← Book details Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 96

Sashe 53

Rayuwa Da Giɓi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin dabara aka sa Firdaus ta tambayeta size ɗin da taƙi turawa Taj. Da ƙyar ita ma ɗin ta sanar da ita. Sannan cikin ƙanen Taj wata ta aunata gwajin riga da siket da na doguwar riga. Sai gashi kafin magrib ta soma sakewa dasu. Naƙasun da aka samu bai wuce na rashin shigowar Kamal ko Salwa ba. Sannan ko sau ɗaya Taj bai kirata ba. Ta shaƙa tayi fam tana jiran ya tsikareta ta fashe.

Ita ma Anti Zahra har fargabar zuwan Ahmad ɗaukarsu take yi. Ta san shi sarai. Laifinta zai fara gani kafin ya saukewa ƙanwar tasa kwandon masifa.

***

Ikon Allah Taj da Kamal su ka gani yayinda Salwa ta soma kuka tun a bakin gate wai Taj yana wulaƙanta ta. Aka yi ta rarrashinta taƙi shiru saboda makirci. A dole Kamal ya ce ta shiga motar. Shi ne su ka tafi Happy Taj. Office ɗin Kamal dake cikin boutique ɗinsa su ka shiga. Ta sami wuri ta zauna tana goge ƙwalla.

"Salwa tunda ku ke da Taj ya taɓa cewa yana son ki?"

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Taj yaji a duniya yanzu babu abin da ya tsana kamar mace ta dinga wasa da yatsunta. Tsaki ya ja ta dubi Kamal.

"Kana ganin abin da yake yi min? Meye laifina don na ce ina son shi? Ba fa cewa nayi ya saki yarinyar da ya aura ba."

"Ki dinga gyara kalamanki akan matata. Sannan kin fi kowa sanin cewa ba zan juyo ba. Ba yaudararki nayi ba so don't give me that crap wai in haÉ—aku."

"HaÉ—amu ma bai taso ba tunda Alhaji ya ce..."

"A wurin wa ki ka ji wannan maganar?" Ya tambayeta muryarsa a sama.

"A wurin Yaya mana." Ta bashi amsa tana tura baki.

Kallonsu Kamal ya yi don bai gane komai ba ya ce "wace magana ce Happy?"

A taƙaice Taj ya yi masa bayanin da bai yi ba saboda rashin lafiyarsa.

"Bana jin Yaya zai faÉ—a mata." Kamal ya faÉ—i yana kallonta "a ina ki ka ji?"

Rigimar da Mami ta ce ta haddasa tsakanin Taj da duk wanda zai goyi bayan yaƙi aurenta ta tuna. Ta kuwa taɓe baki cike da raini.

"Ina ruwanka? Kai dai burinka ba ya saki Hamdi ka aura ba?"

Duka su biyu zabura su ka yi cikin ɓacin rai.

"Salwa!" Kamal ya yi mata tsawar da a tunaninta ba zai taɓa iyawa ba saboda yafi Taj sanyin hali.
"Ki kiyayeni wallahi."

"Idan naƙi fa? Ya Kamal na fa san kana son yarinyar nan. Ko ba abin da ya kwantar da kai ba kenan? Me yasa baka taɓa yin wani ciwon allergy ba sai da Ya Taj ya aureta? Wallahi zan iya dafa izu sittin baka da wani allergy."

"Kinga Salwa, kalleni nan" Taj ya yi mata magana yana cijewa don ta riga ta kai shi matakin da yake son taɓa lafiyarta. Wani abu da bai taɓa yi ba ko da wasa.

Idanunta a bushe ta kalle shi. Bai san bata tunkari wannan rigimar ba sai da ta shirya mata daga gida.
"Ina jin ka"

"Zo ki tafi kafin wani cikinmu ya yi miki rauni."

"Please Taj kada ka biye mata. Ka bar zancen raunin nan kada wani ma yaji." Kamal ya yi maganar da kana gani za ka gane yadda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa.

"Za ka aureni Ya Taj. Allah kuwa..."

Kawai ta sa kai ta fita. Bayan tafiyarta Kamal ya zo zai yi masa rantsuwar zancenta ƙarya ne Taj ya dakatar dashi.

"Idan kana tunanin na yarda da zancenta har ina buƙatar ka wanke kanka to gaskiya akwai matsala tsakaninmu."

Murmushi Kamal ya yi "Allah Ya huci zuciyarka."

"Amma wane irin ciwo gareka Happiness?"

Koda Kamal ya juya ya kalli Taj sai yaga babu alamun wasa a tare dashi. Allah Ya taimake shi ya fara ajiye magungunan allergy su antihistamine saboda rana irin wannan. Durowar magungunan ya buÉ—e ya fiddosu duka.

"Ka ce baka yarda da zancenta ba."

"Daga cikin addu'ar da nake yawan yi mana harda kada Allah Ya haÉ—amu son abu guda da mutum biyu basa tarayya a kansa. Zancen ciwo kuwa ai rantsuwa tayi. Tunda tana sa gaba gabas zancenta zai iya zama gaskiya."

ÆŠaya bayan É—aya yabi magungunan ya dudduba. Pain relievers ne da wanda su ka danganci kwantar da abin da ya shafi allergy.

"Allah Ya baka lafiya Happiness."

"Amin."

***

Tafiyar minti biyar a mota za ta kai mutum wani babban mall da ya yi shura a titin kafin a gina Happy Taj. Ƴan Kano da son sabon abu na yayi kusan kowa ka taɓa zai ce maka ya yi siyayya a Glory Mall. Wurin shaƙe yake da kaya na alfarma. Sannan akwai snacks irinsu shawarma, small chops, popcorn, ice cream da sauransu. Har event centre garesu a ciki. Wurin mallakar wani hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ya damƙawa babban ɗansa alhakin kula da shi. Kuma a shekara biyu da rabin farko uban ya yi alfahari da ɗansa. Ciniki ake yi na bugawa a jarida.

Komai ya soma taɓarɓare musu cikin abin da bai fi sati guda da buɗe Happy Taj ba. Idan kaya ake so boutique ɗin Kamal yana da na kowanne jinsi manya da yara. Abin da ya shafi abinci kuwa harda wanda mutane basu sani ba akwai a ɓangaren Taj.

Kamar wasa su ka dinga tunanin ko irin abin nan ne na ɗokin sabon waje. Idan an kwana biyu abu zai koma normal. Sai aka yi rashin sa'a kasuwa da gaske take damawa da su Taj cikin albarkar Allah. Haka kawai mutane su ka fara janye jiki. Ciniki ya yi wani irin ja da baya mara daɗi. Alh. Usaini ya shiga gagarumar matsala da mahaifinsa. Inda rashin tawakkali yasa uban ya taso shi a gaba da muggan kalamai da tsoratarwa. Indai ciniki bai daidaita ba to ya kwana da sanin zai karɓe mall ɗinsa ne ya bawa wani daban cikin ƴaƴansa. Wannan abu ya yi matuƙar tayar masa da hankali. Ya shiga faɗi tashin hanyar dawo da martabar mall ɗinsu amma abu yaci tura. Har an kai wasu masu kai musu kaya sun fara janye jiki.

A irin wannan yanayin na neman hanya kowacce iri ce Allah Ya haɗa Alh. Usaini da Ummi. Cutar hassada tayi mata lulluɓi tun daga kai har tafin ƙafa a lokacin da taji labarin auren Hamdi da mamallakin Happy Taj. Ranar harda kuka sai da tayi. Zuciyarta a cunkushe tana fama da takaicin yadda ƴar ɗan daudu ta sami miji irin Taj. Ta taɓa zuwa wajen da wani saurayinta. Yadda taga Taj ta san wadda ta fita ma bata isa ta aure shi ba, balle kuma Hamdin da bata kama ƙafarta a gayu da rufin asiri ba.

Wani abin kayan haushin kuma jan kunne da gargaɗin iyayenta da yayanta akan ƙanwar Hamdi da ya aura. Ko kallon banza ta yiwa Zee ya yi alƙawarin canja mata kamanni.

Ranar da ta haɗu da Alh. Usaini, cikin jin zafin auren Hamdi ta fito ds niyyar zuwa Happy Taj ta ɓata ta a gaban Taj. Sai da ta iso kuma ta rasa me ya kawo mata tsoro ta kasa ƙarasawa. Haka kawai ƙafafunta su ka kaita Glory mall. Ta je wurin snacks ta sayi meatpie da lemo ta sami wuri tana ci. Amma hankalinta gabaɗaya yana kan ginin Happy Taj.

"Ki tafi can mana idan nan bai yi miki ba."

Kallonsa Ummi tayi za ta faɗi baƙar sai ta adana. Mutumin zai yi shekara arba'in da biyar. Ya sha shadda ƴar ubansu da ɗinki na alhazawan birni. Ga ƙamshi na waɗanda naira ta tsaga jikinsu ta zauna da kyau.

Murmushi tayi masa "ba kallon son zuwa nake ba. Fatan abin da zai zo ya tayar da wurin gabaÉ—aya koda gobara ce nake yi." Ta kashe masa ido.

"Ko zan san dalili?" Amsarta tasa ya sami interest akanta.

"Kaji daÉ—in kaini gaba? Allah Ya kiyaye." Ta tashi tsaye.

"Ko kusa. Nima burina kenan.." ya kashe mata ido yadda tayi masa.

"Dalili?"

"Sun kashe min kasuwar mall É—ina mana."

Zama ta koma tayi "nan wurinka ne?"

"Eh. Amma yana fuskantar barazanar rufewa saboda su."

Dariyar mugunta Ummi tayi a zuci. Daga ranar su ka ƙulla ita da Alh. Usaini. Suna neman hanyar da za su nakasa Taj domin su gurgunta masa sana'a.

A wannan rana ta asabar da Salwa ta fito daga Happy Taj cikin ɓacin rai, ta faɗa Glory Mall saboda akwai mai POS daga bakin gate ɗinsu. Tana jiran mutumin ya idar daga sallar la'sar a gefen ƴar container ɗinsa take waya da Mami. A ciki take zayyane mata duk fa abin da ta ce tayi ta gwada amma ƙarshe Taj yaci mutumcinta.

"Ni dai Mami da kin barni naje masa a yadda nake. Na tabbata idan ina kwantar da kai zai dube ni."

Zaginta Mamin tayi ta ce mata kuma ta kwantar da hankalinta. Ta sanar da mahaifinsu ya ce zai kira Alhajin su yi magana. Tana da yaƙinin yadda Alhaji yake ragawa Salwa don mutumcin babanta da yake gani nw. Duk taurin kansa ba zai ƙi tayin ƴa ba. Musamman tunda ba son wadda Taj ɗin ya aura yake yi ba.

"Kin nuna musu kin san baya son auren?"

"Eh, kuma ban faÉ—a musu cewa waya naji Yaya Ahmad yana yi da matan gidansu yana sanar dasu ba. Har wani cewa yake su yi wani abu kada a raba Taj da wadda yake so. Ni ko oho."

"Ki daina yin komai. Da kansu za su nemi ki idan babanki ya yi masa magana."

Wayarta duka a kunnuwan Ummi da Alh. Usaini waɗanda su ka yiwa juna wani irin kallo gami da murmushi. Tana gama wayar Ummi ta matsa kusa da ita su ka gaisa. Sai ta nuna kamar ita ma mai POS ɗin take jira. Abin ka da mata in an haɗu. Hira a taɓa nan a taɓa can sai gashi sun yi exchanging number.

Bayan Salwa ta ciri kuɗin ne ta fito Kamal ya kirata. Babu ja in ja ta faɗa masa inda take. Shi ne su ka ɗauketa don darajar Ahmad kawai. A hanya harda basu haƙuri wai ranta ne ya ɓaci. Babu wanda ya kulata a cikinsu har su ka isa gidan. Taj ya yi zamansa a mota.
Chapter 53 · 0% Book details