—in mota kuma a gyara min gida kafin a fita." Ita kuma Salwa ya ce "ke kuma zan kira babanki ya turo mai É—aukarki ki koma gida. Kuma wallahi kin ji na rantse idan ki ka fita daga gidan nan kafin lokacin tafiyarki sai na baki mamaki."

Yana gama magana ya shige ɗakin Salwan ya ɗauko Mami kamar jinjira don duk ta zuge. Kai tsaye ɗakin Zahra ya wuce da ita kowa yana ganin hawaye shaɓe shaɓe da su ka jiƙa fuskarta. Duk abin da aka yi tana ji. Tafi kowa sanin dole ƙanwarta ta zo da wata manufa. Takaicinta da ko magana bata iyawa sosai yanzu sai dalalar yawu. Da ko zama a gidan Zabba'u bata isa tayi ba. Sai kuma murnar Ahmad ya nunawa duniya ya haifu. Wannan sauƙin kan nasa da take ganin za a iya cutarsa yasa ƙafa ya ture. Ya nuna mata shi ɗin jinin Alh. Hayatu ne babu ƙarya.

Sai da ya kwantar da ita sannan ya ce da Anti Zahra ta ɗauko duk abin buƙatarta da na yaran su koma ɗakinsa.

"Idan tana buƙatar wani abu fa?"

"Zan dinga leƙawa."

Bai amince ta kwana ba don ya sani akwai cin zali ma idan yace sai ta kula da Mamin da ta É—ora mata karan tsana tun kafin aurensu.

*

Mummunar shaƙa Salwa taji a wuyanta. Gashi bata san ko wace ce ba domin ta bada baya tana shirin cire kaya.

"Sakar min wuya" ta ce da riƙon ya yi ƙarfi ta tabbatar ba na wasa bane.

"Mu za ki yiwa shigo-shigo ba zurfi ki sa a ci mana mutumci?"

Da mamakin muryar ta ce "Anti ni za ki shaƙewa wuya?"

"Haifarki nayi da ba zan shaƙe ki ba?"

Da zafin nama Salwa ta juyo ta doke hannun nata. Ganin ta buÉ—e baki tana shirin yi mata magana yasa ta ce "tunda baki haife ni ba nima ba zan kasa doke miki hannu ba."

"Wato na kula shiri ku ka yi da Ahmet ki ka taso mu don ku wulaƙanta mu." Cewar Habitti tana hura hanci.

Ba su san ran Salwa yafi nasu ɓaci ba saboda disappointments ɗin da ta kwasa. Shi yasa bata ji nauyin ramawa ba.

"KwaÉ—ayi dai ya kawo ku tunda uwarku na kira ba ku ba..."

Kiffff, taji saukar marin da yafi kama da gwaɓe baki don sai da laɓɓanta su ka amsa. A take kuma idanunta su ka kaɗa da ƙwallar azaba. A makance ta kai hannu domin ramawa akan Hansatu da tayi marin sai hannun ya sauka a kuncin Anti Zabba'u.

Ita kanta Salwa sai da gabanta ya faɗi da taga wa ta mara, sai dai kafin ta gama sanin me za ta yi ƴaƴan gwaggon tasu su ka yi mata rubdugu. Kowa na kai hannu aka lillisa mata jiki. Ihun ma da za ta yi don Ahmad yaji ya kawo mata ɗauki an toshe bakin. Sai da su ka tabbatar tayi laushi su ka barta da ta daina ƙoƙarin kare kanta. Abinka da waɗanda su ka saba da damben gidan haya.

Kukan da take fitarwa a hankali ga jini yana ta zuba daga hancinta ne ya sanya Anti Zabba'u cewa "Yanzu idan Ahmad ya ganta ya zamu yi?"

"Ba ma zai ganta ba. Kafin su tashi zamu kama gabanmu. Banda dare ai da babu abin da zai sa mu kwana" Habitti ta faÉ—i tana sake dungure mata kai.

***

Shiru motar ba ka jin komai sai hawa da saukar numfashin Hamdi dake baccin gajiya. Musu su ke da Taj yana tsokanarta da cewa yau shi ya haskata tana cewa ita ta haska shi. Can sai ji ya yi ta koma uhm da uhm-uhm idan yayi magana. Yana juyawa yaga É—aurinta ya karkace saboda yadda ta kwantar da kai a jikin kujera. Mamaki da haushin ta rusa masa plans É—insa su ka kama shi.

"Lallai ma yarinyar nan. Bacci ma kike yi a irin wannan lokacin?"

KafaÉ—arta ya girgiza a hankali ta É—an buÉ—e ido ta kuma rufewa.

"Ko ki tashi ko in wuce gidanmu dake" ya faÉ—i yana karantar fuskarta.

Ko gezau bata yi ba wanda yasa shi tunanin tabbas bacci take yi. Don da ido biyu take ba za ta yi shiru ba. Ƙwafa ya yi ya kaɗa kai.

"Allah Ya kaimu gobe nima sai na rama. Idan an kawo ki a kwance ina bacci za a ganni akan gadon amarya."

Nauyin baccin da ya rufeta bai hanata jin abin da ya ce ba. Murmushi tayi a ɓoye ta gyara kwanciyarta. Baccin kwanakin nan da bata samu ne ya yi mata kamun kazar kuku.

Taj cigaba ya yi da tuƙin yana yi yana kallonta. A baccin ma tayi masa kyau. Sai da ya kusa shiga unguwarsu ciwon kan da ya soma ji bayan Salwa ta taɓa shi ya dawo masa da ƙarfi. Abu kamar wasa sai gashi yana gumi. Da ƙyar ya iya ƙarasawa ya tsayar da motar amma bai kashe ba. Sai da ciwon ya lafa ya fita ya zagaya gefenta ya buɗe sannan ya ranƙwafa yana kallonta sosai.

Ƙamshin turarensa da numfashin da yake yi daf da ita ne yasa tsigar jikinta tashi tun kafin ta buɗe ido. Yunƙurawar da za ta yi yayi daidai da sake matsowar Taj. Kawunansu su ka haɗu da ƙarfi.

"Ya Salam" Taj ya dafa kansa da hannu É—aya, ya kuma É—ora É—ayan a goshinta inda yake tunanin ta nan su ka buge.

"Fasa min kai za ka...." Hamdi ta fara cewa sai ta kula idanunsa sun yi ja da taimakon fitilar waje ta gidansu.

"Kuka kake yi? Kan nawa da zafi ne?" Ta tambaye shi ganin yana runtse ido. Bata san fami ta yiwa ciwon kan nasa ba.

Yadda tayi tambayar sai da yasa shi yin murmushi.
"Abu kamar auduga ina zafi a nan?"

"Awwnnnn" ta ce tana yi masa murmushi da fari da idanu "wai irin abin nan ace tsabar soyayya ka buge ma baka ji zafi ba."

Taj kasa jira ta gama magana ya yi. Tunda ta rangwaɗa kai ta ce awwnnn ɗinnan ya daina gane komai. Ɗan yatsansa ya ɗora akan bakinta yana zana leɓen wanda ya sanyata shirun dole. Sannan ya zame hannun a hankali ya kawo kansa daidai fuskarta.

" I realy tried to be a gentleman tonight Mrs Happy amma kin hana."
Chapter 74 · 0% Book details